Kotu ta yanke wa dillalan ƙwayoyi hukuncin ɗaurin shekaru 95
Published: 8th, March 2025 GMT
Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas da ta Yola, da Jihar Adamawa, sun yanke wa wasu dillalan miyagun ƙwayoyi huɗu da aka kama da safarar ƙwayoyi da darajarsu ta kai Naira biliyan 4.6 hukuncin ɗaurin shekaru 95 s gidan yari.
Ɗaya daga cikinsu, Ogbuji Christian Ifeanyi, jami’an hukumar NDLEA sun kama shi a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas a bara, yana ƙoƙarin shigowa da hodar iblis ɗauri 817 mai nauyin kusan kilogram 20, wadda kuɗinta ya kai biliyan 46.
Sauran da aka kama sun haɗa da Iloduba Augustine Chinonye, Shuaibu Nuhu Isa (wanda aka fi sani da Don), da kuma Zidon Zurga.
Ko da yake, ba wannan ne karo na farko da aka kama Ogbuji ba.
A baya, an kama shi watanni 16 da suka gabata bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
Hukuncin Da Kotu Ta YankeBaya ga hukuncin ɗaurin shekaru 95 ko tarar Naira miliyan 25, kotu ta kuma umarci a ƙwace motocin da aka yi amfani da su wajen safarar ƙwayoyin.
A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya ce shugaban hukumar, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya yaba da hukuncin kotu da kuma ƙoƙarin jami’an NDLEA wajen kama masu safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gidan Yari ƙwayoyi Tara
এছাড়াও পড়ুন:
Mun yi asarar shanu 340 a hannun ɓarayi a Yuli — Miyetti Allah
Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Nijeriya reshen Jihar Benuwe, a ranar Alhamis, ta bayyana cewa aƙalla shanu 340 na mambobinta ne aka sace a cikin watan Yuli na 2025.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na jiha, Ibrahim Galma ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Makurdi.
Tinubu ya tsawaita wa’adin aikin shugaban hukumar Kwastam Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a JigawaA cewar sanarwar, lamarin ya faru ne a garin Agatu da wasu sassan Ƙaramar hukumar Guma da ke Jihar Benuwe.
Galma ya kuma yi zargin cewa, ɓarayin shanu da ke afkawa jama’a a Ƙaramar hukumar Agatu sun faɗaɗa hare-harensu zuwa sassan Jihar Kogi.
“A ranar 19 ga Yuli, 2025 wasu da ake zargin ’yan ƙabilar unguwar Eguma ne a ƙaramar hukumar Agatu sun sace shanu 73 na wani Sale Abubakar (makiyayi Fulani), kuma har ya zuwa yanzu ba a ƙwato shanun ba.
“A ranar 21/7/2025 wani gungun masu aikata laifuka daga unguwar Agatu sun yi awon gaba da shanu 80 na Ardo Sarkin Fulanin Bagana, an yi awon gaba da shanun ne a Jihar Kogi, kusa da kan iyaka da ƙaramar hukumar Agatu ta Jihar Benuwe.
Ɓarayin sun kwashe shanun zuwa ƙauyukan Agatu. Daga baya kuma, an ƙwato shanu 30 daga cikin 80 a Agatu, inda ba a iya gano 50 ba.
“A ranar 24 ga Yuli, 2025 wasu miyagu matasa ‘yan garin Agatu sun yi awon gaba da wasu shanu 213 na Garah Mobaba, hakan kuma ya faru ne a kan iyaka tsakanin Jihar Kogi da Ƙaramar hukumar Agatu ta Jihar Benuwe, haka kuma lamarin na faruwa a wasu sassan Ƙaramar hukumar Guma ta Jihar Benuwe, inda aka samu rahotannin sace-sacen shanu da kuma kashe-kashen makiyaya.”
Shanun mallakin Sale Abubakar (makiyayin Fulani), kuma har ya zuwa yanzu, ba a ƙwato shanun da aka sace ba.