An sako ɗaliban jami’ar da aka yi garkuwa da su a Binuwai
Published: 6th, March 2025 GMT
Daliban da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jami’ar Tarayya ta Joseph Sarwuan Tarka da ke Jihar Binuwai sun kubuta.
Daliban sun lubauta ne bayan shafe kwanaki takwas a hannun ’yan ta’addan.
.উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya tsawaita wa’adin shugaban hukumar Kwastam
Shugaba Bola Tinubu ya ƙara wa Bashir Adeniyi, Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, karin shekara ɗaya a kan wa’adin da ya kamata ya yi na shugabancin hukumar.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a KolmaniA cewarsa, wa’adin Mista Adeniyi zai ƙare ne a ranar 31 ga watan Agusta, 2025.
Amma yanzu Shugaba Tinubu ya amince da ƙara masa shekara ɗaya, wanda hakan ke nufin zai ci gaba da zama a kan kujerarsa har zuwa watan Agustan 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa ƙarin wa’adin zai ba shi damar kammala wasu muhimman ayyuka da yake yi.
Waɗannan ayyukan sun haɗa da gyara da inganta harkokin Kwastam, kammala wani shiri da zai sauƙaƙa kasuwanci a Najeriya, da kuma taimaka wa ƙasar wajen cika alƙawuran da ta ɗauka ƙarƙashin yarjejeniyar ciniki ta Afirka (AfCFTA).
Shugaba Tinubu, ya yaba da ƙwazon Mista Adeniyi da yadda yake gudanar da ayyukansa.
Ya ce ƙarin wannan wa’adin zai taimaka wajen inganta hanyoyin tara kuɗaɗen shiga a hukumar, da kuma tabbatar da tsaro a iyakokin Najeriya.