Matashi ya yi yunƙurin soka wa mahaifinsa makami a Kano
Published: 15th, April 2025 GMT
Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari kan laifin yunƙurin soka wa mahaifinsa makami a unguwar Fagge da ke Jihar Kano.
Kotun da ke zamanta a yankin Mai Alluna ta yanke wa matashin hukuncin ne bayan bayan alƙali ya kama shi da laifin yunƙurin soka wa mahaifinsa almakashi saboda ya hana shi kuɗin kashewa.
’Yan sanda sun gurfanar da matashin ne a kan laifin ɗura ashariya da barazanar kisa da kuma ɗaukar makami ba bisa ka’ida ba.
Bayan karanta masa takardar tuhumar, matashin ya amsa laifin, inda Alƙali Nasir Ahmad ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara biyu da tarar Naira dubu 20, da kuma karin ɗaurin wata shida tare da bulala 40.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan Boko Haram sun kashe mutum 12 a Borno
Mayakan Boko Haram sun halaka mutum goma sha biyu da jikkata karin biyu bayan wani hari da suka kai kan kauyen Bokko Ghide a Karamar Hukumar Goza ta Jihar Borno.
Wakilinmu ya ruwaito cewa cikin wadanda aka kashe akwai ’yan sa-kai biyu da wasu mutum 10 da suka fita debo itacen girki.
Sulhu da ’yan bindigar Katsina: Gaba aka ci ko baya? Abubuwan da suka faru yayin jana’izar Fafaroma FrancisSarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mayakan sun yi wa ’yan sa-kan kwanton bauna a kan hanyar Kirawa da ke gudunmar Pulka.
“Sun fita neman itace ne a jeji a ranar Asabar, yayin da yaran [mayakan Boko Haram] suka yi musu kwanton bauna, inda suka kashe mutum 10 sannan wasu suka ji munanan raunuka.
“Mun binne mutum 10 sannan biyu da suka jikkata an mika su asibiti.
“Abin takaici shi ne biyu daga cikin yan sa-kai sun sadaukar da rayuwarsu wajen kare mutanenmu wadanda aka kashe ranar Juma’a.”
Bayanai sun ce harin ya auku ne yayin da ake kokarin ganin an mayar da jama’ar yankin garuruwansu don su ci gaba da rayuwa, bayan kwashe shekaru da dama suna gudun hijira a wasu wurare saboda hare-haren na ’yan Boko Haram.