Manchester United Ta Kammala Ɗaukar Cunha Daga Wolves Akan Miliyan 62.5
Published: 2nd, June 2025 GMT
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta sanar da ɗaukar ɗan wasan gaban ƙasar Brazil Matheus Cunha daga Wolverhampton Wanderes akan kuɗi fam miliyan 62.5, Cunha zai zama ɗan wasa na farko da Ruben Amorim zai saya a wannan bazarar yayin da yake ƙoƙarin sake gina ƙungiyar da ta ƙare a mataki na 15 a gasar Firimiya, Manchester United za ta kammala yarjejeniyar ɗaukar Cunha da zarar an buɗe kasuwar saye da sayarwar yan ƙwallo a ƙasar Ingila.
Ɗan wasan mai shekaru 26 ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar a United tare da zaɓin ƙarin shekara, Cunha ya bar Wolves a matsayin ɗan wasa mafi tsada da ta taɓa sayarwa a tarihinta bayan da yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan ta kai ta fam miliyan 62.5, inda ta amince da tsarin biyan sama da shekaru biyu.
Duk da sha’awar da wasu ƙungiyoyin suka nuna akan Cunha, amma ya nuna sha’awar komawa Old Trafford da taka leda, yana mai imanin cewa United na ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyi a duniya kuma duk da rashin samun gurbi a gasar Zakarun Turai da tayi bayan rashin nasarar da suka yi a hannun Tottenham a wasan ƙarshe na gasar Europa.
Arsenal da Aston Villa na daga cikin waɗanda suka tattauna kan sayen ɗan wasan na Brazil a bana, ƙungiyoyin Saudi Pro League suma sun yi niyyar fitar da batun ɗaukar shi, ɗan wasan ya ƙulla yarjejeniya da Wolves daga Atletico Madrid a shekara ta 2022 kan kuɗi kusan fam miliyan 34 inda ya jefa ƙwallaye 15 sannan ya taimaka aka jefa shida a wasanni 33 da ya buga a gasar Firimiyar shekarar 2024/25.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Radda Da Makarrabansa Na Samun Kulawa A Asibiti Bayan Hatsarin Mota A Hanyar Daura
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, tare da wasu mutane goma sha biyu na samun kulawa a asibiti bayan tsira daga wani hadarin mota da ya faru a kan hanyar Katsina zuwa Daura, a Jihar Katsina.
Hatsarin ya faru ne sakamakon taho-mu-gama da wata motar haya kirar Volkswagen a kusa da Tashar Motoci ta KTSTA da ke Daura.
Duk da cewa hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ba ta fitar da sanarwar hukumance dangane da lamarin ba, shaidu da hotunan da aka dauka daga wurin sun tabbatar da cewa motocin biyu sun lalace matuka.
Shaidun gani da ido sun shaida wa Radio Nigeria cewa motar gwamnan ba ta cikin sahun motocin rakiyar gwamnati a lokacin da hadarin ya faru.
Daya daga cikin wadanda suka taimaka wajen daukar wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Tarayya na Daura, ya shaida wa Radiyon Najeriya cewa dukkan fasinjoji tara da ke cikin motar hayar sun samu raunuka.
“Mun kai su Asibitin Gwamnati na Daura inda ake kula da su yanzu,” in ji shi.
A halin yanzu, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Katsina, Alhaji Bala Salisu Zango, ya ziyarci fasinjojin motar hayar da suka jikkata a Asibitin Gwamnati na Daura, inda ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin dukkan kudin maganinsu.
Bakwai daga cikinsu sun samu raunuka kadan ne kawai, yayin da biyu kuma suka sami karaya.
“Gwamnatin Jihar Katsina za ta biya dukkan kudin maganinsu kuma za ta ci gaba da kula da lafiyarsu har sai sun warke.” in ji Zango.
Ya kara da cewa gwamnan ma yana cikin koshin lafiya, kuma tuni aka sallame shi daga Asibitin Tarayya na Daura.
“Na yi magana da shi ta waya ba da dadewa ba, yana cikin koshin lafiya. An kwantar da shi tare da sauran wadanda suka jikkata a Asibitin Tarayya na Daura, kuma an sallame shi bayan an tabbatar da cewa lafiyarsa ta daidaita.”
Haka kuma, wata sanarwa da Sakataren Watsa Labarai na Gwamna Radda, Malam Kaula Mohammed ya sanya wa hannu ta tabbatar da cewa gwamnan yana cikin koshin lafiya.
A wani faifan bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta, gwamnan ya bayyana cewa shi da sauran wadanda hatsarin ya rutsa da su suna cigaba da samun kulawa.
Daga Isma’il Adamu.