Hukumar kula da shirye-shiryen fansho na wucin gadi, wato PTAD, ta nemi afuwar ’yan fansho a fadin Najeriya kan jinkirin biyan wasu daga cikin kudaden fansho da suka taru.

A wata tattaunawa ta waya da Shugaban Kungiyar Tsofaffin Ma’aikatan NIPOST na reshen Jihar Legas, Kwamared Mukaila Ogunbote, jami’an PTAD sun bayyana cewa jinkirin ya samo asali ne daga wasu matsaloli da suka shafi Babban Bankin Najeriya da kuma Ma’aikatar Kudi.

Sai dai hukumar ta tabbatar da cewa dukkan hakkokin da suka rage, ciki har da na wadanda aka sake rijista bayan tantancewar “Ina Raye”, za a biya su a cikin wannan watan.

Kwamared Ogunbote ya ce an tattauna batutuwa da dama da suka shafi walwalar ’yan fansho, kuma ya sha alwashin ci gaba da bibiyar lamarin har sai an warware matsalolin da ke tattare da shi.

Ya kuma roki hadin kai, fahimta da juriya daga tsofaffin ma’aikatan, domin a cimma mafita cikin ruwan sanyi, musamman ganin cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da sakin naira biliyan sittin da takwas domin biyan bashin.

 

Suleiman Kaura

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

HOTUNA: Yadda aka dawo da ’yan Najeriya 203 daga Libya

Kalli yadda aka karɓi ’yan Najeriya guda 203 da aka dawo da su daga ƙasar Libya.

(Hoto: Onyekachukwu Obi).

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka ta sake laftawa wasu kamfaninin mai na Iran takunkumi
  • Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu
  • DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho
  • HOTUNA: Yadda aka dawo da ’yan Najeriya 203 daga Libya
  • NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya
  • Babu Wata Tattaunawa Tsakanin Sin Da Amurka Game Da Batun Haraji
  • Ma’aikata 240 na karɓar albashi biyu, wasu 217 na amfani da lambar BVN ɗaya a Kano
  • Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 115
  • Kissoshin Rayuwa: Imam Al-Hassan 114