Tuƙin Ganganci: Direba Ya Kashe Jami’in KAROTA
Published: 25th, April 2025 GMT
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp.কীওয়ার্ড: KAROTA
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Binuwai
Dakarun Sojin Operation Whirl Stroke (OPWS), sun kashe wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, yayin wani samame da suka kai a Ƙaramar Hukumar Ukum, a Jihar Binuwai.
Mai magana da yawun OPWS, Laftanar Ahmad Zubairu, ya ce sojojin sun samu bayanan sirri kuma suka yi aiki tare da ’yan sandan Zaki-Biam.
Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda Dan sanda ya yi batan dabo a bakin aikinsa a KatsinaMaharan sun kafa shinge a kan hanyar Aturuku–Wembe–Ayati, inda suke tare matafiya suna ƙwace musu kayayyaki.
Da sojoji suka isa wajen, maharan sai suka fara harbe-harbe, wanda hakan ya sa sojojin suka buɗe musu wuta.
Hakan ya yi sanadin mutuwar uku daga cikinsu, sauran kuma suka tsere cikin daji.
Dakarun sun ƙwato babura guda biyu, yayin da suka ci gaba da farautar waɗanda suka tsere.
Bincike ya nuna cewa mutanen da suka mutu suna cikin wata ƙungiya da ta daɗe tana yi wa al’umma barazana ta hanyar garkuwa da mutane da kai hare-hare, musamman kusa da kasuwar doyar Zaki-Biam.
Mutanen gari sun tabbatar da sunan waɗanda dakarun suka kashe.
Kwamandan OPWS, Manjo-Janar Moses Gara, ya yaba wa sojojin bisa ƙwazo da jarumtarsu, tare da alƙawarin ci gaba da kare al’umma da tabbatar da zaman lafiya.