A cewar Ministan, samun wannan ƙwarewar ya zama wajibi a wannan zamani da kowa da kowa – wato daga masana hulɗa da jama’a zuwa shugabannin kamfanoni – yake taka rawa a matsayin mai magana da yawun wani.

 

Idris ya ce: “Yau a wannan zamani da kowa ke zama mai magana da yawu – ko ɗan hulɗa da jama’a ne ko shugaban kamfani a ɓangaren gwamnati da masu zaman kan su – wajabcin samun ilimi kan kafofin watsa labarai ya zama abu mai matuƙar muhimmanci, domin yana ba da damar fahimta, nazari da tantance sahihancin saƙonnin da ke yawo a kafafen watsa labarai, wanda hakan zai ba da damar yanke sahihin hukunci da mu’amala da labarai yadda ya kamata.

 

“A ‘yan kwanakin nan, saboda rashin wannan ilimi – wato rashin iya nazarin abin da ke cikin kafafen labarai da tantance sahihancin sa – jami’an gwamnati da ma al’umma gaba ɗaya sun fara faɗawa tarkon labaran ƙarya da yaɗa bayanan da ba su da tushe.”

 

Ya ce samun wannan ilimi zai ba da dama ga masu magana da yawun hukumomi su inganta dabarun su wajen tantance sahihancin labarai, gano son zuciya ko ɓangaranci a cikin su, da kuma amfani da hanyoyin bincike da tantance gaskiya.

 

Domin cimma wannan buri, Ministan ya bayyana cewa ma’aikatar sa ta kusa kammala shiri domin buɗe Cibiyar Ilimin Kafofin Watsa Labarai ta UNESCO – wacce za ta kasance ta farko a duniya – a Buɗaɗɗiyar Jami’ar Ƙasa ta Nijeriya (NOUN) da ke Abuja.

 

Ya ce: “Na dawo daga Paris, a ƙasar Faransa, kwanan nan inda na gana da manyan jami’an UNESCO, kuma buɗe wannan cibiyar ya kasance babban maudu’i a tattaunawar.”

 

Ministan ya kuma bayyana cewa ma’aikatar sa ta samu gagarumar nasara a bara, inda aka samar da sabon matsayi na “public relations” a cikin tsarin aikin Gwamnatin Tarayya.

 

“Abin da wannan ke nufi shi ne, ‘Public Relations’ yanzu yana da nasa hanyar aikin kai-tsaye a cikin aikin gwamnati tun daga watan Disamba 2023.

 

“Haka nan, tsohuwar muƙamin ‘Information Officer’ yanzu an sake masa suna zuwa ‘Information and Public Relations Officer’, da kuma ‘Executive Officer (Information and Public Relations)’.

 

“Ina kuma so in ƙara da cewa NIPR ce ta taka rawar gani wajen ganin wannan cigaba ya samu.”

 

Idris ya kuma jaddada cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da goyon bayan ‘yancin faɗar albarkacin baki da kuma ƙarfafa kafafen watsa labarai masu zaman kansu.

 

Ya ce: “A ɓangaren mu, za mu ci gaba da faɗaɗa hanyoyin sadarwa a ƙasar nan da kuma bunƙasa damar zuba jari da tattalin arziki da ke cikin ta.”

 

Har ila yau, Ministan ya yaba wa shugaban NIPR, Dakta Ike Neliaku, saboda ƙara sabon ɓangare mai muhimmanci a wannan taro, wato ‘Information Ministerial Clinic’, inda tsofaffin ministocin yaɗa labarai suka raba gogewar da suka samu da abubuwan da suka fuskanta yayin gudanar da aikin su.

 

Tsofaffin ministocin da suka halarci buɗaɗɗen taron sun haɗa da Farfesa Jerry Gana, Cif John Nwodo, Mista Frank Nweke (Jnr), Mista Labaran Maku, da Alhaji Lai Mohammed.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Katsina Ta Amince Da Bayar Da Alawus Na Naira 30,000 Duk Wata Ga Malaman Karkara

Suleiman-Jibia ya ƙara sanar da cewa, majalisar ta amince da kafa Cibiyoyin Horar da Malamai a Katsina, Daura, da Funtua.

 

“Cibiyoyin za su taimaka wajen haɓaka tsarin koyarwar malaman domin samar da ingantaccen ilimi ga ɗalibai a faɗin jihar,” in ji shi

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Anambra Chris Ngige A Abuja December 11, 2025 Manyan Labarai Rikicin PDP Ne Ya Sanya Ni Komawa Jam’iyyar Accord – Adeleke December 11, 2025 Manyan Labarai Za Mu Yi Hisabi Da Buhari A Gaban Allah — Sheikh El-Zakzaky December 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iyaye Sun Yi Fitowar Farin Dango Don Yi Wa “Yayansu Allurar Rigakafi a Sule-Tankarkar
  • Tinubu Ya Yaba Wa Jami’an Tsaro Kan Ceto Dalibai 100 Da Aka Sace A Neja
  • NLC Ta Shirya Zanga-Zangar Rashin Tsaro A Faɗin Ƙasa Ranar 17 Ga Disamba
  • Ƴan Bindigar Daji: Jihohin Arewa 7 Sun Kaddamar Da Rundunar Fatattakar Su
  • ‘Yan Siyasa Ne Ke Zagon Ƙasa Ga Ci Gaban Nijeriya — Sarki Sanusi II
  • Mahajjata 2,235 Ne Suka Yi Rijistar Aikin Hajjin 2026 A Sokoto
  • Katsina Ta Amince Da Bayar Da Alawus Na Naira 30,000 Duk Wata Ga Malaman Karkara
  • NAFDAC Ta Ƙona Kayayyaki Marasa Inganci Na Naira Biliyan 5 A Nasarawa
  • NAJERIYA A YAU: Alfanu Da Kalubalen Sabon Jadawalin Karatun Makarantu Da Gwamnati Ta Bijiro Dashi
  • Ganawa A Tsakanin Mataimakan Ministocin Waje Na Kasashen Saudiyya, China Da Minista Arakci Na Iran