Hukumar OCHA Ta Bayyana Cewa Yahudawan Sahyoniyya Sun Ninninka Ayyukan Korar Falasdinawa A Yamma Da Kogin Jordan
Published: 14th, April 2025 GMT
Hukumar kula da agaji ta MDD (OCHA) ta bada sanarwan cewa, gwamnatin HKI a yankin yamma da kogin Jordan ta kori Falasdinawa a gidaje 5 a yankin bayan sun rusa gidajensu. Hukumar ta kara da cewa wadanda HKI ta rusa gidajensu a yankin sun hada da yara 19 da da iyayensu 33 maza da mata 6.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto OCHA na cewa tun watan Maris da ya gabata zuwa yanzu, HKI ta rusa gidaje da gine-ginen Fafalsadinawa kimani 100 a yankin yamma da kogin Jordan wadanda suka hada da gabacin birnin Qudus da kuma sauran yankuna, da sunan an gina gidajen ba bisa ka’ida ba.
Banda haka suna kwace gonakin Falasdinawa don ginawa sabin yahudawan da suke shigowa kasar matsugunai.
Labarin y ace, a wasu lokutan yahudawan zasu tilastawa Falasdinawa rusa gidajensu da kansu ko kuma idan sun rusa su da kayan aikinsu su tilastawa Falasdinawan kbiyan kudaden aikin rusawan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye dokar ta-baci a Jihar Rivers daga ƙarfe 12 na daren 17 ga watan Satumban 2025.
Shugaban Ƙasar, a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce dokar ta-bacin da ta dakatar da Gwamna, Mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida ta cimma manufarta na dawo da zaman lafiya a jihar.
Tinubu ya bayyana cewa ya yi amfani da Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ne a watan Maris na 2025 sakamakon durƙushewar mulki a Jihar Rivers.
A cewarsa, rashin jituwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Majalisar Dokokin Jihar, da kuma lalata muhimman kadarorin gwamnati sun jefa jihar cikin rikici.
“Lamarin ya kai ga Babbar Kotun Ƙoli ta bayyana a ɗaya daga cikin hukuncinta cewa babu gwamnati a Jihar Rivers.” In ji Shugaban Ƙasa.
Ya gode wa Majalisar Ƙasa bisa amincewa da wannan sanarwa, tare da yabawa Sarakuna da jama’ar jihar bisa haɗin kan da suka bayar.
Tinubu ya kuma yaba wa masu adawa da suka kalubalanci wannan mataki a kotu, yana cewa wannan shi ma wani ɓangare ne na dimokuraɗiyya.
Da yake magana kan sabuwar fahimta tsakanin manyan ‘yan siyasa a jihar, Shugaban Ƙasa ya ce babu dalilin ƙara tsawaita dokar ta-bacin.
Ya bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara, da Mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da Shugaban Majalisar Dokoki Martins Amaewhule da dukkan mambobin majalisar jihar za su koma bakin aiki daga 18 ga Satumban 2025.
Tinubu ya yi kira ga shugabannin siyasa a faɗin Najeriya da su ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai domin isar da fa’idodin dimokuraɗiyya ga al’umma.
Daga Bello Wakili