Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 103
Published: 5th, April 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suak zo cikin al-kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na m,aulana Jalaluddin Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.
///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan lamami na biyu daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (s) diyar manzon All..(s).
A cikin shirimmu da ya gabata mun ji yadda Khalifa na biyu, a lokacinda ya zo mtuwa ya kafa shura na mutane 6 wadanda yace dukkaninsu manzon All…(s) ya yardadasu kafin ya bar duniya sannan ya bukaci su zabi daya daga cikinsu a matsayin khalifa a bayansa. Mun bayyana cewa ya sanya Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) daya daga cikinsu amma ya tabbatar da cewa ba zasu taba zabensa a matsayin Khalifa ba, saboda dalilain da ya kawo, na shugabantar da Abdurrahman dan Auf, wanda ya kasance surukin Uthman Dan Affan, sannan Sa’adu dan Abiwakkasa ba zai sabawa dan amminsa Abdurrahman dan Auf ba, Sannan dama Aliyu (a) baya shiri da Talha dan ubaidullah wanda ya nuna cewa a yawa Uthman zai fishi idan an raba biyu ma Abdurrahman dan Auf baya tare da shi.
Sannan munji yadda Khalifan ya aibatasu gaba daya, daga cikin har’da Amurul muminina (a) inda ya zargeshi da wargi da wasa, amma ya tabbatar da cewa idan da zasu bashi ita da ya kaisu kan hanya madaidaiciya, da kuma ya kaisu kan gaskiya.
Kafin haka yace da Salim maula Abu khuzaifa yana nan da ya nada shi Khalifa, sannan da Abu Ubaida dan jarrah yana nan da ya nadasu a matsayin Khalifa kai tsaye.
Idan muka koma baya zamu ga yadda wadannan mutane biyu suke tare da su a ranar wafatin manzon All…(s) da kuma rawan da suka taka wajen tabbatar da cewa Khalifanci ta fita daga hannun Amirul mumimina (s) ta kuma koma hannun Khalifa na farko.
Amma a cikin shirimmu na yau zamu ga yadda aka gudanar da Zaben khalifa a tsakanin mutane 6 wadanda Khalifa na biyu ya bada umurnin su zabi guda daga cikinsu.
Da farkon dangane da cancantar Amirul muminina da Khalifanci, Khalifa Umar bai fi manzon All..(s) sanin haka ba, don a aikace ya nada shi a Ghadir, sannan a lokacinda ya nada shi yace ‘wanda na kasance shugabansa to Aliyu wannan shugabansa ne” yace Ubangiji ka jibanci wanda ya jibance shi ka kuma tabar da wanda ya tabar da shi, ka kuma risker da gaskiya a gareshi a duk inda ya juya. A wani hadisi, ya ce: Da zasu dora Aliyu da zasu sameshi shiryeyye mai shiryatarwa.
Malamai da dama sun bayyana ra’ayinsu dangane da shuraa ta Umar, kuma sun wadannan al-amura, daga ciki.
01-Ya shirya shura ne kawai don kauda Aliyu (a) daga Khalifanci, saboda ya sanya mafi rinjayen mambobin shoran makiyan Aliyu dan Abitalib (a) wadanda suka hada banu Umayya da Banu Taim. Wato dangin Khalifa na farko. Talha dan ammin Abubakar ne, banu taim, wanda yake adawa da Aliyu dan Abitalib (a). Saboda husuma da yayi da dan amminsa bayan wafatin manzon All..(s) dangane da Khalifanci. Da Uthman da Abdurrahman dan Auf, dangin Banu umayya ne wadanda suke ganin Aliyu ya kashe shuwagabannin su a manya-manyan yake-yaken da aka yi a farkon musulunci. Wato a yakin Badar da Uhudu, da Ahzab da.
Don a lokacinda Aliyu ya karmi khalifanci, Abdurrahman dan Auf ya na daga cikin wadanda suka ki yi masa bai’a bayanda mutane suka zabe shi, Aliyu bai tilasta masa ba.
2-Aliyu dan Abitaliba ya na daukar Zubair dan Awwam, a matsayin shi’arsa ne, saboda yana tare da shi a lokacinda aka kwace khalifanci daga wajensa bayan wafatin manzon All…(s). Zubair ya na gidansa sanda Umar da wasu sahabban suka shiga gidansa suka fitar da shi masallaci don yin bai’a.
Don haka atakaice, Umar ya nufi ya kawar da Khalifanci daga Aliyu dan Abitalib (a) a wannan karon ma.
Sannan wani abin mamaka da shura, shi ne, Khalifa ya ce manzon All..(s) ya rasu yana mai yarda da wadan nan mutane 6, amma kuma yace idan sun wuce kwanaki uku basu zabi wani daga cikinsu ba, aka kashe su. Zababbun kuma wadanda manzon All…(s) ya yi wafati yana mai yarda da su ne za’a kashe? Abin mamaki.
Sannan yace: idan sun rabu gida biyu mutane uku uku, bangaren da Abdurrahman dan Auf yake ne zai zama mai rinjaye. Kamar babu Aliyu dan Abitalib (a) a cikinsu, ta yaya zai gwatanta Abdurraman dan Auf da Amirul muminina (a).? wanda Imam Ali (a) ya halaka danginsa kafirai da dama a yake-yaken badar da Uhud da sauransu.
Sai kuma taron zaben Khalifa, wanda wasu suka ce an yi shi ne Baitul Mali na lokacin a birnin Madina. Wasu kuma suka ce an yi shi a gidan wani mutum wanda ake kira. Musawwar dan Mukhrimah.
Sannan Imam Hassan (s) jikan manzon All..(s) ya halarci wannan taron na zaben khalifa, hakama Abdullahi dan Abbas ( r) , sannan Amru dan Asi da Mughirah dan shiab sun zo kusa da inda ake zabe, a daya daga cikin wuraren nan biyu da muka ambata. Sannan yansanda jami’an tsaro na lokacin suka yiwa wurin kawanya, don tabbatar da cewa an aiwatar da wasiyyar Umar,
Don haka mutanen 6 suka zo kusa, sai Imam Aliyu dan Abitalib,(a) ne ya fara tashi, daga cikinsu ya yiwa mutanen nan 5 wa’azi ya gargade su, yace masu su ji tsoron All..su mayar masa da hakkinsa, wanda All..Ta’ala ya nada shi, manzon All..(s) ya kuma zartar da nadin, a wurare da dama a rayuwarsa.
Da ga karshen ya ja kunnensu kan cewa idan basu na da shi ba, to kuwa zasu ga abinda ba sa so a cikin al-ummar musulmi, zasu rarraba, sannan za’a sami wadanda zasu zubar da jinni musulmi don neman wannan kujerar ta Khalifanci ba tare da suna da hali guda mai kyau daya da ya bashi damar zama Khalifa ba.
Da ba’a zabeshi daga karshe ba, mun ga yadda Mu’awiya dan Abisufyan, wanda bai musulunta bas ai shekaru biyu kafin wafatin manzon All..(s) ya zo yana jayayya da Aliyu dan Abitalib (a), wanda shi ne farkon musulunta, sannan shine jarumin dukkan manya-manyan yake yake a musulunci, kamar Badar da Uhudu da Ahzab. Yana jayayya da shi kan khalifancin manzon All..(s). kuma sai da ya zama, tare da taimakon wasu manufurai, ba ma kawai shi ba, sai da yayansa da jikokinsa suka yi Mulki na shekaru fiye da 100 a bayansa a matsayin Khalifofin manzon All..(s).
Suka yiwa musulunci da musulmi barnan da ba’a taba gyaransa ba har duniya ta nade.
Sun yaki yayan manzon All..Tsarkaka sun koresu a bayan kasa, suka bisu a ko ina suka je a duniya suka kakkacesu. Don haka abinda Imam Ali(a) ya fada masu a taron zaben khalifa bayan mutuwar Umar duk sun faru.
A cikin littafin Tarikhin umammu wal-muluk ya kawo bangare na Khudubar Imam Ali a lokacin zaman zaben khalif ana ukku. Inda yake cewa:
{..ba wani wanda ya rika ni amsa kira zuwa gaskiya, da sada zumunci,..har zuwa inda yake cewa…ku saurari zance na, ku fahinci manufata, -idan baki yi abinda ya dace ba to kuma –da sannu zaku ga wannan al-amari (wato Khalifanci) ana zare takubba don nemansa, sannan a karya alkawulla da don nemansa, sai yak aiga wasu daga cikinsku sun zamo shuwagabannin bata, kuma magoya bayan mutanen jahiliyya} kamar yaddayazo cikin littafin sharhin Nahjul Balagh ana sheikh Muhammad Abduh..
Da masu shura sun ajiye son zuciyarsu gefe, sun dubi maslahar musulunci, suka mayarwa mai hakki hakkinsa, da dukkan wadannan musibu basu sami al-ummar musulmi ba.
Don haka an yi ta ja yayya tsakanin wadanan mutane 6, a rana ta farko, sun kasa zaben day daga cikinsu, an sake yin taro a rana ta biyu an kasa zaben mutum daya. Kuma wasiyar Umar itace a kashe dukkan mutum shida idan sun kasa zaben daya daga cikinsu bayan kwanaki uku.
A nan sai Abu Talha Al-ansari, ya zo wajensu yana cewa, {Ba zan kara baku ko kwana guda ba, idan wa’adin kwanaki uku ya cika zamu zartar da wasiyyar Khalifa a kanku ne}.
A nan ne sai suka kulla wata zaman, sai Talha dan’ubaidullahi ya tashi yace ya bawa bawa Uthman kuri’arsa, wato ya zabi Uthman, wannan kuma a fili yake, saboda fitattun yan takarar sune Aliyu dan Abitalib (a) da kuma Uthman dan Affan. A nan sai Zubair ya tashi shi ma, sai yace, ya bawa Aliyu dan Abitalib (a) kuri’arsa.
Daga nan sai Sa’ad dan Abiwakkas ya tashi yace, ya bawa Abdurrahman dan Auf kuri’arsa, kada ku manta shi dan amminsa ne.
Sannan Abdurrahman ya ga cewa ba zai iya zama Khalifa a kan wadannan biyu ba, wato Aliyu ko Uthman, don haka sai ya nemi shawarar Kuraishawa, suka ce masa ya zabi Uthman.
A nan Abdurrahman bin Auf shi ne mai raba gardama, idan ya koma gefen Aliyu, (a) , shi ne Khalifa, don a lokacin zasu zama masu kuri’u 4. Aliyu, da Zubair da kuma Abdurrahman dan Auf da kuma Sa’ad dan Abiwakkas.
Idan kuma ya koma gefen Uthman, zasu zama ‘kuri’u 4 shi ma, ga Uthman da Talha, ga kuma Sa’adu da kuma shi Abdurrahman. A nan sai ya zabi komawa ga Uthman, sai Uthman ya zama Khalifa. Aka bar Aliyu (a) da kuri’u biyu. Masu sauraro a nan zamu dasa aya sai kuma wata fitowaidan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Abdurrahman dan Auf wafatin manzon All tabbatar da cewa daya daga cikin masu sauraro ya nada shi
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Badakalar Tallafin Man Fetur Ta Zame Wa Nijeriya Alakakai
A cewar Bawa, gwamnatocin da a karkashinsu aka wawashe dukiyar kasa, su ne na Mulkin Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo (daga 1999 zuwa 2006), sai Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua (daga 2007 zuwa 2009), kazalika a mulkin Shugaba Goodluck Jonathan daga (2010 zuwa 2014), sai kuma mulkin Muhammadu Buhari (daga 2015 zuwa 2023).
Wadannan bayanai na kunshe cikin littafin, ‘The Shadow Of Loot and Loss – Uncobering Nigeria’s Petrol Subsidy Fraud,’ wanda tsohon sarkin yaki da cin hanci da rashawa ya rubuta.
Alkaluman da Bawa ya bayyana daga cikin gwamnatocin hudu, shugaba Buhari ne ke kan gaba wajen biyan tallafin da ake ta cece-kuce akai na Naira tiriliyan 11, sai kuma na Jonathan wanda ya kashe Naira tiriliyan 3.9. Gwamnatin Obasanjo ta zo na uku da Naira biliyan 812 yayin da ‘Yar’aduwa ke biye da Naira biliyan 794.
Obasanjo da Buhari sun shafe shekaru takwas suna mulki yayin da Jonathan ya yi mulki na tsawon shekaru shida, tun da farko ya kammala shekaru biyu da gwamnatin Yar’adua ta bari, a matsayin mataimakin marigayin, inda ya lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2011.
A cikin littafin mai shafuka 317, Bawa ya ce kudaden tallafin, wadanda galibi na yaudara ne, ana samun su ne ta hanyar rashin isassun tsare-tsare, raunin tsarin aiwatar da doka, da kuma rashin gaskiya a cikin dukkan tsarin.
Bawa ya ce wadannan kura-kurai sun karfafa karuwar kudaden tallafin daga Naira biliyan 123 a shekarar 2006 zuwa Naira biliyan 886 a shekarar 2014 da kuma mummunan adadi na Naira tiriliyan 11 a shekarar 2023.
Tsohon shugaban na EFCC ya ci gaba da cewa za’a iya bayyana badakalar tallafin man fetur ta Nijeriya ta hanyar amfani da triangle na zamba na “Tsarin (Needs), Opportunity and Rationalisation.”
Ya ce, “Matsi shi ne abin da zai sa mutum ya yi zamba, samun dama kuma ita ce ke bayar da yanayin da mutum zai aikata zambar.
Yadda Aka Aiwatar Da Badakalar
Bawa ya gano hauhawar farashin shigo da kayayyaki, da sauya lokacin daftarin kaya, rashin bayyana dawo da kayan da aka shigo da su ta sama da kasa, da jirgin ruwa mai yawo, shigo da kaya guda daya, tare da biyan tallafi a kansa sau biyu, na daga cikin hanyoyin da aka tafka badakalar tallafin man fetur.
A cewarsa, kamfanonin sayar da man sun yi amfani da yawan shigo da kayayyaki don kara yawan kudaden tallafi daga karshen shekarun 2010.
Ya ce binciken da aka gudanar ya sa hukumar EFCC ta gano haramtattun kudaden da suka haura Naira biliyan 30.
Bawa ya ci gaba da cewa, “A lokuta da dama, an samu jami’an gwamnati da saninsu ko kuma ba da saninsu ba, ta hanyar buga tambari da sanya hannu a cikin takardun jabun, wasu jami’an sun ce sun sanya hannu a kan takardun a lokacin da suke bakin aiki, duk da cewa suna sane da cewa lamarin ba haka yake ba, akwai wadanda suka sanya hannu kan takardun bogi, ba tare da sanin cewa an kirkiresu ba ne.
Ya ba da misali da yadda wani kamfani ya shigo da lita miliyan biyar kasa da mai fiye da lita miliyan 12. An biya kamfanin tallafin Naira miliyan 700, wanda bai cancanta ba.”
Wannan a cewarsa lamari ya ci gaba da haifar da tambayoyi masu mahimmanci game da hanyoyin damfara, gazawar sa ido na hukumomi, da kuma yadda EFCC ta gano wadannan haramtattun ayyuka.
Hanyar Kawo Karshen Lamarin
Dangane da kokarin hukumar na duba matsalar, Bawa ya ba da tarihin bincike, kamawa, tuhume-tuhume, yanke hukunci da kwato haramtattun dukiyoyi da hukumar ta yi.
Ya ce duk da cewa ba a samu wasu laifuka ba a shekarar 2006 da 2007, hukumar ta kwato Naira biliyan 11.5 a shekarar 2008, Naira biliyan 4.88 a shekarar 2009, da kuma Naira biliyan 10.3 a shekarar 2010.
Tsohon shugaban hukumar ta EFCC ya bayyana wata badakala da aka yi a 2011 ta tallafin man fetur, “a lokacin ne muka gano wasu haramtattum ayyukan da suka kai Naira biliyan 41.7.
“A dunkule, ayyukan damfara sun kai kusan Naira biliyan 68, wanda kusan kashi 80 cikin 100 an kwato su,” in ji shi.
Bawa ya kara da cewa, a cikin shekaru 25 na mulkin dimokuradiyya, Nijeriya ta kashe Naira tiriliyan 16.5 wajen bayar da tallafi, inda ya kara da cewa abin da ke daure kai ga daukacin al’amura shi ne yadda aka kashe kaso daga cikin kudaden wajen yin ikirarin karya da satar dukiyar kasa.
Hanyar Samun Ci Gaba
Bawa ya yi nuni da cewa, shi tallafin a kansa ba wani sharri ba ne; amma duk da haka, aiwatar da aikinta na yaudara ya sa gwamnati ta ki amincewa da dimbin albarkatun da aka tanada domin samar da ababen more rayuwa, inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya, wadanda ke amfanar da marasa galihu a Nijeriya.
Don haka ya yi kira da a samar da ingantaccen tsarin bayar da tallafi.
Ya ce, “Kiyaye tsarin tallafin da aka sarrafa da kyau zai iya ba da agajin da ake bukata ga masu rauni ta hanyar tabbatar da cewa an dakatar da tsadar rayuwa, sannan gwamnatin ta tsaya tsayin daka wajen samar da wani abin dogaro ga matsalolin tattalin arziki.
“Wannan yana jaddada muhimmancin samar da ingantattun hanyoyin sa ido da daidaita yadda ake raba tallafin don hana cin zarafi da tabbatar da sun cika manufarsu.”
Bawa ya kuma yi kira da a ji tsoron Allah da gaske da kuma samar da ingantaccen tsarin adalci.
Bawa ya ce, “Tsarin ba wai kawai kayan ya ke ba wa kariya da kuma dakile laifuka ba, har ma ya mallakar karfin bincike da kuma hukunta laifukan da suka dace, yana da matukar muhimmanci, irin wannan tsarin na samar da amana da amincewa a tsakanin ‘yan kasa, tare da karfafa hadin gwiwar jama’a da kuma tabbatar da doka da oda.”
Tsohon shugaban na EFCC ya bukaci ‘yan Nijeriya da na kasashen waje da su canja halayensu, su bi ka’idojin da’a, su sanya al’ummar kasa a zuciyarsu sama da kansu.
Bugu da kari, ya yi kira da a samar da isassun kudade tare da tura fasahar kere-kere a cibiyoyin gwamnati domin dakile cin hanci da rashawa.
“Su koma al’adar yin abin da ya dace, ba tare da la’akari da yanayin ba, hakan na iya haifar da sauye-sauye masu dorewa a cikin al’amuran al’umma,” in ji shi.
LEADERSHIP Sunday ta ruwaito cewa an samu wasu ‘yan Nijeriya da dama da laifin zamba a cikin tallafin man fetur, na baya-bayan nan shi ne Mamman Ali, dan Ahmadu Ali, tsohon shugaban jam’iyyar PDP mai mulki a lokacin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp