’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani a Katsina
Published: 13th, March 2025 GMT
’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani, Abdulsalam Rabi’u Faskari, tare da mahaifinsa da ’yan uwansa a Jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a kusa da Labin Bangori, yayin da suke dawowa Faskari bayan Abdulsalam ya samu lambar yabo wadda Gwamna Dikko Radda ya ba shi saboda nasarar da ya samu a gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa karo na 39 da aka gudanar a Birnin Kebbi, a Jihar Kebbi.
Wani jami’in gwamnati a Faskari, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da sace su.
“Malam Rabe da ’ya’yansa biyar, ciki har da Abdulsalam, wanda aka sace su a Bangori a kan titin Yankara. Har yanzu ba mu ji komai daga gare su ba.”
Abdulsalam, wanda ɗalibi ne a sashen likitanci na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, ya samu matsayi na farko a gasar a ɓangaren maza bayan ya haddace Alƙur’ani.
Har yanzu ’yan sanda a Katsina ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Gasar Karatu Gwarzo hari
এছাড়াও পড়ুন:
UNICEF Ta Jinjinawa Jihohin Kano, Katsina da Jigawa Bisa Inganta Rayuwar Kananan Yara
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta yaba wa jihohin Kano, Katsina da Jigawa kan manyan ci gaba da suka samu a fannin walwalar yara, tana gargadin cewa har yanzu akwai aikace-aikacen da dama da ya rage a yi.
A yayin ƙaddamar da rahoton Nigerian Child 2025 a Kano, Shugaban Ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihhood Mohammed Farah, ya ce jihohin Kano, Katsina da Jigawa sun samu gagarumin ci gaba a fannonin lafiya, abinci mai gina jiki, ilimi da samar da ruwan sha mai tsafta ta hanyar haɗin gwiwar hukumar da gwamnatocin jihohin.
Daga cikin nasarorin da Farah ya ambata akwai Masaki Initiative a Jihar Jigawa, wani shiri da al’umma ke jagoranta wajen yaki da rashin abinci mai gina jiki, inda yanzu sauran jihohi ke koyi da su.
Ya ƙara da cewa Jigawa ta samu babbar nasara a rigakafin cututtuka na yara a cikin shekarun da suka gabata.
A Katsina kuma, UNICEF ta ce gwamnatin jihar ta ware sama da naira biliyan ɗaya domin sayen abincin farfaɗo da yara masu fama da rashin gina jiki (RUTF) ta hanyar Child Nutrition Match Fund.
Ya kuma ce Katsina ta zama jiha ta biyu a Najeriya da ta kai matsayin Open Defecation Free (wato kawar da yin bayan gida a fili).
Sai dai duk da waɗannan nasarori, UNICEF ta ce gibin har yanzu yana da girma domin adadin yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki ya wuce kashi 50 cikin ɗari a kowace daga cikin jihohin uku, tare da miliyoyin yara da har yanzu ba sa zuwa makaranta.
A don haka Farah ya yi kira a ƙara haɗin kai domin cike waɗannan gibuna.