Masu Kira ta Waya a Shirin FRCN Kaduna Sun Koka Kan Jinkirin Biyan Fansho
Published: 23rd, February 2025 GMT
Masu kira ta waya a shirin Zamani Abokin Tafiya na FRCN Kaduna sun bayyana damuwa kan jinkirin biyan basussukan fansho ga tsofaffin ma’aikata duk da umarnin shugaban ƙasa da aka bayar kwanan nan.
Sun jaddada bukatar jami’an da ke kula da lamarin su hanzarta aiwatar da biyan kuɗaɗen domin girmama sadaukarwar da dattawan ƙasa suka yi da kuma rage cin hanci da rashawa a hidimar jama’a.
Masu kiran sun yi kira ga jami’ai da su nuna kishin ƙasa da tsoron Allah a yayin gudanar da aikinsu domin cika burin al’umma da kuma ci gaban ƙasa.
Alhaji Ibrahim Muhammad Katsina, Isya Soba, Ibrahim Allarama, Umar Aliyu Soba, Shafi’u Nalantawa, da Maza Jiya Soba, waɗanda su ma suka yi kira, sun jaddada bukatar inganta tsaro da rage farashin kayan masarufi bisa ga alkawarin da Gwamnatin Tarayya ta dauka.
SULEIMAN KAURA
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Biyan Fansho Shirye Shirye FRCN
এছাড়াও পড়ুন:
Manoma sun koka kan rabon takin gwamnati a Sakkwato
Manoma a Jihar Sakkwato sun koka game da takin da gwamnatin jihar ta ce za ta raba musu don noman damina cewa bai kai hannunsu ba.
Duk da cewa an ƙaddamar da rabon takin kusan mako guda da ya gabata.
Hatsarin Mota: Yadda hanyar Lambata ke laƙume rayuka a Neja Tinubu ya taya ’yan matan Yobe da suka lashe gasa a Ingila murnaGwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya ƙaddamar da shirin sayar da takin zamani da magungunan noma a farashi mai rahusa a Ƙaramar Hukumar Gwadabawa domin bunƙasa harkar noma a daminar 2025.
Sama da buhu dubu 105 na NPK da UREA aka sayar a farashi mai rangwame.
Hakazalika, an sayi maganin kashe ƙwari da keken noma don raba wa manoma.
Sai dai manoma da dama sun ce wannan taki ba na noman damina ba ne, kuma har yanzu ba a fara rabawa ba.
Umar Yusuf, wani tsohon manomi daga Tangaza, ya ce gwamnati ta ƙaddamar da sayar da takin ne bayan damina ta kusa ƙarewa.
Kabiru Muhammad daga Kware, wanda ke da gonaki guda biyar, ya ce yana buƙatar taki amma ba a samun shi a kan lokaci.
Ya ce shirin ba ya zuwa hannun manoman gaskiya saboda ba a tsara shi yadda ya dace ba.
Muhammad Sale daga Illela ya ce ba wani manomi mai gona da ke jiran takin gwamnati, saboda duk shekara sai an makara wajen rabon taki.
Ya ce idan gwamnati ba za ta samar da taki cikin tsari ba, gara ta daina sayen shi gaba ɗaya, ta mayar da kuɗin zuwa wani aikin da zai amfani talaka da jihar.