Iran Ta Soki Kalaman Netanyahu Na Cewa A Kafa Falasdinu A Saudiyya
Published: 11th, February 2025 GMT
Iran, ta la’anci kalaman foraministan Isra’ila dake cewa a kasa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya.
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya yi kakkausar suka ga kalaman na Benjamin Netanyahu da ke nuna cewa a kafa kasar Falasdinu a Saudiyya, yana mai danganta hakan da tsokana da kuma barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin.
Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan a ranar Litinin yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan shawarar Amurka da Isra’ila kan Falasdinu.
A yayin tattaunawar shi ma ministan harkokin wajen Saudiyya ya nuna adawar Saudiyya ta tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga Gaza ko wasu yankunan.
Tunda farko dama kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi kakkausar suka kan munanan kalamai da kuma rashin da’a da firaministan Isra’ila ya yi na yin kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya.
A ranar Alhamis, ne Netanyahu ya ba da shawara yayin wata hira da tashar 14 ta Isra’ila cewa “Saudiyya za ta iya kafa kasar Falasdinu a Saudiyya, suna da kasa mai girma.”
Kungiyar ta OIC ta dauki wannan a matsayin tsokana ga Saudiyya, kuma cin zarafi ne ga ’yancin kai, tsaron kasa da kuma yankinta, da kuma keta dokokin kasa da kasa da kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Falasdinu a
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Tana Maraba Da Kwararru Daga Bangarori Daban Daban Na Kasa Da Kasa Su Zo Kasar
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau 22 ga wannan wata cewa, a yayin da ake raya duniya bisa tsarin bai daya, musayar kwararru a tsakanin kasa da kasa ta sa kaimi ga raya fasahohi da tattalin arzikin kasashen duniya. Kasar Sin tana maraba da kwararru daga bangarori da sana’o’i daban daban na kasa da kasa su zo kasar ta Sin su gudanar da harkokinsu don sa kaimi ga raya zamantakewar al’ummar dan Adam da kuma samun ci gaban sha’aninsu baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp