Nijar : Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci A Saki Mohamed Bazoum
Published: 11th, February 2025 GMT
Gungun aiki na Majalisar Dinkin Duniya kan tsare mutane ba bisa ka’ida ba, ya yi kira da a gaggauta sakin hambararen shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum da matarsa Hadiza.
Tun a watan Yulin 2023 ne ake tsare da Bazoum a wani reshe na fadar shugaban kasar da ke Yamai, inda Likitansa ne kawai aka yarda ya ziyarce shi.
A cewar gungun aiki na Majalisar Dinkin Duniya kan tsare mutane ba bisa ka’ida ba, Mohamed Bazoum da matarsa Hadiza ana tsare da su ba bisa ka’ida ba, wanda ya saba wa dokokin kasa da kasa.
Su ma lauyoyin Mohamed Bazoum A cikin wata sanarwa, sun tunatar da cewa tsohon shugaban da matarsa ”an hana su mu’amala da kasashen waje” dangi, abokai da ma lauyoyi tun daga Oktoba 2023.
A watan Yunin da ya gabata ne Nijar ta cire kariyar Mohamed Bazoum na shugaban kasa, lamarin da ya share fagen yi masa shari’ar da har yanzu ba a sanya ranar da za a yi ta ba.
Lauyoyin Bazoum dai sun ce gwamnatin mulkin sojan kasar na amfani da shi a matsayin garkuwar dan Adam”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Falasdinu: Mahmud Abbas Ya Nada Magaji Da Kuma Mataimakasa
Shugaban Palasdinu da kuma kungiyar kwatar yencin falasdinawa PLO Mahmud Abbas ya nada magajinsa da kuma wasu mataimaka.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran, ta bayyana cewa Abbas dan shekara 89 ya nada mataimakinsa ne bayan taron majalisar gudanarwa ta gwamnatinsa a makon da ya gabata.
Labarin ya kara da cewa kasashen yamma da yankin sun dade suna takurawa Abbas kan ya nada mataimaki da kuma wasu mataimaka sabuda rawar da gwamnatinsa zata taka bayan yakin gaza.
A yau ne majalisar zartarwa ta amince da nada Hussein Al Sheikh a matsayin mataimakin shugaban majalisar da kuma mataimakin shugaban kasa a lokaci guda.
Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Falasdinawan WAFA, ya bayyana cewa gwamnatin Abbas ce da hakkin sa hannu a kan yarjeniyoyi da suka shafi Falasdinu, a madadin dukkan kungiyoyin Falasdinawa, banda wadanda su ka dauke da makamai suna yakar HKI, wato Hamas da kuma Jihadul Islami a Gaza.
Mr Al Sheikh, dan shekara 64 a duniya na hannun daman Abbas ne a kungiyarsa ta fatah.