Kwamandan Rundunar Sojin Saman Iran Ya Ce: Iran Ta Kai Matsayin Dogaro Da Kanta A Fagen Kere-Kere
Published: 8th, February 2025 GMT
Kwamandan rundunar sojin saman Iran ya bayyana cewa: Sun kai ga nasarar cimma matakin cin gashin kai a kere-keren kayayyakin aikin soja
Kwamandan rundunar sojin saman Jamhuriyar Musulunci ta Iran Birgediya Janar Hamid Wahidi ya bayyana cewa: Sojojin saman Iran na ma’aikatar tsaro da taimakon sojojin kasar sun cimma mataki dari bisa dari a fagen gudanar da kere-keren kayayyakin da suke bukata a harkar tsaron kasa, kuma dukkanin kayan aikin wannan runduna an inganta su tare da mayar da su saffarin cikin gida.
A ranar Juma’a 7 ga watan Fabrairu, Birgediya Janar Wahidi ya sanar a gaban taron kwamandojin sojojin saman Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Jagoran juyin juya halin Musulunci a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin cewa: Sojojin sama da na tsaron sararin samaniya su ne manyan makamai biyu na sojojin kasar Iran, kuma duk da takunkumin da aka kakaba musu, sun samu nasarar kare kasar tsawon shekaru takwas a tsawon kare kai daga yakin wuce gona da iri da aka kaddamar kanta a farkon samun nasarar juyin juya halin Musulunci.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Yana Maraba Da Masu Zuba Hannun Jari A Kasarsa Daga Kasashen Waje
Shugaban kasar Iran ya nuna murnarsa da yin maraba lalai da masu zuba hannun jari daga kasashen waje a Iran
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana Iran a matsayin dandalin da ta dace wajen zuba hannun jari da gudanar da harkar kasuwanci, yana maraba da masu zuba hannun jari na kasashen waje da ‘yan kasuwa na duniya da su shiga harkokin tattalin arziki da zuba hannun jari a Iran.
A yayin bikin bude baje koli karo na bakwai na baje kolin kayayyakin da Iran ke fitarwa zuwa kasashen ketare (Iran Expo 2025) a safiyar yau Litinin, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi maraba da baki na kasashen waje da suka halarci wannan baje kolin, yana mai cewa, “Ko da yake ana gabatar musu da wani hoto na daban da ya yi hannun riga da hakikanin Iran da al’ummar kasarta a ketare, amma Iran kasa ce mai karbar baki, kuma al’ummarta masu tausayi da nuna jin kai.”
Yana mai jaddada cewa: Iran wata kafa ce da ta dace da zuba hannun jarin kasuwanci da yawon bude ido na ketare, Pezeshkian ya bayyana cewa da wannan karfin, kuma ta hanyar ciniki, zuba hannun jari, da hadin gwiwa, za a iya samar da makoma mai haske ga duniya, mai cike da tsaro da zaman lafiya.
Ya kuma yi nuni da cewa: Yake-yaken da suka gani a duniya sun samo asali ne sakamakon rashin mutunta hakkokin bil’adama da na kasashe, Pezeshkian ya jaddada mutunta yankin kasar Iran da hakkokin kasashe, yana mai bayyana Shirin Iran na gudanar da duk wani hadin gwiwa a fannin kimiyya, tattalin arziki, siyasa, da zamantakewa da duniya, da kuma mika ilimi ga sauran kasashe ba tare da iyakancewa ba.