Leadership News Hausa:
2025-09-24@17:18:49 GMT

NDLEA Ta Kama Tsoho Mai Shekaru 75 Da Dillancin Ƙwayoyi A Kano

Published: 4th, February 2025 GMT

NDLEA Ta Kama Tsoho Mai Shekaru 75 Da Dillancin Ƙwayoyi A Kano

Hukumar yaƙi a sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Kano ta kama wani tsoho mai shekaru 75, Nuhu Baba, bisa zargin sayar da miyagun ƙwayoyi ga matasa.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Sadiq Muhammad-Maigatari, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Kano, inda ya ce wanda ake zargi ya amsa laifinsa, yana mai cewa ya rungumi sana’ar ne domin rayuwa a unguwarsu da ke ƙaramar hukumar Gezawa.

NDLEA Ta Cafke Masu Ta’ammali Da Ƙwayoyi 18,500 A 1 – Marwa NDLEA Ta Gargadi Iyaye Kan Bayyanar Alawar Ƙwaya A Kano

Hukumar ta kwato nau’ikan kwayoyi daban-daban, ciki har da Tramadol, wiwi, Diazepam, Exol-5 da man shafawa mai sa maye. Kakakin hukumar ya ce Kwamandan NDLEA na Kano, Abubakar Idris-Ahmad, ya jaddada ƙudurin hukumar na yaƙi da sha da fataucin ƙwayoyi tare da buƙatar hadin gwuiwar al’umma domin daƙile wannan matsala.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An Fara Nuna Hotuna Da Shirye-Shiryen Bidiyo Da Matasan Kasa Da Kasa Suka Dauka Don Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafa MDD A Kasar Sin

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Fara Nuna Hotuna Da Shirye-Shiryen Bidiyo Da Matasan Kasa Da Kasa Suka Dauka Don Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafa MDD A Kasar Sin
  • Groosi: Masu Binciken Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Suna Hanyar Zuwa Iran
  • Kotun Indiya ta daure dan Najeriya shekara 10 kan safarar miyagun kwayoyi
  • An kama ɗan sandan bogi a Kano
  • An Kama Ɗansandan Bogi A Kano
  • CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista da fasahar AI
  • Sarkin Ruman Katsina ya rasu
  • Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano
  • An kashe jami’an tsaro 53 a cikin mako biyu —Bincike
  • Mahara sun kashe ’yan sanda a shingen bincike a Kogi