2025-05-02@02:32:45 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2041

«Musa Iliyasu Kwankwanso»:

    Isra’ila ta kashe Palasdinawa 17 tare da jikkata wasu 69 a cikin awa 24 a yankin Gaza, inda ta kai harin sama a wani asibiti da ke yankin Khan Younis. Ma’aikatar Lafiyar Gaza ta sanar cewa jiragen Isra’ila sun kashe wani jami’in lafiya tare da jikkata wasu tara a Asibitin Kuwaiti da ke yankin Al-Musawi...
    Majiyar Falasdinawa a Gaza sun bada labarin kissan wasu sojojin HKI  a unguwar Shuja’iyya kusa da Gaza a jiya Litini,  inda wasu kuma suka ji rauni. Kafafen yada labarai da yahudawan da kuma larabawa sun bayyana cewa kungiyar Jihadul Islami a Gaza ta ce nayakanta masu farautar yahudawa daga nesa sun bayyana cewa suk halaka...
    A zantawarsa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Kuwait, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce tattaunawarsa da Abdullah Ali Al-Yahya ya fi bada karfi kan al-amuran yankin Asiya ta kudu musamman tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan shirinta na makamshin nukliya da kuma dagewa kasar takunkuman tattalin arzikin da aka dora...
    Ministan harkokin noma na JMI Ghulan Reza Noori Ghezelji ya jagoranci wata tawagar jami’an gwamnatin kasar zuwa kasar Brazil don halattan taron ministocin noma na kungiyar BRICS da kuma tattauna al-amura masu muhimmanci wadanda suka shafi ayyukan noma a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta fara aiki...
    Bayan da hukumar zaben kasar Gabon ta tabbatar da nasarar da Brice Oligui yayi a zaben shugaban kasa na karshen makon da ya gabata, shugaban ya gabatar da jawabinsa na farko ga mutanen kasar, inda ya bayyana masu kan cewa, babu jin dadi sai tare da wahala. Shafin tanar gizo na labarai ‘Africa News” ya...
    Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari kan laifin yunƙurin soka wa mahaifinsa makami a unguwar Fagge da ke Jihar Kano. Kotun da ke zamanta a yankin Mai Alluna ta yanke wa matashin hukuncin ne bayan bayan alƙali ya kama shi da laifin yunƙurin soka wa mahaifinsa almakashi saboda...
    Wasu masu dauke da makamai sun kai hari a wasu kauyuka biyu dake jihar Filato inda su ka kashe mutane 52. Rahotannin da suke fitowa daga jihar ta Filato sun ambaci cewa wasu makiyaya ne su ka kai  harin na ranar Litinin din da ta gabata an kai shi ne a kan yankin Bassa. Kamfanin...
    Sojoji a Jihar Filato sun ceto wasu mutum 16 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a kan titin Jos zuwa Mangu. Dakarun Rundunar Operation Safe Haven ne suka ceto mutanen a cikin wata mota da a aka jefar da ita a yankin Mararabar Kantoma da ke Ƙaramar Hukumar Manngu. Jami’in Hulɗa da Jama’a...
    A jiya Litinin daruruwan yahudawa ‘yan share wuri zauna sun kutsa cikin masallacin kudus, suna masu bayar da take na tsokana ga Musulmi. Har ila yau ‘yan share wuri zauna din sun kuma gudanar da na’u’oin ibadu na addinin yahudanci a cikin farfajiyar masallacin na Kudus. Ma’aikatar  da take kula da wuraren ‘wakafi’ na musulunci,...
    Gwamnatin kasar Ajeriya ta bayyana jami’an diflomasiyyar Faransa da suke kasar su 12 a matsayin ‘wadanda ba a bukatar ganinsu” a cikin kasar, tare da yin kira a gare su da su fice a cikin sa’oi 48. Bugu da kari kasar ta Aljeriya ta yi suka da kakkausar murya akan ministan harkokin wajen Faransa Bruno...
    ’Yan bindiga sun kai hari a kan taron masu ibada inda suka yi awon gaba da mutane da dama da ba a tantance ainihin yawansu ba. Mutane suna tsaka da gudanar da ibadar dare ne a kan wani tsauni a lokacin da ’yan bindigar suka kai musu farmakin suka yi garkuwa da su. Lamarin ya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yanzu haka, al’ummar Filato na cikin fargaba da tashin hankali sakamakon jerin hare-haren da suka afku a wasu sassan jihar, inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu, wasu kuma suka tsere daga muhallansu. Ko mene ne dalilin sake dawowar rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin da ake ganin an...
    Tsangayar Ilimi na Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ya shirya wani taron bikin cika shekaru 50 da kafuwa tare da gudanar da taron kasa karo na uku. Taron wanda aka yi wa take da “Ilimi Mai Sauya Rayuwa Don Gaba: Fuskantar Sabbin Kalubale da Buɗe Damar Samun Ci gaba” ya samu halartar manyan masu...
    Rikicin diflomasiyya tsakanin Paris da Algiers na dada kamari, inda Aljeriya ta bukaci wasu jami’an diflomasiyyar Faransa 12 da su fice daga kasar cikin sa’o’i 48. Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noël Barrot ya sanar cewa, Aljeriya ta bukaci jami’an diflomasiyyar Faransa da su fice daga kasar bayan kama wasu ‘yan kasar Aljeriya uku a Faransa....
    Wata Kotun Majistire mai lamba 7 a Kano, ta bayar da umarnin tsare wasu ’yan TikTok biyu kan zargin wallafa wasu bidiyon batsa a shafukansu na dandalin sada zumunta. Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano ce ta gurfanar da ababen zargin biyu — Isa Kabir Brigade da Fatima Adam Kurna — kan wallafa bidiyon da suka...
    Kasurgumin dan ta’addar nan da ke addabar yankin Sakkwato ta Gabas da Zamfara, Kacalla Bello Turji ya kashe manoma 11 a garin Lugu cikin Karamar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato. Dan gwagwarmaya da ke biye da lamarin rashin tsaro a yankin Sakkwato ta Gabas Bashiru Altine Guyawa ya sanar wa manema labarai cewa, Turji ya...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta bada kwangilar sanya kwalta akan hanyar Dolen kwana zuwa Garin Gabas zuwa Hadejia, kan naira miliyan dubu bakwai da miliyan dari takwas. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a wajen bikin kaddamar da aikin sanya kwaltar. Ya ce aikin hanyar mai tsawon kilomita 29, ana sa ran kammalawa nan da...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana alhininsa akan rasuwar Dr. Akbar I’itimadi wanda shi ne na farko da ya kafa hukumar makamashin Nukiliya ta Iran. Wasikar ta’aziyyar da shugaban kasa ta kunsa ta ambaci cewa:  Shakka babu hidima mai kima da wannan masanin ya yi, ya share fagen gina da ci gaban fasahar makamashin...
    A daidai lokacin da ake ci gaba da takaddama a HKI dangane da wasikar da wasu sojojin sama su ka rubuta na sukar yakin Gaza, wasu tsoffin ma’aikatar hukumar leken asiri ta “Mosad” sun bi sawunhu. Kafafen watsa labarum HKI sun ambaci cewa, fiye da tsoffin jami’an leken asirin kungiyar MOSAD 200 ne su ka...
    Majiyar asibiti a yankin Gaza, ta ambaci cewa an sami karuwar shahidai a cikin sassa mabanbanta na zirin Gaza zuwa 38, 3 daga cikinsu a yankin Deir-Balah. Jiragen yakin HKI sun kai wasu hare-hare akan wata mota da take dauke da wasu ‘yan’uwa shakikai su 6, da hakan ya yi sanadiyyar shahadarsu baki daya. ‘Yan’uwan...
    Rundunar ‘yansandan jihar Yobe ta kama wasu mutane biyu da ake zargin barayin wayar wutar lantarki ne a Damaturu babban birnin jihar. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa, rundunar ‘yansanda ta Karasuwa ce ta kama wadanda ake zargin – Yahaya Mustapha,...
    Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta gano wani haramtaccen wurin hada makamai a jihar Kano, lamarin da ya kai ga kama wasu mutane uku tare da kwato bindigogi kirar gida guda 15 tare da harsashi 102. Wadanda ake zargin sun hada da Abdul Sadiq mai shekaru 43; Ahmad Muazu, 22; da Aliyu Sharif, mai shekaru 40, an...
    Sanatan Kudancin Borno, Ali Ndume, ya bayyana cewa a halin yanzu mayaƙan Boko Haram sun ƙwace yankunan ƙananan hukumomi uku a jihar. Ndume ya bayyana cewa mayaƙan kungiyar sun kashe fararen hula sanda a 200 da sojoji 100 a sabbin hare-haren da suka kai a sassan jihar a baya-bayan nan. A wata zantawar da aya...
    Da yake jawabi a madadin shugaban kasa, Gwamna Uba Sani ya bayyana mahimmancin hanyar wadda ta hada babban birnin tarayya da jihohi sama da 12 dake fadin shiyyar Arewa ta tsakiya, Arewa maso Yamma, da Arewa maso Gabas.   A yayin taron da aka yi a Jere a karamar hukumar Kagarko a ranar Lahadin da...
    Fursunoni a gidajen yarin daban-daban a sassan Najeriya sun koka game da munin irin abincin da ake ba su, wanda suka ce na karnuka ya fi shi. Da dama daga cikin fursunonin da muka zanta da su sun bayyana cewa takwarorinsu sun sha mutuwa a sakamakon yunwa. Wannan zargi na zuwa ne bayan da Hukumar...
    Wani babban jami’in Diblomasiyya na kasar Iran ya bada sanarwan cewa zagaye na biyu a tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin JMI da Amurka za’a gudanar da shi ne a kasashen Turai a ranar 19 ga watan Afrilun wannan shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mataimakin ministan harkokin waje...
    Hukumar kula da agaji ta MDD (OCHA) ta bada sanarwan cewa, gwamnatin HKI a yankin yamma da kogin Jordan ta kori Falasdinawa a gidaje 5 a yankin bayan sun rusa gidajensu. Hukumar ta kara da cewa wadanda HKI ta rusa gidajensu a yankin sun hada da yara 19 da da iyayensu 33 maza da mata...
    ’Yan sanda sun kama shahararren mawaƙin zamani a Najeriya Habeeb Okikiola Badmus, wanda aka fi sani da Portable, bayan ƙazancewar rikicinsa da fitaccen ƙwararren mawakin Fuji, Okunola Saheed “Osupa.” A ranar Lahadi da dare ne ’yan sanda daga Jihar Kwara suka yi takakkiya suka kamo Portable mai waƙar “Zazu Zeh” a garin Abeokuta, Jihar...
    Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Gabon wanda kuma ya jagoranci juyin mulkin da aka yiwa Ali Bongo tsahon shugaban kasar ya lashe zaben da aka gudanar a jiya Lahadi tsakanin yan takara 7 har da shi. Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News” ya bayyana cewa Oligui dan shekara 50 a duniya, shi ne...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yanzu haka al’ummar Borno na cikin zullumi sakamakon wasu hare-haren da ake zargin ƙungiyar Boko Haram ce ta kai a wasu sassan jihar. Waɗannan hare-hare dai suna faruwa ne bayan shekaru da dama da iƙirarin hwamnati cewa an yi nasarar nakasa ƙungiyar. Ko mene ne dalilin sake...
    Shugaban Kasa Bola Tinubu ya kaddamar da aikin sake gyaran babban titin Abuja-Kaduna-Zariya-Kano, wadda ke da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin Arewacin Najeriya. Da yake jawabi a taron kaddamarwar a Kagarko, Jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani, ya bayyana yadda aka yi watsi da hanyar da kuma irin mummunan tasirin da hakan ya yi ga rayuka...
    A ranar Lahadi Liverpool ta sake matsa ƙaimi a gasar Firimiya bayan ta doke abokiyar karawarta West Ham United ci 2-1 a filin wasa na Anfield dake birnin Liverpool, yayin da Mohamed Salah ya kafa tarihin cin ƙwallaye a kakar wasa ta bana, sakamakon ya sa Liverpool ta samu tazarar maki 13 tsakaninta da...
    A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Indonesia, Prabowo Subianto suka yi musayar taya juna murnar cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. Inda shugaba Xi ya ce, yana dora matukar muhimmanci kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Indonesia, kuma a shirye yake ya yi...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Makiya suna cike da takaici da fushi kan ci gaban da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take samu A yayin ganawarsa da manyan kwamandojin sojojin kasar Iran a yau Lahadi, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa; Ci gaban da Iran ta samu...
    Kwamandan rundunar sojojin kasa ta Iran ya bayyana cewa: Nan ba da jimawa ba za a yaye labulen ire-iren makamai na musamman da Iran ta mallaka Kwamandan rundunar sojin kasa ta Iran Birgediya Janar Kiomars Heidari ya yi nuni da shirin rufe kan iyakar kasar da ke gabashin Iran, yana mai cewa: Wannan ba kawai...
    Jami’an tsaron Jihar Edo sun sake kama wasu mafarauta hudu daga Kano, makonni kadan bayan kisan gilla da ’yan bangar Jihar Edo suka yi wa ayarin wasu mafarauta 16 daga jihar Kano a jihar. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, ta ce mafarautan da aka kama sun fito ne daga Karamar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano,...
    ’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje fiya da 10 a yankin Biyabiki da ke Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara. ’Yan ta’addan sun cinna kona wuraren ne bayan sallar Isha’i a ranar Asabar a wani da ake zargin na ramuwar gayya ne kan kashe Isuhu Yellow, kanin wani jagoran ’yan bindiga...
    Sakamakon gazawar shugabanci, bayar da tallafi na neman zama wani bangare a tarihin dimokoradiyyar Nijeriya, inda gwamnatocin jihohi da ’yan majalisu da sauran ’yan siyasa suke amfani da shi wajen cusa wa ’yan kasa ra’ayinsu na siyasa. A duk lokacin da al’umma suka koka a kan wani mummunann yanayi da ya hada da matsin tattalin...
    Wata kotu a Amurka ta umurci Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta ƙasar (FBI) da ta fitar da bayanan sirri da aka samu kan Shugaba Bola Tinubu a lokacin wani binciken badaƙalar miyagun ƙwayoyi da gwamnatin ƙasar ta yi a shekarun 1990. Jaridar Premium Times ta ruwaito Alƙalin kotun, Beryl Howell wanda ya ba da umarnin...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, ƙungiyar ta karrama gwamna Lawal tare da gwamnonin Akwa Ibom, Kaduna, da kuma jihar Legas.   “A jiya a Legas, ƙungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya da Amurka (NACC) ta gudanar da bikin cika shekaru 65 da ƙaddamar da Alhaji Sheriff Balogun a matsayin shugaban ƙungiyar na 20.   “Taron mai...
    Matainakin shugaban kasar kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa, daukewa Iran takunkuman zalunci wadanda kasashen yamma suka dora mata na daga cikin asalin hakkin kasar da aka tauye. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aref yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa, kasar Iran...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Bagaei ya godeawa ministan harkokin wajen kasar Omman kan yadda ya shirya ya kuma gabatar da tattaunawa tsakanin JMI da Amurka a birnin Mascat da kuma kai kawon da yayi a  tsakanin bangarorin biyu. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Bagaei yana bayyana haka a...
    Jiragen yakin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan wasu yankunan a kasar Yemen a safiyar a jiya Asabar, wadanda suka Baida Sa’ada da kuma Hudaidah wadanda sune sake zafafa yaki a ciki kasar na baya-bayan nan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai na kasar ta Yemen na fadar cewa...
    Wani matashi ɗan shekara 18 mai suna Bakura Muhammed, ya gamu da ajalinsa a wani rikici da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin matasa masu gaba da juna da ake wa laƙabi da Malians a Maiduguri. Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zaga-zola Makama cewa, rikicin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar...
    Yin garkuwa da mutane domin don karbar kudin fansa ya zama ruwan dare a Jihar Katsina har ta kai ga ana shiga cikin manyan birane ana daukar manyan mutane ko makusantansu. Daga manyan sojoji zuwa sarakuna da malaman addini da ’yan siyasa da attajirai da ma dalibai, babu wanda ya tsira daga wannan matsalar...
     Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ” Amnesty International”  ta bayyana cewa, rundunar kai daukin gaggawa ta “RSF” ta bautar da mata da kuma cin zarafinsu. Kungiyar ta yi tir da abinda rundunar ta “RSF” ta yi akan mata da su ka manyanta da kuma ‘yan mata a tsawon lokacin yakin na Sudan...
    Jiragen yakin HKI sun harba makamai masu linzami guda biyu akan ginin asibitin Ma’amadani dake Gaza. Harin ya yi sanadiyyar rushewar wasu bangarori da su ka hada dakunan yin gwaje-gwaje da kantin sayar da magani.  Saboda hare-haren na Isra’ila a wannan asibitin, da akwai gwamman marasa  lafiya da suke kwance a kasa a waje, yayin...
    Ya soki masu ra’ayin cewa dimukradiyya wani sharadi ne na ci gaba, yana mai cewa “karya ne” shi akwai wata kasa da ta ci gaba a karkashin tsarin dimukradiyya?. Burkina24 ta nakalto cewa “Babu wata kasa da za a iya bayyanawa da ta ci gaba a dimukradiyya. Ya ci gaba da cewa gwamnatinsa za ta...
    Wannan gargadi da Sin da EU suka gabatar ga manyan kamfanonin shirya fina-finai da na fasaha na Amurka, na nuna cewa, gangancin da gwamnatin Amurka ke yi na kakaba haraji barkatai, zai ci gaba da illata kashin bayan fannoninta na cinikayya.   Hadin gwiwa tsakanin Sin da Sifaniya, ya kara bayyana yadda Sin ke fatan...
    Tsohon ɗan wasa, kuma tsohon mai horas da ’yan ƙwallon Super Eagles ta Najeriya, Christian Chukwu ya rasu. Christian Chukwu ya rasu ranar Asabar yana da shekara 74. Fashewar bam a mota ta kashe mutum takwas a Borno An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato Christian Chukwu ne kyaftin ɗin tawagar Super Eagles...