2025-11-03@18:06:20 GMT
إجمالي نتائج البحث: 465

«farashin kayan masarufi»:

    A jiya Juma’a ne dai wanda ya isa birnin Beirut ya yi kira ga al’ummar kasar da su yi riko da hadin kan kasa da dukkanin bangarorinsu, sannan kuma su ci gaba da zage damtse wajen kalubalantar makiyar kasar Lebanon,musamman ‘yan sahayoniya. Goerge Ibrahim Abdullah wanda kuma  ya gabatar da taron manema labaru a garinsu...
    Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Siriya ta tattara bayanan mutuwar mutane 1,400 a loardin Sweida na Siriya Siriya, Faransa da Amurka sun sanar da wata taswirar hadin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya a Siriya, bayan tattaunawar da ba a taba ganin irinta ba a birnin Paris na Faransa,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara tattauna masifar da ta faru a Gaza tare da jaddada kawo karshen kisan kiyashi  yanki Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani sabon zama domin tattauna batutuwan da suke faruwa a Gaza da kuma tabarbarewar al’amuran jin kai a yankin, inda ake ci gaba da yin...
    Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) a ranar Laraba ta ce ta gano wani dakin ajiye kayayyaki da aka makare da lita 88,560 na sinadaran hada bama-bamai a Kano. Shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana hakan lokacin da take yi wa manema labarai jawabi a kofar rumbun...
    Alkaluma da aka fitar a hukumance sun nuna cewa, kasar Sin ta samar da sabbin guraben aikin yi miliyan 6.95 a rabin farko na bana, inda ta cimma kaso 58 bisa dari na burinta na shekara. Kakakin ma’aikatar kula da ma’aikata da walwalar al’umma ta kasar Sin Cui Pengcheng ne ya bayyana haka yayin wani...
      Ko za ka iya fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinka? An haife ni a Unguwar Adakawa cikin birnin Kano, na yi makarantar firamare a Adakawa, daga nan kuma na tafi zuwa makarantar sakandire (Gwammaja One), bayan na sauke Alkur’ani, daga baya na tafi sai na wuce zuwa ‘School of Health Technology’ ta Kano....
    Ana zargin wani direban tirela ya gudu da buhunan masara 463 da aka aike shi da su, bayan da ya bai wa ɗan rakiyarsa guba a cikin shayi a yankin Maraban Jos da ke Jihar Kaduna. Wani ɗan kasuwa da ke safarar hatsi daga Jihar Kano zuwa kamfanoni a sassa daban-daban na Nijeriya, Injiniya Jamilu...
    Har ila yau, manufar ita ce; don rage yawan asarar da manoma ke tabkawa, bayan sun yi girbin farko da kuma jawo hankalin matasan kasar, domin su rungumi aikin na noma; musamman wanda za su yi, su samu riba. Kaddamar da Taraktocin na zuwa ne, daidai da lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar...
      A daya bangaren kuma Fita zuwa wani yanki daban da ba naka a halin yanzu, yana da nasa fa’idar. Domin kuwa, na ziyarci wasu jihohi uku kwanan nan; wadanda labarai a kansu babu dadin ji. Jihohin su ne, Delta, Inugu da kuma Zamfara, wadanda galibi labaransu marasa dadi ne ta fuskar siyasa, ta’addanci da...
    Mai taimaka wa Sarkin Bayero kan harkokin yada labarai, Khalid Uba, ya shaida wa LEADERSHIP cewa magoya bayan Sarkin Bayero ba su da makamai. Uba, wanda ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho, ya ci gaba da cewa babu wani daga cikin tawagar Sarkin Bayero da ke dauke da wani makami, sai dai an tilasta...
    Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan kai hare-hare kan tashar jiragen sama na Bengurion na HKI tare da amfani da makamai masu linzami samfurin Balistic. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar sojojin Yemen na cewa, sun kai hare-hare da makamai masu linzami ka tashar jiragen sama na Ben gurion kuma zasu...
    Idris ya ce: “Ko da yake muna jaddada ‘yancin kowane ɗan Nijeriya na amfani da ‘yancin sa na shiga ko kafa ƙungiya da faɗar albarkacin baki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, yana da muhimmanci a fayyace cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ba za ta bari harkokin siyasa ko hayaniyar ‘yan siyasa su karkatar da...
    Kakakin dakarun rundunar Izzudden-Qassam ya bayyan cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun tarwatsa wani mutum-mutumi da sojojin mamayar Isra’ila suka makare da harsashai dauke da makami mai linzami a lokacin da ake shirya shi A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kakakin rundunar sojin Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas Abu Obeida, ya yi...
    Wannan matakin ya biyo bayan shawarar Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na ASUU wanda ya amince da tsarin “Ba Albashi, Ba Aiki” saboda yawan jinkirin biyan albashi da suke fuskanta. ASUU ta ɗora laifin hakan kan Ofishin Akanta-Janar na Tarayya. Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana a ranar Litinin cewa gwamnatin na...
    Shugaban Kungiyar Harka Islamia a tarayyar Najeriya Sheikh Irahim Zakzaky ya taya mutanen kasar murna saboda nasarar da suka samu kan HKI da kuma Amurka a yakin kwanaki 12 a cikin watan da ya gabata. Ya ce wannan nasarar bata takaita da mutanen kasar Iran kadai ba , hada har da al-ummar Musulmi da kuma...
    Kasar China ta maida martani ga takunkuman tattalin arziki na wasu kayakin kiwon lafiya wadanda tarayyar Turai da dorta maya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar kasar ta Chaina na fadar haka ta kuma kara da cewa gwargwadon takunkuman da suka dorawa kasar gwargwadon maida martanin kasar ta China. Labarin ya...
    Kungiyar Kananan Hukumomin Nijeriya (ALGON) reshen Jihar Kaduna, ta mika sakon taya murna ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa lambar karramawa ta CON da shugaban kasa ya yi masa ado da ita, wacce ke matsayin wata alamar girmamawa a Jamhuriyyar Nijeriya ta Hudu. Wannan karramawar, wata alama ce a sarari ga sadaukarwar mai...
    “Wannan aiki ne, wanda za a iya cewa; tamkar a yanzu ne muka fara dora damba a kansa”, a cewar shugaban. Haka zalika, shugaban ya kuma sanar da wadanda suka halaccin taron kaddamar da shirin tabbacin cewa; wadannan ayyuka na noman zamani, za su kara taimakawa wajen kara samar da ayyuka a fannin aikin noma...
    An fara tuhumar tsohon ɗan ƙwallon Arsenal, Thomas Partey da laifuka biyar da suka haɗa da fyaɗe da kuma cin zarafi, an bayar da rahoton cewa ya aikata laifukan ne a tsakanin shekarar 2021-2022, cewar ‘yansandan Birtaniyya. Daga cikin laifukan akwai fyaɗe akan wasu mata uku waɗanda ake tuhumarsa da cin zarafinsu ta hanyar tursasawa...
    Yayin taron manema labarai na yau Alhamis, kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin He Yongqian, ta ce ba su da wata masaniya, game da cewa shugaban Amurka na shirin jagorantar wata tawagar ‘yan kasuwa zuwa kasar Sin. Sai dai kuma duk da hakan, a cewarta har kullum matsayar Sin a bayyane take, cewa tana fatan ita...
    Ministan tsaron cikin gida na HKI Itamar Ben-Gvir ya yi kira ga babban murya kan cewa dole ne HKI ta mamaye dukka zirin gaza ta kuma kori falasdinawa da suke cikinsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalato Ben Gafir yana fadar haka a jiya ya kuma kara da cewa mamaye gaza da...
    Iran ta nuna makamai masu linzami wadanda suka bude kofofin jahannama kan ‘yan sahayoniyya A martanin da gwamnatin yahudawan sahayoniyya suka kai wa Iran, sojojin Iran da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar sun nuna karfinsu na soji a matsayin wani bangare na “Alkawarin Gaskiya na 3”, inda suka harba daruruwan makamai masu...
    Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce zai yi takarar shugabancin Nijeriya a 2027 domin ba zai shiga duk wata yarjejeniyar haɗakar takara da kowa ba. Obi wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a Zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Labour (LP), ya tabbatar wa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya dangane...
    Masu bincike sun gano cewa sojojin HKI sun kashe Falasdinawa akalla 100,000 tun bayan fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara 2023. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kan cewa farfesa Michael Spagat da kuma Khalil Shikaki  Bafalasdine masanin masanin fasahar siyasa a Jami’ar London na kasar Burtania...
    Alhaji Ahmad Manga ya ce, “an ɗauki matakin ne da haɗin gwiwar gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya”.   Jami’an CPG na Zamfara sun kuma samu goyon bayan dakarun Civilian JTF na jihar Borno, inda suka ƙaddamar da harin a-yi-ta-ta-ƙare na bazata ga maɓoyar ta Bello Turji.   Gwamnatin jihar Zamfara ta ce artabun na ranar...
    Wani mummunan hatsari ya afku a Masar inda ‘yan mata 18 suka mutu sakamakon fashewar wata motar dakon mai Wani mummunan hatsarin mota ya afku a kasar Masar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mata 18 da direban bas a kan hanyarsu ta zuwa gonar inabin domin girbin inabin. Hatsarin ya afku ne a...
    Masana da jami’ai a Nijeriya, sun yaba wa ci gaba na a-zo-a-gani da karin kuzarin da ake samu a hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Nijeriya, suna masu bayyana kokarin da aka yi zuwa yanzu a hadin gwiwar bangarorin biyu a tafarkin zamanantar da kansu. Masanan sun bayyana haka ne yayin taro na biyu na...
    An ji karar jiniyoyin gargadi a wurare da dama a HKI suna tashi bayan sun hango malamai masu linzami wadanda sojojin Yemen suka cilla daga kasar zuwa haramtacciyar kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kafafen yana labaran yahudawan na cewa sun yi shirin kakkabo makaman kafin su isa. Amma basu bada...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin. Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci...
    Yawan gawarwakin da aka tsinta bayan harin duk na mabiyansa ne. Ɗaya daga cikin su, Bashari Maniya, wanda tsohon ɗan bindiga ne da ya ce ya tuba kuma ya fara taimaka wa jami’an tsaro, shi ma ya mutu bayan motar da yake ciki ta faɗa rami mai zurfi. Manga ya bayyana cewa ba da bindiga...
    Tun da farko, Gwamna Aliyu ya ce, gwamnatinsa ta bullo da shirin ne domin ta saukaka farashi da kashi 20 ta hanyar saukar da farashin kayan abinci kasa warwas. Gwamnan ya ce, an tsara shrin ne domin saukakawa ma’aikatan jiha, na kananan hukumomi da masu karbar fansho ta hanyar samar da nau’ukan kayan abinci...
    Fadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai zabi wanda zai yi masa takarar mataimaki a zaben 2027 a hukumance ne kawai bayan a kammala babban taron jam’iyyar APC a 2026. Kakakin shugaban, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawarsa da jaridar Daily Trust a ranar Alhamis. Da yake martani kan dalilin...
    A ci gaba da ƙoƙarinta na tabbatar da kyawawan halaye da kuma samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe ta lalata katan 243 na barasa da galan 100 na barasa da aka haɗa a gida, da aka fi sani da sukudaye. A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Hukumar,...
    Kafin wannan, yana riƙe da sarautar Walin Gaya, wanda aka ba shi lokacin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙiri sabbin masarautu. Masarautar ta ce an ɗauki wannan matakin ne domin kare mutunci da ƙimar sarautun gargajiya bisa tsarin da aka gada. Sai dai matakin ya zo ne mako guda bayan Alhaji Usman ya soki...
    Ta hanyar inganta manufar yafe harajin kwastam a kai a kai, kasar Sin ta samar da yanayin kasuwanci mai karko a kasashen Afirka. Bugu da kari, kasar Sin tana kallon manufofinta na rangwame a matsayin matakan tabbatar da burin samun ci gaba, inda take kokarin kyautata tsarin cinikayyar waje na kasashen Afirka, da kuma ba...
    Borussia Dortmund ta soma buɗe wasanninta na gasar FIFA Club World Cup da canjaras a karon-battar da ta yi da kungiyar Fluminense ta Brazil a ranar Talata. Ana dai ganin babbar kungiyar da ta zama gagarabadau a Rio de Janeiro Fluminense a matsayin mafi hatsari a rukunin F wanda ya kunshi har da kungiyar Ulsan...
    Alhazai 442 sun tsallake rijiya da baya, bayan jirgin da ya ɗauko su bayan sun kammala aikin Hajjin bana ya samu sakon cewa an dasa bom a cikinsa a yayin da yake sararin samaniya a ƙasa Indonesiya. A ranar Talata ne jirgin, mallakin kamfanin Saudia Air, ya yi saukar gaggawa a birnin Jakarta babban birnin...
    “Na ce Shettima ɗanmu ne, kuma muna alfahari da shi. Na kuma gode wa Tinubu bisa yadda ya bai wa ‘yan Arewa maso Gabas muƙamai masu gwaɓi kafin na nemi a mara masa baya,” in ji Salihu. A lokacin taron, wasu matasa sun kusan kai masa hari, amma ya ce hakan ya faru ne saboda...
    Sarkin yankin Oke Agbe a Jihar Ondo ya ci Musulmi tara, tare da barazanar koran su da kuma haramta yin addinin Musulunci a garinsa bayan da wasu dodanni suka kai hari a wani masallaci da gidan limami. Aminiya ta samu rahoto cewa, wasu dodanni sun kai hari a masallaci da gidan wani limami, suka lakaɗa...
    Wasu Hare-haren da gwamnatin Isra’ila ta kai ya haddasa gobara a wasu matatun mai a lardin Bushehr da ke kudancin kasar Iran. Gobarar ta tashi ne a wurin a ranar Asabar bayan da wasu kananan jiragen yakin Isra’ila guda biyu suka kai hare-hare a kan kayayyakin sarrafa iskar gas da ke yankin kudancin Pars. Hare-haren...
    Farashin Man Fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan harin da Isra’ila ta kai wa Iran, lamarin da ya tayar da hankalin masu zuba jari. Ana fargabar cewa rikicin da ke ƙara taɓarɓarewa tsakanin ƙasashen biyu zai iya kawo tangarɗa wajen samar da man fetur daga yankin Gabas ta Tsakiya. An kashe masu garkuwa da...
    Ya ce Jihar Kurus Ribas ita ce ta farko a yankin kudu da ta shiga a dama da ita a harkar noman alkama, lamarin da ke nuni da gayar nasara wajen samar da abinci a kowani sassa na kasar nan. Kyari ya kara da cewa shirin rabar da takin zamani ya taimaka wajen bunkasa samar...
    Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Manjo Janar Hussain Salami ya fada a yau Alhamis cewa; Abokan gaba suna yi mana barazana da yaki, sannan ya tabbatar da cewa a shirye suke su fuskanci duk abinda zai faru. Manjo janar Salami wanda ya gabatar da jawabi ga taron dakarun sa-kai na “Basiji...
    Ma’aikatar leken asiri ta kasar Iran ta fidda farkon bayanan sirra wanda ta samo daga HKI wadanda kuma suke tabbatar da dangantakar da hukumar IAEA take da shi da HKI da kuma sauran kasashen yamma da hukumomin tsaronsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran tace a cikin bayanan da ma’aikatar ta wallafa ya zuwa...
    Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ta bayyana cewa jerin wuraren da zata kaiwa hare hare a HKI a duk wani yakin da zata taso tsakanin kasshen biyu, suna hannu. Daga ciki har da ciboyoyin Nukliyar kasar wadanda ta boye su. Tashar talabjin ta Presstv a nann Tehran ta nakalto majalisar ta na fadar haka...
    Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a yau Litinin 9 ga wata sun nuna cewa, a watan Mayun bana, ma’aunin farashin kayayyakin masarufi, watau CPI na kasar, ya ragu da kaso 0.1 bisa dari, bisa na makamancin lokacin bara, kuma farashin makamashi ya zama babban dalilin da ya haifar da raguwar. Kana,...
    Minitan kiwon lafiya na kasar Iran ya bukaci kamfanonin da suke kera kayalin kiwon lafiya da kuma aikin likita so kara yawan kayakin da ake sayarwa zuwa kasashen waje. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mohammad Reza Zafarkhan yana wannan kiran a jawabin da ya gabatar a taron bude kasuwar baje koli...
    Minitan kiwon lafiya na kasar Iran ya bukaci kamfanonin da suke kera kayalin kiwon lafiya da kuma aikin likita so kara yawan kayakin da ake sayarwa zuwa kasashen waje. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mohammad Reza Zafarkhan yana wannan kiran a jawabin da ya gabatar a taron bude kasuwar baje koli...
    Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya nanata matsayin Taiwan da jaddada manufar Sin daya tak a duniya yayin tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot a jiya Jumma’a. Ya kuma bayyana adawar Sin da shigar kungiyar tsaro ta NATO cikin harkokin yankin Asiya da Pasifik. Wang Yi wanda mamba ne na...