2025-09-17@23:12:46 GMT
إجمالي نتائج البحث: 516
«Sarauniyar Ingila»:
Gwamnatin Jihar Kwara ta ce za ta yi haɗin gwiwa da Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN) da sauran masu ruwa da tsaki domin mayar da jihar cibiyar fitar da kayan gona da na kasuwanci. Kwamishinan Noma da Ci gaban Karkara na jihar, Dakta Afees Abolore, ne ya bayyana haka a wani taron da...
Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa Alhaji Aminu Zakari, yace ziyarar kwamatin a kananan hukumomin jihar 27 tana bada damar ganawa kai tsaye a tsakanin masu ruwa da tsaki domin karfafa dabi’ar aiki tare da juna da kuma kyautata alaka a tsakanin bangarori daban daban. Ya yi wannan tsokaci ne lokacin da...

Bayan Gargadi Daga Gwamnatin Tarayya: Jihohin Arewa 15 Sun Fara Daukar Matakan Dakile Ambaliyar Ruwa
A cikin jahohin da aka lissafa, Kebbi ce ta fi kowacce yawan garuruwa a jerin sunayen, inda take da garuruwa kusan 10 da suka hada da Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, da Birnin Kebbi. Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar gargadin samun ambaliyar ruwa ga jihohi 15 daga cikin 19 na Arewa....
Kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders ta sanar da cewa: Mutane 40 ne suka mutu a Sudan sakamakon barkewar cutar kwalara mafi muni cikin shekaru Kungiyar likitocin ba da agaji ta “Doctors Without Borders” ta sanar da mutuwar mutane 40 sakamakon kamuwa da cutar kwalara a Sudan cikin mako guda kacal, tare da tabbatar da...
“Na zo Banga domin jajanta muku bisa wannan mummunan hari. Lokacin da abin ya faru bana nan, sai na umarci mataimakina ya jagoranci tawaga ta musamman domin yi muku ta’aziyya. “Na dawo Gusau jiya, kuma abu na farko da na fifita yau shi ne zuwa nan da kaina. Gwamnati za ta ƙara ƙoƙari wajen yaƙar...
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya ziyarci wasu garuruwa a Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda, bayan jerin hare-haren ’yan bindiga da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Gwamnan, ya la’anci kisan gillar, tare da bayyana shi a matsayin marasa imani, kuma Allah zai fallasa su ya kunyata su. Majalisar Zartaswa ta dakatar da ƙirƙirar...
Tinubu ya yi kira da a sake duba kudaden gudanar da aikin NNPC da ake cire kashi 30 cikin 100 wanda doka ta tanadar a karkashin dokar masana’antar mai. Shugaban ya bayyana godiya ga mambobin majalisar bisa jajircewarsu da aiki tukuru wajen aiwatar da gyare-gyare masu tsauri da wahala wadanda suka dabaibaye ci gaban...
Ƙungiyar Ci Gaban Masarautar Jama’a (JEDA), ta roƙi Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, da ya kammala manyan titunan Birnin Kafanchan, wanda aikin ya tsaya tun zamanin Nasir El-Rufai. Muƙaddashin shugaban ƙungiyar, Ahmad Usman Husain, ya ce waɗannan tituna na da muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziki da rayuwar yau da kullum a Kudancin Kaduna. Majalisar Kano...
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da kyakkyawar alaka da kafafen yada labarai. Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya, da ‘yan majalisar zartaswar NUJ na kasa (NEC) da suka je Kano domin...
Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU), Jami’ar Jihar Taraba Jalingo, ta bayar da wa’adin makonni biyu ga gwamna Agbu Kefas da shugabannin jami’ar da su gana da ita ko kuma ta shiga yajin aikin. A cikin sanarwar da aka fitar a karshen taron majalisar da aka gudanar a ranar 7 ga wata. Agusta 2025,...
Biyo bayan wani rahoto da ma’aikatar lafiya ta tarayya ta fitar na cewa sama da likitoci 16,000 ne suka bar Najeriya a cikin shekaru bakwai da suka gabata domin neman aiki a wasu kasashe, gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri na cike gurbin da likitocin suka haifar. Da yake zantawa da manema...
Sojojin Yemen sun sanar da cewa: Sun kai hari kan muhimman wurare hudu na haramtacciyar kasar Isra’ila da jirage marasa matuka guda shida Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Talata cewa: Sun kai farmakin soji ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka ciki guda shida, inda suka kai hari kan wasu muhimman wurare...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani basarake, Mohammed Tukur mai shekaru 55, a kauyen Sabon Gari da ke yankin Zambuk na Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya...

Ministan Harkokin Wajen Iraki Ya Bukaci Zaman Tattaunawa Tsakanin Kungiyar Larabawan Yankin Tekun Gulf Da Iraki Da Kuma Iran
Ministan harkokin wajen kasar Iraki ya ba da shawarar gudanar da taron kasashen Larabawan yankin tekun Pasha da Iraki da kuma Iran Ministan harkokin wajen kasar Iraki Fuad Hussein ya gabatar da shawarar gudanar da taron hadin gwiwa tsakanin kasashen Iraki, Iran, da kuma kasashen larabawan yankin Gulf, a tsarin na 6+2, a gefen taron...
Yajin aikin sai baba-ta-gani da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Taraba, da kungiyar Kwadago (TUC) reshen jihar Taraba suka kaddamar a ranar Litinin da ta gabata, ya gurgunta ayyukan gwamnati a ma’aikatu da hukumomin gwamnati a jihar. Matakin wanda ya fara da tsakar daren litinin, ya kasance tare da hadin gwiwar shugabannin...
Rikicin filin gona ya yi sanadin mutuwar mutum biyu tare da jikkata wasu biyu a ƙaramar hukumar Gulani da ke Jihar Yobe. Lamarin ya faru ne a daren Asabar bayan ce-ce-ku-ce tsakanin mazauna ƙauyukan Zango da Azere, waɗanda ke tsakanin iyakokin Gujba da Gulani. Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya bayyana cewa shalƙwatar...
Kungiyar Kwadago da ta ‘yan kasuwa ta Nijeriya (NLC da TUC) reshen jihar Taraba sun bayyana shirin fara yajin aiki tun daga karfe 12 na daren Litinin 11 ga watan Agusta, 2025. Wannan mataki ya biyo bayan sakamakon taron majalisar zartarwa ta jihar da kungiyoyin biyu suka yi a ranar Lahadi a Jalingo, babban birnin...
’Yan ta’adda sun kashe mutum 24 tare da sace wasu akalla 144 a cikin mako guda a sassan Jihar Zamfara. Kungiyar Al’ummar Zamfara mai suna Zamfara Zamfara Circle Community Initiative ta bayyana cewa ’yan ta’addan sun kai hare-haren da suka kai kan kauyuka 15 inda suka jikkata mutane 16 a kananan hukumomi daban-daban. Ta bayyana...
“Baya ga alaƙa da Ruwa, ƙasashen da ke Afirka ta Gabas da kuma waɗanda ke a Afrika ta Tsakiya, da suke yi musharaka da irin ƙalubalensu da kuma sauran damarmakinsu, dole ne mu zage mu amfana da tattalin arzikin da ake da shin a Tekuna, musamman ta hanyar haɗa kanmu da kuma yin haɗaka, wanda...
Al’ummar Japan na gudanar da bikin tunawa da ranar harin Nagasaki da ya faru shekaru 80 da suka gabata, wani hari da ke zama irinsa na farko kuma mafi muni da duniya ta taba gani. Tarihi ya nuna cewa Amurka ce ta fara harba makamin Nukiliya a garin na Nagasaki kwanaki uku bayan na garin...
A cewarsa, daga cikin waɗanda Allah ya yi wa rasuwa akwai mahaifiyar yaran wato Mariya Sani, ‘yar shekara 45 da kuma Mujahid Sani, ɗan shekaru 20, sai Zahariya Sani, ‘yar shekara 18. Sauran sun haɗa da Hauwa Sani, ‘yar shekara 15 da Amira Sani, ‘yar shekara 3 da kuma Nura Sani, ɗan shekara 5. Muhammad...
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ziyarci Jihar Bauchi tare da ba da tallafin Naira miliyan 15 don tallafa wa harkar ilimi. Obi, ya sauka a filin jirgin sama na Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe 9:40 na safe. Sojoji sun yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta a Borno ’Yan...
A fannin noma ma, watsa shirye-shiryen da Sinanci zai taimaka wajen bayyana burin Nijeriya na fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, musamman yadda take neman aikewa da karin kayayyakin amfanin gona zuwa babbar kasuwar kasar Sin, tare da bai wa masu ruwa da tsaki na kasar Sin damar sanin abubuwan da Nijeriya za ta iya...
Akalla magidanta 50 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kauyuka uku na karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sakkwato, sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka tafka a yankunan. Ambaliyar da ta mamaye kauyukan na Tangaza ne da suka hada da Gidan Madi da Baidi da Madarare, kuma ta haifar da rushewar gidaje...
A wata ganawa da ya yi da manyan jami’an tsaro a wannan Talata don kammala dabarun yakin Gaza, Firayim Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya amince da kwace yankin zirin Gaza baki daya da karfin soji, duk da hadarin da ke tattare da sauran fursunonin yahudawa da ke tsare a hannun ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa...
A cewar mahaifin marigayen, Dankama, ya bayyana cewa ba ya gida lokacin da katangar ta fado, inda ya ce ya kadu da jin labarin. “Wannan lamarin ya faru da kusan mutane goma, amma mutane 6 sun riga mu gidan gaskiya. A yanzu haka, uku suna kwance a asibiti suna karbar magani,” kamar yadda ya...
Sojojin Yemen sun kaddamar da hari kan filin jirgin saman Lod da ke birnin Jaffa a haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami Dakarun sojin Yemen sun sanar a yau cewa: Sun kai hari kan filin jirgin saman Lod da ke birnin Jaffa, domin mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da kakaba masifar yunwa...
Wata ɗaliba ’yar shekara 15 daga Jihar Yobe, Rukayya Muhammad Fema, ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 a Gasar Muhawara ta Duniya ta Teen Eagle. Rukayya ta yi zarra ne a wannan babbar gasa da ta gudana a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, inda zaƙaƙuran ɗalibai daga ƙasashe 69 a faɗin duniya suka fafata a tsakaninsu....

Xi Jinping Ya Ba Da Muhimmin Umarnin Jin Ra’ayoyin Masu Amfani Da Intanet Kan Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Na 15
Babban sakatare na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, kana shugaban kasar, Xi Jinping ya bayar da muhimmin umarni game da binciken ra’ayoyin jama’a masu amfani da shafukan Intanet kan aikin tsara shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 a kwanan nan, inda ya ce, ya kamata aikin tattara ra’ayoyin jama’a...
Gwamnatin Kano ta bayyana shirin mayar da tsohon gidan yarin nan na Kurmawa, wanda aka gina fiye da shekara 100 da suka gabata, zuwa gidan adana abubuwan tarihi. Gidan yarin Kurmawa mai ɗaukar fursunoni 690 kacal, wanda aka gina a shekarar 1910 tun a zamanin Turawan mulkin mallaka a kusa da fadar mai martaba Sarkin...
Shirin Makon Kiwon Lafiyar Uwa da Ɗa (MNCH) a Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ya samu gagarumar nasara, inda mata da yara da dama suka amfana da ayyukan kiwon lafiya kyauta iri-iri. Wannan kamfen na mako guda, wanda Gwamnatin Jihar Kano tare da haɗin gwiwar UNICEF da sauran abokan hulɗa suka tallafa masa, na...
Rahotonni sun bayyana cewa: Har yanzu gwamnatin mamayar Isra’ila ta ki bari an gano kashi 88% na irin laifukan da ta aikata a yakin Gaza ba Jaridar The Guardian ta Birtaniya ta bayyana cewa: Hukumomin mamayar Isra’ila sun boye kusan kashi 88% na binciken laifukan yaki ko cin zarafin da sojojin mamayar Isra’ila suka aikata...
“daidaita farashin ya kasance hanya daya tilo da za a iya amfani da ita wajen tafiyar da harkokin kasuwa da kuma tabbatar da gaskiya,” in ji shi. Edun ya nuna ƙalubale a tsarin biyan ciniki a Nijeriya, tare da lura da cewa har yanzu ana samun yawan hada-hadar kasuwanci ta hanyoyin da ba kamata ba....
Dakarun sojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin Lod na Jaffa da makami mai linzami Dakarun sojin Yemen sun sanar da aiwatar da wani zazzafan harin soji kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye. Dakarun kasar ta Yemen sun yi karin haske a cikin wata sanarwa da suka fitar...
Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya ta Najeriya (NANNM), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ta fara a faɗin ƙasar nan. Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata takarda da shugabanta ƙasa, Haruna Mamman, da sakatarenta, T.A. Shettima, suka sanya wa hannu. Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Jami’ar Umaru Yar’adua...
Kungiyar wasan Taekwondo ta JMI kuma guragu, sun zama zakara a wasan taekwondo gurago sun lashe gasar ta Asia karo na 10 a jere. Kanfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto cewa an gudanar da gasar ne a kasar Malasiya, kuma yan wasa 107 ne daga kasashe 18 suka sami damar halattar gasar...
Bincike a kan zargin da ake wa Hukumar Raya ƙasashe ta Amurka (USAID) da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da na ƙasa da ƙasa game da tallafa wa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP da sauran masu tayar da ƙayar baya a Nijeriya har yanzu bai kammala ba. Kawo yanzu babu wata ƙwaƙƙwarar...
Slovenia ta kasance Ƙasar Turai ta farko da ta ba da sanarwar hana tura makamai zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila Kasar Slovenia ta sanar da haramta musayar zirga-zirgan kayayyakin kasuwanci tsakaninta da haramtacciyar kasar Isra’ila musamman safarar makamai da kayan aikin soji zuwa Isra’ila, inda ta zama kasa ta farko ta Turai da ta dauki wannan...
Ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da iska mai karfi da aka tafka a kwanan nan ya yi sanadin mutuwar mutane 44, yayin da wasu tara suka bace a birnin Beijing, kamar yadda aka bayyana a wani taron manema labarai da ya gudana a yau Alhamis. A yayin taron manema labarai da gwamnatin birnin...
Sojojin Yemen sun sanar da kai wasu zafafan hare-hare guda 3 kan mayakan sojojin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya Rundunar Sojin kasar Yemen ta sanar da cewa: Sojojinta sun kai wasu jerin zafafan hare-hare guda uku da jiragen saman yakin soji marasa matauka ciki, inda hare-haren suka janyo barna a muhimman wurare uku na makiya sojojin...
“Muna kira ga gwamnatin jiharmu da ta kawo mana agaji da gaggawa domin da yawa daga cikin kaburburan da ke makabartar, sun rufta bayan ruwan saman, wannan aikin ya fi karfin mu.” In ji shi. A halin da ake ciki dai, rundunar ‘yansandan jihar Borno ta gaggauta gudanar da tantancewa a wurin tare da...
Adamu ya bayar da hujjar cewa, Sarkin Musulmi ne ke shugabantar daular gargajiya mafi girma a Arewacin Nijeriya, tare da dukkan sarakunan yankin karkashin jagorancinsa na ruhi da al’adu. Ya yaba da shugabancin Sarkin Musulmi Abubakar na tsaka-tsaki, samar da zaman lafiya, da jagoranci na hadin kai. Sun bayyana shi a matsayin mutum...
Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin Olumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa. Sabon shugaban hukumar zai fara aiki a hukumance daga ranar 14 ga watan Agusta, 2025. Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno An...
Dakarun Operation Haɗin Kai da ke Arewa maso Gabas, sun ɗakile wani sabon hari da mayaƙan Boko Haram suka kai a Jihar Borno. Sun kai harin ne yankunan Konduga, Bama da Gwoza. Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu Adadin Falasdinawan da Isra’ila take kashewa a Gaza yanzu ya haura 60,000 ’Yan ta’addan sun...
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ba da shawarar a soke ko kara inganta aikin titin gina hanya mai tsawon kilomita biyar a karamar hukumar Gabasawa. Wannan mataki ya biyo bayan karɓar rahoton da Kwamitin Majalisar kan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci ya gabatar dangane da ambaliyar da ta afku a Zakirai, cikin karamar hukumar ta...
Dubban ‘yan Najeriya magoya bayan kungiyar kwallon kafar ta ” Super Falcon” sun yi bikin samun nasarar da kungiyar tasu ta samu, wasan karshe na samun kofin nahiyar Afirka na kwallon kafa na mata. A wasan da aka yi kafin hutun rabin lokaci, ‘yan wasan kasar ta Moroko sun yi bajinta, inda su ka ci...
Kungiyar yan tawaye M23 wacce take iko da yanki mai yawa a gabacin Democradiyyar Kongo ta bada sanarwan cewa idan gwamnatinn kasar Kongo bada gaggauta sakin fursinonin kungiyar ba, to tana iya kauracewa tattaunawan da za’a gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a watan mai zuwa. Shafin yanar gizo na Africanews ya nakalto babban...
A tattaunawarsa da da LEADERSHIP, Shugaban Kungiyar NULGE na Kasa, Aliyu Haruna Kankara, ya zargi gwamnonin jihohi da shirya wani shiri da gangan na yi wa shari’a zagon kasa, wanda hakan ke kawo cikas ga ci gaban kasa da kuma jin dadin ma’aikatan kananan hukumomi. Kankara, ya kuma yi gargadin cewa; kungiyar za ta iya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Allah ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau da ke jihar Zamfara, Dr Ibrahim Bello rasuwa. Ya rasu da safiyar Juma’a a Abuja yana da shekaru 71, bayan ya sha fama da jinya. Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu An kama budurwa mai shekara 19 da ake zargi...