2025-08-10@09:21:07 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7604

«Janareta»:

    An shawarci sabbin mataimaka na musamman da su kasance masu adalci da gaskiya wajen aiwatar da ayyukansu a ƙaramar hukumar Auyo ta jihar Jigawa. Shugaban ƙaramar hukumar Auyo, Alhaji Binyaminu Ahmad Adamu Kafur ne ya bayar da wannan shawara yayin bikin rantsar da sabbin mataimaka na musamman 69 da aka gudanar a Auyo. Alhaji...
    Shugaban tsangayar Kula da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu A Kwalejin Likitanci Ta Ƙasa (NPMCN), Farfesa Ayodeji Oluwole, ya bayyana hanyoyin da shirin ke bi wajen aiwatar da aikin: ” Wannan horo ya samar wa likitocinmu da fasaha ta zamani, kuma a cikin shekaru biyar, muna sa ran raguwar mutuwar mata masu juna biyu. “Babban...
    Gwamnatin kasar Sin ta mika sabon kason tallafin abinci ga Zimbabwe, a wani mataki na bunkasa ikon kasar na samar da isasshen abinci ga al’ummarta, bayan matsanancin tasirin yanayin El-Nino da ya haifar da fari a shekarar bara. Yayin bikin mika kayan abincin a jiya Alhamis, wanda aka gudanar a birnin Harare fadar mulkin Zimbabwe,...
    Wannan irin jita-jitar tana kokain zana shi da kwatankwacin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani rikici da ya ɓarke ya yi sanadin mutuwar wani manomi mai suna Irmiya Yohanna, mai shekara 40, tare da hallaka shanu da tumaki 39, a ƙauyen Kaduna da ke Ƙaramar Hukumar Bogoro, a Jihar Bauchi. Haka kuma  ’yan sanda sun ceto shanu 249 da aka yi ƙoƙarin kashewa. Obi ya ziyarci Bauchi, ya ba...
    Sin ta ci gaba da tabbatar da matsayinta na babbar kasuwar mutum-mutumin inji masu ayyukan masana’antu a duniya, wanda ta rike tsawon shekaru 12, kuma ita ce babbar kasa mai kera mutum-mutumin inji a duniya. Sin daya ce daga cikin kasashe masu samar da mutum-mutumin inji dake sahun gaba a duniya, kuma ana sa ran...
    Dabbobi 199 da aka sace (shanu 161 da tumaki 68) Motoci guda 3 da aka sace Babura 2 da ake zargi an sace su Miyagun ƙwayoyi da yawa ciki har da tabar wiwi Wayoyin wutar lantarki da aka lalata DSP Aliyu ya yaba wa gwamnatin Jihar Katsina da al’ummar jihar saboda haɗin kai da suka...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce ma’aikatar harkokin wajen kasar, da ofishin jakadancin kasar a Philippines, sun gabatar da korafi da babbar murya dangane da kalaman da aka jiyo jagoran Philippines na yi game da batun yankin Taiwan na Sin. Kakakin wanda ya bayyana hakan a Juma’ar nan, ya ce, yayin ziyarar da...
    Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ziyarci Jihar Bauchi tare da ba da tallafin Naira miliyan 15 don tallafa wa harkar ilimi. Obi, ya sauka a filin jirgin sama na Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe 9:40 na safe. Sojoji sun yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta a Borno ’Yan...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a yi dukkan kokarin bincike da ceto da tunkarar ambaliya da ayyukan agaji, bayan aukuwar ambaliya a yankin tsaunika tun daga jiya Alhamis, a lardin Gansu na arewa maso yammcin kasar Sin. Zuwa karfe 3 na rana a yau Juma’a, ibtila’in ya yi sanadin mutuwar mutane 10 da...
    A cewarsa, wannan gamayyar ta faro ne sama da wata 18 da suka wuce, wadda kuma an samar da ita ne saboda fargabar da ake da ita a ƙasar na kar a kasance ana da jam’iyya ɗaya tilo a Nijeriya. Lukman, wanda kuma shi ne tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma kafin...
    Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya tattauna batutuwa da dama a wata zantawa ta wayar tarho da shugaban Rasha Vladimir Putin. Ofishin shugaban kasar Afirka ta Kudu ya ce, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, shugaban kasar ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan rikicin Ukraine da kuma...
    Wannan hukunci ya fito daga kwamitin ɗa’a da ladabtarwa na UEFA, kuma zai fara aiki nan take a wasan Barcelona na gaba a Turai. Barcelona za ta fara sabuwar kakar wasa ne da RCD Mallorca ranar Asabar, 15 ga watan Agusta. Za su ci gaba da fafutukar lashe kofuna a ƙarƙashin sabon kocinsu, Hansi Flick....
    Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ta kai hare-hare ta sama a yankin Rann, wani gari da ke Jihar Borno, wanda ake zargin ya zama mafakar ’yan ta’adda. Wannan aiki na cikin shirin Operation Haɗin Kai, kuma ya yi sanadin hallaka ’yan ta’adda da dama. ’Yan damfara 2 sun shiga hannun ’yan sanda a Yobe...
    A cikin fim din “Dead to Rights”, an ce, “Mu tuna da jinin da aka zubar a yakin, don mu kiyaye hasken da muke da shi yanzu.” Abin haka yake, yau mun waiwayi abubuwan da suka faru a tarihi, ba don neman ci gaba da kiyaya da juna ba, a maimakon hakan, muna son kira...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da damfarar mutane a wajen cirar kuɗi a ATM. Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkareem, ya ce an kama Umar Abubakar mai shekara 24 da Abdulaziz Mohammad mai shekara 25 daga Ƙaramar Hukumar Kumbotso, a Jihar Kano. PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon...
    Jam’iyyar PDP ta ce za ta ɗauki mataki kan wasu mambobinta da ke aikata abubuwan da ke kawo wa jam’iyyar koma baya. Shugabancin jam’iyyar ya fi damuwa da mambobin da ke bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu don sake tsayawa takara a zaɓen 2027. Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma...
    Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce kasarsa ta kammala shirin amfani da sojoji wajen mamaye ilahirin Zirin Gaza na Falasdinawa domin ya koma karkashin ikonta. A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar da safiyar Juma’a, Netanyahu ya tabbatar da shirin inda ya ce, “Sojojin Isra’ila za su shirya karbe iko da Zirin Gaza baki...
    Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Zama Sakatariyar Kungiyar Yaƙi Da Cutar Daji “Ta hanyar gudanar da ɗimbin ayyukan noma a Gandun Dazukan wannan ƙasa, zai yi matuƙar ƙara yawan ayyukan masana’antun ƙasar da ke sarrafa amfanin gona domin fitarwa zuwa kasuwannin duniya,...
        Saƙo Daga Hassana Abubakar Jihar Bauchi: Ina gaida iyayena, sai ƙawayena Anisa Aliyu, Farida Aliyu, Sadiya Garba da sauransu. Sai ‘yan’uwa na gida Maryam Abubakar, Khadija Abubakar, Zainab Abubar, Habib Abubakar, Zahraddeen Abubakar, Sani Abubakar, Anty Karimatu, Kawu Haruna, Yagana, da fatan sun yi juma’a lafiya.   Saƙo daga Maryam Shitu Jihar Kano:...
    A wannan Juma’a ne Australia ta bukaci Isra’ila da ta janye shirinta na mamaye yankin Zirin Gaza, inda ta yi gargadin cewa hakan zai kai ga barkewar matsaloli na jin kai a yankin. Ministar harkokin wajen Australiya Penny Wang a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: Australia ta yi kira ga Isra’ila da...
    Majalisar ministocin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta amince da kudirin firaminista Benjamin Netanyahu na mamaye birnin Gaza, wanda ke zama matakin farko na wani gagarumin farmakin soji da ka iya kaiwa ga mamaye daukacin zirin Gaza, a cewar wani babban jami’in Isra’ila. Matakin ya biyo bayan tattaunawa sama da sa’o’i 10 da aka shafe ana yi...
    Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Abubakar, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira tiriliyan daya da rabi don gina layin dogo na zamani domin saukaka harkar sufuri a cikin birnin Kano. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Kano, inda ya ce aikin zai saukaka...
    Shugaban Sin Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Takwaransa Na Rasha Sakamakon Hadarin Jirgin Saman Fasinja Da Ya Auku A Kasar An Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da 30 A Wani Harin Jirgin Sama A Wurin Daurin Aure A Zamfara A cewar Goɓspend, an kashe maƙudan kuɗaɗe a ƙarƙashin mulkin Shugaba Tinubu a tsakanin Afrilu da...
    Sayyid Abdul-Malik al-Houthi, shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen ya ja kunnen Amurka da HKI kan kara tada hankali a yankin Asia ta kudu. Kamfanin dillancin labaran IP ya nakalto shugaban yana fadin haka a jiya Alhamis, a lokacinda yake jawabi ga mutanen kasar jawabinsa na mako mako.  Sayyid Huthi ya bayyana cewa kasashen biyu...
    Nijeriya ta kasance ƙasa ce, mai girman gaske, wadda kuma ‘yan ta’adda masu iƙirarin jihadi, Al-kamar irinsu; Al- Ƙaeda da ISIS da ke aikata ayyukan ta’addancinsu a yankin Sahel ke kutsowa cikin ƙasar, domin aikata ta’addanci. Bugu da ƙari, ba tun yau ne, wasu ƙwararru a ɓangaren tsaro na ƙasar nan, suke yin gargaɗin cewa,...
    Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da dokoki guda biyu masu muhimmanci da nufin ƙarfafa harkar yawon buɗe ido da hanzarta gudanar da shari’a a faɗin jihar. Shugaban majalisar, Yusuf Dahiru Liman, ne ya sanar da amincewar majalisar  yayin zaman, ta wanda aka gudanar a harabar majalisar da ke Kaduna.   Dokar farko mai taken...
    Sakamakon kama Mu’azu Ɓarga, yanzu haka abokan ta’asar tasa sai tsallakewa suke domin tserewa kamun rundunar ‘yan sanda, duk da gudun da suke rundunar na ci gaba da farautarsu har kuma an samu nasarar ƙara damƙe mutane biyu cikin sama da mutane arba’in da Ɓarga ya bayyana wa ‘yan sanda. Wannan tasa a ranar Juma’ar...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran abbas Aragchi ya rubutawa babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ta OIC Hussain Ibrahim Taha, da kuma tokwarorinsa na kasashen Saudiya da Turkiya, Faisal bin Farhan da kuma Hakan Fidan wasiku dangane da bukatar kasashen kungiyar su gudanar da taron gaggawa kan abinda ke faruwa a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP...
    A dai dai lokacinda ake shirin juya yin 40 na shahadar Imam Hussain (a) jikan manzon All..(s) Iraniyawa fiye da miliyon 1.2 suka shiga kasar Iraki daga Iran don halattar wannan makokin. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana ncewa hotunan bidiyo na jami’ann tsaro sun bayyana cewa a lardin Ilam wacce ta...
    Sayyid Abdul-Malik al-Houthi, shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen ya ja kunnen Amurka da HKI kan kara tada hankali a yankin Asia ta kudu. Kamfanin dillancin labaran IP ya nakalto shugaban yana fadin haka a jiya Alhamis, a lokacinda yake jawabi ga mutanen kasar jawabinsa na mako mako.  Sayyid Huthi ya bayyana cewa kasashen biyu...
    Kungiyar Hizbullah da Amal na kasar Lebanon sun bayyan amincewar gwamnatin kasar Lebanon wajen kwance damarar kungiyar hizbullah wani abu ne wanda kasashen waje suka fada masu su yi haka, wanda ya yi watsi da diyaucin kasar Lebanon da kuma cikekken iko a kan kasar. Labarin ya kara da cewa shuwagabannin kasar ta Lebanon sun...
    Wa jirgin sama na daukar marasa lafiya ya yi hatsari ya kuma fadi a  kan gidajen mutane a kusa da birnin Nairobi babban birnin kasar ta Kenya  a jiya Alhamis.AMREF Flaying Doctor,  jirgi ne karamin samfurin XLS ya tashi daga tashar jiragen sama na Nairobi da nufin zuwa wasu yankuna a kasar Somaliland ya fadi...
    Daruruwan mazauna kauyen Jimrawa da ke karamar hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zangar lumana a Gusau babban birnin jihar kan matsalar tsaron da ta addabe su. Hakan na zuwa ne mako biyu bayan mazauna Gusau din su ma sun yi irin wannan zanga-zangar kan cewa ’yan bindiga sun kashe sama da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci ‘yan takara kan dauki alkawura. Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka? NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma DAGA LARABA: Me Ke...
    Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa yara miliyan 11 da ke ƙasa da shekaru biyar a Najeriya na fama da rashin abinci mai gina jiki, lamarin da ke ƙara yiwuwar wani yanayi mai barazana ga rayuwa saboda rashin kuzari. Shugaban Ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahma Rihood Mohammed Farah,...
    Kudirin gyaran dokar  fansho da sauran fa’idodi na tsaffin jami’an gwamnati ya wuce karatu na biyu a zauren Majalisar Dokokin Jihar Jigawa. Wakilin mazabar Malam Madori, Alhaji Hamza Adamu Ibrahim wanda shi ne shugaban Kwamatin kasafin kudi na majalisar, shi ne ya gabatar da wannan kudurin, ya kuma samu goyon bayan wakilin mazabar Guri Alhaji...
    Sun kara da cewa,”A cikin wannan lokaci, mataimakin kyaftin na yanzu, Ronald Araujo ne zai karbi aikin kyaftin din, Ter Stegen ya buga wa Barcelona wasanni sama da 400 tun lokacin da ya koma kungiyar daga Borussia Monchengladbach a shekara ta 2014, ya lashe manyan kofuna da suka hada da gasar zakarun Turai da kuma...
    Ma’aikatar kudi ta kasar Sin, ta ce tallafin gwamnati na samar da ilimi kyauta ga daukacin daliban dake ajin karshe a makarantun share fagen shiga firamare a kasar zai amfani mutane kusan miliyan 12.   Yayin wata ganawa da manema labarai a yau Alhamis, mataimakin ministan ma’aikatar kudin kasar ta Sin Guo Tingting, ya ce...
    Madugun adawa a Nijeriya, Atiku Abubakar ya bukaci a gaggauta sakin fitaccen ɗan gwagwarmayar, Omoyele Sowore da ke tsare a hannun ’yan sandan kasar. Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriyar wanda ya yi Allah-wadai da lamarin ya ce abin kunya ne cin zarafi da tawagar sa ido ta sufeto janar na ’yan sandan ƙasar suka yi wa...
    Mazauna kauyuka akalla 30 daga Dan-Isa da Kagara dake karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara, sun mamaye gidan gwamnati dake Gusau babban birnin jihar domin nuna takaicinsu kan yadda rashin tsaro a yankin na su “yaki ci yaki cinyewa” a ranar Alhamis. Masu zanga-zangar da suka hada da mata da kananan yara suna dauke da...
    Alkaluman kididdiga na hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna yadda cikin watanni 7 na farkon shekarar nan ta 2025, jimillar darajar cinikayyar kayayyaki ta kasar Sin ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 25.7, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 3.5, wanda hakan ya nuna karuwar kashi 3.5 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokaci na...
    Fitaccen matashin nan mai barkwanci, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Ɗan Bello, ya yi rashin mahaifinsa a yammacin wannan Alhamis din. Matashin lauyan nan ɗan gwagwarmaya, Abba Hikima, ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe...
    Bugu da kari, a baya bayan nan ma jaridar Financial Times, ta bayyana yadda a yanzu haka adadin hajojin da ake shigarwa Amurka daga sassan duniya daban daban suka ragu zuwa kaso 13 bisa dari, sabanin kaso kusan 20 bisa dari da kasar ke shigowa da su a tsawon shekaru 20 da suka gabata. Kamar...
    Wasu daga cikin tsoffin kansilolin da suka halarci tattakin sun bayyana goyon bayansu ga gwamna Abba Kabir Yusuf.   A nasa jawabin, Dahiru Yusuf daga Gezawa kuma tsohon kansila ya ce, shi ma yana cikin wadanda tsohuwar gwamnatin Ganduje ta hana hakkinsu, don haka maganar Abdullahi Abbas ba gaskiya bane! “Sun ga gwamna Abba zai...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini kan rasuwar Sadiq Gentle, wani hadiminsa kan harkokin yada labarai a Ma’aikatar Tarihi da Al’adu ta jihar, wanda wasu da ake zargi ’yan daba suka kai masa harin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a Facebook, ta...
    Ya kuma lura da cewa, tattaunawa da ‘yan bindiga a wasu jihohin suka yi ya kara ta’azzara satar shanu, inda ya ce, Sam hakan, ba za a amince da shi ba.   Dangane da ta’azzarar rashin tsaro, Gwamna Bago ya ce, za a nemi taimako daga shugaba Bola Tinubu da mai bai wa shugaban kasa...
    Manoman gundumar Ɗan Isa da ke Ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara sun ce ’yan bindiga sun yi musu barazana a wannan damina ta bana. Da yake tabbatar da hakan ga Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar tarho, Hakimin unguwar Malam Hassan Yarima, ya ce kowane ƙauyuka 35 da ke ƙarkashin gundumarsa ya...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Amurkawa sun yi kuskure idan suna tunanin cewa hari kan cibiyoyin makamashin nukiliya zai canza matsayin Iran ko kuma ya sa ta ja da baya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Dole ne a fara wani sabon mataki na dangantaka tsakanin Iran da hukumar kula...
    Alummar duniya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan furucin firaministan Israila na fadada mamaya a Gaza. Sakamakon wani nazarin jin raayin jamaa da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar ya nuna cewa, kaso 86.6 na wadanda suka bayar da amsa sun bayyana adawa mai karfi da matakin firaministan, suna masu kira da...