2025-08-03@12:51:33 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1816
«Yan Nijeriya»:
Sakamakon rikicin siyasa a jihar, ne ya sanya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara, mataimakinsa, da dukkanin ‘yan majalisar dokar Jihar Ribas na tsawon watanni shida. Haka kuma, Shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas tare da naɗa mai riƙon kwarya da zai shugabanci jihar na tsawon wannan lokaci. Daga...
“Amma idan yanzu aka sake bai wa Arewa takara, wannan tsari tsakanin Arewa da Kudu zai ruguje.” Wike, wanda tsohon gwamnan Jihar Ribas ne, yana daga cikin fitattun jiga-jigan PDP da ke goyon bayan daidaito da karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. A baya dai, rikici...
Babban hafsan hafsoshin sojojin JMI ya bayyana cewa sojojin kasar musamman sojojin ruwa a shirye suke su shigaba yaki dank are kasar a ko yauce, ya kuma kara da cewa idan makiya sun yi wani kuskure zasu yi nadamar hakan. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Manjo Janar Mohammad Hussain Bakiri yana...
Gwamnatin kasar Iran ta yi kakkausar suka ga gwamnatin HKI kan hare-haren da ta kaiwa wani sansanin yan gudun hijira a gaza inda ta kashe ko takai mutanen da dama ga shahada, daga ciki har da mata da yara jarirai. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran...
Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke hukuncin ratayewa ga wani mutum da ta samu da laifin kashe abokinsa saboda hula. Kotun da ke zamanta a kan titin Miller ta yanke wa mutumin mai suna Adamu Isma’ila Arzai hukuncin ne bayan an gurfanar da shi kan zargin soka wa abokinsa mai suna Auwal Shehu Kabara wuƙa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wasu ’yan Najeriya sun yi Allah-wadai da umarnin da Hukumar Kula da Harkar Wutar Lantarki a Najeriya (NERC) ta bai wa kamfanonin rarraba wutar da su biya diyya ga abokan huldarsu da ke rukunin Band A. NERC ta bai wa kamfanonin wannan umarni ne sakamakon rashin samar wa...
Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta amince da kashe naira biliyan 2 da miliyan 300 domin sayo na’urar binciken cututtukan zuciya (cardiac catheterization machine) a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato. Ministan Lafiya da Jin Daɗin Al’umma, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai bayan zaman...
Mataimakin firaminsitan kasar Sin He Lifeng, ya gana da babbar jami’ar hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, a daren jiya Lahadi a Geneva. Yayin ganawar tasu, He ya ce, kamata ya yi mabambantan bangarori su daidaita bambancin ra’ayi da takaddama bisa shawarwari, kuma cikin adalci karkashin ka’idar WTO. Haka kuma, a hada...
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata taba yin watsi da haƙƙinta na makamashin nukuliya na zaman lafiya ba a kowane yanayi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Iran da gaske take yi wajen gudanar da tattaunawa domin neman cimma matsaya da zata gamsar da kowane bangare, amma neman yin watsi...
Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da mutane biyar yayin da suka kai hari ana tsaka da cin kasuwa a ƙauyen Dogon Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Wase ta Jihar Filato. A cewar mazauna, maharan sun wawushe kayayyaki a shaguna inda suka yi awon gaba da kayan abinci da magunguna masu tarin yawa. Jami’ar...
Wani hari kan gidan yarin Al-Obeid yayi sanadiyyar mutuwa da jikkatan mutane da dama a kasar Sudan Ministan al’adu da yada labarai, kuma kakakin gwamnatin Sudan, Khaled Al-Aiser, ya tabbatar da cewa: Mutane 20 ne suka mutu, yayin da wasu 50 na daban suka jikkata a wani harin da ‘yan ta’addar Daglo na kungiyar Rapid...
Wannan rangwamen farashin duk da cewa ba a hukumance yake ba, amma ya bai wa kwastomomin Dangote damar siyar da mai akan farashi mai rahusa a tsakanin Naira 830 zuwa N835 kan kowacce lita. Wannan nasarar ta zo ne makonni kadan bayan da matatar ta yi ragin farashi sau biyu a jere a cikin...
Kungiyar Kurdawan Turkiya PKK ta sanar da cewa za ta ajiye makamanta ta kuma rusa kanta. Kamfanin dillancin labarum “Furat” mai kusanci da kungiyar ta PKK, ya nakalto cewa; Kungiyar ta yanke zartar da wannan matakin ne a yayin taron da ta yi kaso na 12 da ta yi kwanaki kadan da su ka gabata....
Ɗan Majalisar Wakilai, Honorabul Yusuf Gadgi, ya yi iƙirarin cewa mayaƙan Boko Haram sun ƙwace makaman sojoji da kuɗaɗensu ya kai tiriliyoyin naira a hare-haren da kungiyar ta kai kan sansanonin soji a yankin Arewa maso Gabas. Gadgi ya bayyana haka ne a yayin da yake tsokaci kan ƙudirin da Honorabul Ahmed Satomi daga Jihar...
Sojojin HKI sun ci gaba da kai hare hare kan birane da garuruwan yankin yamma da kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, hare-haren jiya sum sun fi maida hankali ne a garin Tulkaram da kuma sansanin yan gudun hijirar yankin A wannan karomma sojojin HKI sun bada umurni ga...
Kungiyar Hamas wacce take iko da yankin Gaza, ta bada sanarwan cewa a shirye take ta saki fursina mai suna Edan Alexander wanda yake da jinsiyar Amurka da HKI don bude kofa ga tattaunawar tsagaaita wuta a gaza da kuma bude kofar rafa don samar da kayakin abicni a gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na...
Ya ce: “A yau ni ne Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Nijeriya. Ba kawai ɗan watsa shirye-shirye ba ne ni, ni ne babban mai magana da yawun gwamnatin Nijeriya. “Don haka za ka ga yadda burin da ake ganin kamar an kashe shi shekaru da dama da suka wuce, ya dawo...
Wasa na uku da kungiyoyin suka hadu a bana shi ne wasan karshe na kofin Copa Del Rey inda nan na Barcelona ta sake samun nasarar doke Madrid da ci 3-2, a wannan karon kocin Madrid Carlo Ancelotti na fatan ganin kungiyarsa ta samu nasara akan Barcelona duba da cewar wannan ka iya zama wasan...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta jadada cewa ko kadan sojojin kasar ba su keta tsagaita wutar yaki da Indiya ba. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen ta Pakistan ta fitar ta ce; kasar tana ci gaba da aiki da tsagaita wutar yaki wacce aka sanar da ita, kuma sojojin kasar sun kai...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta iran, Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Tsagaita wutar yakin da aka yi a tsakanin Indiya da Pakistan abin yin maraba da shi ne, sannan kuma ya kara da cewa; Ya zama wajibi kasashen biyu su yi amfani da wannan dama domin rage tashin hankali a yankin da...
Manistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Saudiya Faisal Bin Farhan a birnin Jeddah inda bangarorin biyu suka tattauna kan al-amuran da suka shafi yankin, musamman batun Falasdinawa da kuma halin da suke ciki musamman a yankin gaza. Inda HKI take kashesu da yuwan, sannan tana ci gaba da...
Shugaban kasar Rasha Vladimir Puttin Ya gana da tokwaransa na kasar Masar Abdul alfattah Asisi bayan halattar bikin cika shekaru 80 da nasarar da kasar Rasah ta samu kan sojojin Nazi a yakin duniya na biyu wanda aka gudanar a birnin Mosco. Shafin yanar gizo na labarai ya bayyana cewa harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Dole ne duniya ta dauki matakin kalubalantar laifukan ‘yan sahayoniyya da magoya bayansu kan zaluncin Gaza Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, yayin da yake karbar bakwancin dimbin ma’aikata a yau Asabar, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan “Makon ayyuyka da Ma’aikata”...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Ce Kafa Hujja Da ‘Yan Tawaye Kan Iran Yankewar Kauna ce Ga Makiyanta
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Amfanin da fira ministan gwamnatin mamaya ya yi da ƙungiyar ta’addanci babbar alama ce ta cikakkiyar yanke ƙauna Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Matakin da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dauka na yi amfani da wata karkatacciyar kungiyar...
Shugaban kasar Amurka ya sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Indiya da Pakistan Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta nan take, wanda Amurka ta shiga tsakani wajen kulla ta. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaban Amurka...
Da safiyar yau Asabar Falasdinawa 7 sun yi shahada sanadiyyar harin da HKI ta kai a yankin Gaza. Sojojin HKI sun kai harin ne a kan sansanin ‘yan hijira na unguwar ” al-Sabrah” a cikin birnin Gaza, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 5 a iyalai daya na Dulaibh. Shahidan su nel Saqar Ahmad...
Shugaban kungiyar ya yi magana Ibrahim Yusuf Babayo,Shugaban kungiyar Miyetti Allah masu kiwon dabbobi na kasa ya bayyanawa jaridar karshen mako cewar dukkan hare- haren da ake kaiwa dabbobin da kuma kashesu an sanar da jami’an tsaro daban- daban,da suka hada da Kwamanda na rundunar soja ta,3 kuma kwamandan Operation Safe Haben (OPSH), Manjo- Janar...

ECOWAS Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasar Tattalin Arzikin Afrika Ta Yamma – Kwamred Bishir Dauda
Na yi wannan wannan ziyara ne saboda shaukin da nike da shi a kan abin da ya shafi kishin kasata Nijeriya, da kuma neman hadin kan kasashen Afirika ta yamma mu zama tsintsiya madaurinki daya,da son zaman lafiya da ci gaban Dimokaradiyya. Kazalika, na yi wannan rangadi ne domin murnar cikar kungiyar ECOWAS shekara 50...
Duba da yadda yanayin muhalli yake, zai ba da dama wajen rage fuskantar sauyin yanayi tare da inganta kiwon lafiyarsu, abincinsu da kuma ingancin ruwan shansu. 2- Fashin Baki Kan Abin Da Zai Iya Afkuwa A Wajen Kiwon Su: Ga wanda zai fara wannan kiwo, ana so ya zabi wajen da ya dace da kuma...
Janar Hussain Salami babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ya kaddamar da sabon sansanin jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa na karkashin kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Janar Salami yana cewa, wadannan jiragen yakin da ake sarrafasu daga nesa, suna iya daukar hotunan jiragen...
Daga ranar 7 zuwa ta 8 ga watan Mayun nan, tawagar likitocin kasar Sin a kasar Saliyo karo na 26 ta shiga cikin yankunan karkara da dama na kasar Saliyo, inda ta kammala ayyuka hudu na bayar da jinya kyauta cikin kwanaki biyu, tare da bayar da hidimar jinya ga mazauna kauyakan da ma’aikatan kamfanoni....
Wasu daliban jami’a da ke shirin tafiyar aikin yi wa kasa hidima NYSC sun rasu a wani harin da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne suka kai musu a yankin Gbarabtoru-Ekpetiama, Karamar Hukumar Yenagoa. Matasan biyu da suka kammala karatunsu a Jami’ar Niger Delta (NDU), Amassomma, sun rasu ne bayan da gungun wasu mutane da...
Kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage ƙarar tuhumar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello kan zargin badaƙalar kuɗi da hukumar EFCC ta gabatar zuwa ranakun 26, 27 ga Yuni da 4, 5 ga Yuli don yanke hukunci kan buƙatar masu gabatar da ƙara ta “yi wa shaidar tambayoyi” da kuma ci gaba da shari’ar....
Matsalar wutar lantarki a asibitoci a Najeriya ta jefa marasa lafiya cikin halin ni-’yasu, lamarin da ke kara ta’azzara halin da majinyata ke ciki, har ta kai ga asarar rayuwa. Rashin wuta ya yi sanadin mutuwar jariri a cikin wata mai juna biyu, wata ta yi awa 15 tana jiran a yi mata tiyatan haihuwa,...
Matsalar wutar lantarki a asibitoci a Najeriya ta jefa marasa lafiya cikin halin ni-’yasu, lamarin da ke kara ta’azzara halin da majinyata ke ciki, har ta kai ga asarar rayuwa. Rashin wuta ya yi sanadin mutuwar jariri a cikin wata mai juna biyu, wata ta yi awa 15 tana jiran a yi mata tiyatan haihuwa,...
Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bukukuwan cika shekaru 80 da cimma nasara a yakin kishin kasa na tsohuwar Tarayyar Soviet. An gudanar da faretin soja na ranar samun nasara, wanda ke ayyana cika shekaru 80 da samun nasara a yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet ne a birnin Moscow. Shugabanni daga...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukumomi a jihar Yobe sun ɗora alhakin ƙazancewar matsalar tamowa a kan rikicin Boko Haram da rashin shayar da jarirai nonon uwa yadda ya kamata da kuma gurɓacewar harkar kiwon lafiya, da sauran su. Bayanin hakan na zuwa ne bayan Babban Jami’i mai Kula da Ayyukan Jinƙai na...
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-husy ya bayyana cewa kisan kiyashin da HKI take yi wa Falasdinawa a tsawon watanni 19 a jere, shi ne laifi mani muni akan bil’adama da ya faru a cikin karni daya. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma ce, abinda ya kara munin wannan laifin shi ne yadda...
Hukumar kare hakokin masu sayayya ta ta kasa tare da haka da Hukumar Kare Data ta kasa NDPC ne, suka gudanar da binciken na watanni 38. A cikin binciken na su, sun bayyana yadda ake take saba ka’ida tare da take dokar kasa da kuma take hakkin ‘yan Adama na kasa da kasa. ...
Babban Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya ƙaddamar da Ƙwararrun Jami’an tsaro da za su kare makarantu a Bauchi, Egbetokun ya ƙaddamar da tawagar ne a ranar Alhamis a Bauchi. A wajen ƙaddamar da taron masu ruwa da tsaki na ‘Saɓe Schools’ a ɗakin taro na otal ɗin Hazibal. Ya ce,...
Tsohon ministan kudin kasar Amurka John Connally ya ce, dala kudi ne na Amurka, amma matsala ce ga sauran kasashen duniya. Yanzu haka tsarin kudin na haifar da karin radadi ga kasashe daban daban, sakamakon matakan kasar Amurka na kashin kai, lamarin da ya sanya dimbin kasashe neman kauracewa tsarin dalar Amurka. Misali, a rubu’in...
Shugaban kasar Rasha Vladimit Putin ta tokwaransa na kasar China Xi Jinping sun tattauna a birnin Mosco a yau Alhamis, inda kasashen biyu suka kara dankon zuminci a tsakaninsu, da fatan zasu bukasa harkokin kasuwanci da ci gaba a tsakaninsu nan da shekara ta 2030. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa...
Karamar Hukumar Birnin Kudu ta nuna gamsuwa da yadda aikin tantance yan fansho ya gudana a yankin. Shugaban Karamar Hukumar, Dr Builder Muhammed Uba ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin jami’an gudanar da aikin tantance yan fanshon jim kadan da kammala aikin a sakatariyar Karamar hukumar. Yace karamar hukumar ta gamsu...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya shekara arba’in zuwa sama ya san irin tarbiyyar da ya samu daga wurin iyayensa a da, da irin mu’amalar da ke tsakaninsa da iyaye da kuma irin shaƙuwar da ke tsakanin ’ya’ya da iyaye. A yanzu kuwa, abubuwa sun canza daga yadda aka san su,...
“Duk da cewa, ba zan iya yin cikakken bayani dangane da sabbin dabarun da muka dauka ba. Amma mutanen Yobe su kwantar da hankalinsu kuma abubuwa za su inganta.” Har ila yau, ya yi karin haske dangane da wasu muhimman matakan da za a dauka don magance rashin tsaro a jihar, ciki har da...
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta bankaɗo wata haramtacciyar masana’antar man gyaɗan bogi, tare da cafke mutane uku da ake zargin suna da hannu a harkar. Wannan samame da jami’an sashen leƙen asiri na rundunar suka gudanar ƙarƙashin jagorancin SP Sani Bello, ya gudana ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar ranar 5 ga Mayu...
A jiya ne jakadan Sin a Najeriya Yu Dunhai ya gana da ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar. Jakada Yu ya bayyana cewa, ganawar da ta gudana tsakanin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da mista Tuggar a kasar Brazil a baya-bayan nan, ta aike da sako mai karfi cewa, Sin da Najeriya na...
Rundunar sojan Ruwan Amurka ta sanar da cewa; Jirgin sama samfurin F-18 wanda kudinsa ya kai dalar Amurka miliyan 67 ya fadi akan jirgin dakon jiragen ruwa na ” USS Harry Truman” a tekun “Red Sea”. Jaridar ” Washington Post” ta buga labarin dake cewa; Jirgin ta fado ne a lokacin da yake kokarin sauka...
A yau Laraba kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty Interantional” ta fitar da rahoto da a ciki ta yi kira ga HKI da ta kawo karshen shirinta na korar Falasdinawa daga Gaza da karfi, tare da cewa; Har yanzu Isra’ilan tana ci gaba da tafka laifukan yaki a Gaza da yi wa mutane kisan kiyashi.”...
“Dole ne mu daina tallata miyagun ayyukan ‘yan ta’adda. Dole ne mu cire su daga jerin shafukan manyan labarai na jaridunmu, mu rahoto ayyukansu a matsayin masu aikata laifuka, sannan mu kore labaran karya.” Ministan ya jaddada cewa, kungiyoyin ta’addanci da masu aikata laifuka sukan yi amfani da kafafen yada labarai da shafukan sada...