Trump ya yi barazanar korar Gwamnar Babban Bankin Amurka
Published: 27th, August 2025 GMT
Shugaba Donald Trump, ya yi barazanar sauke Lisa Cook, Gwamnar Babban Bankin Amurka (Federal Reserve), yana mai sukar yadda ake tafiyar da harkokin bankin, musamman batun bayar da bashi da tsare-tsaren lamuni.
A wata sanarwa da fadar White House ta fitar, Trump ya zargi Cook da gabatar da “bayanan ƙarya” kan sharuɗan bayar da lamunin gidaje (mortgage), yana mai cewa hakan ya jefa dubban Amurkawa cikin wahala sakamakon hauhawar kuɗin ruwa da kuma tsadar bashi.
Sai dai Lisa Cook ta mayar da martani da cewa shugaban ba shi da ikon sauke ta daga muƙamin da take riƙe da shi, saboda dokar da ta kafa Babban Bankin Amurka ta tanadar da cikakken ’yanci ga ’yan kwamitin gudanarwarsa.
Ta sha alwashin cewa za ta ci gaba da gudanar da aikinta ba tare da wani ɗar-ɗar ba, tana mai cewa manufarta ita ce kare tattalin arziƙi da talakawan ƙasar.
Cook ta yi suna tun lokacin da tsohon shugaban Amurka, Joe Biden, ya naɗa ta a shekarar 2022, inda ta zama mace baƙar fata ta farko ’yar asalin Afirka da ta taɓa zama mamba a kwamitin gudanarwa na Federal Reserve.
Wannan naɗin ya samu yabo daga masu fafutikar kare ’yancin mata da ’yan tsiraru, waɗanda suka ce hakan ya nuna ci gaba a fannin da mata ba su da yawa.
Sai dai tun bayan dawowar Trump kan mulki, gwamnar ta fuskanci matsin lamba daga sabuwar gwamnatin, wacce ke sukar manufofin Babban Bankin musamman kan hauhawar farashin kaya da matsalar gidaje.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Syria: Adadin mutanen da suka mutu a harin Isra’ila a yankin Damascus ya kai 5 August 27, 2025 An Kammala Taron Iran Da E3 A Geneva August 26, 2025 Iran Ta ce Zata Rama Kan Korar Jakadanta Daga kasar Australia August 26, 2025 Najeriya: Jirgin Kasa tsakan Abuja da Kaduna Ya Sauka Kan Layin Dogo August 26, 2025 Iran A Shirye Take Ta Hada kai Da Pakistan Don Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci August 26, 2025 An Kashe Mutum Guda A Harin Isra’ila (HKI) A yankin Duddan Golan Na Siriya August 26, 2025 Jagora: Yahudawan Sahayoniyya Sune Mafi Kyamar Al’umma A Duniya Saboda Muggan Halayensu August 26, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Tarihi Ba Zai Yafe Jinkirin Yin Allah Wadai Da Bala’in Gaza Ba August 26, 2025 Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Tun Bayan Barkewar Yaki Da Iran Babu Wata Hulda Tsakaninta Da Amurka August 26, 2025 Makami Mai Linzamin Sojojin Yemen Ya Zame Mafarki Mai Firgitarwa Ga ‘Yan Sahayoniyya August 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3
Gwamnatin kasar Iran ta sanar da ranar 30 ga watan nuwambar kowacce shekara a matsayin ranar kasa ta tsibirin Abu Musa tumbu babba da tumbu karami da ta karbo daga hannu birtaniya a shekaru da suka gabata, wanda yayi daidai da 9 ga watan Azar na kalandar iraniyawa .
Tsibiran guda 3 da ake takaddama akansu Abu musa da tunbu babba da karami suna yankin tekun fasha ne tsakanin mailand na iran da kuma hadaddiyar daular larabawa, tsibbiran wani bangare ne na kasar iran tun karnoni da suka gabata da ke cike da abubuwa da suka safi doka da tarihi a iran da kuma kasa da kasa.
Iran ta jaddada cewa dukkan wadannan tsibirai guda 3 wani bangare na kasarta da babu tantama akai,don haka ta yi kira ga kasashen larabawa da su guji daukar duk wani mataki akai da zai iya cutar da dangantakar dake tsakaninsu.
A ranar 30 ga watan nuwambar shekara ta 1971 ne dakarun birtaniya suka janye daga tsibiran kuma kwana biyu kafin kafa hadaddiyar daular larabawa a hukumance aka dawo da ikon mallakar tsibiran ga kasar iran bisa doka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci