2025-05-01@02:47:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 148

«a Arewa Maso Gabas»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Cibiyar Bunƙasa Ayyukan Bincike za ta gudanar da gangami domin nazarin dokokin da suka shafi zamantakewar Musulmi a jihohin da ta ke aiki, domin inganta haƙƙoƙin mata da ƙananan yara. Shugaban tawagar cibiyar, Dokts Taofik Abubakar daga Jami’ar Bayero Kano ne, ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da suka kai wa Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, a fadarsa da ke Zariya. Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan Kano NAJERIYA A YAU: Yadda Azumi Ke Inganta Lafiyar Jiki Dokta Taofik, ya ce sun je fadar ne, domin neman albarka da shawarwari kan hanyoyin magance cin zarafin mata. Ya kuma bayyana cewa cibiyar ta ɗauki nauyin malamai da limamai zuwa Jami’ar Al-Azhar da ke Masar...
    Bankin Raya Afirka ya sanar da wasu kasashe 10 da ya ce, su ne tattalin arzikinsu yake bunkasa da sauri a cikin nahiyar, tare da yin hashashen cewa  gabashin Afirka zai zama  sama da sauran  yankunan nahiyar a cigaba. Ana hasashen cewa  a cikin  rabin kasashen nahiyar za a sami habakar jumillar kudaden shiga ( GDP)  daga 4.4% da ya kasance a 2024, ya koma 6.1% a cikin 2026. Sai kuma a cikin kasashen  Rwanda, Uganda, Sudan Ta kudu, Habasha, Tanzania da Kenya mafi karancin karuwarsa zai zama  kaso 5.% a 2025. A cikin yankin yammacin Afirka kuwa, an tsinkayo cewa tattalin arzikinsu zai tashi daga 4.1% a 2024,zuwa 4.6% a 2025, kuma kasashe irin su Togo, Benin, Cote De...
    Kafafen watsa labarun HKi sun ambato jami’an soja na cewa, mayakan Hamas sun sake gina kansu ta hanyar daukar dubban mayaka, kuma suna nan a arewacin Gaza ba su fita daga ciki ba. Kafafen  watsa labarun na HKI sun kuma kara da cewa; mayakan da kungiyar take da su a yanzu, sun rubanya mayakanta na baya, kafin barkewar yaki, kuma kungiyar ta koyi darussa daga yaki da sojan kasa na Isra’ila a baya.” Jaridar “Badiot Ahranot” wacce ta dauki labarin ta kuma ce; Har yanzu Hamas ba ta fito da dukkanin mayakanta a filin daga ba, da adadinsu ya kai 30,000, kuma tana ba su albashi ta hanyar kudaden harajin da take karba. Wani sashen na bayanin kafafen watsa labarun...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa da Kudu Maso Kudu su haɗa kai gabanin zaɓen 2027. El-Rufai, ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma jagoran yankin Neja Delta, Edwin Clark. Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa A cewarsa, Najeriya tana cikin matsala mai tsanani kuma tana buƙatar ɗauki cikin gaggawa. “A shekarun baya, Arewa da Kudu Maso Kudu sun kasance abokan siyasa,” in ji El-Rufai. “Kada mu manta da hakan. Mu koma kam wannan haɗin kai. Mu ceci wannan ƙasa...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa da Kudu Maso Kudu su haɗa kai gabanin zaɓen 2027. El-Rufai, ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma jagoran yankin Neja Delta, Edwin Clark. Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa A cewarsa, Najeriya tana cikin matsala mai tsanani kuma tana buƙatar ɗauki cikin gaggawa. “A shekarun baya, Arewa da Kudu Maso Kudu sun kasance abokan siyasa,” in ji El-Rufai. “Kada mu manta da hakan. Mu koma kam wannan haɗin kai. Mu ceci wannan ƙasa...
    Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa babu wani ɗan Arewa mai mai hankali da zai goyi bayan APC a zaɓen 2027. PDP ta bayyana hakan ne a matsayin martani kan zargin cewa Sanata Lawal Adamu, Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, baya aikin komai sai ɗumama kujera. Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa Gawuna ne ya lashe zaɓen Gwamnan Kano a 2023 — Ata Haka kuma, ana zargin gwamnatin Jihar Kaduna da dakatar da rarraba kayayyakin koyarwa da Sanata Lawal Adamu ya saya domin amfanin makarantun jihar. Yusuf Dingyadi, Mataimaki na Musamman na Shugaban PDP kan Yaɗa Labarai, ya ce ya kamata gwamnatin jihar ta haɗa kai da wakilan jama’a don ci...
    Iran ta jadadda anniyarta ta karfafa alaka da kasashen Afrika, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta tabbatar. A cikin wani sako da ya aike ta shafin X a ranar Juma’a, kakakin ma’aikatar, Esmaeil Baghaei, ya yi tsokaci kan ganawar da aka yi a ranar Alhamis tsakanin mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad Reza Aref da jakadun kasashen Afirka a Tehran. Baghaei ya bayyana cewa, taron ya nuna aniyar Iran na karfafa alaka da fadada hadin gwiwa da kasashen Afirka a fannoni daban-daban na moriyar juna. A yayin ganawar, Aref ya bayyana cewa, dabarun gwamnatin Iran, karkashin shugaba Masoud Pezeshkian, ya yi daidai da ainihin manufofin Iran na inganta alaka da kasashen Afirka. Ya jaddada manufar karfafa hadin gwiwa tsakanin...
    Arziƙin hamshakin attajirin nan ɗan jahar Kano Alhaji Aliko Dangote ya ninka na bara inda ya ƙaru zuwa dala biliyan 23.9, wanda hakan yasa ya cigaba da kasancewa mutumin da yafi kowa dukiya a nahiyar Afrika kuma ya koma matsayi na 86 a jadawalin masu kudin Duniya kamar yadda mujallar Forbes mai ƙididdiga akan masu kuɗin Duniya ta fitar, Forbes ta zaɓi Aliko Dangote a matsayin mutum na 144 mafi arziƙi a duniya a shekarar 2024 da dala biliyan 13.4. Forbes ta yi kiyasin cewa dukiyar Dangote ta kai dala biliyan 23.9, musamman saboda hannun jarin sa na kashi 92.3 na matatar man dangote, Aliko Dangote mai shekaru 67, ya sake zama ɗaya daga cikin manyan attajirai 100 a duniya,...
    Gidauniyar Tunawa Da Sir Ahmadu Bello Za Ta Gudanar Da Taronta Karo Na 11 A Bauchi.Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta sanar da cewa za ta gudanar da bikin tunawa da Sir Ahmadu Bello na shekara karo na 11 a ranar Litinin, 24 ga Fabrairu, 2025, a Bauchi, Jihar Bauchi. Taron, wanda aka shirya tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Bauchi, zai girmama marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato kuma Firaministan tsohuwar Yankin Arewa. A bana, taken laccar shi ne “Arzikin Halitta: Juya Albarkatun Yankin Arewa Zuwa Ci Gaban Tattalin Arziki Mai Dorewa.” Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan yadda za a yi amfani da albarkatun noma da ma’adanai da ruwa don bunkasa ci gaban tattalin arzikin...
    Kamfanin dake gudanar da nazari na Comscore na Amurka ya ba da kididdiga cewa, yawan tikitin da aka sayar a karshen mako na kallon fim din kasar Sin mai suna “Ne Zha 2” ya shiga sahun gaba na fina-finai 5 a arewacin Amurka. An yi kiyasin cewa, yawan kudin da aka samu a kwanaki 3 na karshen makon da ya gabata ya zarce dala miliyan 7, inda fim din ya zama mafi shahara a matakin koli da Sin ta gabatar a karshen makon a Amurka. An ce, an fara nuna wannan fim a gidajen sinima 770 dake arewacin Amurka daga ranar 14 ga watan nan da muke ciki, a matsayin fim din da Sin ta gabatar, kana yawan kudin da...
    An samar da ruwan sha a yankunan Danbatta, da Makoda da Minjibir dake gundumar Kano ta Arewa bayan kwashe kimanin shekaru goma. Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya bayyana haka a wani rangadin da ya kai kananan hukumomin uku domin tantance yadda ake samar da ruwan sha ga al’umma. Umar Doguwa ya bayyana cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya himmatu sosai wajen samar da ruwan sha a dukkan lungu da sako na jihar Kano. Ya ce an gyara kananan cibiyoyin samar da ruwan sha a yankunan inda ake samar da ruwa babu kakkautawa. Kwamishinan ya ce yanzu haka ana samun ruwan sha a kauyukan kunya, da Kilawa da ,wailare duk a karamar hukumar Minjibir yayin da...
    Ya ce ya zama wajibi gwamnati ta tashi tsaye wajen farfado da darajar ilimi, ya kuma nuna damuwa bisa ganin yadda darajar ilimi take kara faduwa a kasar nan. Ya ce dole sai gwamnati tarayya da na jihohi sun hada kai wajen tafiyar da harkar karantawa a kasar nan ta yadda yaran masu karamin karfi za su sami ilimi mai inganci.
    Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya buƙaci Hukumar Bunƙasa Arewa maso Gabas (NEDC) da ma’aikatar raya yankuna ta tarayya da su magance talauci a yankin ta hanyar zuba jari a fannin ilimi. Shettima ya yi wannan kiran ne a yayin wata ganawa da ya yi da mahukuntan hukumar ta NEDC a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda suka yi masa bayani kan wani shiri na harkokin ilimin babbar sakandare — ASSEP. Boko Haram ta kashe kwamandoji da mayaƙan ISWAP 31 a Borno Dalilin da ’yan siyasa ke sauya sheƙa zuwa APC — Tambuwal Ya kuma yaba wa hukumar NEDC kan yadda ta ke ba da gudummawar a fannin ilimi, inda ya ce za a riƙa tunawa da irin wannan...
    Ministan kudi da tattalin arziki na kasar Iran yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiya don halattar wani taro mai muhimmaci na tattalin arziki. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan tattalin yana fadar haka a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa, yana zuwa wannan taron ne tare da gayyar tokwaransa na kasar Saudiya da kuma kum ashugaban hukumar lamuni ta duniya, wato IMF. Abdulnaser Himmati ya bayyana cewa manufae taron itaa ce tattauna hanyoyin bukasa tattalin arzikin kasashe masu tasowa .  Har’ila yau taron tana son kyuatata dangantakar tattalin arziki a kasashen yankin Asia da kuma aiki tare da sauran kasashen duniya sabota ci gaban kasashen duniya gaba daya. Taron na kwanaki biyu, wata...
    Salma Muhammad Salisu matashiya ce da ba ta taba mafarkin yin sana’ar kayan makulashe ba, bayan da ta kammala digirinta na farko a fannin Kididdiga (Statistics). Shekara biyar da kammala jami’a, matashiyar ta tsinci kanta cikin matsalar rashin aikin ofis, duk kuwa da karancin kwararru mata a fannin da ta karanta. Hakan ya sa ta fara tunanin yadda za ta fara sana’a domin dogara da kanta kafin Allah Ya kawo mata aiki. Daga nan ne tunanin fara kasuwancin harkar girke-girke da hada lemo ya zo mata, har ta fara ‘M&S Mannah Wassalwa Kitchen’. Labarin Salma  na kama da matasan Nijeriya da dama da suka kammala manyan makarantu, amma ba su samu aikin ofis  ba. Hakan ne ya sanya a baya-bayan...
    Gwamna Dauda Lawal ya mika makaman da gwamnatinsa ta bayar ga rundunar soji domin kafa hedkwatar rundunar Operation Safe Corridor na jihohin Arewa maso Yamma, a karamar hukumar Tsafe domin kwance damarar makamai, da lalata su da kuma shigar da barayin da suka tuba su koma cikin al’umma.   Gwamnan a wajen bikin mika ragamar sansanin da aka samar, ya jaddada aniyar gwamnatin sa na ci gaba da bin sawun ‘yan bindiga har sai an fatattake su da ruguza su da murkushe su.   Dokta Lawal ya ce gwamnatin jihar ta samar da wurin ne a matsayin wani shiri na taimakawa gwamnatin tarayya wajen magance matsalar ta’addanci da ya addabi Zamfara da Arewa maso Yamma sama da shekaru goma.  ...
    Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar NNPP ita ma ta shiga cikin rikici, inda ake zargin Kwankwaso ne ke jagorantar daya daga cikin bangarorin jam’iyyar. A makon da ya gabata ne wani bangare na jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin wanda ya assasa jam’iyyar, Dakta Boniface Aniebonam ya gudanar da babban taro a Legas, inda aka zabi sabbin mambobin kwamitin zartarwa na kasa. Kwankwaso ya tabbatar da ganawarsa da Aregbesola a wani sako da ya fitar. Ya ce, “A yammacin yau na yi farin cikin ziyartar tsohon gwamnan Jihar Osun kuma tsohon ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, a gidansa da ke Legas. Taron ya ba mu damar tattaunawa a kan harkokin siyasar kasar nan da gudanar...
    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bibiyar ’yan ta’adda har sai an fatattake su, an ruguza su tare da murƙushe su. Gwamnan ya miƙa kayan aikin da gwamnatin jihar Zamfara ta samar domin kafa hedikwatar tsaro ta dakarun sojin ‘Operation Safe Corridor’ na jihohin Arewa maso Yamma. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa ‘Operation Safe Corridor’ zai ta tabbatar da canja ƙwaƙwale, haɗe kai magance duk al’amuran da suka shafi ’yan bindiga. Sanarwar ta ƙara da cewa, an tsara shirin ne a ƙarƙashin Operation Safe Corridor a yankin Arewa maso Gabas, wanda ya yi nasarar sauya ƙwaƙwalen tsoffin mayaƙan Boko Haram tare...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rediyo na daga cikin kafofin da al’umma da dama suka dogara da su don jin labarai, shirye-shirye da kuma samun nishadi. Rediyo na taka muhimmiyar rawa wajen wayar wa da al’umma da dama kai musamman duba da yadda aka bayar da shaidar cewa tafi kowace kafa saurin yaɗa bayanai ba a cikin birane ba, har ma da yankunan karkara. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya? DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Sai dai a wannan gaɓa ana ganin gidajen rediyo a Arewacin ƙasar nan na samun koma baya, la’akari da yadda a wasu lokutan wasu suke rufe harkokinsu su ɓace...
    Kungiyar yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin harin da aka kai a lardin Kunduz na arewacin kasar Afganistan, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla 5 da kuma raunata wasu da dama. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto “Daesh Khorasan” tana fadar haka a shafinta na sadarwa, bayanda wani dan ta’adda ya tarwatsa kansa a kusa da wani banki a garin Kunduz, wanda ya halaka shi ya kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla guda biyar. Labarin ya kara da cewa an kai harin kunan bakin wakenne da misalign karfi 8:35 na safe a yau Laraba, wato 4:05 na safe agogin GMT. Mai gidan bankin da kuma wasu mutane 4 daga cikin akwai fararen hula da kuma wani...
    Kungiyoyin da suke dauke da makamai sun kashe fararen hular da ba su gaza 55 ba a wani hari da su ka kai wa wasu kauyuka da sansanin ‘yan hijira a Arewacin DRC. Mahukunta a yankin na Arewacin DRC sun ambaci cewa wasu masu dauke da makamai na kungiyar CODECO sun kai wa wasu kauyuka da suke yankin Djaiba hare-hare a gundumar Ituri a  jiya litinin da dare. Bugu da kari masu dauke da makaman sun kai hari a cikin sansanin ‘yan hijira da suke a cikin wannan yankin kamar yadda shugaban sansanin Antoinnette Nzale ya fadawa manema labaru. Ita dai kungiyar CODECO  gamayya ce ta kungiyoyin da suke dauke da makamai da su ka fito daga kabiluar Landu, manoma....
      Gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta sanar da cewa za a gudanar da taron Karrama Sir Ahmadu Bello karo na 11 a ranar Asabar, 22 ga Fabrairun 2025, a Bauchi.     Wannan taron, wanda ke tunawa da rayuwa da gado na Sir Ahmadu Bello KBE, Sardaunan Sokoto da Firaministan tsohuwar Yankin Arewa, zai hada da jerin tattaunawa da ayyukan da zasu mayar da hankali wajen magance kalubalen tattalin arzikin yankin.     Taken taron na bana, “Alherin Duniya: Sauyw Albarkatun Halitta na Arewa zuwa Cigaba Mai Dorewa”, na zuwa ne a lokacin da ake fuskantar karin damuwa kan talauci da rashin aikin yi da rashin ci gaba duk da kasancewar Arewa na da yalwar albarkatun halitta.  ...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Dakta Zainab Muhammad na daga cikin matan Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da ƙudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da ƙalubalen da wasu matan yankin ke bayyana cewa suna fuskanta wurin karantar fannin. Dakta Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci ɗaya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kaɗai ba, har da mazan ma na ƙauracewa wannan karatun. Zainab ƙwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa lafiya a asibitoci. NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya? DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’ Shirin Najeriya...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, kasar Iran ba zata taba zama don tattaunawa da kasar Amurka ba a dai-dai lokacin take kara takurawa kasar da takunkuman tattalin arziki ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka bikin ciki shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin musulunci a kasar a yau litinin, a birnin Hamedan. Imam Khumaini (q) ne ya jagoranci kasar zuwa ga nasara a shekara 1979, Juyin juya halin da ya kawo karshen Sarautar Muhammad Reza sha Pahlavi. Ministan ya kara da cewa Jagoran juyin juya halin musulunci ya rika ya bayyana matsayin gwamnatin kasar Iran kan wannan batun, sannan abinda ya fada shi ne duk wani mai...
    Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya gana da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, a birnin Legas. Kwankwaso ya bayyana a shafinsa na X cewa sun tattauna kan batutuwan da suka shafi siyasa da makomar dimokuradiyya a Najeriya. Aisha Binani ce ta lashe zaɓen Adamawa, ina da ƙwararan hujjoji – Ari Ɗan sanda ya rataye kansa har lahira a Neja Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke kira ga haɗin kai domin fuskantar zaɓen 2027. A watan Oktoban 2024, jam’iyyar APC a Jihar Osun ya dakatar da Aregbesola bisa zargin cin amanar jam’iyya da sukar shugabannin jam’iyyar, ciki har da Shugaba Bola Tinubu da tsohon gwamnan...
    Tsohon Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa, Hudu Ari, ya ce bai damu da korar da aka yi masa ba, amma yana nan a kan bakansa cewa Aisha Binani ta jam’iyyar APC ce, ta lashe zaɓen gwamna na 2023. An dakatar da Hudu Ari bayan da ya ayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen tun kafin a kammala tattara sakamakon ƙuri’u. Gobara ta ƙone motoci da shaguna a wajen sayar da gas a Neja Taron Qur’ani: Tsakanin magoya baya da masu kushe Sai dai ya ce yana da hujjojin da ke nuna cewa Binani ta doke Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP. Da yake magana da manema labarai a Bauchi, Ari ya rantse da Alƙur’ani mai girma cewa manyan jami’an...
    LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, an tabbatar da sallamar Ari a matsayin Kwamishinan zaɓen jihar Adamawa bayan da Majalisar wakilai ta tarayya ta amince da buƙatar sallamarsa da shugaban ƙasa ya yi, biyo bayan zarginsa da aka yi da karya ƙa’idojin aiki da shigo da shakku yayin gudanar da aikin zaɓe da ayyana sakamakon zaɓe ba daidai ba, lamarin da har ya kai an gurfanar da shi a kotu.   Ari ya nuna damuwarsa kan yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe suka shafa wa idanunsu toka suka ƙi hango hujjojinsa da ya gabatar na kura-kuran da aka tafka a lokacin zaɓen.   Hudu wanda ya ɗauki Alkur’ani mai girma yayin hirar, ya rantse da...
    Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tabbatar da naɗin Sarkin Yarbawan Funtuwa, Oba Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Jihohin Arewa 19 har da Abuja. Mataimakin Gwamnan JIhar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya tabbatar da naɗin a madadin gwamnan a lokacin da yake karɓar baƙuncin tawagar Sarakunan Yarbawan Arewa da suka miƙa masa takardar amincewarsu ga zaɓen Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Arewa a fadar gwamnati da ke Katsina. Ta kashe saurayinta saboda ya gaisa da tsohuwar abokiyar karatunsa Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Gwamnan ya nuna matuƙar farin ciki da jinjina wa yadda aka gudanar da zaɓen shugabannin Majalisar Sarakunan Yarbawan na Arewa lami lafiya. Ya ce,...
    A zamanin baya, duk da cewa fina-finan nanaye sun fi karbuwa a wajen mutane, amma haka muke kokartawa wajen ganin an shigar da wata koyarwa ta addinin musulinci ko kuma wani abu mai amfani da zai amfanar da al’umma ta wani bangare, amma yanzu duk an daina wannan, masu shirya fina-finai na amfani da labarai masu tsafta da amfanarwa, ba tare da da sanya wakoki ko makamantansu a ciki ba, in ji Malam. “Dalili kuwa shi ne, yanzu ‘ya’yan mutunci da arziki su ne ke yin harkar, sannan kuma su ne suke samun arzikin duniya da na lahira, akwai lokacin da har mata masu zaman kansu din, sai da muka daina samun su idan zamu yi fim, amma yanzu wannan...
    A yau Asabar, 8 ga wannan wata da safe, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya saurari rahoton aiki na kwamitin JKS da gwamnatin lardin Jilin a birnin Changchun dake lardin Jilin. Bayan kammala sauraro, shugaba Xi ya yi jawabi inda ya jaddada cewa, ya kamata hukumomin lardin Jilin su aiwatar da shirin farfado da yankin arewa maso gabashin kasar Sin a dukkan fannoni a sabon zamani da kwamitin tsakiya na JKS ya tsara, da tabbatar da tsaron kasar a fannoni 5, da maida hankali ga aikin samun ci gaba mai inganci, da bin tsarin tunanin sabon ci gaba, da bude kofa ga kasashen waje, da yin kwaskwarima a dukkan fannoni,...
    Gwamnatin kasar Argentina ta sanar da ficewarta daga hukumar lafiya ta duniya WHO. Mai magana da yawun shugaban kasar Manuel Adorni ya fadawa taron manema labarai cewa, shugaban kasar Javier Milei, ya umarci ministan harkokin wajen kasar Gerardo Werthein, da ya dauki matakin janye Argentina daga hukumar lafiya ta duniya. Adorni ya ce, ” ‘yan Argentina ba za su kyale wata kungiya ta kasa da kasa ta tsoma baki a harkokin da suka shafi ‘yancin kasarmu ba. “ Ya kara da cewa,”Ya kamata a fayyace cewa Argentina ba ta karbar kudade daga hukumar ta WHO don kula da lafiya, don haka, wannan matakin, kamar yadda wasu ke cewa, a kalla a shafukan sada zumunta, ba ya wakiltar asarar kudade ga kasar,...
    Mataimakin shugaban kasar Iran Muhamamd Riza Arif ya bayyana cewa, A halin yanzu ba ya cikin shirin gwamnatin Iran yin ganawa a tsakanin shugaban kasa Mas’ud Fizishkiyan da takwaransa na Amurka Donald Trump. A jiya Laraba ne mataimakin shugaban kasar Iran Riza Arif da ya yi Magana da ‘yan jarida inda yake mayar da martani akan fatan  shugaban kasar Amurka Donald Trump na ganawa da shugaba Mas’ud Fizishkiyan na Iran, yana mai kara da cewa hakan ba ya cikin shirin gwamnati a wannan lokacin. Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya kuma ce, ya kamata Trump ya san cewa, bisa fatawa ta addini da jagoran juyin musulunci ya fitar, Iran ba za ta mallaki makamin Nukiliya ba. Riza Arif ce Iran...
    Daminar Bana: NiMet Ta Yi Hasashen Jinkirin Saukar Ruwan Sama A Jihohin Arewa
    HKI tana son aiwatar da wani shiri don kara yawan yahudawa a kasar, a dai dai lokacinda take fama da karancin yahudawa a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce a baya dai gwamnatin yahudawan suna son kara yawan  yahudawa musamman a yankin yamma da kogin Jordan, ammam har yanzun shirin baya tafiyar kamar yadda take so. Labarin ya kara da cewa yawan Palasdinawa a cikin kasar Palasdinu da aka mamaye wata barazana ce babba ga gwamnatin kasar. Banda haka a cikin yakin watanni 15 da ta fafata da Mutanen yankin Gaza, wasu yahudawa sun fice daga kasar kuma da dama daga cikinsu sun sha alwashin ba za su sake dawowa kasarba. Wasu kuma sun kai...
    Shuwagabannin kasashen turai guda uku wato EU3 sun bayyana cewa daukewa Iran takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar ya fi karfinsu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran yana fadar haka a wata hira ta musamman da ta hada ta da tashar. Mohammad Eslami ya ce kasashen turan guda uku wadanda suka hada da Jamus, Faransa da Ingila sun aiko masa da sako inda suke tabbatar haka. A cikin shugaban Muhammad Eslami ya fadawa tashar talabijan ta Presstv irin ci gaban masu yawa wadanda JMI ta samu a cikin shekarun da suka gabata. Shugaban ya kara da cewa sakon da EU3 ya nuna irin yadda rikicin shirin Nukliyar kasar Iran...
    Arsenal ta doke Manchester City a wani yanayi mai ban mamaki a filin wasa na Emirates dake birnin Landan, ƙwallaye da Odegaard, da Partey, da Skelly, da Harvertz da Nwaneri suka jefa ya sanya Man City cikin garari. Tun minti na 2 da fara wasan kyaftin ɗin tawagar Arsenal Martin Ordegaard ya jefa ƙwallo a ragar Manchester City bayan da ɗan wasan baya Nathan Ake ya tafka kuskure. Juma Bah: Balladolid Za Ta Kai Manchester City Kara Gaban Kotu Arsenal Ta Matsawa Liverpool Ƙaimi Bayan Doke Tottenham A Emirates  Duk da ƙwallon da Haaland ya ci bai hana Arsenal raga raga da City a wasan mako na 24 na gasar Firimiyar  ba, wannan sakamakon ya sanya magoya bayan ƙungiyar sa...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Manchester City ta ci 5 da 1 a Gasar Firimiyar Ingila. Ƙungiyoyin biyu sun ɓarje gumi da yammacin ranar Lahadi a filin wasa na Emirates, a mako na 24 na gasar. Fasinjoji 30 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Ondo Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu baƙin gilas shiga harabarsa Ɗan wasan tsakiyar Arsenal, Martin Ordeegard ne ya fara jefa ƙwallo a minti na biyu da fara wasa. Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Erling Haaland, ya warware ƙwallon da Arsenal ta jefa wa Manchester City, a minti na 55. A minti ma 56 Thomas Partey ya ƙara jefa wa Arsenal ƙwallo ta biyu. A minti...
    Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya sha alwashin ci gaba da shirin kasar na kera makaman nukiliya har sai baba ta gani. Kafar yada labaran kasar ta rawaito Mista Kim ya kai ziyara cibiyar da ake kera makaman, inda ya ce shekarar da muke ciki na da matukar muhimmanci a tsarin da kasar ke yi na karfafa shirin makaman nukiliya, da kuma fito na fito da duk kasashen da suka nemi tsoma baki a harkar kasarsa. Kalaman Kim na zuwa ne bayan gwajin makaman da Pyongyang ta yi a ranar Asabar da ta wuce, domin tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, shi ne gwaji na farko tun bayan shugaban Amurka Donald Trumo ya sha rantsuwar kama...
    Sojojin Sudan sun kwace iko da wani birni da ke arewacin Kordofan daga hannun ‘yan tawayen kasar na Rapid Support Forces Rundunar sojin Sudan ta sanar da cewa ta sake kwace iko da birnin Umm Rawaba, birni na biyu mafi girma a arewacin jihar Kordofan da ke kudancin kasar daga hannun dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces. A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Sudan ta fitar ta ce: Godiya ta tabbata ga Allah da yardarSa, sojojin sun tsarkake birnin Umm Rawaba daga hannun mayakan dakarun kai dauki gaggawa da sojojin hayarsu, tare da janyo musumunanan hasarori masu yawa. A cewar shafin yanar gizo na Arabi 21, Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun mamaye birnin...
    Jam’iyyar APC a Jihar Osun, ta kori Tsohon Gwamnan Jihar kuma Tsohon Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola, bisa zargin cin amanar jam’iyyar. Wannan ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da shugabannin jam’iyyar na Ƙaramar Hukumar Ilesa ta Gabas suka gabatar. Yadda Kano ta koma matattarar ’yan TikTok bayan Hisbah ta daina kamensu Muna da ƙarfin aljihun ɗaukar nauyin Taron Al-Ƙur’ani —Sheikh Bala lau Sun nemi a ɗauki mataki a kan Aregbesola saboda zargin kafa ƙungiyoyin da ke raba kan jam’iyyar da yin haɗin gwiwa da jam’iyyun adawa don raunana APC a Osun. A cikin wata wasiƙa da kwamitin zartarwa na APC na Osun ya aike wa shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, sun bayyana cewa Aregbesola ya kafa wata ƙungiya mai...
    Aston Villa na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi da dama da ke son ɗauko ɗan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford, ɗan wasan mai shekaru 27 bai taka leda a United ba tun lokacin da babban kocin ƙungiyar Ruben Amorim ya ajiye shi a wasan Manchester derby a ranar 12 ga watan Disamba. Amorim ya ce a ranar Laraba yana jin ƙungiyarsa za ta fi kyau da Rashford a ciki, amma ɗan wasan bai cika ƙa’idojin da ya buƙata ba, wakilan Rashford sun gana da wasu manyan ƙungiyoyin Turai a cikin ‘yan makonnin da suka gabata a ƙoƙarinsu na ganin ya bar Manchester. Mece Ce Matsalar Manchester United? AC Milan Ta Kammala Ɗaukar Kyle Walker Daga Manchester City A Matsayin...
    Dandalin sada zumunta na TikTok ya sanar da hada gwiwa da kamfanin tallace-tallace ta kafofin zamani na Aleph Holdings da dandalin sayayya kan intanet na kasar kenya wato Wowzi, wanda ake sa ran zai bunkasa tattalin arziki mai nasaba da kirkire-kirkiren jama’a a kasar Kenya. Carl Jordon, shugaban sashen tallace tallace da harkokin cinikayya a yankin kudu da hamadar Sahara na kamfanin TikTok, ya shaidawa manema labarai a Nairobi cewa, hadin gwiwa da kamfanin Aleph holdings zai saukakawa harkokin kasuwanci a kasar wajen tallata kayayyaki da hidimominsu a kan dandalin wallafa bidiyo na wayar salula. Ya ce hadin gwiwar ya nuna kudurin TikTok na karfafa muhallin kirkire-kirkire na jama’a a cikin gida ta hanyar tabbatar da masu basira sun samu...
    Ya kara da cewa, “a halin yanzu ,ana gudanar da aikin shimfida tagwayen hanyoyi a cikin tsakiyar garin Argungu da sauran wasu ayyukan ci gaba a masarautar. Saboda haka, wannan wata dama ce na kara shirye-shirye don tarbar baki da ke zuwa kallon shirin daga cikin gida da ketare. Wannan al’ada ce fitacciya a masarautar Argungu.   “Muna godiya da fahimta da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki, da mahalarta wannan biki,” in ji Mataimakin Gwamnan jihar Kebbl Sanata Abubakar Umar Tafida.
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kan yi rangadi a wurare daban daban kafin bikin bazara na kasar, kana kafin bikin na wannan shekara, shugaban ya ziyarci lardin Liaoning dake arewa maso gabashin Sin. Sai dai wadanne fannonin ya mai da hankali a kai, yayin wannan ziyara? Abu na farko da shugaba Xi ya lura da shi, shi ne aikin sabunta fasahohin masana’antu. A rangadinsa na wannan karo, shugaban ya ziyarci wata masana’antar sarrafa kayayyakin karfe, inda ya duba yadda ake kokarin amfani da sabbin fasahohi a wurin, kana ya nanata bukatar samar da kayayyaki masu inganci, wadanda ba za su gurbata muhalli ba. Yankin Gabashin Kongo(Kinshasa) Yana Cikin Yanayi Mai Hadari Gwamna Nasir Ya Ƙaddamar da Aikin Titin Koko–Zuru...
    Hamas ta bayyana komawar Falasɗinawa a matsayin nasara, tana mai cewa hakan ya karya yunƙurin da aka yi na tilasta wa mutanen barin gidajensu.
    A Yau Litinin ne dai da safe dubban Falasdinawa su ka fara komawa Arewacin Lebanon bayan gushewar watanni 15 na yaki. Dubban Falasdinawan ne dai suke tafiya a kafa, yayin da wasu suke tafiya a cikin manyan motoci suna bi ta titin Salahuddin. Tun da fari tashar talabijin din 12: ta HKI, ta watsa labarin cewa; sojoji sun janye daga mashigar Natsarim, da su ka kafa domin yin bincike tun ranar 27 ga watan Oktoba 2023. Da dama daga cikin Falasdinawan sun kwana a wannan mashigar bayan da sojojin HKI su ka hana su wucewa  a jiya Lahadi. Barin Falasdinawan su koma arewacin Gaza, yana a karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakaninsu da Hamas,dangane da fursunonin yaki. A jiya...
    Dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu sun fara komawa yankin arewacin zirin Gaza da yaki ya daidaita bayan da aka cimma matsaya tsakanin Hamas da Isra’ila. Tuni kungiyar Hamas ta yaba da komawar Falasdinawan zuwa arewacin Gaza wanda ta danganta a abun tarihi. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas bayan shafe watanni 15 ana gwabza kazamin yaki a Gaza. An fara aiwatar da kashin farko na yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Janairu, kuma ana sa ran za’a saki Falasdinawa sama da 1,890 da ‘yan Isra’ila 33, wadanda ke cikin 240 da kungiyoyin Hamas ta yi garkuwa dasu a harin ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Tun lokacin yakin ya lakume rayukan Falasdinawa akalla 47,306,...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare,  da...