An Kashe Mutane Fiye Da 300 A Wani Kazamin Fada A Yankin Darfur Da Ke Yammacin Kasar Sudan
Published: 17th, April 2025 GMT
Mutane fiye 300 ne suka mutu a cikin kwanaki a wani kazamin fada a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan
Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta watsa rahoton cewa: Sama da fararen hula 300 ne aka kashe a wani kazamin fada na kwanaki biyu a yankin Darfur na kasar Sudan mai fama da rikici.
Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun kaddamar da hare-hare a ranakun Juma’a da Asabar a kan sansanonin ‘yan gudun hijira biyu da ke fama da matsalar yunwa a arewacin Darfur da kuma babban birnin da ke kusa, inda rahotannin farko suka nuna cewa sama da mutane 100 ne suka mutu, ciki har da yara 20 da ma’aikatan agaji tara, a cewar wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya.
A halin da ake ciki kuma, ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya sanar da samun karuwar adadin wadanda suka mutu a ranar Litinin, kamar yadda wasu majiyoyi na cikin gida suka tabbatar da hakan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jadadda Cewa: Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kan Iran Zai Fuskanci Mayar Da Martani
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Duk wani harin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci mayar da martani daidai da shi cikin gaggawa
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa Iran na da kwarin gwiwa kan iya dakile duk wani yunkuri da wasu bangarorin ke yi na kawo cikas ga manufofinta na ketare.
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Rudun gwamnatin yahudawan sahayoniyya, wadda take ganin za ta iya gindaya wa Iran abin da ya kamata ko kuma bai kamata ba, rudun tunani ne da ya yi nesa da hakikanin gaskiya, ta yadda bai cancanci mayar da martani ba.
Araqchi ya kara da cewa: “Duk da haka, jajircewar Netanyahu wani abin lura ne, a yayin da yake kokarin neman bayyana wa Shugaba Trump abin da zai iya ko kuma ba zai iya yi a diflomasiyyarsa da Iran ba!”
Ministan harkokin wajen ya yi nuni da cewa: “Abokanan Netanyahu a cikin tawagar Biden da ta gaza – wadanda suka kitsa makarkashiyar hana cimma yarjejeniya da Iran – suna kokarin nuna zaman tattaunawar da ake yi ba na kai tsaye ba da gwamnatin Trump a matsayin wani kuskure ne kuma tamkar hoton sauran yarjejeniyar nukiliya ce da aka gudanar.”