Najeriya da gwamnatin sojin Nijar da Nijar sun sasanta
Published: 17th, April 2025 GMT
Gwmanatin Sojin Nijar ta sanar da cewa sun sasanta da Gwmanatin Najeriya.
Hakan ta faru ne bayan ziyarar aiki da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya kai birnin Yamai, fadar gwamnatin Nijar.
Bayan sanya hannu kan takardar, Ministan Harkokin Wajen Nijar, Bakary You Sangare, ya bayyana cewa, “da ma Najeriya ’yan uwanmu ne, duk wanda ya ce zai raba Nijar da Najeriya, shi da kansa ya san ba gaskiya ba ne, abu ne na Allah.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamnatin sojin Nijar Najeriya Nijar Tuggar Yamai
এছাড়াও পড়ুন:
Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri da Gwamnonin Jihohi Shidda
Daga Bello Wakili
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri da gwamnonin jihohi shidda daga sassan ƙasar a ci gaba da tattaunawar da ake yi domin ƙarfafa batun tsaro a ƙasa.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo, Umar Namadi na Jigawa, Nasir Idris na Kebbi, Ahmed Ododo na Kogi, Lucky Aiyedatiwa na Ondo, da Ahmed Aliyu na jihar Sokoto.
Taron, wanda ya ɗauki kusan mintuna 40, ya mayar da hankali ne kan muhimman matsalolin tsaro da ke shafar jihohinsu, duk da cewa ba a bayyana cikakkun bayanai ba.
Wakilin Rediyon Najeriya da ke fadar shugaban kasa ya ruwaito cewa wannan zaman na daga cikin kokarin shugaban kasa na ƙara haɗin kai da jihohi wajen magance matsalolin tsaro.
Wannan cigaban ya biyo bayan nasarar da Gwamnatin Tarayya ta samu na kubutar da dalibai 100 da aka yi garkuwa da su a Jihar Neja, baya ga wanda aka yi a Jihar Kebbi.
Ci gaba da irin waɗannan tattaunawa na shugaban kasa na nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin ƙasar.