Jami’an lafiya a Gaza, sun ce akalla mutane 1,563 ne aka kashe tun bayan da Isra’ila ta koma kai farmaki a Zirin tun daga ranar 18 ga watan Maris, yayin da al’amuran jin kai ke kara ta’azzara a Gaza.

Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza tun bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas ta Falasdinu a watan jiya ya zarce 1,560 a cewar jami’an kiwon lafiya.

A cikin wata sabuwar sanarwa da ta fitar yau Asabar, ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce hare-haren Isra’ila sun kashe akalla mutane 21 a cikin sa’o’i 24 na baya-bayan nan.

An kashe mutane 50,933 tare da raunata 116,045 tun farkon yakin a watan Oktoban 2023, in ji ma’aikatar a alkalumman data sabunta.

A cewar hukumar ‘yan gudun hijira ta Falasdinawa UNRWA, kimanin Falasdinawa 400,000 ne aka tilastawa barin muhallansu a fadin Gaza tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta fara aiki a watan Janairu ta ruguje kusan wata guda da ya gabata.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: tun bayan da da Isra ila

এছাড়াও পড়ুন:

Amurka Ta Ce: Shugaban Rikon Kwarayar Siriya Al-Julani Ya Yi Alkawarin Cewa Ba Zai Cutar Da Tsaron Isra’ila Ba

A ganawarsa da wata jami’ar Amurka, al-Julani ya yi alkawarin ba zai cutar da tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila ba!

Barbara Leaf, tsohuwar mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin gabas ta tsakiya, ta tabbatar da cewa shugaban rikon kwarya a Siriya, Mohammed al-Julani (al-Shara’a), “ya bayyana fahimtar matsalolin tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila,” a cewarta.

Hakan ya zo ne a wata ganawa tsakanin Leaf da al-Julani a birnin Damascus, jim kadan kafin ta bar mukaminta. Leaf ta bayyana taron a matsayin “mai kyau kuma mai amfani.”

Har ila yau Leaf ta yaba da “hanzari da kuma dabarar da Shara’a ke bi wajen tunkarar al’amurran yankin,” tana mai cewa “yana neman kulla kyakkyawar alaka da bangarorin yankin.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane 12 Da Masu Sayar da Makamai 3 A Taraba Da Kaduna
  •  Falasdinawa 40 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’oi 24 A Gaza
  • Boko Haram Sun Hallaka ‘Yan Zaman Makoki 7, Sun Jikkata Wasu A Borno
  • Bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 26 a Borno
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Jaddada Wajabcin Komawa Kan Shirin Tsagaita Bude Wuta A Gaza
  • Sama Da Masu Sayayya Daga Ketare 220,000 Ne Suka Halarci Bikin Baje Kolin Canton Karo Na 137
  • Jiragen Yakin Amurka Sun Kashe Mutane Da Dama A lardin Sa’ada Na Kasar Yemen
  • Lebanon:  Isra’ila Ta Kai Hari Akan Unguwar Dhahiya A Birnin Beirut
  • Amurka Ta Ce: Shugaban Rikon Kwarayar Siriya Al-Julani Ya Yi Alkawarin Cewa Ba Zai Cutar Da Tsaron Isra’ila Ba