2025-10-21@21:46:30 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1642

«tun bayan da»:

    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira biliyan ɗaya domin gyaran ajujuwan karatu a wasu makarantu na gwamnati. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse. A cewarsa, majalisar zartarwar jihar ta amince da kashe fiye da Naira miliyan 528 domin gyaran ginin ajujuwa a wasu zababbun makarantu na gwamnati a fadin jihar. Ya bayyana cewa, manufar aikin ita ce inganta yanayin karatu, tabbatar da tsaro, da kuma samar da iingantaccen ilimi karkashin shirin gwamnatin jihar na farfado da ilimin asali. Sagir Musa ya kuma ce, majalisar ta amince da kashe sama da Naira miliyan 512 domin  samar...
    Da  misalin karfe 9;30 na safiyar ranar Lahadi ne dai wasu mutane masu dauke da makamai su ka kutsa cikin gidan adana kayan tarihi na ” Louvre”  inda su ka yi awon gaba da kayayyaki masu daraja. Ministun harkokin cikin gidan Faransa  da na al’adu sun ce; barayin sun dauki mintuna 4 zuwa 7  kadai su ka yi satar. Da dama daga cikin kafafen watsa labarun kasar ta Faransa sun bayyana abinda ya faru da cewa ya yi kama da abinda ake gani a cikin fina-finai. Satar dai ta jawo cece-kuce a tsakanin ‘yan siyasar kasar, yayin da kafafen watsa labaru suke yi wa lamarin isgili ta hanyar yin zane-zane. Jaridar “La Progress” ta amabci cewa a baya ma an...
    Bayanai daga Falasdinu na cewa a kalla Falasdinawa 97 ne sojojin Isra’ila suka kashe tare da jikkata wasu 230 tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta fara aiki a Gaza a ranar 10 ga watan Oktoba. A cikin wata sanarwa da ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya fitar, ya ce ‘yan mamayar  sun aikata laifuka 80 tun bayan ayyana tsagaita bude wuta, wanda hakan ya saba wa dokokin jin kai na kasa da kasa. Laifukan sun hada da harbin bindiga kai tsaye kan fararen hula da gangan, da kama fararen hula. A cewar sanarwar, sojojin na Isra’ila sun yi amfani da motocin soji, tankunan yaki da aka jibge a gefuna da wuraren zama, da jirage marasa, lamarin da...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu October 21, 2025 Labarai An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole October 20, 2025 Labarai Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU October 20, 2025
    A jiya litinin ce masu goyon bayan Nnamdi Kanu shugaban kungiyar neman kafa kasar Biafara (IPOP) daga tarayyar Najeriya, wanda ake tsare da shugaban kungiyar tare da tuhumar ayyukan ta’addan sun fito zanga-zanga suka kuma tushe wata babban titi a Abuja. ‘Yansanda sun jefa masu hayakin teargas don tarwatse su a jiya litinin. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa Kanu wanda yake da Passport na kasar Burtania ya yi kokarin wanke kansa daga tuhumar da ake masa tun 2021 amma ya kasa. Kanu yana jagorantar kungiyar IPOP tun da dadewa, da nufin samar da kasar Biafara a yankin kudu maso gabacin Najeriya. Kafin haka dai yan kabilar Ibo sun yi kokarin bellewa daga tarayyar Najeriya a...
    Wannan lamari dai ya janyo ce-ce-ku-ce da fushin jama’a a faɗin jihar, inda al’umma da masu fafutuka ke kira da a bincika tare da ɗaukan mataki cikin gaggawa don hana faruwar irin haka nan gaba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU October 20, 2025 Manyan Labarai Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara October 20, 2025 Labarai Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro October 20, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Siyasa Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027 October 17, 2025 Siyasa Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu October 16, 2025 Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October 16, 2025
    Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a unguwar Danbare a Jihar Kano, ta gurfanar da wani mutum mai suna Malam Shaddadu bisa zargin sayar da gidan ɗansa ba tare da izini ba. Ɗan mutumin wanda ya gabatar da ƙara, Muhammad Shaddadu, ya shaida wa kotu cewa, lamarin ya samo asalin ne tun bayan da mahaifinsa ya saya wa wasu ‘yan uwansa biyu da suke uba ɗaya babura masu kafa uku da aka fi sani da Adaidata Sahu. APC ta rage wa Mata kuɗin tsayawa takara a Borno Dembele ya dawo PSG bayan jinyar makonni Sai dai daga baya, tsautsayi ya rutsa da ɗaya daga cikinsu wanda ɓata-gari suka kai masa hari har suka kashe shi, kuma suka yi awon...
    A daren Lahadi a ƙasar Chile, ƙasar Morocco ta kafa tarihi bayan da ta doke Argentina da ci 2-0 a wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya na ƴan ƙasa da shekaru 20, wanda hakan ya bai wa ƙasar damar lashe wannan kofi a karon farko a tarihin ta. Yassir Zabiri, wanda ke taka leda a ƙungiyar FC Famalicao ta ƙasar Portugal, shi ne gwarzon wasan bayan da ya ci ƙwallaye biyu a ragar Argentina tun a farkon rabin lokaci. Nasarar ta tabbatar da ƙarfin Morocco a gasar, inda ta doke ƙasashe masu ƙarfi irin su Koriya ta Kudu, da Amurka, da Faransa a hanyarta ta zuwa wasan ƙarshe. Wang Yi Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Morocco Morocco Ta Shigar...
    Zakaran kyautar Ballon d’Or ta bana, Ousmane Dembele, ya shiga cikin sahun ’yan wasan ƙungiyar Paris Saint-Germain (PSG) da za ta kece raini da Bayer Leverkusen a gasar Champions League, bayan ya shafe makonni shida a jinya. Dembele, wanda ya samu rauni a cinya yayin da yake wakiltar ƙasar Faransa a farkon watan Satumba, ya shafe makonni yana jinya a cibiyar lafiya ta musamman da ke Qatar, kafin komarwarsa atisaye a makon da ya gabata. Gwamnonin Kano, Katsina da Jigawa sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa wutar lantarki Yadda Morocco ta kafa tarihin ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20 Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewa, kociyan PSG, Luis Enrique, zai yi farin ciki da dawowar Dembele, la’akari da yadda...
    Morocco ta ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20 a karon farko a tarihin gasar, bayan ta doke Argentina da ci 2 da nema, tawagar da ta fi kowace ƙasa a duniya lashewa a tarihi Wannan gagarumar nasara ya sa ta zama ƙasar Afirka ta biyu da ta ɗaga wannan kofi bayan Ghana, wadda ta yi nasara a shekarar 2009. Gwamnonin Kano, Katsina da Jigawa sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa wutar lantarki Kano Pillars ta dakatar da Kocinta A yammacin jiya Lahadi ce aka gudanar da wasan ƙarshe a filin wasa na Estadio Nacional Julio Martínez Prádanos da ke birnin Santiago na Chile, gidan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Universidad de Chile da kuma babbar tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar. ‘Yan wasan tawagar ƙwallon...
    Hukumar gudanarwar Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars ta dakatar da Babban Kocinta Ahmed Garba Yaro Yaro da bai ba da shawara ga  Kocin, Ogenyi Evans, nan take. Ta kuma nada tsohon kyaftin kuma Mataimakin Koci, Gambo Muhammad nan take, ya jagoranci lamuran fasaha na ƙungiyar. Mai horar da masu tsaron raga, Suleiman Shuaibu, zai taimaka masa, yayin da Koci Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai ba da ƙarin goyon baya har sai an fitar da sabbin umarni. Kungiyar ta dauki wannan mataki ne bayan abin da ta kira “rashin tagomashinta” a Gasar Firimiyar Najeriya (NPFL) ta 2025/2026 da ake ci gaba da yi. Sanarwa da kulob ɗin ta fitar, hukumar gudanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bayan...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja October 20, 2025 Labarai Wani Mai Taɓin Hankali Ya Kashe Mutum 1, Ya Raunata 3 A Taraba October 20, 2025 Manyan Labarai ‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta October 20, 2025
    Masu zanga-zangar neman a sako jagoran ’yan awaren Biafra, Nnamdi Kanu sun watse bayan jami’an tsaro sun yi amfani da harsasai masu rai domin tarwatsa su. A safiyar Litinin ɗin nan nan ne masu zanga-zangar suka fito kan titunan Abuja, duk da umarnin kotu da ta hana su zanga-zangar a kuma da a Fadar Shugaban Ƙasa. Zanga-zangar ta samu jagorancin dan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, wanda shi ne mai jagorantar motsin #RevolutionNow. Mutanen sun fara taruwa tun karfe 6:50 na safe a kusa da ofishin Ma’aikatar Harkokin Mata. Shaidu sun ce jami’an tsawon haɗin gwiwar ’yan sanda, da sojoji da DSS da Sibil Difens (NSCDC) ne suka yi dirar...
    Gwamnatin kasar Colombia ta bada sanarwan cewa sojojin Amurka wadanda suke cikin ruwan tekun Carabian sun shiga ruwan yankin kasar kuma sun kashe wani mai kama kifi a itasayen da suke yi a cikin tekun don hana abunda suka kira yaki da safarar miyagun kwayoyi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran IP ya nakalto shugaban kasar ta Colombia yana fadar haka a shafinsa X a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa ‘jami’an gwamnatin kasar Amurka sun aikata laifi, inda suka kashe wani dan kasar mu mai suna Alejandro Carranza a cikin tekun Carabian, sannan ya kara da cewa shi ba mai safarar miyagun kwayoyine ba, aikin kamun kifi shi ne aikinsa tun da dadewa. Gustavo Petro ya kara...
    Gwamnatin kasar Yemen ta kama wasu ma’aikatan MDD a ranar Lahadi a cikin kasar a wani sumamen da Jami’an tsaron kasar suka yi kan sansaninsu, inda suka kama ma’aikatan suka kuma kawace kayakin aikinsu. Shafin yada labarai na Yanar Gizo ArabNews na kasar Saudiya sun ya nakalto kamfanin dillancin labaran Associated Press yana cewa a jiya Lahadi ne jami’an tsaron yemen suka kama yemenawa 11 da kuma yan kasashen waje 15  a wani wurin aikinsu a unguwar Hada na birnin San’a babban birnin kasar. Labarin ya kara da cewa sun sallami 11 daga cikinsu bayan tambayoyi masu yawa. Jean Alam kakakin MDD a yemen ya tabbatar da wannan labarin ya kuma kara da cewa hukumarsa ta tuntubi jami’an gwamnati a...
    Gwamnatin kasar Colombia ta bada sanarwan cewa sojojin Amurka wadanda suke cikin ruwan tekun Carabian sun shiga ruwan yankin kasar kuma sun kashe wani mai kama kifi a itasayen da suke yi a cikin tekun don hana abunda suka kira yaki da safarar miyagun kwayoyi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran IP ya nakalto shugaban kasar ta Colombia yana fadar haka a shafinsa X a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa ‘jami’an gwamnatin kasar Amurka sun aikata laifi, inda suka kashe wani dan kasar mu mai suna Alejandro Carranza a cikin tekun Carabian, sannan ya kara da cewa shi ba mai safarar miyagun kwayoyine ba, aikin kamun kifi shi ne aikinsa tun da dadewa. Gustavo Petro ya kara...
    An saki ɗan jarida, Ibrahim Ɗan’uwa Rano, bayan da ƴansanda suka tsare shi a shalƙwatar Rundunar Ƴansanda ta Zone 1 Kano bisa zargin batanci ga wani mutum. Sakin nasa ya biyo bayan suka da matsin lamba daga ƙungiyoyin fararen hula irinsu Cibiyar Fasahar Bayanai da Ci Gaban Jama’a (CITAD), da Amnesty International, da sauran ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, waɗanda suka bayyana tsarewar tasa a matsayin mataki na keta haƙƙin ɗan Adam da kuma yunƙurin danne ƴancin ƴan jaridu. Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna Fitatccen Ɗan Jarida A Kano Aliyu Abubakar Getso Ya Rigamu Gidan Gaskiya  Ƙungiyoyin sun buƙaci a sake shi ba tare da wani sharaɗi ba, suna mai cewa tsarewar ta saɓawa...
    ’Yan Sanda sun saki ɗan jaridar Kano, Ibrahim Ɗan Uwa Rano, bayan tsare shi da suka yi kan zargin ɓata sunan hadimin Gwamnan Jihar, Abdullahi Ibrahim Rogo. An tsare Rano a Shiyyar ’Yan Sanda ta Ɗaya da ke Kano, bisa zargin ɓatanci. Talauci ne babban maƙiyin ɗan Adam — Atiku ’Yan sanda sun tsare ɗan jarida kan zargin ɓata sunan hadimin gwamnan Kano Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun bayyana tsare shi a matsayin saɓa doka da kuma ƙoƙarin danne ’yancin ’yan jarida.
    A ta bakin shugaban bikin, kuma gwamnan Jihar Tillabery Maina Boukar, taron na wannan karo ya shaida aniyar gwamnatin Nijar, ta bai wa wadanda suka rungumi shirin ajiye makamai damar sauya rayuwarsu, da taimaka musu wajen cimma nasarar komawa cikin al’umma cikin mutunci.   Boukar ya ce, “Wannan muhimmin zabi, ya nuna aniyar gwamnatin Nijar ta kare ikon mulkin kai, da wanzar da tsaro, da tabbatar da zaman lafiya karkashin kyawawan manufofin kasa, ba tare da dogaro ga wasu ajandoji daga ketare ba.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi October 19, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki October 18, 2025...
    Jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Ruguza Gaza “ba abin da za a gaskata ba ne” domin an rusa yankin gaba daya Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai, Tom Fletcher, ya ce: Girman barnar da aka yi a zirin Gaza abu ne da ba za a taba mantawa da shi ba, yana mai jaddada cewa, “an ruguza komai tare da mai da yankin baraguzai,” yana mai nuni da irin barnar da aka yi wa ababen more rayuwa, da gidaje, da kashe fararen hula. A cikin wata sanarwa ga gidan talabijin na Al Jazeera, Fletcher ya nuna cewa an riga an fara shirin ba da agajin jin kai na kwanaki 60. Shiri ne mai...
    “Wannan mummunan lamari da ya faru a ranar 11 ga Oktoba, 2025, a Wawa Cantonment, Jihar Neja, ya haifar da yanayi mai cike da tashin hankali, inda mazauna sansanin suka shiga cikin mamaki kan yadda irin wannan abin takaici zai iya faruwa,” in ji wani bangare na sanarwar.   A cewar rundunar sojoji, an gano gawarwakin Lance Corporal Femi da matarsa a cikin gidansu dake gini na 15, daki mai lamba 24, Corporals and Below Kuarters, a cikin sansanin.   Binciken farko ya nuna cewa sojan yana kan aiki a lokacin kuma ya nemi izini daga babban jami’i domin ya kula da wasu harkokin kansa kafin ya dawo aiki.   “Rundunar Sojin Nijeriya tana matukar bakin ciki kan wannan lamari,...
    Rundunar Sojin Saman Najeriya, ta bai wa mutanen garin Buhari da ke Karamar Hukumar Yunusari a Jihar Yobe, tallafin Naira miliyan 23 tare da alƙawarin gina rijiyar ruwa mai amfani da hasken rana. Wannan tallafi ya biyo bayan wani harin kuskure da jiragen yaƙin rundunar suka kai a watan Satumba 2021, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane takwas da jikkata wasu 30. Wasu jiga-jigan ADC za su dawo jam’iyyarmu — Shugaban Jam’iyyar APC HOTUNA: Al’ummar Jihar Neja sun yi addu’o’in neman zaman lafiya Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritay), wanda shi ne mai bai wa Gwamna Buni shawara kan harkokin tsaro, ya bayyana cewa wannan tallafi ya nuna tausayin gwamnati da rundunar sojan sama ga al’ummar garin. Ya ce, tun bayan...
    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa a Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya yi iƙirari cewa ministoci da manyan hafsoshin sojin ƙasar sun taya shi murnar bayan bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka kammala. Issa Tchiroma Bakary ya bayyana cewa ministoci da manyan jami’an tsaron da ministocin sun kira shi a waya suna jaddada goyon bayansu da niyyar biyayya ga kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma abin da al’umma suka zaɓa. Ya bayyana haka ne wani a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, yana mai nuna godiya ga waɗanda suka goyi bayansa, tare da jaddada cewa wannan lokaci yana da muhimmanci matuka ga kasa. Ya ce, “Ina godiya daga zuciyata ga ministoci...
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yaman Sayyid Abdul-Malik Badreddin al-Houthi ya yi jawabi a yammacin yau alhamis kan batutuwa daban-daban da suka shafi duniyar musulmi, musamman abubuwan da suka faru a Gaza da Yemen. Ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ba tare da la’akari da duk wani matsin lamba ba, ta yi sadaukarwa ta karshe a kan turbar goyon bayan Falasdinu, kuma ta bayar da dama ga kwamandojin gwagwarmayar ‘yanci, daga cikinsu akwai babban kwamandan shahidi Qassem Soleimani. Yayin da yake magana kan zagayowar shahadar babban kwamanda Yahya al-Sinwar, Sayyid Abdul-Malik Badreddin ya ce: “Babban darussan da ya bari na tsararraki, da kuma matsayinsa na sadaukar da kai da jihadi, suna wakiltar muhimman dabi’u da kuma babban...
    Jakadan Amurka na Musamman kan Harkokin Larabawa da Afirka, Massad Boulos, ya ƙaryata iƙirarin cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya babu gaira babu dalili. Ya ce hare-haren ta’addanci da ke faruwa a ƙasar suna shafar Kiristoci da Musulmai baki ɗaya. An rantsar da Randrianirina shugaban Madagascar Gwamnan Gombe ya ƙaddamar da shirin tallafa wa karatun yara mata Boulos, wanda mashawarci ne ga Shugaban Amurka Donald Trump, ya faɗi hakan ne bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a ranar Jumma’a. Wasu ’yan majalisar dokokin Amurka sun nemi gwamnatin Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashe masu hatsari wadda ake zaluntar Kiristoci. Sai dai Jakadan ya ce lamarin ba haka yake ba. “Waɗanda suka san...
    An rantsar da Kanal Michael Randrianirina a matsayin sabon shugaban gwamnatin sojin Madagascar, bayan ya jagoranci hamɓarar da shugaba Andry Rajoelina. Sabon shugaban Madagascar kuma ya jaddada cewa hawan sa, ba juyin mulki ba ne, domin ya samu goyon bayan kotun tsarin mulkin ƙasar. Gwamnonin APC sun yi taro a Jihar Kebbi ’Yan sanda sun ƙwato miyagun ƙwayoyi a Gombe Bayan ya sha rantsuwar kama aiki Kanal Randrianirina ya ce abubuwan da zai fi bai wa fifiko sun haɗa da ruwan sha da abinci da kuma kafa gwamnati. Tsohon shugaban Ƙasar Rajoelina wanda ’yan majalisar ƙasar suka tsige bayan tserewarsa waje a ƙarshen makon jiya, ya yi Allah wadai da juyin mulki kuma yaƙi amincewa da murabus duk da baya cikin...
    Abokan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa: Sake dawo da takunkumi bayan karewarsa baya da wani tushe na doka ko tsari Kungiyar aminan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wata sanarwa game da cikar kudiri mai lamba 2231 kan yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran a ranar 18 ga watan Oktoba, inda ta bayyana cewa matakin da Amurka da Turai suka dauka na sake daukar matakin kakaba takunkumin da ya kare kan wata kasa tsari ne da baya ya kan wani tushe na doka ko yarjejeniyar kasa da kasa. Kungiyar aminan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wata sanarwa a ranar Alhamis da ke nuna cikar kuduri mai lamba 2231 na kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya...
    Zanga-zangar miliyoyin mutane a birnin Sana’a na sabunta alkawarin da aka yi wa shahidai tare da tabbatar da shirin tallafawa Falasdinu Babban birnin kasar Yemen, Sana’a, ya halarci wani tattaki na miliyoyin mutane a yau Juma’a mai taken “Shekaru biyu na bayar da gudummawa… da aminci ga jinin shahidai”, tare da tabbatar da gwagwarmaya na goyon bayan al’ummar Falastinu tare da sabunta alkawarin bin tafarkin shahidai da azama. Daruruwan jama’a a dandalin Al-Sabeen a lokacin tattakin bayar da amana ya kunshi zurfafa fahimtar al’amuran al’umma. Sun yi nuni da cewa al’ummar Yemen duk da killacewar wuce gona da iri, amma suna nan a fagagen alfahari da daukaka, da tsayin daka kan tafarkinsu na imani da jihadi. Daruruwan mutane daga cikin...
    Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka, inda ta gudanar da samame a wata maɓoya da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci da safarar ƙwayoyi a cikin jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ta bayyana cewa jami’an da ke ƙarƙashin Gombe Division ne suka gudanar da samamen da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar Alhamis 10 ga Oktoba, 2025. Dantawaye ya zama sabon kwamishinan ’yan sandan Abuja Wani mutum ya ƙona tsohuwar budurwarsa a Oyo A cewar sanarwar, jami’an sun kai samamen wata maɓoya da ke bayan jerin shagunan Ƙaramar hukumar Gombe, (Local Government Shopping Complex), inda ake zargin...
    Saboda haka, an samu labari daga bangaren Obi cewa, tsohon dan takarar shugaban kasa ba za yi zaben fid da gwani ba da Atiku. Sai dai kuma, sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya ki cewa uffan kan jita-jitan da ke cewa jam’iyyar ta yanke shawarar gudanar da zaben fid da gwani, wanda hakan ya saba wa tsammanin wasu mambobin, musamman daga bangaren Obi. A cewar Bolaji, a halin yanzu ADC ba ta mai da hankali kan wane zai tsaya takara a karkashin tutan jam’iyyar ADC a zaben 2027 ba. “A halin yanzu dai, babu wanda aka tattaunawa kan cewa shi ne sahihin dan takara ko kuma za su gudanar da zaben fitar da gwani. Idan mun kai...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima  October 17, 2025 Labarai Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma October 17, 2025 Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025
    Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Shugaba Tinubu ya yi wa akasarinsu sassauci ne, bisa rahotannin da ke cewa; wadanda aka yanke wa hukuncin, sun nuna matukar nadama da kuma halin kirki. Haka zalika, ya yafe wa wasu saboda tsufa da samun sabbin fasahohin sana’o’i, ko shiga Jami’ar NOUN. Shugaba Tinubu ya kuma gyara rashin adalcin tarihi, wanda Turawan mulkin mallaka na Burtaniya suka yi wa Sir Herbert Macaulay, daya daga cikin masu kishin kasa a Nijeriya.   A takaice dai, kwamitin bai wa shugaban kasa shawara, kan jinkai, karkashin jagorancin babban mai shari’a; kuma ministan shari’a, Prince Lateef Olasunkanmi Fagbemi, ya bayar da shawarar yin afuwa ga fursunoni biyu da 15 da aka yankewa hukunci, wadanda 11 daga cikinsu sun...
    Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Shugaba Tinubu ya yi wa akasarinsu sassauci ne, bisa rahotannin da ke cewa; wadanda aka yanke wa hukuncin, sun nuna matukar nadama da kuma halin kirki. Haka zalika, ya yafe wa wasu saboda tsufa da samun sabbin fasahohin sana’o’i, ko shiga Jami’ar NOUN. Shugaba Tinubu ya kuma gyara rashin adalcin tarihi, wanda Turawan mulkin mallaka na Burtaniya suka yi wa Sir Herbert Macaulay, daya daga cikin masu kishin kasa a Nijeriya.   A takaice dai, kwamitin bai wa shugaban kasa shawara, kan jinkai, karkashin jagorancin babban mai shari’a; kuma ministan shari’a, Prince Lateef Olasunkanmi Fagbemi, ya bayar da shawarar yin afuwa ga fursunoni biyu da 15 da aka yankewa hukunci, wadanda 11 daga cikinsu sun...
    A jiya Alhamis jiragen yakin HKI sun kai hare-hare na wuce gona da iri garuruwa mabanbanta na kudancin Lebanon da hakan ya yi sanadiyyar shahada da kuma jikkatar mutane da dama. Majiyar tsaro daga kudancin Lebanon ta ambaci cewa, mutum daya ya yi shahada yayin da wasu 7 su ka jikkata. Hare-haren sun shafi garin Kafar-Tabinet da kuma akan hanyar Kausariyyah al-siyadah. Haka nan kuma jiragen na ‘yan sahayoniya sun kai wasu hare-haren a garin Ansariyyah, da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar mutane 6. Hare-haren na HKI suna a karkashin keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label...
    Hakazalika, ta bai wa mata 30 masu kananan sana’o’i tallafin buhun gawayi, da kilo 10 na Shinkafa da litar man girki.   Bugu da kari, ga kungiyoyi shida na mata manoma, kowacce za ta karɓi fanfunan feshi, famfun ruwa, da kuma maganin feshin ciyawa.   Hajiya Shema’u, ta yaba da karuwar adadin mata a harkar noma, inda ta ce, manoma mata da suka yi rajista da NAWIA a yanzu sun haura 2000, yayin da wadanda ba su yi rajista ba sun kai 5,000.   Shemau ta kuma mika godiyarta ga Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajjiya Hurriya Dauda bisa namijin kokarin da take yi na bunkasa noman mata a Jihar Zamfara.   Sauran hukumomin da kungiyoyin da suke tare da NAWIA...
      Ya ce kamar ko da yaushe, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan muhimmiyar rawar da FAO ke takawa a bangaren aikin gona da samar da abinci a duniya.   An kafa hukumar FAO ne a ranar 16 ga watan Oktoban shekara ta 1945, kuma Sin na daya daga cikin kasashe mambobi da suka kafa ta. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar? October 16, 2025 Daga Birnin Sin Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin October 16, 2025 Daga Birnin Sin Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da...
    Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-med mai hedkwata a Geneva ta yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da shiga Gaza ba tare da ‘yan jarida, masu bincike, da masana harkokin shari’a don tattara bayanan kisan kiyashin da Isra’ila a Gaza da kuma hukunta wadanda suka aikata laifin. A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, Hukumar ta ce, biyo bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a Masar ranar Litinin, “Dole ne duniya ta ga abinda ya kasance a Gaza.” Kungiyar ta ce a yanzu dole ne a bar duniya ta ga irin barnar da aka yi, wa matsugunai, da kuma haddassa wahalhalun ga bil adama sanadin yakin da Isra’ila ta yi na...
    Gwamnatin Jihar Kano ta ce nan ba da jimawa ba za a fara ƙera fanel da sauran kayayyakin samar da wutar lantarki daga hasken ranar a jihar. Hakan a cewar gwamnatin ya biyo bayan samun masu zuba jari a fannin na makamashi, bayan rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanoni biyu da suka shahara a fannin, wato Tricell Solar Solutions da IRS Green Energy.. ’Yan sanda sun kama gungun masu fashi a kan hanyar Katsina zuwa Kano Ka da a ɗora wa Tinubu laifin rikicin da ke faruwa a PDP — Fayose An kulla yarjejeniyar ne tare da haɗin gwiwar Hukumar Wutar Lantarki ta Karkara (REA) domin bayar da shawarwari na fasaha da daidaita ayyuka, a yayin taron Sabunta Makamashi na...
    Wani daga cikin waɗanda suka ji rauni, wanda shi ne mai kuɗin, ya gode wa jami’an FRSC bisa gaskiya da amana da suka nuna, yana mai cewa abin koyi ne ga kowa. FRSC ta gargaɗi direbobi da su riƙa kula da motoccinsu akai-akai tare da bin ƙa’idojin hanya domin guje wa aukuwar haɗura. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato October 16, 2025 Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October 16, 2025 Labarai Kafafen Sada Zumunta Na Zamani Suna Taimakawa Wajen Ta’azzara Matsalar Tsaro A Arewa – Yari  October 15, 2025
    Hukumomi a Isra’ila sun ce gwamnatin ƙasar ta yanke shawarar taƙaita shigar da kayan agaji zuwa zirin Gaza, sannan za ta ɗan dakata ta buɗe bakin iyakar zirin daga Rafas. Isra’ila ta ce ta ɗauki wannan matakin ne saboda abin da ta kira jan ƙafa da a cewarta Hamas ke yi wajen mayar da sauran gawarwaki da ke hannunsu. Zuwa yanzu dai gawarwaki huɗu kawai Hamas ta miƙa, sannan akwai rahotannin da ke cewa ƙungiyar za ta miƙa wasu gawarwakin guda huɗu, amma ta ce nemo gawarwakin na da wahalar gaske. Shi ma Donald Trump ya yi ƙorafi, inda ya buƙaci Hamas ta mayar da gawarwakin “kamar yadda aka yi alƙawari,” in ji shi. Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta...
    Kwanturola na hukumar gyaran Hali a Najeriya reshen jihar Zamfara, Murtala Muhammad Haruna, ya yi kira da a shigar da fursunoni cikin tsarin inshorar lafiya na kasa (NHIS) domin tabbatar da samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya.   Ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga kwamishiniyar lafiya ta jihar Zamfara, Dakta Nafisa Muhammad Maradun, a ofishinta da ke Gusau.   Haruna ya ce shirin ya yi dai-dai da hangen nesan babban kwamandan hukumar gyaran hali ta Najeriya da nufin inganta jin dadin fursunonin da ke gidajen yari.   Kwantirolan ya kuma jaddada bukatar inganta asibitin hukumar da ke cibiyar tsaro ta matsakaita, Gusau, da samar da isassun kayan aikin likita da magunguna masu mahimmanci...
    Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Sanata Ahmed Wadada Aliyu murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya bayyana shi a matsayin ma’aikaci mai tawali’u, mai aminci, kuma mai kishin kasa wanda irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasa abin a yaba ne.   Shugaban ya yaba wa Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma kuma shugaban kwamitin majalisar dattijai kan asusun gwamnati bisa “kishin sa na gaskiya, rikon amana, tsarin kasafin kudi, da dokoki masu tasiri da ke magana kan makomar kasarmu.”   Da yake karin haske kan tarihin Sanata Wadada a Majalisar Dokoki ta kasa, Shugaba Tinubu ya lura cewa “a cikin shekaru biyu kacal a Majalisar Dattawa, kun bambanta kanku a cikin doka, wakilci, da kuma kulawa...
    Hukumar Noma da Raya Karkara ta Jihar Kano (KNARDA) ta yi kira ga manoma da masu ruwa da tsaki a harkar noma da masu kirkire-kirkire a jihar da su shiga baje kolin noma na kasa da ke tafe.   A cikin wata sanarwa da Sashen Kula da Ayyukan Yada Labarai, KNARDA ya fitar, ta bayyana taron a matsayin wani babban dandali na baje kolin kayayyakin amfanin gona, da fasahohin zamani, da ke inganta samar da abinci da raya karkara.   Hukumar ta ja hankalin daidaikun jama’a da kungiyoyi a Kano da su yi amfani da wannan damar wajen gabatar da nasarorin da suka samu da kuma gano sabbin hanyoyin kasuwanci a fannin noma.     KNARDA ta kuma jaddada aniyar...
    Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar ‘yan baruwanmu a  taronsu karo na 19  da ke gudana a birnin Kampala na kasar Uganda a ranakun 15 da 16 ga wannan wata na Oktoban 2025, sun bayyana matukar damuwarsu kan halin da ake ciki a yankin Caribbean, tare da tabbatar da cikakken goyon bayansu ga Jamhuriyar Venezuela wajen fuskantar duk wata barazana daga waje. Ministocin sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, inda suka nuna matukar damuwa kan yadda lamurra suka kara tabarbarewa sakamakon tura karin sojoji da kayan yaki da Amurka ta jibge a yankin, wanda hakan ke nuni karuwar barazana ta tsaro a daukacin yankin. Haka nan kuma Ministocin sun yi nuni da muhawarar baya bayan nan...
    An tallafawa ‘yan Kasuwa ƙanana, kuma an rage fitar da hayakin da ke gurɓata muhalli a faɗin nahiyar Afirka.   Gwamna Uba Sani ya bayyana wannan nasara a matsayin babbar gagarumar bajinta da kuma abin alfahari ga Jihar Kaduna da NIjeriya baki ɗaya, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a fannin kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire domin bunƙasa tattalin arziki da bai wa matasa dama.   “Wannan nasara ta sake tabbatar da ƙwarewar ƙirƙira da ƙarfin tunanin matasan Jihar Kaduna. Muna gina tattalin arzikin da ke dogaro da kirkira wanda ke daraja ra’ayi tare da haɓaka baiwa” in ji Gwamna Uba Sani.     “Daga ajujuwa zuwa manyan matakan duniya, matasan Kaduna suna jagorantar makomar...
    Shugaban kasar Indonusiya  Prabowo Subianto ya sanar da irin ci gaban da aka samu game da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a gaza, kana ya sanar cewa Jakarta a shirye take ta aike da dakarun tabbatar da zaman lafiya, domin nuna irin tsawon lokacin da kasar ta dauka tana nuna goyon bayanta ga alummar falasdinu a gwagwarmyar neman yanci da suke yi. Kasar Indonusiya tana da tsohon tarihi wajen nuna goyon bayan neman bada yancin ga alummar falasdinu, sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi a Gaza ya bude wata kofa ta tabbatar da zaman lafiya a yankin, kuma kasar a shirye take ta aike da kayan agaji,  bangaren diplomasiya, aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiya...
      Bugu da kari, shugaba Xi ya ce a shirye yake ya hada hannu da Patrick Herminie wajen aiwatar da sakamakon taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC a matsayin wata dama ta ci gaba da daukaka dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare zuwa manyan matakai da kara kyautatawa jama’arsu. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya October 14, 2025 Daga Birnin Sin Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani October 14, 2025 Daga Birnin Sin Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka...
    Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta zuba jari a fannin kayan aikin wanke hannu da kuma ilimin tsafta. Asusun ya kuma ce kaso 35 cikin 100 na makarantu ne kawai ke da kayan wanke hannu na asali, yayin da kashi 8 cikin 100 na ’yan Najeriya ne kawai ke iya nuna yadda ake wanke hannu daidai. Gwamnan Bayelsa ya fice daga jam’iyyar PDP Kotu ta umarci a tono gawarwakin wadanda gobara ta kashe a Legas don yin bincike Yayin wata ziyara da aka kai makarantu a Jihar Borno a ranar Laraba, a wani ɓangare na bikin Ranar Wanke Hannu ta Duniya ta shekarar 2025, Shugabar Ofishin UNICEF a Maiduguri, Dr....
    Kwamatin harkokin lafiya na majalisar dokokin jihar Jigawa ya ce gyaran fuskar da aka yiwa dokar da ta kafa asusun adashen gata na kiwon lafiya na jihar ya sahalewa asusun damar samo kudade daga wasu bangarori da ba na gwamnati ba. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Guri, Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari, ya yi wannan tsokaci lokacin da ya jagoranci ‘yan kwamatin domin ziyarar aiki a ofishin asusun da ke Dutse. Ya bayyana bukatar ganin asusun JICHIMA ya nemo kudade daga hannun masu taimakon al’umma da cibiyoyi da ‘yan siyasa da kwamitocin zakka da na waqafi domin bunkasa asusun, ta yadda zai biya bukatun kiwon lafiyar al’ummar jihar. Alhaji Usman Musari ya lura cewar fadada hanyoyin samun kudade ga...
    Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya kungiyar kwallon kafa ta kasaSuper Eagles murnar nasarar da suka samu ta ci 4 da nema a kan Cheetahs ta Jamhuriyar Benin, tare da yabawa ƙungiyar bisa ƙoƙarin da take yi na ci gaba da kokarin cika al’umma, yayin da suke neman cancantar zuwa gasar cin Kofin Duniya ta FIFA a shekarar 2026. Shugaban ƙasar ya jinjina wa Super Eagles bisa ƙwazo, da jajircewar da suka nuna a filin wasa na Uyo, yana mai cewa wannan gagarumar nasarar ta sake karfafa ‘yan Najeriya kan harkar ƙwallon ƙafa. “Yanayin farin ciki da ake ciki a fadin ƙasar nan na nuni da yakinin da muke da shi  cewa Najeriya ta cancanci samun gurbi a gasar...
    Yansanda a kasar Italia sun kara da masu zanga zanga masu kuma goyon bayan Falasdinawa, don hana a gudanar da wasan kwallon kafa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta HKI da kuma ta kasar Italia a filin wasa na Udine a jiya Talata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa gwamnatin kasar Italia ta aika yansanda fiye da 1000 guda, tare da jiragen sama masu saukar ungulu don hana masu zanga –zangar isa filin wasan. Labarin ya kara da cewa zanga-zangar wacce kwamitin masu goyon Falasdinawa ya shirya. Zanga-zangar don hana wasan ta ilimunation wato fidda goni na masuhalattar gasar duniya ta FIF 2026. Daga karshe  dai an yi gasar kuma kasar Italiya ta lallasa HKI da 3-0....
    Jagoran ’yan adawa na kasar Kenya kuma tsohon Firaministan kasar, Raila Odinga, ya mutu yana da shekaru 80 a lokacin da yake karɓar magani a ƙasar Indiya, kamar yadda majiyoyin asibiti da ’yan sanda suka tabbatar a ranar Laraba. Rahotanni daga Asibitin Devamatha da ke Kerala, kudancin Indiya, sun ce Odinga ya samu bugun zuciya mai tsanani a lokacin da yake yawo da safe kusa da otal ɗinsa a birnin Kochi. Kotu ta umarci a tono gawarwakin wadanda gobara ta kashe a Legas don yin bincike Majalisa ta gayyaci CBN da bankunan kasuwanci kan yawan cire wa kwastomomi kuɗaɗe An garzaya da shi zuwa asibiti nan take, amma likitoci sun tabbatar da rasuwarsa lokacin da suka isa. Hukumomin ’yan sanda...
    Wasu kudurori guda 3 da ke dauke da bukatun kafa wasu hukumomi 3 sun samu karatu na biyu a zauren majalaisar dokokin jihar Jigawa. Kudurorin guda 3 sun hada da na kafa Hukumar Samar da Hanyoyin Mota a yankunan karkara, da na kafa Hukumar Samar da Kudade Domin Ayyukan Hanyoyin Mota a yankunan karkara da Kuma na Hukumar Bunkasa Kwazon Malamai ta jihar Jigawa. A lokacin ya ke gabatar da kudurorin domin neman goyon baya kan bukatar kafa hukumar bunkasa kwazon malamai, mataimakin shugaban masu rinjaye na majlaisar, Alhaji Sani Sale Zaburan ya ce gwamnatin jihar na da nufin inganta aikin koyarwa ta hanyar kafa hukumar da za ta rinka horas da malamai akai akai. Da su ke tattaunawa kan...
    Mahaifin margayi Bilyaminu wanda matarsa Maryam Sanda ta kashe,  ya ce shi ne ya roki Shugaba Tinubu ya yafe mata duk da hukuncin kisa da kotu ta yanke mata kan laifin. Malam Ahmed Bello Isa ya bayyana haka ne yayin ganawa da ’yan jarida, tare da mahaifin Maryam, Alhaji Garba Sanda. Sun gudanar da taron ’yan jaridar ne bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan yafiyar da Shugaban Kasa ya yi mata tare da wasu mutane 174 da ke tsare a gidajen yari bayan an yanke musu hukunci kan manyan laifuka daban-daban. Aminiya ta ruwaito dangin Bilyaminu ta hannun Dakta Halliru Bello Muhammad, wanda kawu marigayin ne kuma a hannunsa ya taso  yana bayyana yafiyar da aka yi wa Maryam Sanda...
    Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Islamic Jihad ta yi maraba da sako Falasdinawa kusan 2000 daga gidajen yarin Isra’ila, tare da cewa jarumtakar mayakan gwagwarmaya da hadin kan al’ummar Falasdinu ne ya haifar da wannan babbar nasara. A cikin wata sanarwa da babban sakataren kungiyar Ziyad al-Nakhalah ya fitar ya bayyana cewa, wannan yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta samo asali ne sakamakon jajircewa da tsayin daka da hadin kan al’ummar Falasdinu, wanda idan ba tare da hakan ba yarjejeniyar ba za ta taba cimma ruwa ba. Bayan shafe sama da shekaru biyu ana kai hare-hare ba kakkautawa wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubun dubatan Falasdinawa, gwamnatin Isra’ila bisa matsin lambar kasa da kasa ta amince da yarjejeniyar da Amurka ta kulla...
    Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da PDP ke shirin gudanar da babban taronta na ƙasa da za a yi a Ibadan, a Jihar Oyo, daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan October 14, 2025 Siyasa Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi October 11, 2025 Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025
    Rasha ta kai harin jirage kan ayarin kayan agajin Majalisar Dinkin Duniya a makwabciyarta kasar Ukraine da suka fi shekara biyu suna yaki. Hukumomin Ukraine sun dakarun soji da ke yankin kudancin Kherson da suka mamaye a Ukraine ne suka kai harin a ranar Talata, inda suka lalata motocin Shirin Abinci na Duniya, a yayin da ma’akatan agajin suka shafe kimanin awa hudu ba su motsa ba saboda luguden bamabaman. Kwamandan hukumar soji da ke yankin ta bayyana cewa an kona motoci hudu tare da lalata wata a cikin tawagar kayan agajin, amma ba a samu asarar rayuka ba a harin da aka kai da jirage marasa matuka da manyan bindigogin atilare a garin Bilozerka. Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Andriy Sybiga...
    Duban dubatan mutane sun gudanar zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa da kuma yin tir da kokarin samar da huldar jakadanci da HKI a maida kome kamar ba abinda ya faru. Sun kuma bayyana tsagaita wutan da aka samar da Hamas tana tangal tangal saboda tun farko ba’a gina shi kan yadda zata dore ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu zanga-zanga suna cewa, wannan sulhun da kasashen yamma suka kulla da Hamas wani makirci ne na kara samun iko kasashen musulmi da ma wasu kasashen wadanda ban a musulmi ba. Sun kuma bayyana cewa, bayan shekaru biyu da kissan kiyashi sun samar da abinda suka kira sulhu ne na wani lokaci, amma zaman lafiya ba zata taba...
    Dangin Marigayi Bilyaminu Ahmed Bello sun bayyana takaicinsu bisa sanya matarsa, Maryam Sanda, wadda kotu ta ɗaure ta kan laifin soka masa wuka har lahira, a cikin jerin mutanen da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa afuwa. A shekarar 2020 ne kotu ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun ta da laifin kashe mijinta Bilyaminu. Sanarwar da dangin marigayin suka fitar ɗauke da sa hannun Dakta Bello Haliru Mohammed (Dangaladiman Gwandu) ta bayyana afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda a matsayin “mummunan famu,” da kuma ƙololuwar rashin adalci ga ɗan uwansu. Sun bayyana takaici bisa sakin Maryam Sanda daga gidan yari, wanda suka kira da neman faranta wa danginta rai, ba...
    Rahotanni sun bayyana cewa wani ƙazamin faɗa ya barke tsakanin wata ƙabilar Palasɗinawa masu ɗauke da makamai da ƙungiyar Hamas a yankin zirin Gaza bayan an kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ila. A ranar Litinin da aka fara musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra’ila ne rahotanni suka ɓulla game da faɗan da ya ɓarke tsakanin mayaƙan Hamas da ƙabilar Doghmush a ranar Lahadi. Wani jami’in Hamas ya bayyana cewa an samu asarar rayuka daga kowane ɓangare a yayin musayar wutan daga misalin ƙarfe 9.30 na dare ranar Lahadi. Wani mazaunin yankin Sebra da ke Birnin Gaza, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa “Mayaƙan Hamas kimanin 200 ne suka zo aka fafata da su, har sai da suka...
    Rahotanni sun bayyana cewa an gano daruruwan gawawwaki a karkashin burabutsai a yankin gaza bayan sanar da dakatar da bude wuta tsakanin isra’ila da kuma kungiyar Hamas, adadai lokacin da tawagar agaji ke ci gaba da gano gawarwaki da suka makale a karkashin duwatsu bayan kwashen shekaru 2 Isra’ila na kisan kare dangi, Majiyar Asibiti a yankin Gaza ta sanar a yau litinin cewa akalla an gano gawarwakin mutane 323 da suke karkashin burabutsai,  kuma har yanzu akwai gawarwarki sama da 10,000 da ke karkashin gine –gine da aka rusa a yankin Gaza. Bisa kidddigar da majalisar dinkin duniya ta gabatar ya nuna cewa an rusa gidaje 430,000 a yankin Gaza sakamakon hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai...
    Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a cibiyar ASUU ta ƙasa da ke Jami’ar Abuja, inda ya zargi gwamnatin tarayya da rashin gaskiya wajen tattaunawa kan buƙatun ƙungiyar. Don haka sun fara yajin aiki daga yau na gargadi na tsawon mako biyu. Ana ta bangaren Gwamnatin tarayya ta gargadi ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) da ta guji shiga yajin aiki, tana mai jaddada cewa dokar “babu aiki, babu albashi” tana nan daram. Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, tare da ƙaramin Ministan Ilimi, Farfesa Suwaiba Sai’d Ahmed, sun bayyana haka a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ya fitar a ranar...
    “Shekaru goma da suka wuce, gudummawar da ma’adanai ke bayarwa ga GDP na kasarmu bai wuce 0.5% ba, amma a yau ya karu zuwa 1.8% – alkalumman NBS suka nuna a cikin rabi na biyu na 2025 wanda ba a taba ganin irinsa ba”.   Da yake tsokaci kan ci gaban fannin, Ministan ya bayyana cewa, makon hako ma’adanai na Nijeriya ya yi nuni da yadda masana’antar ke sauya tunani zuwa tsari mai kyau, da sabbin abubuwa, da ke lalubo masu zuba jari na kasa da kasa.   Ya bayyana cewa, sauye-sauyen sun tattara ne a kan gaskiya, rage haɗari, da inganta masana’antar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27...
    Sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram 9 tare da kwato kudi fansa kimanin Naira miliyan 5 a  yankunan Magumeri da Gajiram a jihar Borno. Kakakin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), Laftanar Kanar Sani Uba , ya ce sojojin da suke sintiri a yankunan ne suka hallakan mayakan bayan sahihan bayanan sirri kan zirga-zirgar ’yan ta’addan a kusa da Goni Dunari a Karamar Hukumar Magumeri. Sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 11 ga Oktoba, 2025 ta ce, “Dakarun mu sun yi gaggawar daukar matakin dakile barazanar bayan da suka ga yadda ’yan ta’addan suka kona gidaje tare da tsoratar da mutanen yankin.” Ya bayyana cewa sojoji sun yi artabu da ’yan ta’addan ne bayan sun shafe sa’o’i hudu suna...
    Sufeton ƴansanda na Ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, ya maye gurbin Kwamishinan ƴansandan birnin tarayya, CP Ajao Adewale, sakamakon ƙaruwar matsalolin tsaro a Abuja. Wannan mataki ya biyo bayan matsin lamba da yake fuskanta saboda rashin gamsuwa da aikinsa tun bayan karɓar ragama daga CP Benneth Igwe. Majiyoyi daga cikin rundunar sun bayyana cewa sauya shi ya shafi yadda matsalolin tsaro ke ƙaruwa a Abuja, musamman bayan harin fashi da makami da ya yi sanadin mutuwar mai gabatar da shirye-shiryen gidan talabijin ɗin ARISE, Somtochukwu Maduagwu, da mai gadi Barnabas Danlami, a Katampe, ranar 29 ga Satumba, 2025. Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna  NAFDAC Ta Rufe Manyan Shaguna 2 Na...
      Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF) ta tabbatar da cewa ta dauki matakin gaggawa bayan faruwar lamarin inda aka aike da wani jirgin sama daga Legas domin jigilar tawagar zuwa Uyo, sai dai lamarin ya haifar da tsaiko a shirin da tawagar ta ke yi na tunkarar jamhuriyar Benin a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2026. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0 October 9, 2025 Wasanni Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane October 7, 2025 Wasanni Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni October 6, 2025
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Maryam Sanda afuwa, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Haliru Bello. Maryam,’ mai shekara 37, ta shafe shekaru shida da watanni takwas a gidan yarin Suleja kafin yi mata afuwa. Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro Rahotanni sun nuna cewar an yi mata afuwar ne bayan yin nadama da aikata kyakkyawan halaye. Iyayen Maryam sun roƙi gwamnati da ta sake ta saboda ’ya’yanta biyu da ta ke da alhakin kula da su, tare da alƙawarin sauya...
    Haka zalika, sun ki bayyana takamaiman wajen da za a daura auren, har sai bayan an kammala, inda suka bayyana yin hakan a matsayin wata hanya ta kawar da cece-kuce daga al’umma.   Kazalika a ‘yan watannin da suka gabata kuma, an sake daura auren jaruma a masana’antar Kannywood, Rahama Sadau tare da angonta Ibrahim Garba, a wani biki wanda za a iya kira da na sirri da aka gudanar a birnin Kaduna, daura auren shahararriyar jarumar Kannywood din, Rahma Sadau da mijinta Ibrahim Garba, wanda aka gudanar a ranar Asabar, ya yi matukar bai wa mutane mamaki, duba da cewa; kafin daurin auren babu wata alama ko sanarwa da aka fitar daga makusantan mijin ko matar.   An yi...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Maryam Sanda afuwa, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Haliru Bello. Maryam,’ mai shekara 37, ta shafe shekaru shida da watanni takwas a gidan yarin Suleja kafin yi mata afuwa. Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro Rahotanni sun nuna cewar an yi mata afuwar ne bayan yin nadama da aikata kyakkyawan halaye. Iyayen Maryam sun roƙi gwamnati da ta sake ta saboda ’ya’yanta biyu da ta ke da alhakin kula da su, tare da alƙawarin sauya...
    Kungiyoyin matasa na ci gaba da gudanar da zanga-zanga a Morocco, Sarkin Mohammed na shida, ya bukaci zababbun jami’ai a kasar da su daina jan kafa wajen kyautata rayuwar al’ummar kasar, yana mai cewa inganta harkonin ilimi da kiwon lafiya shi ne abinda ya kamata a fi ba muhimmanci. An jima ana dakon jawabin sarkin na wannan juma’a, tun bayan da masu zanga-zangar, suka fara mamaye titunan biranen kasar kusan ko wanne dare tun daga ranar 27 ga watan da ya gabata na Satumba. Masu zanga-zangar dai wadda ake yiwa lakabi da Gen Z, na ci gaba da ƙ kiraye-kirayen kawo sauyi, ko da yake a yayin jawabin Sarkin na wannan Juma’a bai yi magana kai tsaye game da ita...
    Baya ga Maryam Sanda, Shugaba Tinubu ya kuma yafe wa wasu mutane da dama, ciki har da Janar Mamman Vatsa, Herbert Macaulay, da Faruku Lawan, wanda tsohon ɗan majalisar tarayya ne daga Jihar Kano. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025 Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025 Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025
    Farfesa Jeffrey Sachs na jami’ar Columbia, ya yaba wa nasarorin da Sin ta samu, inda ya ce, “shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, wani shiri ne mai ban mamaki kuma na musamman.”   Farfesa Sachs ya fadi hakan ne a kwanan nan, yayin da wakiliyar rukunin gidan rediyo da talibijin kasar Sin wato CMG ta zanta da shi. Ya kuma bayyana cewa, kamar yadda shugaban kasar Xi Jinping ya fada a karon farko, yayin gabatar da wannan shawara, tushen ta ya samo asali ne daga hanyar kasuwanci ta hanyar siliki, hanyar dake da tarihin fiye da shekaru dubu biyu tsakanin yankin gabas da yamma. Ya ce, “Idan kina nazarin tattalin arziki kamar yadda nake yi, za ki yi imanin cewa,...
    Mataimakin shugaban kasar Iran Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa, batun kifar da gwamnatin JMI bayan yakin kwanaki 12 ya kuma fita daga abinda makiya zasu iya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar yanakalto mataimakin shugaban kasa na farko yana fadar haka a ranar Alhamis da ta gabata, ya kuma kara da cewa a cikin yakin kwanaki 12 wanda kasashen Amurka da HKI suka dorawa kasar sun so su kifar da gwamnatin JMI a cikin kwanaki 3 zuwa 4 amma suka kasa. Ya ce hatta babban sakataren MDD Antonio Guterres ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da shi dangane daha. Ya kuma tabbatar da cewa makiyan JMI ba zasu iya tumbuke tsarin ba. Yasashen yamma musamman Amurka suna kokarin...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Guguwar Ritaya Na Barazana Ga Ayyukan Hukumar Kwastam Yayin Da Jami’ai 825 Za Su Yi Ritaya October 10, 2025 Labarai Haramcin Haƙar Ma’adanai: Majalisa Za Ta Kawo Ƙarshen Asarar Dala Biliyan 9 Duk Shekara October 10, 2025 Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Iran tana goyon bayan duk wani Shirin zaman lafiya da ya hada da dakatar da kisan kiyashi a Gaza Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana goyon bayan duk wani mataki ko wani yunkuri da ya hada da kawo karshen yakin kisan kiyashi a Gaza, janyewar sojojin mamayar Isra’ila, shigar da kayan agajin jin kai, sakin fursunonin Falastinawa, da kuma tabbatar da dukkanin hakkokin Falasdinawa. Haka kuma ta kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na mai goyon bayan halastacciyar gwagwarmayar al’ummar Falastinu samun tabbatar da ‘yancin kai, ta yi amfani da dukkanin karfinta na diflomasiyya a cikin shekaru biyun da suka gabata, musamman...
    Ministar wadda ta je kamfanin domin daukar sabuwar motarta ta alfarma kirar Nord Demir SUB da kamfanin ya hada nataimakin Shugaban jami’ar na sashen kula da ilimi da gudanar da bincike Farfesa Bola Oboh da kuma Shugaban kamfanin Mista Oluwatobi Ajayi ne, suka karbi bakuncinta.   A jawabin da ta gabatar a lokacin ziyarar ministar ta bayyana cewa,Duba da yarjejeniyar hada-hadar kasuwanci wajen fitar da kaya zuwa ketare kamfanin zai iya yin amfani da wannan samar waken fitar da motocinsa zuwa ketare.   Ta kara da cewa, Nijeriya na da gurare biyu ne da ake hada motoci da suka hada da, na wannan jami’ar da kuma na EPs, inda ta yi nuni da cewa, karfin da kamfanin ya ke da...
    Shugaban ya ci gaba da cewa, a karkashin shugabancinsa, Hukumar za ta yi namijin kokari wajen bayar da goyon bayanta, wajen fitar da kayan da ba su shafi dangogin Mai ba, zuwa kasar waje, musamman ta hanyar cin giyar albakatun yanayin na Abuja da kuma na bangaren aikin noma, da birnin ke da shi. Ya kara da cewa, ta hanyar wadannan alkatun kasar da birnin ke da su, Hukumar za ta kara bayar da gudunmwarta, wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar nan da kuma kara fitar da kayan da ba su shafi Man ba, zuwa ketare.   A cewarsa, domin Hukumar ta tabbatar da na kara mayar da hankalin wajen ganin ana bin ka’ida da kuma tabbatar da ingancin...
    Wannan lamari ya haifar da tambaya kan yiwuwar dorewar shirin sauye-sauye da na zamani da ake gudanarwa a karkashin jagorancin Babban Kwanturola Janar, Adewale Adeniyi.   Adewale Adeniyi, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kara wa wa’adin mulki na shekara guda, shima zai yi ritaya daga hukumar a watan Agusta, 2026.   A halin yanzu, za a dauki babban mataki kafin a cike gibin ma’aikata da ake bukata a hukumar kwastam, musamman idan aka yi la’akari da cewa jami’ai 825 za su bar aiki ba tare da sabon daukar ma’aikata ba.   Binciken da leadership Hausa ta gudanar ya gano cewa ritayar ta shafi kowane mataki a hukumar daga manyan shugabanni, zuwa matsakaita, har da kananan jami’ai.   Daga cikin...
      Bugu da kari, Xi Jinping ya yi wa jam’iyyar WPK fatan samun karin nasarori, yana mai fatan abotar Sin da Korea ta Arewa za ta dore har abada. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal October 9, 2025 Daga Birnin Sin Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025 October 9, 2025 Daga Birnin Sin Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza October 9, 2025
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta samu nasarar ceto wasu mutum uku da aka sace, bayan wani samame da ta kai a jihohin Kano da Kaduna. Wannan na daga cikin ƙoƙarin da rundunar ke yi domin yaƙi da laifuka da tabbatar da tsaron jama’a. ’Yan sanda sun manta hularsu a motar dalibi bayan karɓar ‘cin hancin’ N99,000 NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa an gudanar da samamen ne tsakanin ranar 7 zuwa 9 ga watan Oktoba, 2025, bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori. A cewar Kiyawa, samamen farko ya gudana ne a ranar...
    Wani dalibi mai suna Olawale Ayomide ya zargi wasu ’yan sanda da ke aiki a ofishin Igbeba da ke yankin Ijebu Ode a jihar Ogun da tatsar Naira 99,000 daga hannunsa ba bisa ka’ida ba. Ayomide ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata, inda ya ce ɗaya daga cikin ’yan sandan da ake zargi ya manta hular aikinsa a cikin motar bayan sun aikata abin da ake zarginsu da yi. A cewarsa, ’yan sandan sun tsayar da shi ne a lokacin da yake tafiya daga Shagamu zuwa Ijebu-Ode a cikin motar mahaifiyarsa, inda suka zarge shi da tuƙi ba tare da lambar mota ba. Kwastam ta kama buhunan lalatacciyar fulawa 10,000 ana ƙoƙarin shigo da ita Najeriya ’Yan...
    Hukumar Kwastam shiyyar bodar Najeriya ta Seme da ke jihar Legas ta ce ta cafke motoci biyar da ke maƙare da buhuna 10,000 na lalatacciyar fulawa da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.2. Rundunar ta kuma ce ta tara jimillar kuɗin shigar da ya kai Naira biliyan daya da rabi a watan Satumba, wanda hakan ya nuna kari da kaso 182 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira miliyan 531 da aka tara a watan Agustan da ya gabata. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da wasu mutum 173 afuwa Kwamandan rundunar a shiyyar, Wale Adenuga, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na...
    Kazalika, tarihin Dimokiradiyyar kasar ya sha cin karo da kwam gaba kwam baya kusan za a iya cewa, tun bayan dawowar mulkin Demokaradiyya a 1979 da kuma sake dora kasar a wata turbar ta Demokiradiyyar a 1999.   Alal misali, jamhuriyya ta hudu ta kasance ta jima sosai, amma kusan babu wasu ayyukan na inganta rayuwar ‘yan kasar da za a bigi Kirji a ce gasu an gani a kasar a zahiri.   Idan aka dubi bangaren samar da hasken wutar lantarki kusan za a iya cewa, karni da dama da suka bace, har zuwa yau Nijeriya ta gaza samar da karfin wutar da kuma rabar da ita da ta kai karfin Megawatts 5,000 musamman duba da cewa, wannan adadin...
    Mai Magana da yawun gwamnatin Iran Fatemeh Mohajerani ta tabbatar da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar Palastinu a gwagwarmayar neman ‘yanci da mutunci. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Mohajerani ta ce Iran za ta goyi bayan duk wani mataki ko wani shiri da zai kai ga dakatar da kisan kiyashin da ake yi a Gaza, da janyewar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila, da shigar da kayayyakin jin kai, da sakin fursunonin Falasdinu, da kuma tabbatar da hakkinsu na yau da kullun. Ta yi nuni da cewa goyon bayan Iran ga al’ummar Palasdinu “ba matsayi ne na siyasa kawai ba, a’a yana dogara ne akan  imani da ‘yancin al’ummar Palasdinu da kuma...
    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da afuwar Shugaban Kasa ga mutane 175. Daga ciki har da wadanda aka yi wa afuwar bayan mutuwa ga marigayi Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa da ɗan gwagwarmayar kwato ’yancin kan Najeriya, Herbert Macaulay. An dauki wannan mataki ne bayan amincewa da shawarwarin da Majalisar Tsofaffin Shugabannin Ƙasa ta bayar a taronta da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja. Gwamnatin Kano ta shirya ɗaurin auren ma’aurata 2,000 Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC A cewar sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin bayanai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma yi afuwa ga tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan da wasu mutum uku, Misis Anastasia...
      Cikin darussan da wannan rikici ya tabbatar mana, akwai rashin tasirin amfani da karfin tuwo wajen warware duk wani rikici. Tabbas karfin soji kadai ba zai iya magance takaddama ko tashin hankali ba, ballantana ya wanzar da tsaro da walwalar bil’adama.   Muna iya ganin hakan a zahiri, idan mun lura da yadda Isra’ila ta nuna a fili cewa hare-haren da ta kwashe shekaru biyu tana kaiwa sassan Gaza za su iya kawo karshen barazanar da ta ce kungiyar Hamas ke haifar mata, amma sai ga shi daga karshe sakamako ya nuna akasin haka. Har yanzu dai sannu a hankali ana komawa ga shawarar da kasashe masu son zaman lafiya suka jima suna bayarwa, wato a rungumi tattaunawa, da...
    Shugaban kasar Ecuador ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi da aka yi Ministan Makamashi na Ecuador, Ines Manzano ya sanar a ranar Talata cewa: An yi yunkurin kashe shugaban kasar Daniel Noboa kuma an kama wasu mutane biyar da ke da hannu a ciki makarkashiyar. Manzano ya ce “Motar Noboa na kewaye da gungun mutane kusan 500 da suke jefanta da duwatsu a lokacin da yake tafiya a cikin ayarin motocin zuwa lardin Cañar, inda aka shirya zai sanar da jerin ayyukan samar da ababen more rayuwa.” Ta kara da cewa: “Daga baya an samu alamun harsashi a motar, amma Noboa bai samu rauni ba a harin.” Hukumomin kasar sun sanar da cewa: Wadanda ake tsare...
    Shugaban kasar Venuzuwla Nicolas Maduro ya kaddamar da atisayan soji mai fadi, a jiya laraba, a daidai lokacin da rikici ke kara Kamari tsakaninsa da Amurka, kuma an gudanar da atisayan ne a jihar coast a la guara, minti 30 da birnin karakas ,kuma ya kunshi sojojin kasar da hadin guiwar na kasar Bloviya. Wannan Atisayan yana nuna irin karfin sojin da venuzuala take da shi da kuma shiri na tunkarar  barazanar da take fuskanta daga waje, kuma yana nuna irin yadda yankin karebiya ke cikin rikici inda ayyukan sojin ruwan Amurka ke fuskantar suka daga gwamnatin karakas. Dangantaka tsakanin venuzuwela da Amurka ta dade da samun damuwa na tsawon shekaru,inda Amurka ta kakaba mata takunkumi kuma take goyon bayan...
    Dalibai da malaman Jami’o’i a kasar Burtania sun bar ajujuwansu don halattar ganganmi a cikin jami’o’insu, na goyon bayan al-ummar Falasdinu da kuma yin tir da gwamnatin kasar saboda goyon bayan da take bawa HKI a kissan kiyashi, wanda ya kai shekaru biyu kenan a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa  zanga zangar bata takaita a jami’o’in birnin London kadai ba, sai dai an gudanar da su a manya –manyan biranen kasar duk tare da gargadin jami’an yansandar kasar kan cewa an haramta zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a kasar. Sauran biranen da aka gudanar da gangamin dai sun hada Glasgow, Manchester, Bristol, Sheffield da Edinburgh. Daliban da kuma malamansu suna rera taken “Yanci ga Falasdinu...
    Dakarun bangaren sojin kungiyar Jihadul Islama ta Falasdinu Sarayal-Quds ta bayyana cewa: Fursunonin mamaya ba za su ga hasken rana ba har sai an sharuddan Falasdinawa Dakarun bangaren sojin kungiyar Jihadul Islama ta Falasdinu, sun jaddada cewa: Fursunonin mamayar Isra’ila ba za su ga hasken rana ba, sai dai ta hanyar tattaunawa da musayar ra’ayi da yahudawan sahayoniyya da suka kuduri aniyar kawo karshen yakin Gaza. A cikin wata sanarwa da dakarun Sarayal-Quds suka fitar, sun jaddada cewa su da dukkanin bangarorin gwagwarmaya ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen samar da hanyar kawo karshen yakin Gaza da kuma wahalhalun da Falasdinawan suke ciki. Har ila yau, sun tabbatar da cewa: “Makaman ‘yan gwagwarmaya makamai ne da aka...
     Wannan sanarwar ta baya bayan nan da kasar Sin ta yi, ya samu yabo sosai, musammam daga sakatare janar na MDD, yana jaddada cewa, shirin na Sin na da muhimmanci matuka ga tunkarar sauyin yanayi. Su ma kafafen yada labarai na kasa da kasa da manyan jami’an hukumomi da kasashe da dama, sun yaba wa shirin, wanda ya nuna cewa, ana kara ammana da irin rawar da kasar Sin ke takawa a harkokin da suka shafi duniya. Ba alkawari da gabatar da shirin kadai take yi ba, ta kasance mai aiwatar da su a aikace kuma ana ganin nasarorin da take samu a zahiri. Zuwa yanzu, babu wata kasa da ta bayar da gudunmuwa a wannan bangare kamar kasar Sin, kuma...
     Kasashe masu tasowa sun yi jawabi daya bayan daya, suna masu bayyana kudurin a matsayin wanda ya haska bukatar da daukacin jama’a ke da ita ta amsa kiraye-kirayen kasashe masu tasowa na kara zuba jari a fannin tabbatar da hakkokin da suka shafi tattalin arziki da zamantakewa da al’adu. Haka kuma bangarori da dama ciki har da Tarayyar Turai, sun yaba wa kudurin. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinFiraministan Sin Zai Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Na Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Korea Ta Arewa October 7, 2025Daga Birnin SinHabakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu    October 6, 2025Daga Birnin SinKaramin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas...
    Dubban mutanen kasar Moroko ne su ka fito kan titunan birnin Rabat domin yin Zanga-zangar nuna goyon bayansu ga al’ummar Falasdinu da HKI take yi wa kisan kiyashi. Mahalarta Zanga-zangar sun hada lauyoyi, dalibai, kungiyoyin fararen hula da sauran mutanen gari, suna dauke da tutar Falasdinu, tare da kuma da bayar da taken: “Yanci ga Falasdinu, da yin kira da a shigar da kayan agaji a cikin yankin na Gaza. Bugu da kari, masu Zanga-zangar sun yi gangami a bakin ginin majalisar dokokin kasar. Mutanen sun nuna rashin amincewarsu da  halin da mutanen Gaza suke ciki, tare da yin kira da a kawo karshensa. Mahalarta Zanga-zanagr dai sun fito ne daga biranen Tangier, Casbalanca da Feiz, da kuma wasu garuruwa...
    Shugaban ofishin jagoran juyin musulunci na Iran, Hujjatul Islam Wal Muslimina Muhammad Gulpayagani ya bayyana yunkurin nan na: Goyon Bayan Iran.” Da cewa, aikin da suke yi yana a karkashin amsa kiran jagoran juyi ne wanda ya yi kira da a taimakawa waddanda su ka cutu daga hare-haren HKI. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto Hujjatul-Islam Muhammad Gulpayagani yana bayyana muhimmin matakin da Ayatullah Khamnei yake dauka a fagen gwgawarmaya, yana mai kara da cewa; Shi ne wanda yake dauke da tutar gwgawarmaya akan wannan tafarkin cikin dogara da Allah madaukakin sarki da tafiya akan tafarkin Ahlul Bayti ( a.s). Hujjatul-Islam golpayagani ya ambaci wasu ayyukan da yukurin na Iran take yi wajen taimakawa wadanda su ka cutu daga hare-haren...
    Shugaban Kamaru Paul Biya, ya bayyana cewa zai tsaya takara a wa’adi na takwas a watan Yuli, yana mai kafa hujja da cewa hakan  amsa kiraye-kirayen jama’a ne da ke neman ya ci gaba da mulkin kasar. Duk da sukar da ake yi, da kuma dimbin kalubalen tsaro da tattalin arziki, shugaban kasar da ya fi dadewa kan karagar mulki a duniya na da  damar samun nasara a zaben da za a gudanar a ranar 12 ga watan Oktoba a kasar da ke da tsakiyar nahiyar Afirka,  mai arzikin koko da man fetur. Sai dai watakila babban abin da ke fuskantar Biya a wannan karon shi ne lafiyarsa, wadda aka dade ana ta cece-kuce a kai, musamman yadda ya shafe...
    Wani saksmkon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da cibiyar dimokuradiyya ta Isra’ila ta gudanar ya nuna cewa kashi 66 cikin 100 na Isra’ilawa sun yi imanin cewa lokaci ya yi da za a kawo karshen yakin Gaza, tare da bayyana hadarin da fursunoni ke fuskanta. Wannan adadi na kashi 66% ya karu da kashi 13% a kan sakamakon da aka fitar a shekara guda da ta gabata lokacin da aka yi musu tambaya iri ɗaya. Sakamakon  ya kuma nuna cewa kashi 45% na Isra’ilawa sun yi imanin cewa ya kamata Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya yi murabus nan da nan kafin karshen yakin, tare da dora masa alhakin abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba, 2023. Sakamakon ya nuna...
    Ma’aikatar yakin HKI ta tabbatar da halakar sojojinta fiye da dubu guda a yakin tufanul aksa, wanda aka fara a yanar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023. Tashar talabijin ta Al-Mayadden ta nakalto kafafen yada labaran HKI na fadar cewa, ma’akatar da ce an kashe sojoji 1152 tun bayan fara yakin tufanul Aksa tsakanin sojoji da wasu jami’an tsaron. Labarin ya kara da cewa kashi 42% na wadanda suka halaka, wato 487 daga cikinsu basu kai shekara 21 a duniya ba. Sannan 141 daga cikinsu sun dara shekaru 40 a duniya. Banda ya haka yakin ya samar da sauyi babba a cikin rayuwar yahudawan sahyoniyya. Sannan wadanda suka ji rauni kuma sun dara 18,500. Share 0 0 votes Article...
    Firaministan ƙasar Faransa, Sebastien Lecornu, ya yi murabus daga muƙaminsa kwana guda bayan ya kafa gwamnatinsa. Fira Minista Sebastien Lecournu ya sanar da ajiye mukaminsa ne a safiyar Litinin ɗin nan bayan ya yi wata da Shugaba Emmanuel Macron. Ya yi murabus ne washegarin da ya kafa majalisar ministocinsa domin tafiyar da gwamnati, kuma ƙasa da wata guda bayan Shugaba Macron ya naɗa shi a kujerar. A jiya  Lahadi ne ya sanar da sunayen mambobin sabuwar majalisar ministocinsa inda ya naɗa sabbin muƙamai, amma ya bar wasu da dama a kan kujerunsu, lamarin da bai yi wa ’yan adawa daɗi ba. Zargin takardun bogi: Jami’ar Nsukka ba ta taɓa ba ni takardar digiri ba — Minista ’Yan bindiga sun kashe...
    Iran ta sanar cewa tana goyon bayan “duk wani shiri” da zai ba da damar samar da ‘yancin kai ga al’ummar Falasdinu, gabanin tattaunawa da ake shirin farawa a Masar tsakanin Isra’ila da Hamas da nufin kawo karshen yakin zirin Gaza. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, iran ta ce “a ko da yaushe tana goyon bayan duk wani yunkuri na kawo karshen laifukan yaki, da cin zarafin bil’adama a Gaza da duk wani yunkuri na share fagen tabbatar da ‘yancin kai na al’ummar Palasdinu.” Sanarwar ta ce, tilas ne yanke duk wata shawara kan tsagaita bude wuta ko sasantawa ta siyasa ta rataya a wuyan Falasdinawa da kansu. Tehran ta ce tana maraba da...