Gwamna Namadi Na Jihar Jigawa Ya Cancanci Karramawar LEADERSHIP – Hamisu Gumel
Published: 11th, April 2025 GMT
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp.কীওয়ার্ড: Gwamna Namadi Jigawa Karramawa Lambar Yabo
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Abba Kabir Zai Gabatar Da Kudirin Kafin 2026 Ga Majalisar Kano Ranar Laraba
Daga Khadijah Aliyu
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta karɓi wasiƙa daga Gwamna Abba Kabir Yusuf kan gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 wanda ya kai Naira tiriliyan 1, irinsa na farko a tarihin jihar.
Za a gabatar da kudurin ne a ranar Laraba, 19 ga watan Nuwamban 2025.
Wasiƙar, wadda Kakakin Majalisar, Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya karanta a zaman majalisar, ta bayyana cewa gabatar da kasafin ya yi daidai da sashe na 121 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999, wanda aka yi wa gyara.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa yawan kasafin da ya karu sosai na nuna ƙudurin gwamnatinsa na ƙarfafa manyan ayyukan gine-gine, shirye-shiryen sabunta birane, da haɓaka ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a fadin jihar Kano.
Shugaban Majalisar ya ce Gwamna Yusuf ya yi bayanin cewa kasafin na 2026 zai mayar da hankali ne kan raya gidaje, aikin gona, ilimi, kiwon lafiya, da tallafawa ƙanana da matsakaitan sana’o’i, domin farfaɗo da tattalin arziƙi da samar da hanyoyin dogaro da kai ga al’ummar Kano.
Da zarar an gabatar da kudirin, za a miƙa kasafin kuɗin zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano domin nazari da amincewa. Idan aka amince da shi, zai kasance kasafin kuɗi na farko mai irin wannan girma da jiha daga Arewa ta gabatar.
Gwamna Yusuf ya sake tabbatar da aniyarsa ta gaskiya, bin ƙa’ida wajen kashe kuɗi, da tabbatar da cewa kowane bangare ya samu tallafi isasshen da zai ba shi damar samar da ingantattun ayyuka ga jama’ar Kano.