HausaTv:
2025-11-02@18:11:16 GMT

Syria: Adadin mutanen da suka mutu a harin Isra’ila a yankin Damascus ya kai 5

Published: 27th, August 2025 GMT

Adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-hare biyu da Isra’ila ta kai a yankin Damascus ya karu zuwa 5, yayin da wasu ma’aikatan ma’aikatar tsaron kasar Syria suka samu raunuka, a cewar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Syria.

Cibiyar sa ido ta kasar Syria ta sanar a yammacin jiya Talata cewa, hare-haren biyu an kai su ne a yankin al-Kiswah da ke yankin Damascus, kusa da hanyar Suwayda, tare da raunata wasu sojojin sabuwar gwamnatin kasar ta Syria, wanda  suka kasance mambobin kungiyar Hay’at Tahrir al-Sham mai alaka da kungiyar da Aqaida.

Majiyoyin cikin gida sun kuma tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari a wani shingen binciken sojojin sabuwar gwamnatin da na jami’an tsaron cikin gida da ke birnin al-Sanamayn da ke arewacin Daraa.

Wannan lamari dai na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kara zafafa hare-harenta da keta hurumin kasar Siriya, musamman kan iyaka da tuddan Golan da ta mamaye.

Bayan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan kan fagen siyasar kasar Siriya, Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Siriya (SANA) ya bayar da rahoton wata ganawa tsakanin ministan harkokin wajen kasar Siriya Asaad al-Sheibani da tawagar Isra’ila a birnin Paris na kasar Faransa, wanda shi ne karon farko da aka taba wata gudanar da wata ganawa a tasakanin jami’an Syria da Isra’ila.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Kammala Taron Iran Da E3 A Geneva August 26, 2025 Iran Ta ce Zata Rama Kan Korar Jakadanta Daga kasar Australia August 26, 2025 Najeriya: Jirgin Kasa tsakan Abuja da Kaduna Ya Sauka Kan Layin Dogo August 26, 2025 Iran A Shirye Take Ta Hada kai Da Pakistan Don Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci August 26, 2025 An Kashe Mutum Guda A Harin Isra’ila (HKI) A yankin Duddan Golan Na Siriya August 26, 2025 Jagora: Yahudawan Sahayoniyya Sune Mafi Kyamar Al’umma A Duniya Saboda Muggan Halayensu August 26, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Tarihi Ba Zai Yafe Jinkirin Yin Allah Wadai Da Bala’in Gaza Ba August 26, 2025 Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Tun Bayan Barkewar Yaki Da Iran Babu Wata Hulda Tsakaninta Da Amurka August 26, 2025 Makami Mai Linzamin Sojojin Yemen Ya Zame Mafarki Mai Firgitarwa Ga ‘Yan Sahayoniyya August 26, 2025 Shugaban Kasar Faransa Ya Ce: Kakaba Yunwa Laifi Ne Da Ya Wajaba Dakatar Da Ita Cikin Hanzari August 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasar Siriya

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher

Qatar ta bayar da tallafin gaggawa ga mutanen da suka rasa matsugunansu a Sudan

Gwamnatin Qatar ta aika da agajin gaggawa da tallafin jin kai zuwa birnin Ad-Dabba da ke Jihar Arewacin Sudan domin rage wa dubban mutanen da suka rasa matsuguninsu da ke tserewa daga El Fasher, babban birnin Jihar Arewacin Darfur.

Ma’aikatar Harkokin Waje ta Qatar ta bayyana cewa: “Wannan tallafin ya zo ne a cikin tsarin jajircewar Qatar na tallafawa ‘yan uwantaka na Sudan, musamman idan aka yi la’akari da mawuyacin halin jin kai da fararen hula ke ciki, ciki har da karancin abinci mai tsanani da kuma karuwar bukatar matsugunai da kayan masarufi.”

Sanarwar ta kara da cewa wannan tallafin wani bangare ne na kokarin da Qatar ke yi na tsayawa tare da ‘yan uwantaka na Sudan da kuma rage musu wahalhalun da rikicin yaki da makamai ya haifar. Haka nan ya kunshi rawar da Qatar ke takawa wajen karfafa martanin jin kai da kuma gina gadoji na hadin kai da al’ummar da abin ya shafa a fadin duniya.

Tallafin ya kunshi kimanin buhuhunan abinci 3,000, tantuna 1,650, da sauran kayayyakin bukatu, wanda Asusun Ci Gaban Qatar da kuma Hukumar Ba da Agaji ta Qatar suka bayar, don tallafawa wadanda suka rasa matsuguninsu daga El Fasher da yankunan da ke kewaye. Ana sa ran sama da mutane 50,000 za su amfana daga wannan tallafin, wanda ya haɗa da kafa sansanin agaji na musamman na Qatar mai suna Qatar Charity.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya November 2, 2025 Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci November 2, 2025 Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza November 2, 2025 Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Pezeshkian: Bunkasa Masana’antar Makamashin Nukiliyar Iran Don Inganta Rayuwar Al’ummar Iran Ne
  • Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
  • Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher
  • Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran
  • Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan
  • Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Duk Wani Kutse Na Isra’ila A Kudancin Kasar