Mai Martaba Sarkin Kano 16 Ya Nada Mannir A Matsayin Sabon Galadiman Kano
Published: 10th, April 2025 GMT
A ranar Talata ne mai martaba Sarkin Kano Malam Mohammad Sunusi II ya amince da nadin Alhaji Mannir Sunusi a matsayin sabon Galadiman Kano.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ‘yan jarida da yada labarai na masarautar Kano, Saddam Nasir Na’ando ya fitar, kuma ya mika wa gidan rediyon Najeriya da ke Kano.
Haka kuma Sarki Sunusi II ya amince da nadin Alhaji Kabiru Tijjani Hashim zuwa Wamban Kano.
Sauran nada nade sun haɗa da “Alhaji Mahmoud Ado Bayero ya tashi daga Tafidan Kano zuwa Turakin Kano da Adam Sanusi yanzu ya zaman Tafidan Kano sai kuma Ahmed Abbas Sanusi ya zamaYariman Kano.
Sanarwar ta kara da cewa wadannan nade-naden sun fara aiki ne nan take, a wani bangare na kokarin da Masarautar Kano ke yi na karfafa shugabancin gargajiya da kuma adana kayayyakin tarihi.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Sarki
এছাড়াও পড়ুন:
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA