Ruwa Ya Ci Rayukan Mata Biyu A Kano
Published: 10th, April 2025 GMT
Mazauna karamar hukumar Gezawa ta Kano sun shiga cikin tashin hankali da makoki sakamakon nutsewar wasu mata biyu a cikin wani tafki.
Rahotanni sun nuna cewa matan (an sakaya sunansu) sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke wanka a kogi bayan sun dawo daga aiki a wata masana’antar sarrafa hibiscus.
A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Yusif Abdullahi Gezawa hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa daga ‘yan banga da ke yankin tare da bayyana cewa “Yan uwan matan biyu ne suka kai rahoton lamarin ga dan banga”
Ya yi nuni da cewa, nan take aka tura tawagar masu aikin ceto zuwa wurin, inda suka yi nasarar zakulo gawarwakin su a sume, daga bisani jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarsu.
Saminu ya bayyana cewa an mika gawarwakin ga wani dan sanda Musa Garba na sashin ‘yan sanda na Gezawa.
Ya shawarci jama’a da su daina zuwa kusa da kogi domin gujewa abubuwan da ba a zata ba.
KHADIJAH ALIYU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Ruwa
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige dan majalisar wakilai, Abubakar Gummi daga kujerarsa saboda sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Gummi yana wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum ta Jihar Zamfara a majalisar wakilai.
An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkukuMai shari’a Obiora Egwuatu ne, ya yanke hukuncin, inda ya umarci kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, da ya daina amincewa da Gummi a matsayin dan majalisar da ke wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum.
Haka kuma ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta shirya sabon zabe cikin kwanaki 30 domin cike gurbin kujerar dan majalisar.
Jam’iyyar PDP tare da shugaban ta na jihar Zamfara, Jamilu Jibomagayaki, ne suka shigar da karar dan majalisar.
Sun ce bai dace Gummi ya ci gaba da zama a kujerar ba bayan barin jam’iyyar da ta tsayar da shi takara.
Gummi, ta bakin lauyansa ya ce ya fice daga PDP ne saboda rikicin cikin gida da jam’iyyar ke fama da shi a matakin kasa da kuma a mazabarsa.
Amma kotu ta yi watsi da wannan hujjar, inda ta bayyana cewa babu takaddama da za ta ba shi damar ya sauya sheka.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Egwuatu ya ce ’yan siyasa dole su mutunta zabin jama’ar da suka kada musu kuri’a a karkashin jam’iyyar da ta tsayar da su takara.
Ya ce doka ba ta yadda da dan siyasa ya bar jam’iyyar da ta taimaka masa wajen lashe zabe sannan ya koma wata jam’iyya ba tare da ajiye mukaminsa ba.
Ya kara da cewa kuri’un da aka kada don dan takarar na jam’iyya ne, ba nasa ne na kashin kansa ba.
“Idan mutum yana son sauya sheka, ka da ya dauki amanar jama’ar da ta zabe shi ya tafi da ita,” in ji alkalin.
Kotu ta kuma umarci Gummi da ya daina karbar albashi da wasu hakkoki a matsayin dan majalisa, tare da mayar da duk kudaden da ya karba daga ranar 30 ga watan Oktoba, 2024, zuwa ranar da aka yanke hukuncin.
Haka kuma, ya gabatar da hujjar mayar da kudaden ga kotu cikin kwanaki 30.
Mai shari’a Egwuatu ya kuma ci Gummi tarar Naira N500,000, domin biyan PDP kudaden da ta kashe wajen shigar da kara.