Fitaccen Malamin Musulunci Mai Da’awar Sunnah A Nijeriya, Dr. Idris Dutsen Tanshi Ya Rasu
Published: 4th, April 2025 GMT
Ana yi wa Shehin Malamin laƙabi da Dr. Tauhidi saboda da’awarsa ta ƙarfafa ne akan Tauhidi da kuma riƙo da Sunnar Annabi (S.A.W.) da kuma yaƙi da fararrun al’amura a cikin addinin Islama.
Za a yi sallah jana’izar Babban Limamin da misalin ƙarfe 10 na safe a Masallacin Idi na Games Village, Jihar Bauchi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Da awa
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴan Ta’adda Sun Kashe Maharba 10 A Adamawa
Ƴan ta’adda da ake zargin Boko Haram ne sun kashe mutane 10 na yawucin dabbobi da kuma mambobin jami’an tsaron sa kai (CJTF) a garin Kwapre, dake cikin ƙaramar hukuma ta Hong a Jihar Adamawa.
Shugaban ƙaramar hukuma, Hon Usman Wa’aganda, ya tabbatar da wannan lamarin ga LEADERSHIP ta waya a ranar Lahadi a Yola, inda ya bayyana cewa wani mutum da ya samu raunuka daga harin ‘yan ta’addan yana samun kulawar likita a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba.
Daidaikun Kasashe Za Su Kara Karfi Idan Suka Hada Hannu Tare ‘Yansanda Sun Kama Wani Kato Bisa Zargin Cin Zarafin Wata Mata A AdamawaWa’aganda ya ce ‘yan ta’addan sun ƙone gidaje da dama da kuma amfanin gona, yana mai cewa wannan harin ba na farko bane, domin garin ya sha hare-hare sau da dama wanda ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.
Ya nemi hukumomin tsaro su ƙara tura jami’ai a yankin domin taimakawa wajen kare al’umma da kuma tabbatar da tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp