Al-Houthi: Hare-haren Amurka sun kasa dakatar da gwagwarmayar Yeman
Published: 5th, April 2025 GMT
Madugun kungiyar Ansarallah ta kasar Yeman ya yi ikirarin cewa, zafafan hare-haren wuce gona da iri da Amurka ke kaiwa kasar Yemen, ya kasa dakatar da ayyukan gwagwarmayar Yeman na goyon bayan al’ummar Gaza ko kuma kare jiragen Isra’ila a tekun Bahar Rum.
A wani jawabi da ya yi a ranar Juma’a, Abdul-Malik al-Houthi ya ce Amurka ta zafafa kai hare-hare a kan kasar Yemen, inda wasu lokutan ta kai hare-hare sama da 90 a kowace rana, a wani bangare na goyon bayan da take baiwa kasar Isra’ila a yakin kisan kare dangin da ta ke yi a zirin Gaza.
Duk da haka, ya jaddada cewa, hare-haren na Amurka “sun kasa dakatar da ayyukan soji da ke tallafawa al’ummar Falasdinu, ko kuma tabbatar da kare zirga-zirgar jiragen ruwa na Isra’ila a cikin Bahar Maliya, Gulf na Aden da kuma Tekun Oman.”
Ya kuma ce jami’an sojin Amurka sun amince cewa hare-haren sun kasa dakile karfin sojojin Yemen.
Al-Houthi ya ce: “Amurka ta gaza cimma burin da ta sanya a gaba na kawar da shugabanni da kuma kawar da ‘yantacciyar kasar Yemen.”
Ya yi alkawarin cewa kasar Yemen za ta ci gaba da kai hare-hare na daukar fansa, kafin ya bayyana cewa: “Amurka ba ta tsoratar da mu.”
Shugaban kungiyar Ansarallah ya kuma gargadi gwamnatocin kasashen Larabawa da kasashen da ke makwabtaka da su kan goyon bayan hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen sannan ya kara da cewa kutsawar da Ministan Isra’ila mai tsatsauran ra’ayi, Itamar Ben-Gvir ya yi a harabar masallacin Kudus, shaida ce ta ci gaba da cin zarafi da Isra’ila ke yi kan “daya daga cikin mafi girman wurare masu tsarki ga musulmi.”
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Yemen
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’in Kasar Yemen Ya Aike Da Sako Ga Mahalarta Taron Birnin Doha Na Kasar Qatar
Mamban a majalisar koli ta siyasar kasar Yemen ya aika sako ga mahalarta taron birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar
Mohammed Ali al-Houthi, mamba a majalisar koli ta siyasar kasar Yemen, ya aike da sako ga shugabannin kasashen Larabawa da na kasashen musulmi da suka hallara a yau, Litinin, a taron Doha. Wannan taron na zuwa ne biyo bayan ha’incin yahudawan sahayoniyya da suka yi yunkurin halaka tawagar Hamas a babban birnin kasar Qatar.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, al-Houthi ya ce: “Sakonsa ga taron da za a yi a yau Litinin a birnin Doha na kasar Qatar, shi ne cewa: Matsayi mafi karfi shi ne tabbatar da halaccin jihadi da ‘yan mamaya da goyon bayan gwagwarmaya da kuma ayyana Isra’ila a matsayar ‘yar ta’adda.”
Ya kara da cewa: “Wannan zai kawo karshen rikici tare da dakatar da tashe-tashen hankula da wuce gona da iri.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000 September 15, 2025 Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces September 15, 2025 Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar September 15, 2025 Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila September 15, 2025 Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa September 15, 2025 Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Isra’ila Za ta Gamu Da Mummunar Martani Idan Tayi Gigin Afkawa Iran September 14, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Fara Taro A Qatar. September 14, 2025 Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Sabon Sharadi Na Bude Asusun Banki September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci