Kwallon Mata: Nijeriya Ta Nuna Wa Afrika Ta Kudu Kwanji A Pretoria
Published: 10th, March 2025 GMT
Tawagar matasan yan wasan ƙwallon ƙafa ta Nijeriya ta mata (Flamingos) ta yi nasarar doke mai masaukin baƙi Bantwana ta Afrika ta Kudu da ci 3-1 a wasan farko na gasar cin kofin duniya na mata ‘yan kasa da shekaru 17 na shekarar 2025 a filin wasa na Lucas Moripe, Pretoria a ranar Asabar, in ji jaridar Prompt News.
Shakirat Moshood ce ta jefa wa Nijeriya ƙwallon farko a wasan cikin mintuna 20 kacal da farawa, Harmony Chidi ta ninka damar da Nijeriya ke da ita daga bugun fanareti mintuna biyar kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Cinikayyar ‘Yan Kwallon Da Aka Yi A Watan Janairu Hadin Gwiwar Sin Da Nijeriya Za Ta Ba Mata Damar Cimma BurikansuAfrika ta Kudu ta dawo daga hutun rabin lokaci cikin azama da sa rai ta kuma rage giɓin dake tsakanin ƙasashen biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, kyaftin ɗin tawagar Afrika ta Kudu Success Malebana ne ta ci daga bugun fenariti.
Chidi kuma ta ƙara jefawa Nijeriya ƙwallo a ragar masu masauƙin baƙin a minti na 68, kungiyoyin biyu za su sake karawa ne a fafatawar da za a yi a filin wasa na Remo Stars, Ikenne mako mai zuwa ranar Asabar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ba Zai Yarda Hayaniyar Siyasar 2027 Ta Ɗauke Masa Hankali Ba – Ministan Yaɗa Labarai
Idris ya ce: “Ko da yake muna jaddada ‘yancin kowane ɗan Nijeriya na amfani da ‘yancin sa na shiga ko kafa ƙungiya da faɗar albarkacin baki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, yana da muhimmanci a fayyace cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ba za ta bari harkokin siyasa ko hayaniyar ‘yan siyasa su karkatar da ita daga aikin da ta sa a gaba ba.”
Ministan ya ce ko da yake ana ta raɗe-raɗi a kafafen yaɗa labarai game da sabuwar haɗakar siyasar adawa da ke tasowa, Shugaban Ƙasa Tinubu yana ci gaba da maida hankali ne kan Shirin Sabunta Fata domin ciyar da ƙasa gaba.
“Hayaniya a kafafen yaɗa labarai kan fitowar wata sabuwar haɗakar siyasa abin fahimta ne, amma ‘yan Nijeriya sun damƙa wa Shugaba Tinubu wata gagarumar amanar sauyi, wadda aka gina bisa Shirin Sabunta Fata,” inji shi.
A cewar sa, shekaru biyu kacal bayan hawan Tinubu mulki, gwamnatin ta fara samun gagarumin cigaba a fannonin tattalin arziki da tsaro inda ake samun raguwar satar ɗanyen mai, hauhawar farashin kaya na raguwa, Naira na daidaita, da kuma ƙarin ƙwarin gwiwar masu zuba jari a ɓangaren man fetur da gas.
“Fasa bututun man fetur ya ragu ƙwarai, ƙwarin gwiwar masu zuba jari a ɓangaren man fetur da gas na dawowa, hauhawar farashin kaya na raguwa, Naira na samun daidaito, ana fuskantar matsalolin tsaro kai-tsaye, kuma miliyoyin ‘yan Nijeriya — iyalai, ɗalibai, masu aikin hannu, da ‘yan ƙananan sana’o’i — na amfana daga shirye-shirye irin su lamunin karatu, samun bashi na kayayyakin masarufi, sauya motocin haya zuwa masu aiki da iskar gas, da ingantattun ayyukan gwamnati da ababen more rayuwa,” inji Ministan.
Ya kuma bayyana wasu muhimman matakai da aka ɗauka kwanan nan, ciki har da rattaba hannu kan dokoki huɗu na gyaran haraji da za a fara aiwatar da su daga shekarar 2026, da kuma ƙaddamar da mafi girman shirin amfani da injuna a aikin gona da aka taɓa yi a Nijeriya.
“Makonni biyu da suka wuce, Shugaban Ƙasa ya rattaba hannu kan dokoki huɗu masu muhimmanci na gyaran haraji, wanda ke zama ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen tsarin kuɗi da aka taɓa yi a tarihin Nijeriya. Ana sa ran waɗannan gyare-gyare za su haɓaka walwala da cigaban iyalai da ‘yan kasuwa a faɗin ƙasar nan,” inji shi.
“Kafin hakan, Shugaban Ƙasa ya ƙaddamar da mafi girman shirin amfani da injuna a aikin gona da aka taɓa yi a tarihin Nijeriya — wanda ya kasance fara aiwatar da Shirin Sabunta Fata na amfani da injuna a aikin gona. Wannan kuwa yana daga cikin jerin manyan shirye-shiryen amfani da injuna a aikin gona da ake aiwatarwa domin tabbatar da wadatar abinci,” inji shi.
Ministan ya zargi wasu ‘yan siyasa da ƙoƙarin dagula hankali domin a ɗauke hankalin gwamnati daga cigaban da ake samu. Ya ce gwamnati ba za ta amince da hakan ba.
“Ba abin mamaki ba ne cewa sababbin haɗakar siyasa da ƙungiyoyin adawa ba sa son a ci gaba da maida hankali kan irin cigaban da Nijeriya take samu. Sai dai gwamnati ba za ta bari a jawo ta cikin hayaniyar da waɗanda ke son Nijeriya ta tsaya cak maimakon ta ci gaba da samun sauyi suka ƙirƙira ba,” inji shi.
A ƙarshe, Idris ya tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da aiwatar da ƙudirin ta na inganta rayuwar al’umma.
Ya ce: “Gwamnatin Tinubu tana maida hankali sosai tare da jajircewa wajen gina Nijeriya mai wadata ga kowa da kowa.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp