Cocin Katolika Ya Yi Bikin Ma’aurata 21 A Neja
Published: 17th, February 2025 GMT
Bishop na Cocin Katolika da ke Kontagora, Babban Rabaran Bulus Yohanna ya gudanar da bikin aure ga ma’aurata ashirin da daya a jihar Neja.
A lokacin da yake jawabi yayin bikin daurin aurea cocin St. Mark Catholic da ke Nsanji Nkoso a karamar hukumar Magama ta jihar Neja, Bishop din ya bayyana cewa, bai kamata masoya na zama tare ba har sai coci ya tabbatar da su a matsayin ma’aurata bayan an biya sadaki da kuma bin ka’idoji.
A cewar Most Reverend Bulus Yohanna “mafi yawansu sun fi dogaro da auren gargajiya wanda a baya ya basu damar zama tare. “Kuma muna bukatar mu tabbata cewa babu wani daga cikinsu da aka tilastawa”.
“Dole ne mu ƙarfafa su su yi abin da ya dace musamman a matsayinmu na ’yan Katolika. Da wannan albarkar aure, wadannan ma’aurata ashirin da daya sun yi aure a bisa doka kuma a hukumance”.
Bishop Yohanna wanda kuma shi ne Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Jihar Neja, ya kara da cewa, aure alkawari ne na rayuwa wanda ya kamata a gina shi bisa soyayya
A nasa jawabin Rev. Fr. Francis Yasak Joshua, ya bayyana cewa ma’auratan su 21 sun kammala ibadar aurensu na gargajiya musamman biyan kyaututtuka ga amare, ya ce an yi musu nasihar aure na tsawon watanni uku.
Su dai wadannan ma’aurata sun kasance tare na tsawon lokaci ba tare da coci ya tabbatar da auren nasu ba, inda wadanda suka fi dadewa tare su ne wadanda suka kwashe shekaru 24 a matsayin ma’aurata, yayin da masu mafi karancin shekaru kuma su ne wadanda suka shekara daya.
Daya daga cikin wadanda suka dauki nauyin ma’auratan Lydia Ishaya ta bayyana jin dadinta inda ta ce “na yi matukar farin ciki, ina kuma rokon Allah Ya albarkaci aurensu”.
Wasu daga cikin ma’auratan sun bayyana jin dadinsu bisa yadda cocin ya tabbatar da aurensu a hukumunce.
Wasu daga cikin ma’auratan, Mista da Misis Cyprian Uche da suka kwashe shekaru 22 suna rayuwa tare, sun ce yanzu haka suna da ‘ya’ya 5, inda wasunsu sun kammala manyan makarantun gaba da sakandire, sauran kuma suna makarantar sakandare.
Daga Aliyu Lawal
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: wadanda suka
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Za Ta Ba Da Tallafin Kula Da Yara A Fadin Kasar
Kasar Sin ta bullo da wani shirin bayar da tallafin kula da yara a fadin kasar wanda zai fara aiki daga shekarar 2025, a wani bangare na kokarin tallafa wa iyalai da kuma karfafa yawan haihuwa.
Shirin zai bai wa iyalai tallafin yuan 3,600, kimanin dalar Amurka 503, a kowace shekara a kan kowane yaro da bai kai shekaru uku da haihuwa ba.
Za a kebe tallafin daga cire harajin kudin shiga kuma ba za a kidaya shi a matsayin kudin shiga na iyalai ko na mutum daya ba a yayin da ake tantance masu karbar taimakon, inda abun zai zama kamar dai irin na wadanda ke karbar alawus na cin abinci ko kuma wadanda ke rayuwa cikin matsananciyar wahala. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp