Shirin ACRESAL Na Jihar Jigawa Zai Samar Da Fitilu Akan Titunan Garuruwa 6
Published: 16th, February 2025 GMT
Shirin Inganta Muhalli da Samar da Ruwan sha da kuma bunkasa aikin gona ACRESAL a jihar Jigawa yace zai zabo garuruwa masu wahalar shiga guda 6 domin sanya musu fitilun kan titi masu amfani da hasken rana.
Shugaban shirin na jihar Jigawa, Alhaji Yahaya Muhamamad Uba Kafin Gana ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse, babban birnin Jihar.
Yana mai cewar, a yanzu haka ma tuni an zabi karin wasu garuruwa 60 domin basu bashin kudi marar ruwa.
A don haka, ya bukaci wadanda aka baiwa bashin a baya da su tabbatar sun biya domin wasu su amfana.
Alhaji Muhammad Uba yace Gwamna Umar Namadi ya amincewa shirin ACRESAL sayo karin injinan yashe kogi guda 2, wadanda za a rika amfani da su wajen yashe kogin Hadejia, domin samun saukin sarrafa ruwan kogi don hana ruwa shiga gonaki.
A cewarsa, ACRESAL da ma’aikatar kare muhalli ta jihar za su reni dashen itatuwa miliyan biyar da dubu dari biyar a bana, domin yaki da zaizayar kasa.
Shugaban shjirin na ACRESAL ya kara da cewar a yanzu haka ACRESAL tana gudanar da biyan diyyar naira miliyan 187 ga wadanda aikin zaizayar kasa ya shafi kadarorinsu a unguwannin Dan Masara da kuma Kalgo dake karamar hukumar Dutse.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban SUBEB Yayi Alkawarin Bayar Da Tallafin Ilimi A Jihar Nasarawa
A wani gagarumin ci gaba na inganta walwala da ci gaban yara da matasa wadanda suka isa makaranta, Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Farko ta Jihar Nasarawa NSUBEB, Dokta Kasim Mohammed Kasim ya karbi tawagar Kids & Teens Resource Center K&TRC a wani taron bayar da shawarwari da aka mayar da hankali kan shirin Ilimi don Lafiya da walwala, wanda UNESCO ke tallafawa.
An gudanar da babban taron ne a hedkwatar Hukumar NSUBEB, inda ya samu halartar kwamishinonin hukumar su uku, da Daraktoci da dama, da kuma tawagar K&TRC karkashin jagorancin wanda ya kafa kuma Shugaba, Mista Martin-Mary Falana.
Tattaunawar a yayin zaman ta tabo batutuwan da suka shafi rayuwar yara da matasa a jihar, wadanda suka hada da yawaitar cin zarafin mata kamar lalata da fyade, cin zarafi a makarantu, kananan yara da auren dole, kaciyar mata, da kuma yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.
Mahalarta taron sun amince da bukatar gaggawar samar da cikakken martani ta bangaren ilimi domin tunkarar wadannan kalubale.
Shugaban hukumar ya yi alkawarin ba da cikakken kudurin siyasa na hukumar tare da ba da tabbacin baiwa kungiyar K&TRC na NSUBEB goyon baya wajen samar da yanayi mai dacewa don samun nasarar aiwatar da aikin.
COV/Aliyu Muraki/Lafia.