NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kuɗi Da Yawa Ba
Published: 4th, February 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Mutanen da ke da sha’awar shiga harkar noma don sama wa kansu abin da za su ci ko kuma don samun kuɗaɗen shiga na fuskantar ƙalubale.
Wannan ƙalubale ya haɗa da ƙarancin ilimin noman, da na irin shuka, da rashin gonaki da dai sauran su.
NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe Biliyan N2.
DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan batu tare da samar da hanyoyin noma ba tare da kashe kuɗi masu yawa ba.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Li Chenggang, wakilin cinikayyar kasa da kasa na ma’aikatar kasuwanci kuma mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin, ya gana da tawagar cinikayyar kayan noma ta Amurka a birnin Beijing a jiya Talata 4 ga watan Nuwamb, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra’ayoyi kan huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, da cinikayyar kayayyakin noma, da sauran batutuwa masu alaka.
Li Chenggang ya bayyana cewa kyakkyawar alaka ta tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka tana da alfanu ga kasashen biyu da kuma duniya baki daya. Tun daga watan Mayu na wannan shekarar, tawagogin tattalin arziki da cinikayya na bangarorin biyu sun tattauna har sau biyar bisa jagorancin muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, wanda hakan ya karfafa daidaituwar alakar tattalin arziki da cinikayyar Sin da Amurka. Wannan ya tabbatar da cewa, Sin da Amurka suna da yakini a kan ci gaba da samun daidaito, girmamawa, da kuma cin gajiyar juna, kuma za su iya samun mafita a kan matsaloli ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa.
A nasu bangaren, membobin tawagar ta Amurka sun bayyana cewa kasar Sin muhimmiyar kasuwa ce ta fitar da kayan noma na Amurka, kuma manoman Amurka suna girmama hadin gwiwar da ke tsakaninsu da kasar Sin, kana suna da niyyar hada hannu don fadada hadin gwiwa da kasar Sin. Sun kara da cewa, dangantakar tattalin arziki da cinikayya mai dorewa tsakanin kasar Sin da Amurka tana da matukar muhimmanci ga cinikin kayan noma tsakanin kasashen biyu, kuma suna fatan ci gaba da samun kyakkyawan yanayin bunkasa huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA