Fatara Da Talauci Na Yi Wa ‘Yan Nijeriya Miliyan 13 Barazanar Fadawa Kangin Talauci A 2025 — Rahoto
Published: 31st, January 2025 GMT
A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024.
Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar yawan jama’a cikin sauri, ya tsananta matakan talauci.
Tashin farashin kayayyaki shi ne ke kan gaba wajen janyo wa tattalin arzikin Nijeriya matsaloli. Zuwa watan Disamban 2024, kason hauhawar farashin kayan masarufi ya kai zuwa kaso 34.8 lamarin da ke kara lafta wa ‘yan Nijeriya damuwuwi musamman na yadda suke kasa iya sayen ababen bukata kama daga kayan abinci, gidaje da kuma kiwon lafiya.
Daga watan Janairu zuwa Satumban 2024, sufuri da kayan abinci su ne aka samu karuwa sosai a kansu. Tashin kudin man fetur shi ne ya janyo dukkanin tashin kudin sufuri da na kayan abinci.
Karuwar farashin kayan abinci na nuni da barazanar adana abinci da ake ciki, wanda ya shafi ‘yan Nijeriya miliyan 25.1 a 2024. Sai dai rahoton na PwP ya yi gargadin cewa adadin zai iya karuwa zuwa miliyan 33.1 a 2025 muddin hauhawar farashin ya ci gaba da tashi.
Duk da cewa gwamnatin tarayya ta biyo da wasu tsare-tsaren da take ganin za su saukaka kamar karancin albashi, sai dai kaso 4.1 cikin 100 kacal na ‘yan kasar ne ke aiki, lamarin da ke nuni da cewa hakan ba zai yi tasiri ba.
Masu ruwa da tsaki sun lura da cewa lamarin karuwar masu fadawa cikin talauci lamari ne da ke bukatar daukan matakan gaggawa na shawo kan matsalolin da suka dabaibaye tattalin arziki. Duk da karuwar tattalin arzikin Nijeriya na GDP da kaso 3.0 a 2024 akwai bukatar kara himma a 2025.
Rahoton ya yi kira da a samar da ingantattun matakan kawar da fatara, gami da sa kaimi ga al’umma da gyare-gyaren tsari don magance hauhawar farashin kayayyaki da bunkasar tattalin arziki mai dorewa.
A cewar rahoton, idan ba a dauki kwakkwaran mataki ba, matsalar tattalin arzikin da miliyoyin ‘yan Nijeriya ke fuskanta zai kara tabarbarewa tare da jefa dimbin iyalai cikin fatara da kuma kawo cikas ga ci gaban kasar na dogon lokaci.
কীওয়ার্ড: tattalin arzikin yan Nijeriya kayan abinci
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an Tsaro Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara, Sun Ƙwato Bindigogi
Majiyoyi daga cikin jami’an tsaron sun bayyana cewa sojoji da ‘yan sa-kai sun fafata da ‘yan bindigar.
Sun kashe ‘yan bindiga da dama, sannan suka ƙwato bindigogi AK-47 guda uku daga hannunsu.
‘Yan bindigar sun gudu, wasu daga cikinsu na da raunuka ko kuma an kashe su, sai dai adadin ba a tabbatar da shi ba tukuna.
Bayan faɗan ta yi tsanani, an tura ƙarin sojoji zuwa yankin domin ci gaba da matsa wa ‘an bindigar da suka tsere lamba tare da hana su sake kai hari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp