2025-05-08@16:57:20 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2958
«Miyagun Laifuka»:
Da safiyar Alhamis ɗin nan ne Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya halarci zauren Majalissar Wakillai ta ƙasa domin sheda ficewar Ƴan Majalissa uku na Jihar Katsina daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC Ƴan majalissar sun haɗa da Ɗan majalisa mai wakiltar (Mashi/Dutse) Hon. Salisu Yusuf Majigiri, da na (Bakori/Ɗanja) Hon. Abdullahi Balarabe Dabai,...
Karamar Hukumar Birnin Kudu ta nuna gamsuwa da yadda aikin tantance yan fansho ya gudana a yankin. Shugaban Karamar Hukumar, Dr Builder Muhammed Uba ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin jami’an gudanar da aikin tantance yan fanshon jim kadan da kammala aikin a sakatariyar Karamar hukumar. Yace karamar hukumar ta gamsu...
Rundunar ’yan sandan Jihar Akwa Ibom ta ce, ta kama wasu mutum shida da ake zargi da yin garkuwa da wasu mutane a jihar kwanan nan. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, DSP Timfon John ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sanarwa manema labarai a ranar Alhamis a garin Uyo,...
Har ila yau, kwamitin zai bada shawara akan hukuncin da Jam’iyar za ta dauka Idan har aka sami wanda ake zargi da laifin almundahana da kuma zagon Kasa ga LP a lokacin da yake Shugabantar jam’iyar. Sanata Usman ta zargi Abure da mukarrabansa da aikata laifufuka dake janyo rabuwar Kai ga ‘ya’yan Jamiyar...
Har ila yau, kwamitin zai bada shawara akan hukuncin da Jam’iyar za ta dauka Idan har aka sami wanda ake zargi da laifin almundahana da kuma zagon Kasa ga LP a lokacin da yake Shugabantar jam’iyar. Sanata Usman ta zargi Abure da mukarrabansa da aikata laifufuka dake janyo rabuwar Kai ga ‘ya’yan Jamiyar...
Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da shawarar yin amfani da fasahar zamani wajen yaƙi da ta’addanci da ’yan fashi a Nijeriya. Shugaban ya bayar da shawarar ne a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da ya jagoranci mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na ƙasa a ziyarar jaje ga...
Tawagar jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta haɗa da sakataren gwamnatin jihar, da masu ba da shawara na musamman guda biyu, da babban sakataren ZITDA, tare da Siobhan Wilson, shugaban Oracle na Ingila da kuma babban mataimakin shugaban EMEA. Sanarwar ta ƙara da cewa: “Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata...
Amurka ta matsa wa gwamnatocin wasu ƙasashe da Shugaba Donald Trump ya ƙaƙaba musu haraji su amince da kamfanin intanet na Starlink mallakin Elon Musk a ƙasashensu. Elon Musk shi ne mai kuɗin duniya kuma babban makusanci ne ga Shugaba Donald Trump. Jaridar Washington Post ce ta ruwaito hakan a ranar Laraba, tana mai ambaton...
Houthis sun kai hari kan babban filin jirgin sama na Isra’ila kusa da Tel Aviv a ranar Lahadi, a wani ɓangare na yaƙi da ‘yan tawayen ke yi kan Isra’ila, a matsayin tallafin ga Falasdinawa a Gaza. Iran ta musanta cewa ta goyi bayan Houthis a harin. Duk da haka, Isra’ila ta mayar da martani...
An gabatar da shirin talabijin na kasa da kasa mai taken “Kalaman Magabata dake Jan Hankalin Xi Jinping” jiya Laraba a kasar Rasha, yayin da shugaban Sin Xi Jinping ya isa birnin Moscow domin ziyarar aiki a kasar da kuma halartar bukukuwan cika shekaru 80 da samun nasarar yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Fira ministan kasar Siriya ya bayyana cewa: Kasar Siriya zata gudanar da tattaunawa ba na kai tsaye ba da haramtacciyar kasar Isra’ila! Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Siriya Abu Mohammed al-Julani ya sanar a jiya Laraba cewa: Kasar Siriya zata gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya shekara arba’in zuwa sama ya san irin tarbiyyar da ya samu daga wurin iyayensa a da, da irin mu’amalar da ke tsakaninsa da iyaye da kuma irin shaƙuwar da ke tsakanin ’ya’ya da iyaye. A yanzu kuwa, abubuwa sun canza daga yadda aka san su,...
“Duk da cewa, ba zan iya yin cikakken bayani dangane da sabbin dabarun da muka dauka ba. Amma mutanen Yobe su kwantar da hankalinsu kuma abubuwa za su inganta.” Har ila yau, ya yi karin haske dangane da wasu muhimman matakan da za a dauka don magance rashin tsaro a jihar, ciki har da...
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta bankaɗo wata haramtacciyar masana’antar man gyaɗan bogi, tare da cafke mutane uku da ake zargin suna da hannu a harkar. Wannan samame da jami’an sashen leƙen asiri na rundunar suka gudanar ƙarƙashin jagorancin SP Sani Bello, ya gudana ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar ranar 5 ga Mayu...
A jiya ne jakadan Sin a Najeriya Yu Dunhai ya gana da ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar. Jakada Yu ya bayyana cewa, ganawar da ta gudana tsakanin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da mista Tuggar a kasar Brazil a baya-bayan nan, ta aike da sako mai karfi cewa, Sin da Najeriya na...
A cewar sa, wannan bita tana da nufin tantance yadda aka samu cigaba a aiki, da kuma tabbatar da cewa hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar suna tafiya daidai da abin da aka ɗora masu a matsayin nauyi. Ya ce: “Muna nan ne don sauraron shugabannin hukumomi domin mu ga yadda suka aiwatar da muhimman...
Gane sahihancin irin shuka da yake sa tsiro ya yi yabanya sosai na taka muhimmiyar rawa wajen samun girbi mai albarka, don haka wannan na’ura take da matukar muhimmanci, kana tana taimaka wa manoma su fahimci irin shukan da ya dace da yanayin yankinsu kamar yadda wani masanin ilimin injiniyancin aikin gona, Bai Lianyang ya...
Rundunar sojan Ruwan Amurka ta sanar da cewa; Jirgin sama samfurin F-18 wanda kudinsa ya kai dalar Amurka miliyan 67 ya fadi akan jirgin dakon jiragen ruwa na ” USS Harry Truman” a tekun “Red Sea”. Jaridar ” Washington Post” ta buga labarin dake cewa; Jirgin ta fado ne a lokacin da yake kokarin sauka...
A yau Laraba kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty Interantional” ta fitar da rahoto da a ciki ta yi kira ga HKI da ta kawo karshen shirinta na korar Falasdinawa daga Gaza da karfi, tare da cewa; Har yanzu Isra’ilan tana ci gaba da tafka laifukan yaki a Gaza da yi wa mutane kisan kiyashi.”...
Wani rahoto na musamman da HKI ta gudanar akan asarar da ta fuskanta sanadiyyar yaki da Hizbullah, ya bayyana cewa, a fagen aikin gona kawai sun yi asarar dalar Amurka miliyan 108 wacce ta fara daga 8 ga watan Oktoba 2023. Kungiyar ReGrow Israel” ta ce, yakin da aka yi da Hizbullah ya yi barna...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Sharhin bayan Labarai: Mahangar Iran Dangane Da Tattaunawa Kan Shirinta na Makamashin Nukliya Na Zaman lafiya
Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayana labarummu na yau zai yi magana dangane da ‘Mahangar Jumhuriyar Musulunci na Iran ta yadda za’a kai ga fahintar juna a tattaunawanta da kasar Amurka da suke yi wanda ni tahir amin zan karanta. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a wata tattaunawa ta wayar tarho da tokwaransa...
Al’ummar garin Izge da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno sun fatattaki ’yan ƙungiyar Boko Haram bayan kai musu hari a ranar Laraba. Ƙungiyar ‘yan ta’addan ta kuma kashe wani kaftin ɗin soji a harbin na ba zata. Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum Jami’an tsaro na...
“Dole ne mu daina tallata miyagun ayyukan ‘yan ta’adda. Dole ne mu cire su daga jerin shafukan manyan labarai na jaridunmu, mu rahoto ayyukansu a matsayin masu aikata laifuka, sannan mu kore labaran karya.” Ministan ya jaddada cewa, kungiyoyin ta’addanci da masu aikata laifuka sukan yi amfani da kafafen yada labarai da shafukan sada...

Kasar Sin Ta Yi Karin Haske Game Da Tattaunawar Cinikayya Da Za A Yi Tsakanin Babban Jami’inta Da Na Amurka
Ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin, ta ce sabuwar gwamnatin Amurka ta dauki jerin matakan kakaba haraji na ba gaira ba dalili, lamarin da ya kawo tsaiko ga dangantakar cinikayya da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu da ma tsarin cinikayya da tattalin arziki na duniya, tare da kawo kalubale mai tsanani ga farfadowar...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi zargin cewa sojoji da sauran jami’an tsaro na bayar da gudunmawar aikata miyagun laifuka da cin zarafin jama’a a Nijeriya. Zulum ya faɗi hakan ne yayin da yake haramta sayar da barasa a birnin Maiduguri da kewaye. Ka-ce-na-cen da ya biyo bayan ziyarar Tinubu a Katsina DAGA...
Duk da yadda Amurka ke haifar wa tattalin arzikin duk fadin duniya da barazana da kalubale bisa matakin harajin kwastam da ta kara kakkaba wa sauran kasashen, da yanayi maras tabbas da Sin take fuskanta a waje, ingancin tattalin arzikin Sin yana shaida abun da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fada, wato tattalin...
Malam Bala Dutse, wanda ɗansa Amadu yana cikin waɗanda aka kashe, ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin mantawa da al’amarin. “An ce an kama wasu, amma har yau ba mu ji komai ba. Na rasa ɗana, kuma rayuwata ta shiga taka mai wuya. Mafi ƙaranci, gwamnati ta fito ta faɗa mana abin da ke faruwa,”...
Gwamnan Jihar Katsina Umaru Dikko Raɗɗa, ya ce ba shi da masaniyar wani allo da aka kafa mai ɗauke da saƙon ce wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu babu ƙorafi a Katsina ba kamar yadda ake ta muhawara a kai a ƙasar. Hakan na ƙunshe cikin wani saƙon murya ta gwamnan da aka fitar da...
Kasashen duniya na ci gaba da nuna matukar damuwa game da rikicin da ya barke tsakanin Pakistan da Indiya. Iran na daga cikn jerin kasashen da a baya bayan nan suka nuna damuwa. Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar ta ce “Jamhuriyar Musulunci ta bayyana matukar damuwarta kan yadda takun saka tsakanin Indiya...
Kungiyar gwagwarmaya ta Ansarullah ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaiat wutar da ta cimma da Amurka, ba ta sauya matsayin kasar ba na kai wa Isra’ila hari. Kakakin kungiyar Ansarullah Mohammed Abdul-Salam ya jaddada cewa Dakarun Yeman za su ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila domin goyan bayan Falasdinawa a zirin Gaza. Yarjejeniyar da Amurka...
Sai dai, rikice-rikicen cikin gida da matsalolin tsaro da tattalin arziƙi sun sa gwamnatin ke ci gaba da yin gyare-gyare don samar da hanyoyin da za su ba ta kariya da cikakken iko kan harkokin leƙen asiri da tsaro. Wannan mataki yana iya nuni da cewa Nijar na ƙoƙarin zama mai dogaro da kai a...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk shekara, dalibai kan rubuta jarabawa a matakai daban-daban na makarantu daban-daban. Ɗaya daga cikin nau’ukan jarabawa da ɗaliban Najeriya suke yi ita ce Jarabawar Neman Shiga Manyan Makarantu, wato UTME. Kamar kowace shekara, a bana ma ɗalibai sun rubuta wannan jarabawa kuma a cewar Hukumar Shirya Jarabawar...
Yaƙi ya ɓarke tsakanin Indiya da Pakistan yayin da a safiyar wannan Larabar ƙasashen biyu suka riƙa yi wa juna musayar wuta da manyan makaman atilari. Hakan na zuwa ne bayan harin da Indiya ƙaddamar kan Islamabad da sassafe, lamarin da ke nuna ɓarkewar rikici tsakanin maƙwaftan biyu masu makaman nukiliya. Indiya ta ce ta...
A ranar Litinin ne hukumar JAMB ta bayyana cewa daga cikin ɗalibai miliyan 1.95 da suka zauna jarabawar bana, kusan miliyan 1.53 — wato kashi 78 cikin 100 — ba su samu maki 200 ba. Sai dai ɗalibai 12,414 kacal suka samu maki 300 ko sama da haka. Ministan ya jaddada cewa wannan mataki na...
Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta mabiya Al-Houthi ta sanar da cewa: Sanarwar da shugaban Amurka ta fitar kan Yemen gazawa ce ga Netanyahu Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta sanar a jiya Talata cewa: Sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi dangane da kasar Yemen gazawa ce ga Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar...
Gwamnatin kasar Indiya ta yi luguden makamai masu linzami kan kasar Pakistan, yayin da Pakistan ta sha alwashin mayar da martani Gwamnatin Indiya ta kai hare-haren makamai masu linzami kan wasu wurare a kasar Pakistan da yammacin jiya Talata, kuma sojojin Pakistan sun sha alwashin mayar da martini, yayin da ake ci gaba da samun...
Kasar Sudan ta yanke huldar jakadancinta da kasar Hadaddiyar Daulart Larabawa tana mai ayyana UAE a matsayin ‘kasa mai cin zali’ Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron kasar Sudan ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata cewa: Sudan ta yanke...
Da yake tsokaci game da wasan na karshe na jiya, Mark Williams daga yankin Wales, ya ce Zhao abokin karawa ne mai hazaka. Don haka ba abun da zai fada game da shi illa jinjinawa. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
Wata ƙungiya mai rajin kare muradun al’ummar Hausawa a Nijeriya mai suna Kungiyar Hausawan Nijeriya ta tsaya kai da fata cewa dole a ƙyale Hausawa su kafa ƙungiyarsu kamar kowacce ƙabila tun da dai doka ba ta hana su ba. Martanin nasu na zuwa ne a daidai lokacin da masu kiran ke shan sukar cewa...
Majalisar Dattawa ta kafa kwamiti mai mambobi 18 domin sanya idanu kan yadda gwamnan riƙo na Jihar Ribas Vice Admiral Ibok Ete Ibas mai ritaya ke tafi da aikinsa. Majalisar ta ce ta ɗauki matakin ne a wani yuƙuri na ƙarfafa shugabanci na gari ba tare da rufa-rufa ba a jihar da ke kudu maso...
Trump ya bayyana cewa, waɗanda suka zabi barin ƙasar da kansu na iya samun dama ta hanyar doka don dawowa cikin Amurka nan gaba idan suka cika ka’idojin da suka dace. A cewar rahoton, an riga an sayo tikitin jirgi ga mutum na farko da ya karɓi wannan tayin — daga birnin Chicago zuwa...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaaei ya bukaci kasashen turai da su shiga a dama da su kan tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar Iran na zaman lafiya. Ya kuma jaddada cewa Iran tana turjiya ga dukkan tunanin Amurka na wargaza shirin Nukliyar kasar Iran kwata-kwata. Baghaei ya kara da cewa duk da...
A yau, rukunin farko na tawagar wanzar da zaman lafiya da martanin gaggawa na kasar Sin kashi na biyu wadda za ta je yankin Abyei, ya tashi daga birnin Zhengzhou na kasar Sin, da jirgin saman soja domin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya na tsawon watanni 12. Bugu da kari, ana shirin tura...
Kawamcen jam’iyyun siyasa na kasar Ivory Coast ya bukaci a sake lalen yadda aka tsara yadda ake ristar jam’iyyu a hukumar zaben kasar, ganin yadda ta hana rijistar wasu jam’iyyun saboda dalilai daban daban. Shafin yanar gizo na labarai Afirka news ya bayyana cewa an kafa kawancen ne wanda aka sanyawa suna CAP-CI a farkon...
A safiyar yau ne jiragen yakin HKI suka kai hare-hare kan tashar Jiragen sama na birnin San’a na kasar Yemen inda ake ganin hakan kara ruruta wutan yaki a yankin ne. Klamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a dai-dai lokacinda jiragen yakin Amurka suka dauki kimani watannin biyu suka kai hare...
Karamar Hukumar Birnin Kdu tace tana nazarin samar da cibiyar horas da maniyyata aikin hajji ta dindindin a yankin domin karawa mahajjata kaimi wajen gudanar da aikin karbabbe. Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Muhammad Uba Builder ya bada wannan tabbacin a lokacin rufe bitar da aka shiryawa maniyyatan yankin na Birnin kuudu. Yana mai...
Friedrich Merz na jam’iyyar CDU ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus. Majalisar Dokokin Jamus ta Bundestag ta zabi Merz a matsayin sabon shugaban gwamnati lokacin zaɓen zagaye na biyu, bayan ya gaza samun ƙuri’un da yake buƙata a zagayen farko na zaɓen. A zaɓen farko Merz ya samu ƙuri’u 325 na jam’iyyun ƙawance daga majalisar...
A bidiyon da wani mai suna Nawab Sheikh ya fitar na nuna yadda ya hau motarsa, wacce yake tuka ta a kan titunan birnin Murshidabad a cikin ƙasar Indiya, don nishaɗantar da mahaya babur, wanda ya sa bidiyon yake ta yaɗuwa a shafin sada zumunta na Instagram. Babu wani wuri mafi kyawun nuna bajintar kirkira...