2025-09-18@02:41:32 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2089

«tazaran haihuwa»:

    A zagayen duba farashin kayayyakin da aka gudanar a kasuwannin ƙasar nan, ya nuna cewa, farashin 50-kilogramme na buhun shinkafa ƴar gida ana sayar da shi ne a kan naira dubu 65,000 zuwa naira 68,000, inda kuma ake sayar da masara kan naira dubu 35,000 zuwa 37,000 a kan kowani buhu, yayin da na ƙasashen...
    Mai Martaba Sarkin Dutse, Dr Hameem Nuhu Muhammadu Sunusi ya kaddamar da rabon zakkar kudi ta shekarar musulunci ta 1446 a gundumar Yayari dake Karamar Hukumar Buji. A jawabin sa, Mai Martaba Sarkin ya ja hankalin al’umma da su ci gaba da fitar da hakkin Allah domin samun makoma a nan duniya da kuma gobe...
    Gwamnatin jihar Borno na shirin sake tsugunar da ‘yan gudun hijira kusan 5,000 daga al’ummomin Bama su biyar kafin damina ta kare. Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana haka a wata ziyarar ban girma da ya kai wa Shehun Bama, Dakta Umar Kyari Umar El-Kanemi a ranar Juma’a. Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar...
    Minista Idris ya bayyana damuwa da irin martanin da al’umma da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai suka nuna dangane da lamarin. Amma ya jaddada cewa hukumar da ke da hurumin dakatar da lasisin gidajen rediyo da talabijin ita ce Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), kamar yadda doka...
    “daidaita farashin ya kasance hanya daya tilo da za a iya amfani da ita wajen tafiyar da harkokin kasuwa da kuma tabbatar da gaskiya,” in ji shi. Edun ya nuna ƙalubale a tsarin biyan ciniki a Nijeriya, tare da lura da cewa har yanzu ana samun yawan hada-hadar kasuwanci ta hanyoyin da ba kamata ba....
    Nijeriya, wadda take ta daya a jerin ƙasashen da suka fi iya ƙwallon mata a Afirka, ta zura ƙwallon da ta ba ta nasara ne a gab da tashi wasa a karawarta da Afirka ta Kudu a wasan kusa da na ƙarshe. A yanzu za a iya cewa Nijeriya ta cimma burinta na ‘Mission ɗ’,...
    “Kazalika sarkin ya bayyana cewa, mun kuma duba yanayinmu. Me muke da shi? Me za mu iya yi? Me ya kamata mu yi domin inganta rayuwar mutanenmu? Allah ya albarkaci ƙasarmu, ƙasa ce mai faɗi sosai, kuma ta dace da ayyukan noma. Mun kuma yi la’akari da fannin ilimi. Jihar Neja, an san tana gaba...
    Wani mutum ya rasu, yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin mazauna ƙauyen Kuchibiyi da jami’an ’yan sanda a Ƙaramar Hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja. Wani mazaunin ƙauyen, Samuel Dangana, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa rikicin ya samo asali ne yayin da wasu da ake...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa na shirin mayar da mutum 5,000 gida daga sansanin ‘yan gudun hijira kafin wucewar damina domin su samu damar yin noma. Mutanen za su fito ne daga garuruwan Goniri, Bula Kuriye, Mayanti, Abbaram, da Darajamal. Ma’aikatan jinya sun dakatar da yajin aiki a faɗin Najeriya Rufe...
    A’isha ƴar shekara uku da suke zaune a ƙarƙashin inuwar bishiyar ɗogoyaro a wani ƙauye mai nisa a yankin Arewa maso Gabas (sansanin gudun hijira). Babu takalmi a ƙafarta, ta yi shiru, saboda radaɗi da take ji. ƙafafuwanta sirara sun yi rauni, cikinta ya dan kumbura saboda yunwa, idanunta sun fito tana cikin halin da...
    Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na bada managartan shawarwari da za su yi wa kananan hukumomin jihar jagoranci wajen gudanar da ayyukan su kamar yadda yakamata. Shugaban Kwamatin Kananan Hukumomi na Majalisar, Alhaji Aminu Zakari, ya bada wannan tabbacin lokacin rangadin kwamatin majalisar a sakatariyar karamar hukumar Birniwa. Alhaji Aminu Zakari Wanda...
    A yau Asabar, hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin Beijing ta sanar da cewa, an dawo da wutar lantarki da ayyukan sadarwa a dukkan kauyukan da ibtila’i ya shafa a fadin birnin na Beijing, biyo bayan mamakon ruwan sama da iska mai karfi da aka tafka, yayin da kuma ake ci gaba da aikin...
    Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Jihar Katsina ta kori ɗalibanta 57 kan laifin satar jarabawa. Hukumar gudanarwar jami’ar ta kuma dakatar da wasu dalibai biyar na tsawon shekara guda tare da ba wasu biyu takardar gargaɗi kan aikata laifukan jarabawa. A safiyar Asabar kakakin jami’ar, Hajiya Fatima Sanda, ta sanar da cewa majalisar jami’ar...
    A bisa ƙiyasin da babban bankin Nijeriya (CBN) ya yi, ya ce; tumatirin da ake nomawa a   shekara a Nijeriya, ya kai kimanin tan miliyan 1.701, wanda kuma ake amfani da shi a shekara ya kai aƙalla tan 2.93, inda wannan adadin ya nuna cewa; a shekara, ana samun ƙarancinsa da ya kai na...
    Bincike a kan zargin da ake wa Hukumar Raya ƙasashe ta Amurka (USAID) da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da na ƙasa da ƙasa game da tallafa wa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP da sauran masu tayar da ƙayar baya a Nijeriya har yanzu bai kammala ba. Kawo yanzu babu wata ƙwaƙƙwarar...
    daga ƙarshe, kwamitin ya tabbatar da cewa zai miƙa dukkan shawarwarin da al’ummar yankin suka bayar gaban Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina Malam ɗikko Raɗda don daukar matakin da ya dace.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Asusun kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ya ce Najeriya ce ƙasa ta biyu da aka fi samun ɓullar cutar kwalara a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka. Darektan Hukumar UNICEF mai kula da yammacin Afirka da Afirka ta tsakiya, Gilles Fagninou  ne ya bayyana hakan tare da cewar annobar kwalara ta zama...
    Slovenia ta kasance Ƙasar Turai ta farko da ta ba da sanarwar hana tura makamai zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila Kasar Slovenia ta sanar da haramta musayar zirga-zirgan kayayyakin kasuwanci tsakaninta da haramtacciyar kasar Isra’ila musamman safarar makamai da kayan aikin soji zuwa Isra’ila, inda ta zama kasa ta farko ta Turai da ta dauki wannan...
    Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), za ta fara rajistar ƙuri’a ta intanet a ranar 18 ga watan Agusta, 2025, domin tunkurar zaɓen 2027. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da Hukumar NOA ta masa a hedikwatar INEC da ke Abuja. Rundunar sojin ruwa za...
    “Kiyasin ƴan Nijeriya miliyan 20 ke rayuwa da cutar hanta, kuma mutum miliyan 18.2 sun kamu ne da cutar rukunin B, sannan wasu mutum miliyan 2.5 sun kamu da cutar rukunin C. Abin takaici, ƴan Nijeriya 4,252 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon ciwon hanta da aka kasa maganceta ke haifarwa,” ya shaida.  A...
    Akalla ’yan gudun hijira miliyan daya da dubu 400 da ke Arewa maso gabashin Najeriya ne suke fuskantar barazanar yunwa bayan yanje tallafin da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ke bayarwa. Wani rahoton majalisar a kan abinci da tsaro wanda gwamnatin Najeriya, Shirin Kula da Abinci na Majalisar (FAO) da sauran masu ruwa da tsaki a...
    Ministan kasuwanci na Afirka ta Kudu Parks Tau ya fada jiya Alhamis cewa kasarsa na shirin yin shawarwarin kasuwanci da nufin kaucewa harajin kashi 30% na Amurka a kan kasarsa, wanda  zai fara aiki daga wannan Juma’a. A farkon watan Mayu ne Afirka ta Kudu ta gabatar da wani shirin  yarjejeniya ta kasuwanci ga gwamnatin...
    Ya nuna rashin jin daɗinsa da rabon ayyukan tituna kamar yadda aka samu a cikin wata sanarwa da ma’aikatar ayyuka ta fitar a watan Mayun 2025, wanda a cewarsa, an ware Naira tiriliyan 1.394 wa yankin Kudu-maso-Yamma, yayin da ɗaukacin yankin Arewa-maso-gabas suka samu Naira biliyan 30, sai kuma yankin Arewa-maso-Yamma Naira 105 biliyan. “Rashin...
    Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana Sai dai, abin dubi a nan shi ne, yadda kusan yanzu a kasar, tabbatar da doka da oda, a cikin kasar, ya koma kachokam, a huunun...
    Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da kashe Naira biliyan 712.26 don yi wa wani sashe na filin jirgin saman a Murtala Muhammad da ke Legas garambawul. Hakan dai ya biyo bayan zaman majalisar wanda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a Abuja ranar Laraba. NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan...
    Gwamnatin Nijeriya ta bayanna cewa za ta soma yi wa ɗaliban jami’o’in ƙasar nan gwajin miyagun ƙwayoyi a wani mataki na daƙile yaɗuwar ta’ammali da ƙwayoyin. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tare da haɗin gwiwar Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA ne za su jagoranci aikin....
    Ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da iska mai karfi da aka tafka a kwanan nan ya yi sanadin mutuwar mutane 44, yayin da wasu tara suka bace a birnin Beijing, kamar yadda aka bayyana a wani taron manema labarai da ya gudana a yau Alhamis. A yayin taron manema labarai da gwamnatin birnin...
    Allah Ya yi wa Mai Martaba, Sarkin Gudi Alhaji Isa Bunuwo Ibn Khaji rasuwa a asibitin Nizameye da ke Abuja ranar Alhamis. Mai martaba Sarkin wanda ke garin Gadaka a Ƙaramar hukumar Fika cikin Jihar Yobe ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya. Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamani Peter...
    Ɗaya daga cikin jigo da suka kafa Jam’iyyar PDP, Farfesa Jerry Gana ya yi iƙirarin cewa tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi zai kayar da duk wani ɗan takara a jihohin Arewacin Najeriya idan ya tsaya takara a PDP. Da yake bayabni a tashar talabijin ta Arise TV a ranar Laraba, Gana ya ce, “Ni...
    Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin wa’adin shekara guda ga shugaban hukumar Kwastan ta Nijeriya, Bashir Adewale Adeniyi. Kafin wannan ƙarin wa’adin, aikin Adeniyi zai kare ne a ranar 31 ga Agusta, 2025. Sai dai sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya...
    Manchester United ta soma tattaunawa da Paris St-Germain kan golan Italiya Gianluigi Donnarumma, mai shekara 26, amma Chelsea da Manchester City na cikin masu sha’awar golan. (Telegraph – subscription required, external) Yayin da ɗanwasan gaba na Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, ya amince ya koma Liverpool, Newcastle ta saka ɗanwasan Brazil Rodrigo Muniz, mai shekara 24 cikin lissafinta. (Mail – subscription required, external) Crystal Palace ta sanar...
    Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara, ta bayyana matukar damuwarta kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a jihar, inda ta bayyana hakan a matsayin abin ban tsoro da rashin fahimta.   A wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar, Yusuf Idris Gusau, jam’iyyar APC ta ce yawaitar ‘yan fashi da makami,...
    Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta sanar da cewa, a halin yanzu ana iya  bayyana kadarorin ma’aikatan ta hanyar yanar gizo, wani mataki da aka tsara domin saukaka aikin da kuma kara yin lissafi.   Daraktan ofishin na jihar Jigawa Abubakar Bello ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci shugaban ma’aikatan jihar Alhaji...
    Gwamnatin jihar Kwara ta kori mabarata 94 daga titunan Ilorin, domin tantancewa, gurfanar da su da kuma mayar da su gida.   Da take magana da ‘yan jarida yayin aikin, kwamishiniyar jin dadin jama’a da ci gaban jihar Dr Mariam Nnafatima Imam ta ce wadanda aka kama domin dawo da su sun hada da mata...
    Shugaban kwamitin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce kwamatin ya jinkirta rangadin kananan hukumomin jihar 27 a Zango na uku na shekarar 2024 ne a sakamakon zaben kananan hukumomi, don haka akwai bukatar ba su damar gudanar da ayyuka kafin tantance kwazon su.   Alhaji Aminu Zakari ya yi...
    “Muna kira ga gwamnatin jiharmu da ta kawo mana agaji da gaggawa domin da yawa daga cikin kaburburan da ke makabartar, sun rufta bayan ruwan saman, wannan aikin ya fi karfin mu.” In ji shi.   A halin da ake ciki dai, rundunar ‘yansandan jihar Borno ta gaggauta gudanar da tantancewa a wurin tare da...
    Kwamitin da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umari Radda, ya kafa domin binciken ayyukan makarantun gaba da sakanadare masu zaman kansu na jihar, ya tabbatar da cewa, 37 cikin 39 ba su da rajista da gwamnati. Shugaban kwamitin, Farfesa Ahmed Muhammad Bakori, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar...
    Adamu ya bayar da hujjar cewa, Sarkin Musulmi ne ke shugabantar daular gargajiya mafi girma a Arewacin Nijeriya, tare da dukkan sarakunan yankin karkashin jagorancinsa na ruhi da al’adu.   Ya yaba da shugabancin Sarkin Musulmi Abubakar na tsaka-tsaki, samar da zaman lafiya, da jagoranci na hadin kai.   Sun bayyana shi a matsayin mutum...
    A cewarsa, binciken da ake yi ya nuna cewa, shawarar da aka yanke na fara gudanar da aikin matatar man ta Fatakwal kafin a kammala cikakken aikin gyaranta bai kamata ba.   Ya kara da cewa, duk da cewa an kokarta kan farfado da dukkan matatun man guda uku. Sai dai da dama na kira...
    Shugabannin Hukumomin Watsa Labarai Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa Aisha Buhari Shugabannin manyan hukumomin watsa labarai na ƙasa Hukumar Rediyon Najeriya (FRCN), Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA), da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) – sun kai ziyarar ta’aziyya ga tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, bisa rasuwar mijinta, tsohon...
    Kwamandan, Nigerian Defence Academy NDA, Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya bukaci dalibai da su jajirce wajen ganin sun samu nagartar ilimi. Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya yi wannan kiran ne a yayin bikin yaye dalibai da jawabai da kuma bayar da kyaututtuka da aka yi a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Malali Kaduna. Kwamandan...
    Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sauke Farfesa Muhammad Sani Bello daga matsayin Kwamishinan Yaɗa Labarai kuma memba na majalisar zartarwa ta jihar. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Ibraheem Musa, ya fitar a ranar Talata, an bayyana cewa Ahmed Maiyaki, wanda shi ne Manajan Darakta na Kamfanin Yaɗa...
    Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da zagayen farko na makon lafiyar mata da jarirai da jarirai (MNCHW) na shekarar 2025 tare da raba fakiti 6,000 na kayan haihuwa da na’urar (C/S) 500 ga cibiyoyin lafiya a fadin jihar.   Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta shi ne ya jagoranci...
    Sauran sun haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu, tsoffin gwamnoni, ministoci da hafsoshin tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Fira ministan Birtaniya ya bayyana cewa: Za su amince da kasar Falasdinu a watan Satumba idan yanayin Gaza bai canza ba Keir Starmer ya kara da cewa, an dauki wannan matakin ne domin kare tsarin kasashe biyu, kuma kasarsa na da wani nauyi na musamman da ya rataya a wuyanta wajen ganin an samar da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wasu al’ummomi sun bayyana dalilan da suka sa suka karbi tsarin yin gwajin lafiyar ma’aurata kafin a daura musu aure. A wasu lokutan, akan samu matsaloli sakamakon rashin gwajin jini kafin a hada mace da na miji aure. Matsalolin sun hada da yaduwar cututtuka, samun ‘ya’ya marasa lafiya...
    Kwamitin neman sabuwar Karamar Hukumar Kanya Babba daga Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa, ya gabatar da takardar bukatarsa ga kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da kirkiro jihohi da kananan hukumomi a zaman da aka yi a jihar Kano. A yayin mika takardar, Shugaban kwamitin kuma Hakimin Kanya Babba,  Makaman Ringim, Malam Mohammed Ibrahim...
    Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara wanda ke jagorantar ƙasar tun daga shekarar 2011, na fuskantar suka na neman mayar da shugabancin ƙasar mutu ka raba. Wannan dai na zuwa ne bayan Ouattara mai shekaru 83 ya tabbatar da aniyar sake takara wa’adi na hudu a zaben da za a yi ranar 25 ga watan Oktoba....
    Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kammala gyaran makarantu fiye da 1,200 a kananan hukumomi 44 na jihar a wani yunkuri na farfado da harkar ilimi. Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Ali Haruna Makoda, ne ya bayyana hakan yayin taron bitar yini guda kan kara kaimi a tsarin duba ingancin karatu, da aka gudanar a...
    Gwamnan Jihar Filato, Barr. Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa babu wata ƙaramar hukuma a cikin jihar da ƴan ta’adda ko ƴan bindiga ke da iko da ita. Ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da ƴan jarida da aka gudanar a sabon gidan gwamnati da ke Little Rayfield, Jos, a ranar Talata. Gwamna Mutfwang...