2025-08-09@11:19:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7568
«Jihar Benuwe»:
Kudirin gyaran dokar fansho da sauran fa’idodi na tsaffin jami’an gwamnati ya wuce karatu na biyu a zauren Majalisar Dokokin Jihar Jigawa. Wakilin mazabar Malam Madori, Alhaji Hamza Adamu Ibrahim wanda shi ne shugaban Kwamatin kasafin kudi na majalisar, shi ne ya gabatar da wannan kudurin, ya kuma samu goyon bayan wakilin mazabar Guri Alhaji...
Sun kara da cewa,”A cikin wannan lokaci, mataimakin kyaftin na yanzu, Ronald Araujo ne zai karbi aikin kyaftin din, Ter Stegen ya buga wa Barcelona wasanni sama da 400 tun lokacin da ya koma kungiyar daga Borussia Monchengladbach a shekara ta 2014, ya lashe manyan kofuna da suka hada da gasar zakarun Turai da kuma...

Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12
Ma’aikatar kudi ta kasar Sin, ta ce tallafin gwamnati na samar da ilimi kyauta ga daukacin daliban dake ajin karshe a makarantun share fagen shiga firamare a kasar zai amfani mutane kusan miliyan 12. Yayin wata ganawa da manema labarai a yau Alhamis, mataimakin ministan ma’aikatar kudin kasar ta Sin Guo Tingting, ya ce...
Madugun adawa a Nijeriya, Atiku Abubakar ya bukaci a gaggauta sakin fitaccen ɗan gwagwarmayar, Omoyele Sowore da ke tsare a hannun ’yan sandan kasar. Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriyar wanda ya yi Allah-wadai da lamarin ya ce abin kunya ne cin zarafi da tawagar sa ido ta sufeto janar na ’yan sandan ƙasar suka yi wa...
Mazauna kauyuka akalla 30 daga Dan-Isa da Kagara dake karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara, sun mamaye gidan gwamnati dake Gusau babban birnin jihar domin nuna takaicinsu kan yadda rashin tsaro a yankin na su “yaki ci yaki cinyewa” a ranar Alhamis. Masu zanga-zangar da suka hada da mata da kananan yara suna dauke da...

Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan
Alkaluman kididdiga na hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna yadda cikin watanni 7 na farkon shekarar nan ta 2025, jimillar darajar cinikayyar kayayyaki ta kasar Sin ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 25.7, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 3.5, wanda hakan ya nuna karuwar kashi 3.5 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokaci na...
Fitaccen matashin nan mai barkwanci, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Ɗan Bello, ya yi rashin mahaifinsa a yammacin wannan Alhamis din. Matashin lauyan nan ɗan gwagwarmaya, Abba Hikima, ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe...
Bugu da kari, a baya bayan nan ma jaridar Financial Times, ta bayyana yadda a yanzu haka adadin hajojin da ake shigarwa Amurka daga sassan duniya daban daban suka ragu zuwa kaso 13 bisa dari, sabanin kaso kusan 20 bisa dari da kasar ke shigowa da su a tsawon shekaru 20 da suka gabata. Kamar...
Wasu daga cikin tsoffin kansilolin da suka halarci tattakin sun bayyana goyon bayansu ga gwamna Abba Kabir Yusuf. A nasa jawabin, Dahiru Yusuf daga Gezawa kuma tsohon kansila ya ce, shi ma yana cikin wadanda tsohuwar gwamnatin Ganduje ta hana hakkinsu, don haka maganar Abdullahi Abbas ba gaskiya bane! “Sun ga gwamna Abba zai...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini kan rasuwar Sadiq Gentle, wani hadiminsa kan harkokin yada labarai a Ma’aikatar Tarihi da Al’adu ta jihar, wanda wasu da ake zargi ’yan daba suka kai masa harin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a Facebook, ta...
Ya kuma lura da cewa, tattaunawa da ‘yan bindiga a wasu jihohin suka yi ya kara ta’azzara satar shanu, inda ya ce, Sam hakan, ba za a amince da shi ba. Dangane da ta’azzarar rashin tsaro, Gwamna Bago ya ce, za a nemi taimako daga shugaba Bola Tinubu da mai bai wa shugaban kasa...
Manoman gundumar Ɗan Isa da ke Ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara sun ce ’yan bindiga sun yi musu barazana a wannan damina ta bana. Da yake tabbatar da hakan ga Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar tarho, Hakimin unguwar Malam Hassan Yarima, ya ce kowane ƙauyuka 35 da ke ƙarkashin gundumarsa ya...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Amurkawa sun yi kuskure idan suna tunanin cewa hari kan cibiyoyin makamashin nukiliya zai canza matsayin Iran ko kuma ya sa ta ja da baya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Dole ne a fara wani sabon mataki na dangantaka tsakanin Iran da hukumar kula...
Alummar duniya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan furucin firaministan Israila na fadada mamaya a Gaza. Sakamakon wani nazarin jin raayin jamaa da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar ya nuna cewa, kaso 86.6 na wadanda suka bayar da amsa sun bayyana adawa mai karfi da matakin firaministan, suna masu kira da...
Babban Hafsan Hafsoshin sojin Iran ya bayyana cewa; Martanin da Iran za ta mayar kan duk wani hari zai kasance murkushewa ne, kuma ba zata jira izinin kowa ba Babban hafsan hafsan sojin kasar Iran ya gargadi makiya, yana mai cewa: Suna yi wa shahidai alkawari cewa: Za su ci gaba da bin tafarkinsu, kuma...
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun jaddada cewa: Duk wata barazana ga tsaron Iran za ta fuskanci kakkausan martani mai zafi fiye da tunani Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun fitar da sanarwar cikan kwanaki 40 da shahadar shahidan Iran a lokacin wuce gona da iri na yahudawan sahayoniyya...
Falasdinawa masu yawa ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin ‘yan sahayoniyya suka kai kan tantuna da gidaje da ‘yan gudun hijira a Gaza Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkatan wasu masu yawa da sanyin safiyar yau Alhamis a wasu munanan hare-hare da jiragen yakin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka...
Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Human Rights Watch ta tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun rusa makarantu sama da 500 a Gaza A cikin wani sabon rahoton da kungiyar ta Human Rights Watch ta fitar, kungiyar ta zargi sojojin mamayar Isra’ila da kai hare-hare ba bisa ka’ida ba kan makarantun da ke suka...
Waɗannan bayanai duk suna ƙunshe ne a cikin jawaban da aka gudanar a gangamin wayar da kai game da wannan cuta, wanda ya gudana a Kaduna. Lokacin da ta ke zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan wannan gangami, Dr. Maimuna Lawal Garba, ƙwararriyar Likita a fannin hanci, kunni da maƙogwaro, ta fara bayanin...

Kasar Sin Ta Kammala Gwajin Farko Na Sauka Da Tashin Kumbon Binciken Duniyar Wata Mai Dauke Da Bil Adama
Kasar Sin ta sanar a yau Alhamis cewa ta yi nasarar kammala cikakken gwajin sauka da tashin kumbun binciken a duniyar wata mai dauke da bil adama, a wani yankin gwaji dake gundumar Huailai ta lardin Hebei. Gwajin da aka kammala ranar Laraba na nuni da wani muhimmin ci gaban da Sin ta samu...
’Yan bindiga ɗauke da makamai sun shiga ƙauyen Bimasa a Ƙaramar Hukumar Tureta a Jihar Sakkwato sun kashe mutum huɗu sun jikkata wasu da dama a daren ranar Laraba. Ɗaya daga cikin jagorori a ƙauyen ya yi wa Aminiya ƙarin bayani ya ce, a daren ranar Laraba da ƙarfe 12:40 na tsakar dare ɓarayi suka...
“An kashe da dama, kuma wasu da yawa sun sami munanan raunuka.” In ji Kaftin Adewusi Bayan farmakin ta sama, sojojin kasa na Birget 1 dake karkashin sashe na 2 na OPFY sun kaddamar da wani samame ta kasa a ranar 5 ga watan Agusta, inda suka yi nasarar dakile wani harin kwantan bauna...
A yau Alhamis aka yi bikin bude gasar wasanni ta duniya ta 2025 a birnin Chengdu na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa (CEO) na Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC). Haka kuma, ya naɗa Abubakar Yusuf a matsayin Kwamishinan Harkokin Abokan Hulɗa, da Dr. Fouad Olayinka Animashun a matsayin Kwamishinan Kudi da Harkokin Gudanarwa. A cikin...
Manoma sama da 500 daga gundumomi 15 na karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara sun samu horo kan kiwon awaki na zamani da kuma yadda ake samar da abincin dabbobi, a wani yunƙuri na rage yawan rikici tsakanin manoma da makiyaya tare da inganta rayuwar al’ummar karkara. An gudanar da wannan horo a Idofian karkashin...
Da yake la’antar kisan a matsayin “mummuna, dabbanci, kuma lamarin da ba za a lamunta ba,” gwamnan ya yi alkawarin tabbatar da adalci. Ya umurci hukumomin tsaro da su dau mataki tare da kama wadanda ke da hannu a kisan nasa nan take. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta bayyana alhinita kan kisan gilla da aka yi wa Umar Abdullahi Hafizi, dalibi da ke matakin karatu na 3 a Sashen Ilimin Zamantakewa (Sociology), wanda wasu masu kwacen waya suka daba wa wuka har lahira a gidansa da ke unguwar Dorayi a ƙaramar hukumar Gwale. Wannan na ƙunshe...
Mun san cewa, ci gaban harkokin matasa na bukatar bunkasar sana’o’i. Cikin shekarun nan, aikin zuba jari ga kasashen Afirka da kasar Sin ke yi na samun ci gaba yadda ake bukata. Inda yawan kudin da Sin take zubawa kai tsaye a fannin samar da kayayyaki a kasashen Afirka, ya kai fiye da dalar Amurka...
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ekiti, Joseph Eribo, ya tabbatar da ƙwato jaririn da aka sace a wani asibiti da ke Ado-Ekiti ranar Litinin. An miƙa jaririn ga iyayensa, Mustapha Aliyu mai shekara 29 da kuma Salmatu Lawal mai shekara 22, bayan da jami’an ’yan sanda suka tsananta binciken lamarin. An kashe matafiya biyu da yin...
Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu mutum uku a Ƙauyen Ganmu da ke kusa da Babanla a Ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara. An samu rahoton cewa, harin ya faru ne a lokacin da waɗanda harin ya rutsa da su, ke kan hanyar Legas zuwa Babanla suka samu...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta biya iyalai 14 da aikin sake gina Babban Masallacin Gumel ya shafa kudaden diyya da suka kai Naira miliyan 277 da dubu 44. An gudanar da bikin bayar da takardun cekin kudin ne a Fadar Mai Martaba Sarkin Gumel, Dr. Ahmad Muhammad Sani, tare da halartar masu rike da sarautu, da...
Mazauna kauyen Chatta da ke karamar hukumar Hawul a jihar Borno sun fada alhini sakamakon rasuwar wasu mutum hudu ’yan gida daya. Ba a dai tabbatar da ainihin musabbabin rasuwarsu ba, amma mazauna yankin da lamarin ya faru sun ce suna zargin hayakin injin samar da lantarki na janareta ne ya yi ajalin su. An...
Sayar da Nunez zai ba Liverpool damar siyan Alexander Isak daga Newcastle. Sai dai Newcastle ta ƙi karɓar tayin fam miliyan 110 daga Liverpool, saboda tana so ta siyar da Isak ne abkan fam miliyan 150. Liverpool ta riga ta siyo Florian Wirtz daga Bayer Leverkusen a kan fam miliyan 116 da kuma Hugo Ekitike...
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bada motocin aiki ga shugabannin hukumomi, jami’an tsaro da wasu manyan jami’an gwamnati a jihar. An gudanar da bikin mika motocin ne a Fadar Gwamnati da ke Minna. Gwamna Bago ya bayyana cewa wannan mataki na bayar da motocin aiki na da nufin tallafa wa harkokin sufuri da...
Gwamnatin amurka ta kwace kudaden Jami’ar Calfoniya da ke birnin Losangelis saboda abinda ta kira samuwar masu goyon bayan Falasdinawa a cikin dalibai da kuma malaman jami’ar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, wannan babban kalu bale ne ga Jami’ar saboda rashin wadan nan kudade. Gwamnatin amurka ta zargi hukumomin Jami’ar...
Gwamnatin amurka ta kwace kudaden Jami’ar Calfoniya da ke birnin Losangelis saboda abinda ta kira samuwar masu goyon bayan Falasdinawa a cikin dalibai da kuma malaman jami’ar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, wannan babban kalu bale ne ga Jami’ar saboda rashin wadan nan kudade. Gwamnatin amurka ta zargi hukumomin Jami’ar...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama wasu bama-bamai da ba su fashe ba da wasu tarin makamai da aka shigar da su jihar cikin kayan gwangwan daga jihar Borno. Lamarin dai ya jefa fargaba a zukatan mutane kan yadda kayayyaki ke yawo babu bincike daga jihohin da ke fama da rikici. Yadda kwacen babur...
Jami’an tsaro a kasar Lebanon sun bayyana damuwarsu da yiyuwar sojojin HKI su farwa kasar da yaki da nufin kwace kasar da kuma sunan yaki da kungiyar Hizbullah. Jaridar da nation ta kasar amurka ta bayyana cewa, HKI ta jibje sojojin masu yawa da kuma tankunan yaki a kusa da Jabal sheikh da suka mamaye,...
Ana zargin wasu ‘yan sanda daga Sashen Binciken ‘yan sanda na Kasa sun kutsa inda ake tsare dan gwagwarmaya Omoyele Sowore a Abuja, inda suka fita da shi da karfin tuwo zuwa wani wuri da har yanzu ba a sani ba. Haka kuma kamar yadda Sowore ya sanar a shafinsa na sada zumunta na...
Ministan Harkokin wajen Masar Badr Abdelatty ya fara ayyukan diblomasiyya inda ya fara tattaunawa da Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi dangane da farfado da tattaunawa kan shirin Iran na makamashin Nukliya tare da shugaban hukumar, IAEA Rafael Grossi, da kum wakilin Amurka na musamman a gabas ta tsakiya Steve Witkoff,. Amma a yanzun...
“Ko da yake lamarin ya faru ne a wajen harabar jami’a, Hukumar Gudanarwa ta jami’ar na cikin jimami matuƙa da wannan mummunan lamari, kuma tana miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, abokansa da sauran ɗalibai,” in ji sanarwar. Shugaban Jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya bayyana cewa jami’ar na aiki tare da hukumomin tsaro domin a...
Ana zargin ‘yan sandan da karya hannun Sawore Ana zargin wasu ‘yan sanda daga Sashen Binciken ‘yan sanda na Qasa sun kutsa inda Hukumar ‘Yan sanda ta Qasa ke tsare xan gwagwarmayar neman haqqin bil’Adama Omoyele Sowore a Abuja, inda suka fita da shi da qarfin tuwo zuwa wani wuri da har yanzu...
Matasan Kauru Sun zargin Dan Majalisar Dokoki Barnabas Danmaigona da Rashin tabuka komai Wata kungiyar matasa, Kauru Youth Ambassadors (KYA) a karamar hukumar Kauru sun nuna matukar damuwa kan yadda Barnabas Danmaigona, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kauru a majalisar dokokin jihar Kaduna, ya gaza samar da ingantaccen wakilci tun bayan zaben sa. A...
Majiyoyi daga cikin jami’an tsaron sun bayyana cewa sojoji da ‘yan sa-kai sun fafata da ‘yan bindigar. Sun kashe ‘yan bindiga da dama, sannan suka ƙwato bindigogi AK-47 guda uku daga hannunsu. ‘Yan bindigar sun gudu, wasu daga cikinsu na da raunuka ko kuma an kashe su, sai dai adadin ba a tabbatar da shi...
Bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin tubabbun ’yan bindiga da jama’ar gari a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, mazauna yankin sun ce yanzu matsalar tsaron ta dauki sabon salo. A watan Oktoban 2024 ne dai aka kulla yarjejeniyar sulhun tsakanin bangarorin biyu. Yarjejeniyar na zuwa ne bayan shafe sama da shekara 10 ana...
Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce bai dace a riƙa bai wa mutanen da suka wawure dukiyar ƙasa manyan muƙaman gwamnati kamar ministoci ba. A cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, Sanusi II, ya bayyana damuwarsa game da yadda ’yan Najeriya ke son dukiya fiye da gaskiya...
Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce bai dace a riƙa bai wa mutanen da suka wawure dukiyar ƙasa manyan muƙaman gwamnati kamar ministoci ba. A cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, Sanusi II, ya bayyana damuwarsa game da yadda ’yan Najeriya ke son dukiya fiye da gaskiya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Amurka, Donald Trump, yana shirin ƙara tsaurara wa Rasha takunkumi idan har ba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba kafin ranar Juma’a, 8 ga watan Agusta. Ko da yake Rasha ita ce ƙasar da aka fi ƙaƙaba wa takunkumi a duniya, har yanzu tana amfani da arziƙin man fetur da iskar gas da ta...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana bukatar samar da wata sabuwar hanyar yin mu’amala da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA, inda ya bayyana cewa, ba a kayyade lokacin shiga wasu shawarwari da Amurka ba, ya kuma tabo batun muhimmancin dangantakar dake tsakanin Iran da kasashen Rasha, Sin...