2025-07-10@02:10:41 GMT
إجمالي نتائج البحث: 277
«Filayen Jiragen Sama»:
Binciken ya nuna cewa, mutum biyu daga cikin wadanda ake zargin ma’aikatan Dangote ne kai tsaye, yayin da sauran ke aiki da kamfanonin da ke da alaka da safarar mai daga matatar Dangote zuwa wuraren ajiya na kamfanin da ke Ibese da Obajana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ta sha bamban da majalisun da ke goyon bayan masu goyon baya masu laifi misalin masu kisan gilla a Gaza Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada a yau Laraba cewa: Matsayin majalisar shawarar Musulunci ta Jamhuriyar Musulunci...
Iran ta ce za a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa da Amurka a ranar Lahadi mai zuwa a Muscat, babban birnin kasar Oman. Kakakin ma’aikatar Esmail Baghai a wata sanarwa da ya fitar ya ce “An shirya zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a ranar Lahadi mai zuwa a birnin...
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a yau Litinin 9 ga wata sun nuna cewa, a watan Mayun bana, ma’aunin farashin kayayyakin masarufi, watau CPI na kasar, ya ragu da kaso 0.1 bisa dari, bisa na makamancin lokacin bara, kuma farashin makamashi ya zama babban dalilin da ya haifar da raguwar. Kana,...

Iran Ta Musanta Zargin Amurka Kan Cewa Kungiyoyi Masu Fada Ha HKI Suna Daukar Umurni Daga Wajenta Ne
Jakadan kasar Iran a MDD Amir Sa’eid Iravani ya musanta zargin kasar Amurka na cewa falasdinawa dauke da makamai a Gaza suna aiki ne tare da umurnin Iran. A kuma dukkan yankunan da HKI take mamaye da su a kasar Falasdinu da ta mamaye. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Iran vani...
Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya sake tabbatar da cewa Iran ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba kan ‘yancinta na tace Uranium, yana mai cewa ci gaban da kasar ta samu a fannin makamashin nukiliya ya samo asali ne sakamakon sadaukarwa da kuma saka hannun jari na kasa. A cikin wani sako da...
Har ila yau, ya bayyana cewa, bangaren tekun kudancin kasar Sin gaba daya yana cikin kwanciyar hankali kuma babu wata matsala game da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa da na sama da dukkan kasashe ke morewa bisa doka. Ya ce, a ko da yaushe, kasar Sin na dagewa kan amfani da tattaunawa da tuntubar juna wajen...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi wanda yake ziyar aiki a kasar Lebanon bayyana cewa kasarsa tana goyon bayan hadin kan mutanen kasar Lebanon. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka bayan ganawarsa da shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon a yau Talata a birnin Beirut babban birnin...
Wasu kuma sun ce akwai rashin jituwa tsakanin Gwamnan da mahaifinsa, Oba Akinruntan. Bayan saukar Akinruntan, an zaɓi Ololade Gbegudu daga Okitipupa a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar. Gbegudu, mai shekara 42, ya riƙe muƙamin shugaban kwamitin tsaro da ci gaban al’umma a majalisar kafin wannan sabon muƙamin. Oluwatoyin James daga Akoko ta Arewa Maso...
Dillalan rago a jihar Kano sun nuna damuwarsu kan rashin zuwan masaya da suke fuskanta duk da ‘yan kwanaki da suka rage ayi bukukuwan Sallah. Ziyarar da aka kai kasuwar dabbobi ta Gandun Albasa ta nuna cewa, da yawa daga cikin masu sayar da kayayyaki sun shafe tsawon yini ba tare da yin cinikin...
Sojojin Yemen sun kai jerin hare-hare har sau 4 kan filin jirgin saman Ben Gurion tare da wasu wurare masu muhimmanci a cikin Isra’ila Sojojin Yemen sun sanar da aiwatar da hare-haren soji masu tsanani guda hudu a kan filin jirgin sama na Lod, wanda aka fi sani da “Ben Gurion” a haramtacciyar kasar Isra’ila,...
Kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya sun bayyana rashin jin dadinsu ga Isra’ila, kan hana su ziyartar yankunan Falasdinawa Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun bayyana rashin jin dadinsu ga gwamnatin Isra’ila, game da rashin amincewa da tawagar kungiyar kasashen ta ziyarci yankin da aka mamaye a Gabar Yamma da kogin Jordan don tattaunawa da shugaban...
Mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da cewa a ranar hawan arfa na bana, za a fassara hudubar da za a yi da harsuna 34 daga cikinsu da akwai Hausa da filatanci. Wasu harsunan Afirka da za a fassara hudubar ta Arfa da su, sun hada yarabanci, Sawahili, Somali da kuma Amharic na kasar Habasha. A...
Dakarun gwagwarmayar kasar Yemen sun bayyana cewa: Za su mayar da jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila abin ba’a Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat, ya tabbatar da cewa: Tsaron sararin samaniyar sojojin kasar Yemen zai iya tunkarar jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da suke kai hare-haren wuce gona da iri...
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Makaman nukiliya ba su da gurbi a cikin akidar Jamhuriyar Musulunci ta Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta taba yin watsi da haƙƙin da doka ta tanada ba ta fannin inganta sinadarin uranium, domin inganta harkar kiwon lafiya, aikin gona da masana’antu,...
Sojojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin saman Ben Gurion da makami mai linzami lamarin da ya tarwatsa cinkoson jama’a a filin jirgin Sojojin Yemen sun sanar da kai farmakin soji kan filin tashi da saukan jiragen saman Ben Gurion tare da yin barazanar ci gaba da toshe hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama da na...
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Harin da “Isra’ila” ta kai wa filin saukar jiragen saman Sanaa, manufarsa ita ce yin matsin lamba akan matsayarmu ta taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta.” Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kara da cewa; Komai girman hare-haren da Isra’ilan za ta kai ba zai...
Gwamna Uba Sani ya amsa da cewa gwamnati ta kashe sama da Naira biliyan 100 cikin watanni shida don magance matsalar ƙarancin ruwa a faɗin jihar, tare da alƙawarin cewa za a maye gurbin dukkan kayan aikin da suka lalace. Ya ƙara da cewa an riga an kashe sama da Naira miliyan 400 wajen gyara...
Majalisar dokokin kasar Iran ta sake zaben Mohammad Baqir Qalibof a matsayin shugaban majalisar dokokin kasar na wata shekara a zaben da aka gudanar a cikin majalisar a jiya Litinin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya bayyana cewa ya sami kuriu 219 daga cikin Jimillan kuri’u 272, wanda ya bashi babban rnjaye a...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Kuma taron zai baiwa jama’a damar yi wa gwamna tambayoyi kai tsaye, kuma su sami bayani kan ayyukan gwamnati.” “Wannan shi ne ci gaba a siyasance, kuma ba sabon abu bane a duniya, amma a jihar Yobe, wannan wani sabon salo ne. Mataki ne na sauke nauyi, gaskiyar da jama’a suka baiwa gwamnati, samun hadin...
Ministan gina hanyoyi da ci gaban kasa na JMI Farzaneh Sadegh ta ziyarci kasar Iraki don bin duddugin aikin layin dogo da ake ginawa tsakanin kasashen biyu. Farzaneh Sadegh ta isa bienin Bagdaza a jiya Asabar inda mataimakin ministan sifiri na kasar Iraki da kuma jakadan kasar Iran a Bagdaza suka yi maraba da ita....
MDD ta bayyana cewa; Da akwai damuwa mai zurfi akan halin da ‘yan Hijirar Sudan suke ciki a gabashin kasar Chadi saboda rashin masu bayar da kudaden taimakon kula da su. Ma’aikatan MDD a fagen ayyukan ceto sun ce ana samun kwararar ‘yan hijira daga Sudan zuwa gabashin kasar ta Chadi, da kuma ‘yan kasar...
An gudanar da Jana’izar Malam Maikudi Umar (Cashman) Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa a garin Zariya, Jihar Kaduna. Marigayin dan shekaru 62, jarumi ne, mai shirya finafinai kuma ma darakta da ke gudanar da aikace aikacen sa a masana’antar Kannywood da Nollywood. Dan uwan mamacin, Abdul Azeez Muazu, Talban Tudun Jukun yace...
Iran ta sanar da lokaci da kuma wurin da za a yi sabon shawarwari tsakanin Iran da Amurka Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa: A gobe Juma’a ne za a gudanar da zagaye na biyar na shawarwari tsakanin Iran da Amurka a birnin Roma. A lokacin da ya isa birnin Shiraz...
Manyan kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa da dama sun tsawaita dakatar da zirga-zirgar jiragensu zuwa yankunan Falasdinawa da Isra’ila ta mamaye, a daidai lokacin da kasar Yemen ta sha alwashin daukar mataki kan kasar. Kamfanin jirgin sama na Air France ya sanar cewa, bayan dakatarwar da aka yi na tsawon watanni, zai ci...
Ministan Harkokin wajen kasar Omman ya bada sanarwan cew za’a gudanar da tattaunawa zagaye na 5 tsakanin Iran da Amurka kan shirin Iran na makamshin nukliya a ranar 23 gawatan Mayun da muke ciki a birnin Roma nakasar Italiay. Tashar talabijin ta Presstv a nnan Tehran ta ce Har yanzun ba’a ji tabakin kasashen biyu...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da fitar da kudi sama da naira miliyan 279 ga Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta Najeriya (NURTW reshen jihar Jigawa karkashin shirinta na tallafawa masu sana’o’i. Kwamishinan Muhalli, Sabunta Makamashi da Sauyin Yanayi na jihar, Dr. Nura Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan...
Wani harin kwanton bauna da rundunar sojin al-Qassam suka kai kan sojojin mamayar Isra’ila a Beit Lahiya ya yi sanadiyar halaka tare da jikkatan sojojin mamaya masu yawa Rundunar Izzuddeen al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta sanar da cewa: Mayakanta sun kai wani kazamin harin kwantan bauna a yankin al-Atatra da ke...
Gwamnatin kasar Masar na shirin yin arangama ta soji da haramtacciyar kasar Isra’ila Kafofin yada labaran Isra’ila, musamman tashar talabijin ta 14, sun watsa wani rahoto cewa: Gwamnatin kasar Masar na kokarin karfafa karfinta na soji a tsibirin Sinai, tana mai gargadin abin da ta bayyana a matsayin “yiwuwar rugujewar yarjejeniyar zaman lafiya” da aka...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, tattaunawar dake tsakanin Iran da Amurka za ta iya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. A yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen dandalin tattaunawa na Tehran, Araghchi ya ce kasashen yankin suna goyon bayan tattaunawar da...

Kungiyar Hizbullah Ta ce Marigayi Shahid Ra’isi Ya Kasance Mai Taimakawa Kasar Lebanon Da Kuma Falasdinawa Ne
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Na’im Kasim a wani jawabinda da ya gabatar don tunawa da cika shekara guda da shahadar shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi da abokan tafiyarsa, ya bayyana cewa shugaban ya kasance mai kaunar falasdinawa ne har cikin zuciyarsa. Sheikh Qasim ya kara da cewa, shugaba Ra’isi ya rike...
Iran ta yi kira da a kawo karshen neman shafe wata al’umma daga kan doron kasa tare da kawo karshen rashin hukunta shugabannin ‘yan sahayoniyya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan hare-hare da laifukan da gwamnatin ‘yan sahayoniyya take ci gaba da yi a cikin ‘yan kwanakin nan...
An gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu a sassa daban-daban na duniya, a yayin zagayowar cika shekaru 77 da ranar ‘’Nakba’’ cewa da masifa. A Faransa da Ingila duk an gudanar da wannan zanga zanga a wasu sassan kasar. A cikin jerin gwanon, an daga allunan da ke dauke da sakonni irin...
A kokarin da yake yi na jigilar maniyyatan aikin hajjin bana, Kamfanin jiragen sama na Max Air yace zai kwashe daukacin Alhazan Jihar Jigawa cikin kwanaki biyu. Mataimakin mai kula da ofishin kamfanin dake jihar kano, Mr Barnabas Anderson ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a shelkwatar...
Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriryar musulunci ta Iran ta sanar da cewa, saboda yadda Amurka take bai wa ‘yan sahayoniya cikakken goyon baya ne, ya sa su cigaba da aikata laifuka na kisan kiyashi akan mutanen Gaza. Bayanin da ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta fitar, ya zo ne saboda tunawa da zagayowar lokacin da aka...
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Amurka tana da hannu dumu-dumu a muggan ayyukan da gwamnatin ‘yan shayoniyya suka aikata nakisan kare dangi a Gaza Jakada kuma wakilin dindindin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya yi nuni da ire-iren laifuffukan da gwamnatin ‘yan sahayoniyya suke...
A jiya Laraba ne dai da aka rattaba hannu akan wata yarjejeniya a tsakanin sarkin Katar Tamim Bin Hamad ali-Thani da kuma shugaban kasar Amurka Donad Trump wanda ya kai Ziyara kasar. Shugaban kasar Amurka wanda ya bayar da labarin kulla wannan yarjejeniya ya kusa sanar da cewa, kasar ta Katar za ta sayi jiragen...
Ɗan wasan Manchester United, Leny Yoro da Matthijs de Ligt da kuma Ayden Heaven ba suyi atisaye ba, bayan da ƙungiyar ke shirin buga wasan karshe a Europa League da Tottenham a makon gobe. Ranar Juma’a United za ta je Stamford Bridge domin karawa da Chelsea a Premier, amma dai hankalinta yana wasan da za...
Gwamnatin jihar Kwara ta shirya wani gagarumin horo ga likitocin kiwon lafiya a fadin cibiyoyin kiwon lafiya na jihar kan yadda za a shawo kan cutar zazzabin cizon sauro. Da yake sanar da bude horon a Ilorin, daraktan kula da lafiyar jama’a na jihar, Dokta Oluwatosin Fakayode, ya jadadda bukatar gaggawar gano cutar da...
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata taba yin watsi da haƙƙinta na makamashin nukuliya na zaman lafiya ba a kowane yanayi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Iran da gaske take yi wajen gudanar da tattaunawa domin neman cimma matsaya da zata gamsar da kowane bangare, amma neman yin watsi...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar Iran da Amurka ba zata shafi matakin jan layi da Iran ta gindaya ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa da gaske kasarsa tana tattaunawa da Amurka, kuma tana neman cimma matsaya, amma batun neman yin watsi da cibiyoyin nukiliyarta wani zabi ne da ba za...
Kasar Siriya ta rikide daga Jihadi da zaluncin gwamnatin mamayar Isra’ila zuwa ga kulla kyakkyawar alaka da gwamnatin ‘yan mamaya Gaskiya ta fara bayyana daya bayan daya, sannan makirci da makarkashiyar kungiyoyin masu dauke da makamai bisa da’awar gudanar da jihadi a Siriya suka fara bayyana ga al’umma, masu da’awar jihadi sun kama hanyar fitar...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin JMI da Amurka zagaye na hudu, yana tafiya kamar yadda ya dace. Kuma kasashen buyu sun kara fahintar ra’yin juna. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran da nakalto Aragchi yana fadar haka a wani hira da da ya...
Kungiyar Magajunan Gari Na Kasashen Asiya Ta Zabi Birnin Esfahan na tsakiyar kasar Iran a matsayin cibiyar yawan bude ido na wannan shekara ta 2025. Manufar zaben birnin Esfahan a wannan karon shi ne gabatar da shi ga kasashen Asiya saboda sa mutanen Nahiyar Asiya su su ziyarci kasar da kuma birnin don sanin dumbin...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bukaci shugaban kasar Ukraine ya amince da tayin shugaban Putin na Rasah na sun hadu a birnin Istambul na kasar Turkiya don tattauna yiyuwar tsagaita budewa juna wuta. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto shugaban Trump yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma bayyana cewa...
Iran ta bayyana cewa tattauanwa ta hudu data wakana tsakaninta da Amurka tana da wahala amma kuma tana da amfani. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya ce zagaye na hudu na tattaunawar da Amurka abu ne mai wahala amma mai amfani ce. M. Baghaei ya bayyana hakan ne a wani sako da ya...
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba da shawarar yin tattaunawa “kai tsaye” ba tare da sharadi ba” tsakanin kasarsa da Ukraine a ranar 15 ga Mayu a Istanbul. A martanin da ya mayar, shugaban na Ukraine ya ce a shirye ya ke don tattaunawa kai tsaye, amma ya zama dole a tsagaita bude wuta...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Dole ne duniya ta dauki matakin kalubalantar laifukan ‘yan sahayoniyya da magoya bayansu kan zaluncin Gaza Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, yayin da yake karbar bakwancin dimbin ma’aikata a yau Asabar, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan “Makon ayyuyka da Ma’aikata”...