Jagora: Hadin Kan Al’umma, Jami’ai Da Sojojin Kasa Da Suke Dauke Da Makamai Jan Layi Ne
Published: 25th, August 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Hadin kan al’umma, jami’ai, da sojojin da ke dauke da makamai, jan layi ne
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Bayan da makiya suka kasa murkushe al’ummar Iran ta hanyar yaki, a halin yanzu suna neman cimma manufarsu ta hanyar haifar da sabani da rarrabuwar kawuna.
Jagoran ya jaddada bukatar tallafa wa masu yi wa kasa hidima, musamman ma shugaban kasar wanda ya bayyana a matsayin mai jajircewa da kuzari, yana mai jaddada cewa hadin kan al’umma, gwamnati, da sojojin kasar ya zama katanga da ba za a taba mantawa da shi ba daga makircin makiya.
Imam Khamenei ya gabatar da wata muhimmiyar tambaya: Mene ne dalilin kiyayyar da Amurka ta yi wa Iran tsawon shekaru 45? Ya yi bayanin cewa: Duk gwamnatocin da suka shude a Amurka, duk da mabanbantan ra’ayoyinsu, sun dauki matakin iri daya na barazana, da kuma takunkumi kan Iran.
Ya kara da cewa a baya, Amurka ta boye dalilinta karkashin lakabi irin su “ta’addanci,” “yancin dan Adam,” “matsalolin mata,” da “dimokradiyya,” ko kuma ta yi magana kan “canza halayen Iran.”
Ya jaddada cewa shugaban Amurka na yanzu ya fito fili ya bayyana ainihin manufarsa, yana mai cewa, “Suna son Iran ta bi umarninmu.”
Iran
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Bukatar Gudanar Da Hidima Ga Al’umma Daga Kowane Dan Kasa August 25, 2025 Kwamandan Sojojin Iran Ya Jaddada Aniyar Iran Na Wurga Makiya Cikin Nadama August 25, 2025 Kafofin Watsa Labaran Isra’ila Sun Ce: Ba Za A Iya Hana Sojojin Yemen Kai Hare-Hare Kan Isra’ila Ba August 25, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Kai Hari Kan Kungiyar Red Crecent A Kasar Sudan August 25, 2025 Hamas: Da gangan Netanyahu ya dakatar da tattaunawar zaman lafiya August 25, 2025 Iran: Pezeshkian ya yaba da kalaman Jagora Kan hadin kan al’umma August 25, 2025 Isra’ila ta kai hari kan ababen more rayuwa na fararen hula a Yemen August 25, 2025 Araqchi ya isa Saudiyya don halartar taron gaggawa na OIC a kan Gaza August 25, 2025 Jagora: Iran Ba Za Ta Taba Zama Mai Biyayya Ga Amurka Ba August 24, 2025 An Gudanar Da Tarukan Makoki Shahadar Imam Ridha (AS) A Hubbarensa Da Ke Mashhad August 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: jaddada cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam ” Nahid 2″ Da Zai Samar Wa Yankunan Karkara Hanyar Sadarwa Ta “Internet”
Ministan sadarwa na Iran Sitar Hashimi ya bayyana cewa, an sami nasara a gwajin da aka yi na sabon tauraron dan’adam, mai suna “Nahid 2” wnada aikinsa shi ne samar da hanyoyin sanarwa na internet masu nagarta.
Ministan sadarwar ya kuma ce dukkanin bangarorin tauraron dan’adam din sun yi aiki yadda ake so a yayin gwajin da hakan yake a matsayin wani ci gaba a fagen sadarwa a Iran.
Har ila yau ministan Sadarwar Sitar Hashimi ya kuma ce; A tsakanin kauyuka 10,000 da ba su da hanyoyin sadarwa, yanzu an rage su da 2000, kuma ana ci gaba da aiki tukuru domin isa ga kauyunan da suke nesa,masu wahalar zuwa.
Ministan sadarwar na Iran ya kuma kara da cewa; ma’aikatarsa tana son amfani da tauraron dan’adam domin fadada hanyoyin sadarwa na internet wanda yake da inganci sosai, kuma zai samarwa da dukkanin yankunan karkara hanyoyin sadarwa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Za A Kada Kuri’ar Raba Gardama Akan Sabon Tsarin Mulki A Kasar Guinea September 17, 2025 Larijani: Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Aiki Tare A Fagagen Kasuwanci Da Tsaro September 17, 2025 Hukumar Tarayyar Turai Ta Gabatar Da Shawarar Jingine Aiki Da Yarjejeniyar Kasuwanci Da HKI September 17, 2025 Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa Kisan Kiyashi A Gaza September 17, 2025 Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila September 17, 2025 Hamas Ta Karyata Gwamnatin Mamayar Isra’ila Kan Shirga Karya Don Kare Muggan Manufofinta September 17, 2025 Iran Ta Bayyana Abubuwan Da Bata Amince Da Su Ba A Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar OIC A Birnin Doha September 17, 2025 Chadi: Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa September 17, 2025 Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila September 17, 2025 Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza September 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci