Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah
Published: 29th, August 2025 GMT
Annabi (SAW), shi ne farkon wanda kasa za ta tsage wa ya tashi a ranar Alkiyama, shi ne farkon wanda zai shiga Aljannah, shi ne wanda Allah ya kebanta da tsani da wasilah, shi kuma ya kebanci muminai masoyansa da ita.
Allah ya girmama Manzon Allah (SAW) da abin da bai girmama wani dan Adam da shi ba.
Allah ya yi masa budi (Fatahi) na Zahiri – Sulhu a Hudaibiyya, Fat’hu Khaibara, da Fat’hu Makkah; da Badini – Fatahi a Sifa, Fatahi a Suna da Fatahi a Zati.
Allah ya gafarta wa Manzon Allah (SAW), ya tafiyar da dauda ga ‘ya’yan gidansa, ya yi Isra’i da shi, ya rantse da zamaninsa da garin da aka haife shi, ya ba shi alkairi mai yawa (Alkausar), sannan kuma mu’ujizarsa ta wanzu har tashin alkiyama. Zamaninsa yana kara tsawo mu’ujizarsa tana kara fitowa amma sauran Annabawa, akasin haka ne.
Allah ya aiko Manzon Allah (SAW) zuwa ga halitta baki daya, Annabin duka nahiyoyin duniya ne.
Ya zo a cikin maganar waliyyai na abin da suka fada dangane da bambancin Annabi (SAW) a matsayin “Habibullahi” da Annabi Ibrahim AS a matsayin “Kalilullahi”: mukamin Annabi Ibrahim shi ne kwadayin gafara, saboda jirwaye mai kamar wanka da ya yi kan wata waki’a biyu da ta faru da shi; 1. Ya sare gumaka, ya ce a tambayi babbansu 2. Ya kira matarsa, Saratu da cewa ‘yar uwarsa ce.
Amma a bangaren Annabi (SAW), Ubangiji bai fadi laifin ba sai dai hukuncin kawai, da cewa, “mu muka yi maka budi, budi mabayyani, don mu yafe maka laifinka da wanda ka yi, da wanda za ka yi gaba…”, Abun nufi a nan, ittifakan Allah ya gafarta wa Annabi Ibrahim (AS) amma gafarar da aka yi wa Annabi (SAW), sai da aka hado ta da Gara – budi bayyananne, da gafarar abin da ya gabata da wanda zai zo a nan gaba, cika ni’imarsa a kan Habibinsa, shiriya kan tafarki madaidaici, da taimakon nasara mabuwayiya. Babu yadda za a yi wanda ke neman gafara ya yi daidai da wanda aka hado shi da irin wannan Gara.
Annabi Ibrahim ya roki Allah kar ya tozartar da shi ranar Alkiyama, amma shi Annabi (SAW), Ubangiji bai bayyana inda ya roka ba duk da cewa yana roko, sai ga shi Ubangiji ya sanya wa ranar Alkiyama suna da “ranar da Allah ba zai tozartar da Annabi (SAW) da wadanda suka yi imani da shi ba.” Alhamdulillah… duk wanda ya yi imani da Annabi (SAW), ya tsira. Duk wannan ukuba da ake ruwaitowa ta ranar Alkiyama, ba wanda yace karya ne amma wanda ya amsa Darikar Shehu Tijjani (Abul Abbas), sai dai ya farka a Aljannah ya ji duk an gama komai, wata kila aka ce Shehu ina hujjar fadin wannan, sai ya ce, Hadisi ya zo, ranar Alkiyama Umar zai amsa littafinsa na Shari’a da hannun dama, sai aka ce, ina Abubakar fa, aka ce yana cikin Aljannah lokacin.
Annabi Ibrahim (AS) ya roki Allah ya sa a yi ta yabonsa, ana fadin aikin alkairinsa har tashin Alkiyama, kuma Allah ya amsa masa wannan. Duk addinatai suna iya fadan batanci a kan wasu Annabawa amma Annabi Ibrahim duk addinatai suna yabonsa, kowa cewa yake nashi ne, sabida wannan addu’a (waj alliy lisana sidkin fil akhirin). Amma Annabi (SAW), ba a fada inda ya roka ba, sai ga shi Ubangiji yana ce masa (wa rafa’ana laka zikraka) mu muka daukaka ambatonka. Annabi (SAW) ya ce, ya Jibrilu mece ce fassarar haka? Ya ce, ban sani ba amma bari in tambaya, Jibrilu ya dawo da amsar cewa, Ubangijinka na nufin, duk in an ambace shi, sai an ambace ka. To yanzu ne aka yi zikiri. Ina masu da’awar Akida? Masu shirin sai sun kawar da ambaton Annabi (SAW), to Sahabbai dai sun gane! A yayin da ake yakin zubar da jini, ana sare wuya amma Annabi suke kira (ya Muhammada) kuma ba su yi shirka ba. A ko ina aka ambaci Ubangiji sai an ambaci Annabinsa (SAW). A wasu wurare ma da yawa a Alkur’ani Allah ya hade sunansa da Annabinsa (SAW), “wallahu wa rasuluhu a hakku an yurduhu – da Allah da Annabinsa, shi yafi cancanta a yarda da shi”.
Annabi Ibrahim ya yi addu’ar cewa, Ubangiji ya tsare shi da zuriyarsa daga bautar gunki, wanda ake bautama wa, amma ‘yar tsana, ko zanen sarakuna ko na mazan jiya da ake zanawa don jinjina ba don bauta ba, wannan ba sunan shi gunki ba. Annabi Ibrahim yana nufin zuriyarsa ta bar bautar Ubangiji ta koma ta Gumaka, Allah ya tsare su. Kuma Allah ya yi masa haka.
Da wannan, wasu Malamai suka kafa hujjar cewa, iyayen Annabi (SAW), suna kan addinin Annabi Ibrahim (Hanafi).
Annabi Ibrahim ya roki Ubangiji ya tsare shi da zuriyarsa daga bautar gunki amma Annabi (SAW), Allah ne ya tafiyar da kazanta daga zuriyarsa da ke cikin bargo gaba daya ba bautar gunki kadai bai.
Mece ce kazanta (Rijsu)? Giya da caca da bautar gumaka, da kuma rantsuwa da gumaka. Sannan kuma, ya tsarkake su tsarkakewa. Don haka, yadda dan Adam ba zai iya tashi sama ba, haka zuriyar Annabi (SAW) ba za ta iya sabo ba. Da wannan za mu fada cewa, Annabi Ibrahim ya roki abu daya, amma Annabi (SAW) sai da aka bashi hudu.
Fadakarwa game da cikar Manzon Allah (SAW) shekara 1,500 da haihuwa
Muna kira ga daukacin al’ummar Musulmi kowa ya yi tanadi na musamman kar ya bari a bar shi a baya, Allah ya kawo mu watan Rabi’ul Auwal, maulidin da za a yi na ranar 12 ga watan shi ne zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa.
Yadda abin yake shi ne, idan ka dauki shekarun haihuwar Manzon Allah (SAW) 40 kafin a fara aiko masa da manzanci ka hada da shekarun da ya yi a Makkah guda 13 bayan fara saukar da manzanci, zai ba ka shekaru 53. To, idan ka hada shekaru 53 da shekarar Hijira 1447 ta bana, lissafin zai ba ka cewa Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1500 da haihuwa.
Hatta wadanda ba su yin maulidi ya kamata a bana su yi kokari su yi wani abu ko yaya kar a bar su a baya, saboda yanzu da Allah ya ja da rayuwarmu muka ga watan Rabi’ul Auwal na bana, lokacin da Manzon Allah ya cika shekara 1,500 da haihuwa, to zai yi wahala mu ga lokacin da zai cika shekara 2,000 kuma. Domin da wahala a samu wani daga cikin mutanen da ke rayuwa a doron kasa yanzu da zai kara wasu shekaru 500 a raye.
A lokacin da Annabi Isah (AS) ya cika shekaru 2,000 da haihuwa an ga yadda duk duniya ta dauki murna, to mu ma ya kamata Musulmi mu girgiza duniya da bukukuwa na murnar mu ma Annabinmu (SAW) ya cika shekaru 1,500 a duniya. Wannan babban alheri ne da tarihi a rayuwarmu. Allah ya hore mana dukkan abun da za mu yi hidima da shi Albarkar Annabi (SAW).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp ShareTweetSendShare Previous Post Tinubu Ya Umarci A Yi Bincike Kan Hatsarin Jirgin Kasa Daga Abuja Zuwa Kaduna Relatedকীওয়ার্ড: Zai Cika Shekara 1 500 Da Haihuwa A Shekarar Dausayin Musulunci Annabi Ibrahim ya ya cika shekaru ranar Alkiyama Ubangiji ya Da Shekarar
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Gano Wani Dutse Mai Sassaka Na Daular Qin A Kan Tsaunin Qinghai-Tibet
Hukumar kula da al’adun gargajiya ta kasar Sin ta sanar a yau cewa, an gano wani dutsen da aka yi sassaka kan sa a kan tsaunin Qinghai-Tibet, wanda ya kasance irinsa daya tilo na daular Qin da har yanzu ke mazauninsa na asalin, kuma a wuri mafi tsawo.
Dutsen wanda ke arewacin bakin tabkin Gyaring na gundumar Maduo, dake arewa maso yammacin lardin Qinghai, na wuri mai tsawon mita 4,300.
Gano dutsen na tattare da wata muhimmiyar daraja ga tarihi da fasaha da kimiyya. Sarki Qinshihuang na daular Qin ne ya fara hada kan kasar Sin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp