Shugabar Ma’aikatan Abuja ta rasu
Published: 1st, September 2025 GMT
Allah Ya yi wa Shugabar Ma’aikata ta Babban Birnin Tarayya, Abuja, Misis Grace Adayilo, rasuwa a safiyar Litinin ɗin nan.
Shaidu sun tabbatar wa wakilinmu cewa ta rasu ne ’yan sa’o’i kaɗan da suka gabata. Kodayake kawo yanzu ba a sanar da rasuwar a hukumance ba.
Misis Grace Adayilo ita ce mace ta farko kuma ’yar asalin yankin Babban Birnin Tarayya ta farko da ta riƙe wannan muƙami.
ta kasance tsohuwar Sakatariyar Ilimi ta Ƙaramar Hukumar Birnin Abuja (AMAC), kafin Minista Nyesom Wike, ya naɗa ta Shugabar Ma’aikata.
Rushe Kasuwar Alaba Rago: Ya kamata a biya ’yan Arewa diyya Gargaɗi kan zagin Sahabban Annabi Muhammad (SAW)Ita ce ta wakilci Wike a babban taron Majalisar Taro ta Ƙungiyar G-7 da aka gudanar a ranar Larabar da ta gabata a Abuja.
Ko a ranar Lahadi ta samu halartar ibada a coci, inda washegari aka samu labarin safiyar Litini.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Grace Adayilo shugabar ma aikata ta rasu
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
Rundunar Sojojin Nijeriya (AFN) za ta gudanar da bikin kammala aiki na tsohon Shugaban Tsaron Ƙasa (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya) a ranar Jumma’a, 31 ga Oktoba, 2025, domin girmama ayyukan da ya gudanar a lokacin hidimarsa.
A cewar sanarwar da shalƙwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta fitar a ranar Alhamis, an shirya bikin Pulling Out Parade ɗin ne da ƙarfe 09:00 na safe, inda manyan hafsoshin Soja, da jami’an gwamnati da ƴan uwa za su halarta. Wannan biki na nuni da kammala aikin Soja a matakin ƙoli, kuma yana ɗaya daga cikin manyan al’adun da ake yi wa manyan jami’an da suka yi aiki da ƙwarewa da sadaukarwa.
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP Kasashen Afirka Biyar Da Suka Fi Karfin SojiJanar Musa ya yi aikin Soja na tsawon shekaru masu yawa, kuma ya yi shugabanci a matsayin Shugaban Tsaron Ƙasa daga Yuni 2023 zuwa Oktoba 2025. A wannan lokaci, ya jagoranci manyan hare-haren yaƙi da ta’addanci tare da ƙarfafa hulɗar haɗin gwuiwa tsakanin sassan Sojojin Nijeriya.
A ranar 24 ga Oktoba, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sabon tsarin jagorancin rundunar Soja, inda ya naɗa Manjo Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon Shugaban Tsaro, wanda hakan ya kawo ƙarshen wa’adin Janar Musa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA