Yarjejeniyarmu da IAEA zatayi tasiri matukar ba’a dauki wani matakin takala kan Iran ba_ Araghchi
Published: 11th, September 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, sabuwar yarjejeniyar da Iran ta kulla da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, kan batun dawo da hadin gwiwa, za ta ci gaba da wanzuwa matukar dai ba a dauki wani mataki kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba, ciki har da yunkurin mayar da takunkumin da MDD ta kakaba mata.
A ranar 29 ga watan Agusta ne, kasashen Faransa, Jamus, da Biritaniya (E3) suka yunkura ganin an sake dawo da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya da manyan takunkumin banki da na ruwa a kan Iran.
Iran ta yi Allah-wadai da wannan matakin, inda ta ce kasashen uku sun bi sahun Amurka, wadda ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a shekarar 2018.
Mista Araghchi ya ce sabuwar yarjejeniya da hukumar ta IAEA, ta yi la’akari da sabbin sharuddan da aka dauka bayan harin da Amurka ta kai kan wuraren zaman lafiya na Iran.
“A matsayinmu na mamba a yarjejeniyar hana yaduwar makamman nukiliya ta duniya (NPT) kuma bisa ga yarjejeniyoyin da aka kulla a baya, muna ba da hadin kai da Hukumar, sannan kuma shirin namu ya kasance cikin lumana kuma a karkashin kulawar Hukumar.” »
Duk da haka, “bayan harin (Amurka), yanayi ya canza, kuma yayin tattaunawa da Hukumar, mun jaddada cewa ba za a iya ci gaba da yin hadin gwiwa kamar da ba, kuma dole ne a bayyana wani sabon tsari na wannan.”
Ministan na Iran ya bayyana cewa, babban jigon yarjejeniyar shi ne, ta amince da sabbin sharuddan da iran ta gindaya a hukumance, kuma dole ne hadin gwiwar Iran da hukumar ta IAEA ya kasance cikin wani sabon tsari.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka “Kasashen Larabawa ma basu tsira ba daga hare-haren Isra’ila” (Naim Qassem) September 11, 2025 Faransa : Mutane 250,000 suka shiga zangar zangar ‘’a Toshe komai’’ inji CGT September 11, 2025 MDD ta yi maraba da yarjejeniyar Iran da IAEA dangane da komawa bincike September 11, 2025 Sauyin Yanayi : Shugabannin Afirka sun bukaci a yi adalci September 11, 2025 Sheikh Qasim: Hare-Haren HKI Kan Qatar Sashe Ne NA Shirinta Na “Isra’ila Babba” September 10, 2025 Majiyar Gwamnatin Yamen Ta Ce HKI Ta Kai Wasu Sabbin Hare-Hare Kan Kasar September 10, 2025 Aragchi: Yarjeniya Da IAEA Ya Nuna Hakurin Iran Bayan Hare-Hare Kan Cibiyoyin Nukliyarta September 10, 2025 Iran Ta Bukaci Kasashen Musulmi Su Dauki Mataki Guda kan HKI bayan Harin Qatar September 10, 2025 Sojojin HKI Sun Ragargaza Hasumiyyar Tayyib II A Kokarin Korar Falasdinawa Daga Birnin Gaza September 10, 2025 Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan Al-Mujtaba (a) 138 September 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadi a matsayin martani ga sanarwar Washington na ci gaba da gwajin makaman nukiliya, yana mai kiran hakan a matsayin wani mataki na koma-baya da Rashin yin da’a ga dokokin kasa da kasa.
Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya soki Washington saboda sauya wa Ma’aikatar Tsaron kasar suna zuwa Ma’aikatar Yaki, kuma ya yi Allah Wadai da Shirin Amurka na yin gwajin makaman nukiliya, tare da bayyana hakan a matsayin yunkurin tayar da zaune tsaye da jefa duniya a cikin bala’i.
Wanda yake aikata irin wannan halayya ne ke ci gaba da yin barazanar sake kai hari kan cibiyoyin nukiliya na Iran bisa hujjar hana Iran mallakar makaman nukiliya da sunan kare kansu daga Iran domin kada ta mallaki makaman kare dangi.” in ji ministan harkokin wajen Iran.
Ya yi Allah wadai da Amurka saboda sukar da ta dade tana yi wa shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran yayin da ita kuma take ci gaba da gwajin makamanta na nukiliya, wanda hakan ya saba wa dokokin duniya.
Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Laraba ya bayyana cewa makaman nukiliya na Washington su ne mafi girma a duniya, kuma ya danganta wannan matsayin da gyare-gyare da aka yi a lokacin gwamnatinsa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci