2025-10-14@19:32:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8062

«Ruwan zafi»:

    A kowane wata, hauhawar farashi ta kan kai kashi 0.74, yayin da a watan Agusta, hauhawar farashin abinci ya kasance kashi 1.65. A shekara-shekara, hauhawar farashi yana raguwa da kashi 12.03 idan aka kwatanta da kashi 32.15 da aka samu a watan Agusta 2024. Hukumar ƙididdiga ta bayyana cewa duk da hauhawar farashin na nan,...
    ’Yan bindiga sun kai hari shingen bincike na ’yan sanda a Jihar Kogi, inda suka kashe jami’ai da wani mutum. Harin farko ya faru da misalin ƙarfe 10:30 na safe a ƙauyen Abugi da ke Ƙaramar Hukumar Lokoja. Mata 400 sun amfana da kayan haihuwa a Gombe Bayan biyan N50m an sako ma’aurata da ’yarsu...
    Ya gargadi cewa, tarihi ba zai gafarta wa shugabannin Arewa ba idan suka kasa daukar matakin gaggawa wajen dakile kashe-kashe, garkuwa da mutane da rikice-rikicen da ke addabar yankin. Ya ce shiru da fifita wasu akan wasu daga cikin shugabanni suna kara ta’azzara matsalar tsaro a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina, Filato da Benuwe.   Ya...
    Wannan yana faruwa sosai gaskiya, kuma ƙarshe ba a wayewa da lafiya gaskiya. Masu yi gaskiya tun wuri su daina wallahi, dan aure ya sha mutuwa ta sanadin haka ƙarshe azo ana nadama mara amfani. Sosai ana samun gagarumar matsala tsakanin ma’aurata zargi ya shiga tsakani, daga nan ma dai wani aure ka ji ya...
    Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin New York na Ƙasar Amurka, domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80. Taron zai gudana daga ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, zuwa ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025. Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu Jami’ar European-American ta musanta bai wa...
    A daren ranar 19 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump sun tattauna ta wayar tarho, inda shugaba Xi ya jaddada cewa, alakar Sin da Amurka na da matukar muhimmanci, Sin da Amurka na iya cimma nasarar bai daya da wadata tare, ta yadda za su amfani...
    Ƙaramar Hukumar Gombe, ta raba wa mata masu juna guda 400 kayan haihuwa kyauta, domin kare lafiyarsu da rage mace-mace a yankin. An gudanar da rabon ne a Cibiyar Haihuwa ta Gombe a ranar Alhamis, inda shugaban Ƙaramar Hukumar, Barista Sani Ahmad Haruna, ya jagoranci rabon. Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 4, 16 sun...
    Aƙalla mutum ne sun rasu, yayin da wasu 16 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a Ƙaramar Hukumar Karasuwa, a Jihar Yobe. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkareem ne, ya tabbatar da faruwar hatsarin ya faru a ranar Asabar da misalin ƙarfe 2:50 na rana a ƙauyen Zangon Kanwa....
    Abdulahi, wanda ke jigilar kaya daga Agbara a Jihar Ogun zuwa Ibadan, ya ce yana kashe har Naira 25,000 a kowace tafiya da yake yi, inda mafi yawan kuɗin ke shiga hannun ƴ an Agbero a Legas, waɗanda ke gudanar da ayyukansu sa’o’i 24 a rana, kwana 7 a mako. Ya ce daga Berger, gefen...
    Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bai wa ƙungiyar maharba ta ƙasa (PROHAN) reshen Gombe, kyautar motoci Hilux guda biyu da kuma babura guda biyar domin taimaka musu wajen yaƙi da ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane. An miƙa wa shugaban ƙungiyar, Rabiu Baushe (Baushen Gombe) kyautar, wanda yana cikin shirin gwamnatin na...
    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta SERAP tare da Amnesty International sun nemi Shugaba Bola Tinubu ya janye ƙarar da aka shigar a kotu kan ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore, da kuma kamfanonin sada zumunta X da Facebook. Ƙungiyoyin sun bayyana damuwa cewa hukumomin tsaro na ƙara amfani da kotu wajen tsoratar da ƴan Nijeriya da...
    Sabo da irin mawuyacin halin da ake ciki ta fannin tsarin jagorancin duniya musamman a daidai wannan lokaci, ya sa shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar inganta tsarin jagorancin duniya a kwanakin baya, shawarar da ta yi nuni da cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka a kan kin yarda da daukar...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama mutum biyar da ake zargi da satar fakiti 7,871 na abincin yara, wanda aka fi sani da Tamuwa, wanda aka tanada don yara masu fama da cutar yunwa. Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 19 ga Satumba,...
    A yayin da ake gudanar da shagulgulan ranar zaman lafiya ta Duniya ta Bana, Kungiyar rajin tabbatar da zaman lafiya da hadin Kai da kuma cigaban Arewacin Nigeria ta yi Kira ga Gwamnati a dukkan matakai da kuma Hukumomin tsaro su karfafa amfani da bayanan tsaro na sirri wajen kare rayukan al’ummar Kasa. Shugaban Kungiyar...
    Wanda zan iya tunawa za su kai goma haka. Ko akwai wani fim wanda bayan fitar sa ka samu ƙalubale daga dangi ko wajen masu kallo? Gaskiya a fim dai har yanzu ban samu wani ƙalubale ba, saboda duk abin da nake fitowa a rol na malunta ne. Kawai dai akwai wata waƙa da na...
    Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin New York na Ƙasar Amurka, domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80. Taron zai gudana daga ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, zuwa ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025. Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu Jami’ar European-American ta musanta bai wa...
    Duk tawagar da ta ƙare a mataki na ɗaya daga kowane rukuni guda tara na nahiyar Afirka, ita ce za ta samu gurbi kai-tsaye. Daga baya sai a zaɓo huɗu mafiya ƙoƙari da suka ƙare a mataki na 2, inda za a fitar da ɗaya daga cikinsu sannan ta kara da takwararta ta wata nahiyar....
    “A yayin binciken motar, an samu waɗannan abubuwa daga hannun wanda ake zargin: bindiga ta gida guda ɗaya, harsashi guda huɗu, harsashi biyu da aka harba a baya, katin shaida na ƴ an sanda na bogi, da kuma ƙarin lambar rijistar mota ta (Kano FGE 68).” “Wanda ake zargin yana tsare a hannun jami’an tsaro...
    Ƙasar Birtaniya a wannan Lahadin za ta amince a hukumance da kafa ƙasar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta. Birtaniya wadda ta daɗe tana goyon bayan Isra’ila za ta juya mata baya, sakamakon hare-haren da Isra’ilar take kai wa Zirin Gaza, wanda ya samo asali bayan da ƙungiyar Hamas ta kai wani mummunan...
    Ministan harkokin wajen Iran ya kore abinda wasu kafafen watsa labaru su ka watsa na zantawa a tsakaninsa da manzon Amurka a gabas ta tsakiya Steven Witkoff. Ministan harkokin wajen na Iran, Abbas Arakci ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Tasnim” na Iran cewa; Babu gaskiya a cikin labarun da wasu kafafen watsa labaru su...
      Al’amari mai rikitarwa Hakikanin gaskiya ya fi an rikitarwa. Bisa al’amari, ana kiyasta cewa mutane kimanin 15,000 zuwa 20,000 ne suka mutu a sakamakon kashe-kashen da suka shafi ƴ an bindiga da ta’addanci a Arewa maso Yamma kaai cikin shekaru 10 da suka wuce. Wannan adadi yana daidai da yawan rayukan da aka rasa...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, an bayar da ƙarin kayayyakin da za a raba a matsayin tallafin ne daga Hukumar Kula da Ilimi ta Duniya (UBEC) da UNICEF.   A jawabinsa a wajen taron, Gwamna Lawal ya sake nanata cewa gwamnatinsa ta zo ne da aikin ceto da sake gina jihar.   Ya ce: “Tun...
    A ɓangare ɗaya kuma Turkiyya na ƙara nuna damuwa bayan harin da Isra’ila ta kai a birnin Doha. Mai magana da yawun ma’aikatar tsaro ta Turkiyya, Rear Admiral Zeki Akturk ya yi gargaɗin cewa “Isra’ila za ta iya faɗaɗa hare-harenta baya ga Ƙatar. Za ta iya ingiza yankin baki ɗaya cikin bala’i.” Mece ce shawarar...
    “Sanarwar jan hankaki – Taron bogi ‘convocation’ a Nijeriya – Jami’ar ba ta ba Dauda Kahutu Rarara digirin girmamawa ba”.   A yau (Lahadi) ne aka sanar da Jami’ar EAU labarin wani biki da kafafen yada labarai na Nijeriya suka rahoto ƙaryar cewa, Jami’ar ta gudanar da wani taro a ranar Asabar a Hotel din...
    Jami’ar European American University ta musanta bai wa fitaccen mawaƙin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara, digirin girmamawa na dokta. A jiya Asabar ce dai wani bidiyo da ya karaɗe dandalan sada zumunta ya nuna yadda ake karrama Rarara da digirin girmamawa a wani bikin yaye ɗalibai da aka gudanar a otel ɗin NICON Luxury da...
    Ya ƙara da cewa, “Ina fatan hakan ba gaskiya ba ne, domin kuwa idan wannan mutum ya zama shugaban INEC, ko shakka babu; wannan gwamnati kai tsaye na gayyato yaƙin Basasa ne.” Da yake mayar da martani a kan batutuwan da jam’iyyun siyasa suka fara yi na yaƙin neman zaɓe, ya zargi hukumar zaɓe ta...
    A ranar Alhamis 18 ga watan nan, aka kaddamar da fara nuna fim din nan mai taken “Evil Unbound” a dukkanin sassan duniya, fim din da ya ba da labarin yadda a yayin yakin kin mamayar dakarun Japan, wata rundunar dakarun sojin kasar Japan ta aiwatar da wani shirin sirri, na gwaje-gwajen kimiyya ta makamai...
    Al’ummar Jihar Sakkwato na cike da fargaba da alhini bayan da wasu mazauna kauyuka da dama suka rasu a hatsarin kwale-kwale a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne lokacin da jama’a ke tserewa daga wani sabon harin da ‘yan ta’addan Lakurawa suka kai, inda kwale-kwalen da ke dauke da mutane...
    Rundunar Sojin Saman Najeriya, ta kashe ’yan ta’addan Boko Haram 32, a wani farmaki da ta kai garin Banki da ke Ƙaramar Hukumar Bama, a Jihar Borno. Rahoton ya bayyana cewa farmakin ya auku ne a ranar 18 ga watan Satumba da misalin ƙarfe 10:15 na safe. Bayan biyan N50m an sako ma’aurata da ’yarsu...
      Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, lamarin wanda ya faru ne a lokacin da ake gudanar da aikin a ƙarshen mako a masana’antar, ya yi sanadin mutuwar ma’aikata biyu ciki har da wani jami’in soji da ke aiki tare da jikkata wasu huɗu.   “Na ji wani babban ƙara har sai...
    A kwanan nan ne aka rufe taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice, a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, inda shugaban kasar, Xi Jinping ya gabatar da shawarar tsarin inganta jagorancin duniya. Wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ta zanta da shugaban kasar Iran,...
    Sama da mako uku da suka gabata, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da wani magidanci da matarsa mai juna biyu da kuma ’yarsu a unguwar Kanada da ke Ƙofar Ƙaura a garin Katsina. Masu garkuwar sun fara neman a biya su naira miliyan 100 kafin su sako su, amma daga baya aka daidaita da...
    Sama da mako uku da suka gabata, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da wani magidanci da matarsa mai juna biyu da kuma ’yarsu a unguwar Kanada da ke Ƙofar Ƙaura a garin Katsina. Masu garkuwar sun fara neman a biya su naira miliyan 100 kafin su sako su, amma daga baya aka daidaita da...
    Mutum tara sun rasu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a ƙauyen Zalla Bango, da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, a Jihar Sakkwato. Wani mazaunin yankin ya ce hatsarin ya faru ne bayan sallar Magariba a ranar Alhamis, lokacin da jirgin da ya ɗauki mata, maza da yara, domin tsallaka ruwa saboda hanyar...
    A baya, ƙasashe biyu kawai na Afirka ba sa shigo da man fetur, amma abin takaici, yanzu sun koma shigo da kaya. Wannan yana da illa ga Afirka,” in ji shi. Dangote ya bayyana cewa aikin masana’antar ya kasance mai haɗari sosai. Ya ce ya samu gargaɗi sau da dama daga masana harkokin mai, masu...
    A nasa bangare kuwa, shugaba Trump cewa ya yi alakar Amurka da Sin ita ce mafi muhimmancin dangantaka a duniya, yana mai cewa aiki tare tsakanin kasashen biyu ka iya haifar da manyan abubuwa da za su ingiza zaman lafiya da daidaito a duniya. Daga nan sai ya yi fatan wanzar da babbar dangantaka mai...
    Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar mutuwar mutane 58 sanadiyyar kamuwa da cutar amai da gudawa (kwalara) inda ta gano sabbin masu dauke da cutar mutane 258, wanda aka samu a kananan hukumomi 14 cikin 20 na jihar. Duk shugaban da bai yi aiki ba bai kamata a sake zaɓarsa ba — Jonathan An tsinci gawar...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce duk wani shugaba da bai yi aiki yadda ya kamata ba, bai kamata a sake zaɓarsa ba. Ya yi gargaɗin cewa maguɗin zaɓe na ɗaya daga cikin manyan barazana ga dimokuraɗiyya a Afirka, kuma idan ba a gyara tsarin ba, ’yan kama-karya za su zama wajen zama. Yadda...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne, sun kai hari ƙauyen Sayinna, da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato. Sun kashe Hakimin ƙauyen, Malam Murtala Sa’adu, tare da wani mutum mai suna Ibrahim Mai-Kuɗi. Yadda za ka dawo da kuɗinka da ka yi kuskuren turawa wa wani An tsinci gawar kwamandan hukumar NDLEA...
    Wasu mazauna ƙauyen Zalla Bango a ƙaramar hukumar Sabon Birni, Jihar Sokoto, sun rasa rayukansu a wani haɗarin jirgin ruwa yayin da suke tserewa daga harin ƴan bindiga. Lamarin ya faru ne da yammacin Alhamis, 18 ga Satumba, lokacin da Kwale-Kwalen da ke ɗauke da jama’a yayi karo da dirkar gadar ruwa da ta rushe...
    Daga nan ya wuce gidan tsohon shugaban ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari domin yi wa matar sa Aisha da sauran ‘yan uwa ta’aziyya. Tinubu a gidan marigayi tsohon shugaban kasa, Buhari Ya bayyana Buhari a matsayin “shugaba mai kishin ƙasa da sadaukarwa, wanda gudunmawarsa ga haɗin kan Najeriya da ci gabanta ba za a manta da...
    Gundumar Bakori ta jihar Katsina ta kaddamar da shirin dashen itatuwa domin rage zaizayar kasa a yankin. A cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin aikin gona, Cigarin Bakori Alhaji Shehu Ishiye ya fitar, ya bayyana cewa Hakimin Bakori, Makaman Katsina Alhaji Garba Tukur Idris, ya yi kira ga jama’a da su daina sare itatuwa ba...
    Sheikh Na’im Kassima wanda ya gabatar da jawabi a jiya  juma’a ya kuma kara da cewa; A halin yanzu kungiyar gwagwarmaya tana fuskantar matsanancin yanayi mai hatsari,tare da jaddada cewa; Wanzuwar HKI, manufarsa ita ce a samar da wani yanki na turai da Amurka a cikin wannan yankin domin hana al’ummar yankin ci gaba da...
    Duk da cewa, Nijeriya ce kan gaba wajen kiwon dabbobi a nahiyar Afirka, amma har yanzu, mahukunta a ƙasar sun gaza gudanar da wani kyakkyawan tsari da kuma samar da kayan aiki wajen samar da kashin na dabbobi, inda rashin hakan ke ci gaba da haifar da damuwa ga waɗanda ke fannin a faɗin ƙasar....
    Kimiyyar sadarwa ta kawo sauƙin rayuwa a harkokin kasuwanci da mu’amalar kuɗi ta banki. Yawaitar amfani da wayar hannu wajen yin hada-hadar banki a Nijeriya ya sa mutane da dama ke tura kuɗi cikin sauƙi. A shekarar 2024 kaɗai, rahoton Hukumar Biyan Hada-hadar Banki ta Ƙasa (NIBSS) ya nuna cewa darajar kudin da aka tura...
    Tsarin ya ƙunshi na “ kwas na ƙwarewa kan lamarin koyarwa na gajeren lokaci wanda akan yi wata uku zuwa shida ne,  bayan haka ne waɗanda suka yi kwas ɗin ne za su cancanci yin rajista da hukumar , har su samu Lasin na amincewa da sun cancanta  su yi aikin koyarwa.” Tsarin na ma’aikatar...
    An tsinci gawar Igbonna Uzoma, kwamandan hukumar da ke yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) a otel da ke birnin Kalaba, Jihar Kuros Riba, a ranar Juma’a. Rahotanni sun ce Uzoma, wanda aka dawo da shi aiki daga wata jiha zuwa Kuros Riba a kwanan nan, bai daɗe da kama aiki a sabon ofishin ba...
    Ukraine ta ce Rasha ta kai sabbin hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka wasu yankuna da dama na kasar cikin dare. A gabashin birnin Dnipro, an kai hari kan wani gini kuma an ji ƙarar fashewar wasu abubuwa a Zaporizhzhia kusa da tungar da ke zaman iyakar dakarun Rasha da na Ukraine...
    A ci gaba da kokarin da take yi na tsaftace harkar ilimi, wata kotu a Kano ta bayar da umarnin rufe wasu makarantu masu zaman kansu nan da nan, 6 saboda saba ka’idojin jihar da suka hada da kara kudin makaranta da kuma tilasta iyayen yara sayan litattafai na dole da sauran tsarabe-tsarabe da suka...
    An bukaci gwamnatin jihar Kwara da ta gaggauta shiga tsakani kan rufe kasuwar Kara da ke yankin Kwara ta Kudu da shugaban karamar hukumar ya yi domin ceto harkokin kasuwanci daga durkushewa.   Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Kwara, Alhaji Shehu Garba ne ya yi wannan roko a wata sanarwa da ya rabawa manema...