Jiragen yaki sun kashe ’yan ta’adda 35 a iyakar Najeriya da Kamaru
Published: 25th, August 2025 GMT
Sojojin Najeriya sun kashe ’yan ta’adda kimanin 35 da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP ne a kusa da iyakar Najeriya da Kamaru.
’Yan ta’addan sun taru a yankin Kumshe, wani gari da ke kan iyaka a Jihar Borno, da safiyar Asabar domin kai hari kan sansanin sojoji da ke yankin.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa bayan samun bayanan sirri, sojojin kasa sun nemi taimakon rundunar sojin sama, inda jiragen yaki suka kai hare-hare a wuraren da aka gano ’yan ta’addan sun taru.
“Ranar Asabar, 23 ga Agusta, sojojin runduna ta 21 sun dakile wani hari da ’yan ta’adda suka kai da daddare, inda jiragen yaki suka ragargaza ’yan ta’addan,” in ji wata majiya.
Binciken bayan harin ya nuna cewa an binne gawarwaki fiye da 20, ciki har da sassan jikin da suka tarwatse, an kuma kwato makamai daga hannun ’yan ta’addan.
Kakakin rundunar sojin sama, Iya Komodo Ehimen Ejodame, ya tabbatar da harin, yana mai cewa fiye da ’yan ta’adda 35 ne aka kashe a hare-haren.
Ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen murkushe ’yan ta’adda a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hare hare jiragen yaki yan ta addan yan ta adda
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Duk da cewa gwamnati na da dubban kwararrun malamai a makarantunta, har yanzu ana ganin ɗaliban makarantun gwamnati na kasa da na makarantun masu zaman kansu wajen ƙoƙari da kuma sakamakon jarabawa.
Wannan matsala ta daɗe tana jawo muhawara tsakanin iyaye, malamai da hukumomin ilimi.
Wasu na ganin matsaloli ne da ba za su rasa nasaba da rashin kulawa da watsi da harkar ilimi da gwamnati ta yi ba.
Ko wadanne dalilai ne suka daliban makarantun masu zaman kansu suka fi kokari idan aka kwatanta da daliban makarantu na gwamnati?
NAJERIYA A YAU: Shin Ko Sauya Hafsoshin Tsaro Zai Kawo Karshen Aikin Ta’dda A Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyyaWannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan