Aminiya:
2025-09-18@00:44:34 GMT

Za a yi amfani da Hausa wajen samar da zaman lafiya — Abdulbaqi Jari

Published: 25th, August 2025 GMT

Za a yi amfani da harshen Hausa a matsayin hanyar samar da zaman lafiya a yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na goma (10), wanda za a gudanar a Daura da ke Jihar Katsina, a ranar Talata, 26 ga watan Agusta, 2025.

Jagoran taron, Abdulbaqi Aliyu Jari, wanda shi ne ya ƙirƙiri wannan rana, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Katsina.

Jiragen yaki sun kashe ’yan ta’adda 35 a iyakar Najeriya da Kamaru Jami’an tsaro sun tsare jagoran Falasdinawa mazauna Najeriya

Ya ce dukkan shirye-shirye sun kammala, kuma manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya tuni sun fara isowa domin halartar bikin.

Jari ya ce an tsara taron ne domin baje kolin al’adun Hausawa da kuma jaddada muhimmancin harshen Hausa a matsayin alamar alfahari da haɗin kai.

A cewarsa, za a yi baje kolin kayan tarihi da dama, ciki har da hawan doki, sana’o’in gargajiya, saƙa da sauran su, domin nuna gadon al’adu da darajar harshen Hausa.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da su ƙara bai wa harsunan asali dama, musamman Hausa wanda mutum fiye da miliyan 200 ke amfani da shi a duniya.

Ya ƙara da cewa lokaci ya yi da Hausa za ta samu ƙarin ƙarfafawa a matsayin harshen ƙasa a hukumance, duba da yaɗuwar harshen musamman yadda ya ƙetare iyakokin Najeriya zuwa wasu ƙasashen Afirka ta Yamma, ƙasashen ECOWAS da maƙwabta.

“Idan aka amince da Hausa a matsayin harshen ƙasa, hakan zai ƙara sauƙaƙa mu’amala, ya bunƙasa kasuwanci, ya inganta alaƙa tsakanin jama’a, tare da taimakawa wajen samar da zaman lafiya,” in ji shi.

Taken bikin na bana shi ne: “Amfani da Harshen Hausa Don Samar da Zaman Lafiya.”

Abdulbaqi ya bayyana cewa manufar babban taron shi ne ƙarfafa fahimtar juna da wayar da kan jama’a kan rawar da harshen Hausa da al’adun Hausawa za su iya takawa wajen wanzar da zaman lafiya.

Kazalika, Jari ya ce ana sa ran halartar gwamnoni, ministoci, sarakunan gargajiya da manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar, tare da kira ga jama’a daga nesa da kusa da su hallara a Daura domin shaida baje kolin al’adun Hausawa a idon duniya.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Abdulbaqi Aliyu Jari Bikin Ranar Hausa Daura Jihar Katsina Ranar Hausa ta Duniya da zaman lafiya harshen Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • UNICEF Ya Ba Da Tallafin Kayayyakin Aiki Ga Cibiyoyin Lafiya A Kirikasamma
  • Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
  • Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari
  • Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki Guda 5 A Wajen Taron Kolin kere-kere .
  • Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi
  • Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya
  • NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha