2025-10-13@15:52:55 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2915

«jiragen Ruwan»:

    A safiyar yau litinin ce majiyar gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa shugaban kasa Masoud Pezeshkiyan ko kuma ministan harkokin wajen kasar ba zasu halarci taron sanyawa yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin HKI da Falasdinawa a birnin Sharm sheikh na kasar masar ba. Saboda ba sa son haduwa da shuwagabannin kasashen yamma azzalumai wadanda da makaman sune aka kashe falasdinawa kimani 70,000 a gaza a cikin shekaru 2 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar gwamnatin na cewa shuwagabannin kasar Iran ba zasu amince su zauna kusa da wadanda suka kashe iraniyawa a cikin watan yunin da ya gabata, da kuma jinin mutanen da dama a yankin ba, suna mika masu hannu ba. A taron...
    An kammala kada ƙuri’a da yammacin Lahadi a zaɓen shugaban ƙasa na Kamaru, inda shugaban ƙasa mai shekaru 92, Paul Biya — wanda shi ne tsohon shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya — yake neman wa’adi na takwas a mulki. Biya, wanda ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, ya fafata da ’yan takara 11, ciki har da tsoffin muƙarrabansa. Ɗaya daga cikinsu shi ne Issa Tchiroma Bakary, tsohon ministan ma’aikata wanda ya yi murabus daga gwamnati a watan Yuni bayan fiye da shekaru 20 yana aiki tare da Biya. Bakary, mai shekaru 79, ya zama babban abokin hamayyar Biya bayan Kotun Tsarin Mulki ta ƙi amincewa da takarar fitaccen ɗan adawa Maurice Kamto — matakin da ƙungiyoyin kare haƙƙin...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta gayyaci muqaddashin jakadan kasar Oman a kasarta Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gayyaci babban jami’in ofishin jakadancin kasar Oman a birnin Tehran a jiya Lahadi, bayan wani rade-radin da ake yadawa cewa; Mutane biyu a kasar Oman sun mutu sakamakon shan ruwan ma’adinai da aka shigo da su daga kasar Iran. Bayan wasu zarge-zarge marasa tushe da wasu kafafen yada labarai na kasar Oman suka wallafa na alakanta mutuwar mutane biyu a masarautar Oman da shan ruwan ma’adinan da aka shigo da su daga kasar Iran, a ranar Lahadin da ta gabata ne Abdul Rasoul Shabibi, shugaban sashen  ma’aikatar kula da tekun Farisa ta ma’aikatar harkokin wajen kasar ya gayyaci mai kula...
    Shugaban kasar Amurka ya yi barazana ga shugaban kasar Rasha na aike wa Ukraine makamai masu linzami kirar Tomahawk Shugaban Amurka Donald Trump ya ce: Zai gargadi takwaransa na Rasha Vladimir Putin cewa: Akwai yiwuwar Ukraine za ta iya samun makamai masu linzami kirar “Tomahawk” idan Rasha ba ta kawo karshen yakin Ukraine ba. Da aka tambaye shi a cikin jirgin Air Force One da ke kan hanyarsa ta zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila da Masar da yammacin ranar Lahadi ko shi da kansa zai tattauna da Putin kan batun, Trump ya ce, “Yana iya magana da shi. Yana cewa: Idan ba a warware wannan yakin ba, zai aika wa Ukraine da makamai masu linzami na Tomahawk.” Trump ya kara da...
    Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya. Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja. Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro Ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025. ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025. A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da...
    Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da ta danganta da na karya da Amurka ke yi wa kasar cewa ta na da hannu a yakin da ake yi a Ukraine, tana mai daukar wadannan zarge-zarge a matsayin wani makirci na siyasa da nuna kiyayya. A cewar ma’aikatar harkokin wajen Cuba, hukumomi “ba su da wani takamaiman bayani kan ‘yan kasar Cuba” da suka shiga ko kuma suke shiga cikin rikicin “da kansu” a cikin “dakarun sojan bangarorin biyu da ke rikici da juna” tsakanin Rasha da Ukraine. Tsakanin shekarar 2023 zuwa 2025, kotunan kasar Cuba sun saurari kararrakin laifuka tara da suka shafi ayyukan sojan haya, inda suka yanke wa wadanda ake tuhuma 26 hukuncin zaman gidan yari tsakanin...
    Sojojin Nijeriya sun kashe wani kwamandan ƙungiyar ƴan ta’adda IPOB/ESN da ake nema ruwa a jallo, mai suna ‘Alhaji’, tare da wasu mutane 26 a jerin hare-haren da suka kai a sassan ƙasar tsakanin 8 zuwa 11 ga Oktoba, 2025. Rundunar Sojin ta ce an kuma ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su, tare da kwace makamai, da harsasai, da kuɗaɗe. A kudu maso gabas, Sojojin Operation UDO KA sun kai farmaki a Izzi, jihar Ebonyi, inda suka kashe ‘Alhaji’ bayan ya yi yunƙurin kwace bindiga daga hannun wani Soja lokacin kama shi. Haka kuma, a jihar Imo, an rusa wata maboyar IPOB/ESN da ake amfani da shi wajen horar da mambobi. Sojoji Sun Cafke Babban Kwamandan IPOB...
    Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya. Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja. Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro Ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025. ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025. A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da...
    Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya sauke Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Ajao Adewale, daga muƙaminsa. Ko da yake ba a bayyana cikakken dalilin da ya sa aka sauke shi ba, majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa hakan ya faru ne sakamakon yadda rundunar Abuja, ta tafiyar da lamarin sanya gilishin mota mai duhu da kuma mutuwar ’yar jaridar gidan talabijin na Arise News. Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi Ɗaya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa waɗannan matsalolin guda biyu ne suka janyo sauya masa wajen aiki. Ta ƙara da cewa za a tura Adewale wani waje daban, inda za a...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Makaie ya tir da HKI saboda hare-haren da ta kai kan wasu wurare a kudancin kasar, Lebanon wanda ya sabawa da farko yarkeniyar tsagaita wutan da ta cimma da kungiyar Hizbulla a cikin watan Nuwamban shekara ta 2024 sannan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Baghaei ya bayyana cewa ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon a kai a kai, da kuma shirun da kasashen duniya suka yi duk sun sabawa dokokin kasa da kasa wadanda HKI da wadanda suke riya daukar nauyin kola da cewa an dabbaka yarjeniyar MDD na kuduri mai lamba 1107. Ya zargi kasashen Faransa da kuna Amurka wadanda suka gabatar da kansu a matsayin masu lamuni don aiwatar...
    Irabor ya ce, littafin nasa na ƙoƙarin kawo tarihin “tasirin Boko Haram a Nijeriya ta fannoni daban-daban” da kuma “hakikanin gaskiya a kan Boko Haram, wanda na samo a lokacin ina matsayin kwamandan soji na yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.”   Tsohon babban hafsan tsaron ya ce, babban abinda ya fi tayar da hankali a yaki da Boko Haram shi ne yawan rayukan da aka rasa. A cewarsa, “irin rayukan mutanen da aka kashe a rikicin Boko Haram yana da yawa kuma ana iya kwatanta shi da annoba.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna  October 12, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Yi...
    Al’ummomin dake garin Warwade da kewaye a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta yashe madatsar ruwa ta Warwade wanda ta kasance daya daga cikin hanyar samun aikin dogaro da kai ga Mazauna yankin. Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ziyarci al’ummomin da ke zaune a kusa da mmadatsr ruwan wanda aka gina ta sama da shekaru hamsin da suka gabata. Madatsar ruwan ta Warwade ta kasance hanyar samun sana’o’in dogaro da kai ga mazauna yankin, wadanda suke kamun kifi da noman rani domin samun na yau da kullum. Malam Umar Sani, wanda masunci ne a Warwade, yace da abin da yake samu daga kamun kifi yake kula da iyalan shi da kuma sauran...
    Haka zalika, sun ki bayyana takamaiman wajen da za a daura auren, har sai bayan an kammala, inda suka bayyana yin hakan a matsayin wata hanya ta kawar da cece-kuce daga al’umma.   Kazalika a ‘yan watannin da suka gabata kuma, an sake daura auren jaruma a masana’antar Kannywood, Rahama Sadau tare da angonta Ibrahim Garba, a wani biki wanda za a iya kira da na sirri da aka gudanar a birnin Kaduna, daura auren shahararriyar jarumar Kannywood din, Rahma Sadau da mijinta Ibrahim Garba, wanda aka gudanar a ranar Asabar, ya yi matukar bai wa mutane mamaki, duba da cewa; kafin daurin auren babu wata alama ko sanarwa da aka fitar daga makusantan mijin ko matar.   An yi...
    Bayanan da suka fito daga kasar Indunusiya sun nuna cewa gwammnatin kasar ta ki bada visa ga tawagar wasan jiminastik din HKI da aka shirya za’a yi wasa a birnin Jakarta a wannan watan, domin nuna rashin amincewa da kisan kare dangi da HKI ke yi a yankin Gaza. Wannan matakin yana kara nuna irin yadda batun kisan kiyanshin gaza yayi tasiri sosai hatta a harkar wasanni, kasar dake da yawan musulmi tana aikewa da sako na siyasa ne ta hanyar takawa yan wasan isra’ila birki, da kuma neman goyon bayan duniya ga alummar falasdinu. An tsara cewa tawagar wasan Jemanastik din HKI ta za shiga gasar jiminastik na duniya da za’a yi a Jakarta daga ranar 19-25 ga wannan...
    Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da kyautar motoci ƙirar Hilux guda shida da babura 30 domin taimaka wa sojoji wajen yaƙi da ’yan bindiga a faɗin jihar. Gwamnan, ya miƙa motocin da baburan ga Kanal Hussaini Rabi’u Toro na rundunar sojoji ta takwas a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi. ’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi Ya ce wannan kyauta na cikin ƙoƙarin gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da walwalar al’umma. “Tsaro shi ne babban abin da gwamnatina ta mayar da hankali a kai. Ba za mu yi wasa da harkar tsaro ba. “Za mu ci gaba da tallafa wa jami’an...
    Mataimakin shugaban kasar Iran Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa, batun kifar da gwamnatin JMI bayan yakin kwanaki 12 ya kuma fita daga abinda makiya zasu iya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar yanakalto mataimakin shugaban kasa na farko yana fadar haka a ranar Alhamis da ta gabata, ya kuma kara da cewa a cikin yakin kwanaki 12 wanda kasashen Amurka da HKI suka dorawa kasar sun so su kifar da gwamnatin JMI a cikin kwanaki 3 zuwa 4 amma suka kasa. Ya ce hatta babban sakataren MDD Antonio Guterres ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da shi dangane daha. Ya kuma tabbatar da cewa makiyan JMI ba zasu iya tumbuke tsarin ba. Yasashen yamma musamman Amurka suna kokarin...
    Masu zanga-zanga a nan Iran a jiya jumma’a a manya-manyan garuruwan kasar bayan sallar Jumma’a sun bayyana goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu a Gaza, sannan sun bukaci HKI ta aiwatar da yarjeniyar da ta cimma da kungiyoyi masu gwagwarmaya. Har’ila yau sun bukaci a gaggauta shigo da abinci da magungunacikin zirin Gaza. Tashar talabijin talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga zangar wadanda suka hada da mata da maza, malaman addini, daliban jami’o’i da sauransu suna tattaki daga dandalin inkilab zuwa dandalin azadi. Har’ila yau sun rera wakoki na goyon bayan masu gwagwarmayar, dauke da hotunan shahidai da kuma  shuwagabannin kawancen masu gwagwarmaya a yankin. An gudanar da jerin gwanon a cikin manya manyan biranen...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tsaro ‘Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Wata Ba’amurkiya Da Ta Ziyarci Saurayinta A Jihar Delta October 11, 2025 Tsaro Sojoji Sun Ƙaryata Rahoton Cewa Ƴan Bindiga Sun Mamaye Sansaninsu A Kwara October 5, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 450, Sun Ceto Mutane 180 A Satumba — DHQ October 4, 2025
    Aƙalla mutane biyu ne suka mutu a rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a unguwar Dambo, wani kauye da ke da tazarar ’yan kilomita daga Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi. Wani mazaunin yankin mai suna Ɗanladi Usman ya ce rikicin ya fara ne bayan an kashe wani mutum mai suna Sule yayin da yake aiki a gonarsa. “Kashe Sule ya tayar da hankulan al’umma, inda manoma suka ɗauki fansa suka kashe wani makiyayi da har yanzu ba a gano sunansa ba,” in ji shi. Ya ƙara da cewa makiyayan sun sha faɗa da manoma a kwanakin baya bayan sun aike musu da sako cewa su hanzarta girbe amfanin gonakinsu domin za su riƙa wucewa da shanunsu ta...
    A cewarta, shirin ya taimaka wajen noman shinkafa da ta kai kimanin tan 99,452, wacce kuma kudinta ya kai kimanin Naira biliyan 13.527 tare kuma da noman rogo da ya kai kimanin tan 87,237, wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 3.925, musamman domin a kara samar da wadataccen abinci da kuma kara bunkasa fannin tattalin arzikin jihar.   Sai dai, ta bayyana cewa; har yanzu a jihar ba a samar da wani cikakken tsari a hukumance ba, a kan tsarin na shirin na CAF wanda hakan ke haifar wa da shirin koma baya a jihar.   Ta yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki a fannin bunkasa aikin noma, domin samun riba a jihar da su bayar da hadin...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya October 10, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa October 10, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka October 10, 2025
    Hukumar Tsaro ta Sibil Difens a Jihar Kano, ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a Ƙaramar Hukumar Doguwa. Hukumar ta miƙa su ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a kotu. ’Yan bindiga sun kashe Civilian JTF 8 a Zamfara Sojoji sun mutu yayin da Boko Haram ta kai hari sansanin soji a Borno Kwamandan hukumar na Jihar Kano, Bala Bawa Bodinga ne, ya bayyana hakan yayin da yake magana da ’yan jarida a hedikwatar hukumar a ranar Juma’a. Ya ce an kama mutanen ne da sanyin safiyar ranar Talata, 7 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihin bayaai. Jami’an hukumar daga...
    “Ta yaya Jonathan zai zama barazana? Mun doke shi a baya lokacin da PDP take kan mulki.   “Idan mutum yana ganin cewa PDP ita ce kololuwar jam’iyya a Nijeriya, kuma ya sha kaye a lokacin da yake ganiyarsa, ina ganin sai makiyinsa ne kawai zai tilasta masa ya kara tsayawa takara a zaben 2027,” in ji shi.   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa ya ce a yanzu haka Jonathan ya kasance dan siyasa mai daraja, yana mai cewa komawa fagen siyasa na iya rage masa kima da kuma zubar masa da darajar da yake da shi a idon duniya.   Ya jaddada cewa Jonathan ya samu damar nuna cewa mulki bai tsole masa ido ba, domin haka ne...
    “Muna kira ga majalisar kasa da ta yi la’akari da shirin gyaran tsarin kudurorin zabe cikin gaggawa. Amincewa da dokar cikin lokaci yana da muhimmanci ga shirinmu na gudanar da zabe a 2027.   “Rashin tabbas game da tsarin doka na zabe na iya kawo matsaloli masu yawa ga ayyukan hukumar INEC yayin da lokacin zabe ke karatowa,” in ji shi.   Shugaban INEC ya bayyana cewa hukumarsa ta aiwatar da shawarwarin da aka mika mata kai tsaye a rahoton EU na zaben 2023.   “An dauki mataki kan wasu bangarori na shawarwarin da ake bukatar hukumar ta aiwatar da su. Haka kuma, ana daukar mataki kan shawarwarin da suka shafi fannoni da dama wadanda ake bukatar hadin gwiwa tsakanin...
    A yayin da ake yawan samun ɓarnar dorinar ruwa a garuruwan Daɗin Kowa da Kupto da Malleri da Wade a yankunan Ƙananan hukumomin Kwami da Yamaltu Deba a Jihar Gombe ta kai ga samun asarar amfanin gona da rayuka. Hakan ne ya sa Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Yamaltu/ Deba a Jihar Gombe Inuwa Garba ya gabatar da ƙudiri a gaban zauren Majalisar Wakilai ta tarayya domin neman ɗaukar matakin gaggawa kan ɓarnar dorinar ruwa. ’Yan sanda sun ceto mutum 3 da aka sace a Kano da Kaduna Kwastam ta kama buhunan lalatacciyar fulawa 10,000 ana ƙoƙarin shigo da ita Najeriya Inda ya ce dorinar na yi wa manoma ɓarna sosai da ke janyo asarar rayuka, dukiyoyi da lalacewar...
    Rundunar ƴansanda ta Jihar Kano ta ce ta ceto mutane uku da aka sace a yayin wani aiki biyu da ta gudanar a Kano da Kaduna, tare da ƙwato babur da wasu shaidu. Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a. A cewar Kiyawa, a ranar 7 ga Oktobar 2025, rundunar daƙile garkuwa da mutane (Anti-Kidnapping) tare da tawagar sa-ido daga ofishin ƴansanda na Bebeji sun gudanar da sumame bayan samun bayanan sirri kan wani mutum da ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutane. Wanda aka sace, Abdul Hamid Bello, mai shekaru 21, ya taimaka wajen kai jami’an tsaro inda aka ceto wani mutum mai...
    Hukumar Kwastam shiyyar bodar Najeriya ta Seme da ke jihar Legas ta ce ta cafke motoci biyar da ke maƙare da buhuna 10,000 na lalatacciyar fulawa da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.2. Rundunar ta kuma ce ta tara jimillar kuɗin shigar da ya kai Naira biliyan daya da rabi a watan Satumba, wanda hakan ya nuna kari da kaso 182 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira miliyan 531 da aka tara a watan Agustan da ya gabata. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da wasu mutum 173 afuwa Kwamandan rundunar a shiyyar, Wale Adenuga, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na...
    Rahotanni daga Gaza na cewa Isra’ila ta fara janye sojojinta daga wasu yankuna na zirin Gaza. Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamantin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta dake kunshe a shirin zaman lafiya na Trump da ta cimma da kungiyar Hamas. Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa da Hadin Kan Kasa da Kasa ta Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Gaza Mohammad Al-Moughayyir, ya ce sojojin Isra’ila sun janye daga yankuna da dama a cikin birnin Gaza da arewacin zirin da kuma wasu yankunan kudancin yankin. A Khan Younis da ke kudancin zirin Gaza, Motocin Isra’ila sun janye daga kudancin birnin da tsakiyar birnin zuwa yankunan gabashi. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of...
    Ma’aikatar baitul malin Amurka ta sanya takunkumi kan wasu mutane sama da 50 da hukumomi da jiragen ruwa da ake zargi da hannu a cinikin man fetur da Iran. A cewar sanarwar da hukumar ta fitar, ofishin kula da kadarorin kasashen waje (OFAC) ta kara matsin lamba kan Iran ta hanyar kakaba mata takunkumi ga mutane sama da 50, kamfanoni da jiragen ruwa masu saukaka sayarwa da jigilar danyen mai da iskar gas daga Iran. A cewar hukumomin Amurka, wadannan hanyoyin sun baiwa Iran damar fitar da mai da kayayyakin da suka kai na biliyoyin daloli. Sabon takunkumin ya shafi kamfanoni uku da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, kamfanoni uku na bogi a Hong Kong, da wata matatar mai a China....
    Wata kafar labarai daban, Peoples Gazette, tun da farko a shekarar 2024, ta ruwaito labaran da ke zarginsa da yin jabun takardar shaidar NYSC.   Sai dai Nnaji ya karyata labarin da Premium Times ta wallafa, yana mai cewa zargin aiki ne na abokan hamayyar siyasa a Jiharsa ta Enugu.   Tsohon ministan, wanda aka nada a watan Agusta 2023, ya mika takardar murabus dinsa a ranar Litinin ga Shugaban Kasa, inda ya nuna godiyarsa kan damar da aka ba shi ta yi wa kasa hidima.   A cikin wasikar tasa, tsohon ministan ya bayyana cewa ya zama abin kai hare-hare na “tsananin batanci” daga abokan hamayyar siyasa da ke neman bata masa suna.   “Ina gode wa Shugaban Kasa...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama mutum 26 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da kwato makamai da kudade daga hannunsu. Daga cikin abubuwan da aka samu nasarar kwatowar har da bindigogi na gida guda huɗu, makamai masu hatsari da kuma tsabar kuɗi Naira 546,000 da ake zargin wani ɓangare ne na kuɗin fansa. Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da wasu mutum 173 afuwa Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC An kama waɗanda ake zargin ne a cikin jerin samame da aka gudanar daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Oktoban 2025, a sassa daban-daban na jihar. Samamen ya haɗa jami’ai daga sashen ’yan sanda na Anchau, Hukumar Kula da Tsaro...
    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da afuwar Shugaban Kasa ga mutane 175. Daga ciki har da wadanda aka yi wa afuwar bayan mutuwa ga marigayi Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa da ɗan gwagwarmayar kwato ’yancin kan Najeriya, Herbert Macaulay. An dauki wannan mataki ne bayan amincewa da shawarwarin da Majalisar Tsofaffin Shugabannin Ƙasa ta bayar a taronta da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja. Gwamnatin Kano ta shirya ɗaurin auren ma’aurata 2,000 Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC A cewar sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin bayanai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma yi afuwa ga tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan da wasu mutum uku, Misis Anastasia...
    Gwamnatin Jihar Kano ta umurci Hukumar Hisba ta jihar da ta fara shirye-shiryen ɗaurin auren ma’aurata aƙalla 2,000 a ƙarƙashin shirinta na ɗaurin auren gata. Mataimakin babban Kwamandan hukumar, Sheikh Mujahid Aminudeen ya shaida wa kafar PUNCH a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Alhamis, inda ya ce nan ba da daɗewa ba hukumar za ta fara shirin don ganin an samu nasarar gudanar da taron bikin. An kama 26 da ake zargin masu garkuwa da mutane Ma’aikatan jami’a sun yi zanga-zanga a Jami’ar Bayero “Muna shirin gudanar da ɗaurin auren wani rukunin ma’aurata guda 2,000 kamar yadda gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta umarta,” in ji shi. Duk da cewa, babban kwamandan bai bayyana ainihin...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI October 9, 2025 Labarai Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA  October 9, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC  October 9, 2025
    Mai Martaba Sarkin Nafada, Alhaji Dadum Hamza ya ƙaddamar da sabuwar doka ta rage tsadar aure a masarautarsa, a Jihar Gombe domin sauƙaƙa wa matasa yin aure da kuma magance matsalolin da ke hana sauƙin yin aure a cikin al’umma. Wakilin Sarkin, Alhaji Umaru Muhammad Baraya (Madakin Nafada), ne ya gabatar da dokar yayin taron ƙaddamarwa da aka gudanar a Unguwar Madaki da ke Nafada ta Tsakiya, tare da halartar jami’an gwamnati, Alƙalan kotun majistare da jami’an tsaro. ’Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da kashe ma’aikaciyar Arise TV a Abuja Najeriya ta tafka asarar tiriliyan 14.5 sakamakon rikicin Boko Haram – UNICEF Dokar za ta fara aiki daga wannan shekara ta 2025, inda aka gargaɗi matasa da su...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Kira ga tsayar da sallah wani aiki ne na wajibi ga hukumomin da’awar addini da malamai Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa: Kira ga tsayar da sallah da koyar da ita, da bayyana ma’anonin da ke cikinta, da riko da ita, wani aiki ne na wajibi da ya rataya a wuyan hukumomin da’awar addini da malamai da ma’abuta addini. Dole ne a yi amfani da hanyoyin zamani domin watsa wannan fanni. A cikin sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike ga zaman taron cibiyar karfafa tsayar da sallah karo na 32 ya bayyana cewa: Taron karfafa tsayar da sallah yana daya daga cikin mafi...
    An shawarci mata a karamar hukumar Kirikasamma da ke jihar jigawa da su kawo ‘ya’yansu domin yi musu rigakafin cutar shan inna, kyanda, da Gaida da sauran cututtuka masu ban tsoro.   Uwargidan Shugaban Karamar Hukumar, Hajiya Fatima Maji Marma ta ba da wannan shawarar a lokacin kaddamar da shirin rigakafin cutar kyanda da na rigakafi na yau da kullum a fadar Hakimin Marma.   Ta kuma jaddada aniyar karamar hukumar na bayar da tallafin da ake bukata domin samun nasarar gudanar da aikin rigakafin.   Hajiya Fatima ta kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa bullo da inshorar lafiya ga marasa galihu a matakin unguwanni a kananan hukumomin jihar 27.   A nasa jawabin manajan hukumar kula da lafiya matakin...
    Hukumar Tsare-tsare da Cigaban Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) ta jaddada aniyar ta na karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomi da inganta ci gaban birane ta hanyar hadin gwiwa da hukumar tsaro ta NSCDC.   Tawaga daga KNUPDA, karkashin jagorancin Manajan Darakta, Arc. Hauwa Hassan T/Wada, ta kai ziyarar gani da ido hedikwatar hukumar NSCDC da ke Kano a wani bangare na kokarin fahimtar juna da hadin gwiwa tsakanin hukumomi.   Da yake jawabi yayin ziyarar, Arc. Hauwa ta bayyana cewa ingantaccen tsare-tsare da ci gaban birane na bukatar hada karfi da karfe da manyan jami’an tsaro domin tabbatar da kare kadarorin gwamnati, tabbatar da doka da oda a cikin babban birni.   Ta bayyana irin shirye-shiryen KNUPDA da ke ci...
    Cristiano Ronaldo ya zama biloniya na farko tsakanin ƴan wasan kwallon kafa a duniya Bloomberg mai sharhi da kididdiga tarin dukiya tsakanin attajiran duniya, ta fayyace tarin kudin da mai shekara 40 dan kwallon tawagar Portugal mai taka leda a Al-Nassr ta Saudiya ke da shi. Ta ce yana da dalar Amurka biliyan daya da miliyan 400 daga kudin da yake samu na albashi da ladan wasa da tallace-tallace da zuba hannun jari. Ya samu albashin sama da dalar Amurka miliyan 550 tsakanin 2002 zuwa 2023 da kwantiragin da ya kai  dalar Amurka miliya 18. Lokacin da Ronaldo ya koma Al-Nassr ta Saudiyya a 2022, ya zama wanda ke kan gaba da ake biya albashi mafi tsoka a tarihi. da...
    Bankin Duniya ya ce har yanzu talauci na ci gaba da yaɗuwa a Najeriya duk da sauye-sauyen tattalin arziƙi da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar domin daidaita tattalin arziƙin ƙasar. A wajen ƙaddamar da rahoton ci gaban da aka samu a Abuja, Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ya bayyana cewa aƙalla mutum miliyan 139 ne ke rayuwa cikin ƙangin talauci a shekarar 2025. Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahoton Bankin Duniya kan yawan talakawa a Najeriya NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Nada Shugaban Hukumar Zabe Ya ce duk da cewa tattalin arziƙin Najeriya ya ɗan bunƙasa, kuma gwamnati tana samun ƙarin kuɗaɗen shiga, yawancin jama’a har yanzu na fama da tsadar...
    Adaidai lokacin da ake taron cika shekaru 2 da fara yakin Gaza Babban sakatare janar din Majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya sake yin kira da a gaggauta cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta din din din a yankin Gaza .inda ya bayyana yakin a matsayin babban bala’I da ba’a taba ganin irinsa ba Yakin ya jawo mummunar asarar rayukan mutane fararen hula da kuma lalata abubuwan amfani na jama’a , kuma ya jawo matsaloli masu yawa a ayyukan jin kai da yake bukatar kulawa ta gaggawa da kuma warware matsala ta hanyar siyasa Guterres ya halarci wannan taron ne inda yayi alkawarin ganin an kawo karshen yakin Gaza kuma ya amince da dukkan shawarwarin da Amurka ta bayar...
    Fadar Shugaban Ƙasa ta yi fatali da sabon rahoton tattalin arziki da Bankin Duniya ya fitar, wanda ya kiyasta cewa mutane miliyan 139 na rayuwa cikin talauci. Fadar ta bayyana adadin a matsayin wanda ya saba da zahiri kuma ya kauce wa hakikanin halin tattalin arzikin ƙasar. SSANU da NASU za su yi wa gwamnati zanga-zanga kan rashin cika musu alƙawari 2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — Kalu Mai ba Shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya bayyana a shafinsa na X a ranar Laraba cewa dole ne a rahoton bai duba yanayin tsarin auna talauci na duniya ba. “Duk da cewa Najeriya na daraja...
    Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Makarantun Najeriya (SSANU) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ilimi (NASU), sun shirya gudanar da zanga-zangar gargaɗi ta rana ɗaya a yau Alhamis saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza cika musu alƙawuran da ta ɗauka. Ƙungiyoyin, ƙarƙashin jagoranci Joint Action Committee (JAC), sun gudanar da taron gaggawa a ranar Laraba don shirya zanga-zangar. 2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — Kalu ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da Kamaru Sun ce za su gudanar da tattaki a cikin jami’o’i, tare da ɗaukar kwalaye masu rubuce-rubuce, sannan za su yi wa manema labarai jawabi domin bayyana ƙorafe-ƙorafensu. Sun zargi gwamnati da rashin adalci wajen rabon Naira biliyan 50 na alawus-alawus, ƙin...
    ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinYawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana October 8, 2025Daga Birnin SinAdadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7 October 8, 2025Daga Birnin SinSin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa October 8, 2025
    Gamayyar Jiragen ruwan ceto ko (FFC) ta bada sanarwan cewa sojojin HKI a yau Laraba sun kai faramaki kan wasu jiragen gamayyar a tazarar kilomitan ruwa 120nm kacal daga zirin Gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar FFC tana cewa hotunan bidiyo da na tsaye, duk sun nuna lokacinda sojojin yahudawan suka farwa jiragen na ceton Gaza. Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun dakatar da wasu jiragen a ruwayen kasa da kasa, wanda bata da hakkin yin hakan. Jiragen ruwan ceton dai suna dauke da kayakin agaji wadanda suka kai dalar Amurka $110,000, kama hada da kayakin aikin likita da magunguna da wasu kayakin asbiti. Labarin ya nakalto kafafen yada labaran yahudawan na cewa...
     Muluku ya bayyana hakan ne a ranar Talata a babban birnin jihar Lafiya, yayin wani taron bayar da rahoton ma’aikatu da Kwamishinan Bayanai, Al’adu da Yawon Bude Ido, Dr. Ibrahim Tanko, ya shirya domin bai wa jami’an gwamnati damar bayyana nasarorinsu. Kwamishinan ya ce wannan yunkuri na cikin ƙoƙarin gwamna Sule na inganta samun ruwan sha mai tsafta da haɓaka ci gaban karkara a fadin jihar. Ya bayyana cewa gwamnati ta kuma gyara burtsatse 300 a kauyuka da birane domin rage matsalar ƙarancin ruwa da kuma ƙara wa jama’a damar samun ruwan sha mai tsafta. Muluku ya ƙara da cewa, akwai gidan ruwa fiye da tara (9) a Awe, Obi, Keana, Lafia, Nassarawa-Eggon, Akwanga, Wamba, Nasarawa da Toto, kuma dukkansu gwamnati tana kula...
    ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025
    Tsohon Ministan Ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya ce bai yi murabus daga muƙaminsa ba saboda yana da laifi. Nnaji, ya yi murabus ne a ranar Talata bayan cece-ku-ce ya karaɗe kafafen watsa labarai tambaya kan sahihancin takardun karatunsa. Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERC Zulum ya ba ma’aikaciyar lafiya ’yar kabilar Igbo kyautar gida, ya ba danta aiki Rahoton da jaridar PREMIUM TIMES ta wallafa ya nuna cewa Jami’ar Nsukka (UNN), ta ƙaryata bai wa Nnaji takardar shaidar kammala digir a jami’ar. Jami’ar ta ce Nnaji ya fara karatu a makarantar a shekarar 1981, amma bai kammala karatunsa ba kuma ba a ba shi shaidar kammala digiri ba. Sai dai...
    Hukumar da ke Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta ce kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 sun tara Naira biliyan 546.71 daga hannun abokan cinikinsu a cikin zango na biyu na shekarar 2025. Sai dai hukumar ta ce wannan adadi bai kai kaso 60 cikin 100 na wutar da aka tura musu daga babbar hanyar rarraba wuta ba, sakamakon matsalolin lissafin wutar da suka karɓa da kuma yadda aka raba wutar ga rukunan abokan ciniki daban-daban. Zulum ya ba ma’aikaciyar lafiya ’yar kabilar Igbo kyautar gida, ya ba danta aiki Matar aure mai ’ya’ya huɗu ta rataye kanta a Jigawa Hakan, a cewar hukumar, ya haifar da gibin biyan kuɗi na naira biliyan 167.25. kazalika, NERC ta ce...
    Al’umma a kauyen Sumore da ke Ƙaramar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa sun shiga cikin alhini bayan mutuwar wata mata mai shekaru 30, Adama Hannafi, wacce ake zargin ta rataye kanta. Lamarin, wanda ya faru a ranar Talata, ya tayar da hankulan mazauna kan ƙalubalen da ke tattare da rashin lafiyar kwakwalwa a cikin al’umma, musamman a yankunan karkara. ‘Akwai ɗaliban da ke yin digiri yanzu ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ba saboda AI’ Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Lawan Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an samu gawar matar a rataye a jikin wata bishiya a kauyen. “Mun samu kiran...
    Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata daina samar da magungunan da take yi ta hanyar fasahar makamashin nukiliya ba Kakakin Kwamitin Tsaro da Harkokin Waje na Majalisar Shawarar Musulunci (wato Majalisar Dokoki) Ibrahim Reza’ei, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da samar da magungunan ta hanyar fasahar makamashin nukiliya a Iran, kuma ba a taba dainawa ba, kuma za a ci gaba da gudanarwa. Reza’i ya bayyana cewa: Kwamitin tsaron kasar ya gudanar da zaman hadin gwiwa tare da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI), Mohammad Eslami, da wasu jami’an kungiyar. Islami ya gabatar da wani rahoto kan ci gaban da aka samu a fannin makamashin nukiliya, da hasarar da aka samu...
    Rahotannin daga Gaza na cewa Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a yankin Falasdinawa, a daidai lokacin da wakilan kungiyar da kuma masu shiga tsakani ke tattaunawa a Masar. Tankunan yaki da jiragen sama da jiragen ruwa na Isra’ila sun yi luguden wuta a wasu sassa na Gaza a ranar Talata. A cewar tashar Aljazeera, Hamas ta nunar da cewa ci gaba da kai hare-haren bama-bamai da Isra’ila ke yi a zirin Gaza, wani cikas ne ga sako mutanen da aka yi garkuwa da su. Qatar mai shiga tsakani a yakin Gaza, ta bayyana cewa, kamata ya yi Isra’ila ta dakatar da ayyukan soji a yankin Falasdinun, kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ya tsara, idan dai har ikirarin...
    Uche Nnaji, Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, ya yi murabus daga mukaminsa. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Talata. Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Jerin ministocin da zargin takardun bogi ya tabaibaye su Nnaji na fuskantar zarge-zarge kan sahihancin takardun karatunsa, inda binciken da jaridar Premium Times ta gudanar ya gano cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ta ce ba ta ba shi takardar kammala digiri ba. A cewar jami’ar, tsohon Ministan bai kammala karatunsa a cikinta ba, kuma ba ta taɓa ba shi takardar shaidar kammala ta ba. A cewar jaridar, Simon U. Ortuanya, Shugaban Jami’ar UNN, ya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A zamanin nan, ana alakanta almajirai da bara – hasali ma a lokuta da dama akan yi amfani da kalmar “almajiri” idan ana nufin mabaraci. Amma a da ba haka lamarin yake ba – almajiri baya bukatar yin bara ko roko kafin ya sami na sakawa a bakin salati. NAJERIYA A YAU: Tasirin Takardun Shaida Na Bogi Ga Rayuwar Al’umma DAGA LARABA: Tasirin Bambance-bambance Tsakanin ‘Yan Najeriya Shekara 65 Da Samun ‘Yancin Kai Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan yadda almajirci ya sauya salo a wannan zamani da ma irin halin da almajirai suka tsinci kan su a ciki. Domin sauke shirin, latsa nan
    Shugaban ofishin jagoran juyin musulunci na Iran, Hujjatul Islam Wal Muslimina Muhammad Gulpayagani ya bayyana yunkurin nan na: Goyon Bayan Iran.” Da cewa, aikin da suke yi yana a karkashin amsa kiran jagoran juyi ne wanda ya yi kira da a taimakawa waddanda su ka cutu daga hare-haren HKI. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto Hujjatul-Islam Muhammad Gulpayagani yana bayyana muhimmin matakin da Ayatullah Khamnei yake dauka a fagen gwgawarmaya, yana mai kara da cewa; Shi ne wanda yake dauke da tutar gwgawarmaya akan wannan tafarkin cikin dogara da Allah madaukakin sarki da tafiya akan tafarkin Ahlul Bayti ( a.s). Hujjatul-Islam golpayagani ya ambaci wasu ayyukan da yukurin na Iran take yi wajen taimakawa wadanda su ka cutu daga hare-haren...
    ShareTweetSendShare CGTN Hausa and Sulaiman Related Daga Birnin SinHabakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu    22 hours agoDaga Birnin SinKaramin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas Ya Yi Bikin Bunkasa Al’adu Na Bikin Tsakiyar Kaka 23 hours agoDaga Birnin SinNazari Ya Gano Falalen Dutse Na Yanki Mai Nisa A Duniyar Wata Ya Fi Tsananin Sanyi Fiye Da Na Yanki Na Kusa 24 hours ago
      Shugaban Kwamitin Amintattu na Ƙungiyar Tuntuba ta Arewa, Alhaji Bashir M. Dalhatu, Wazirin Dutse, ya yi kira ga mambobin ƙungiyar da su ƙara haɓaka ɗa’a, bin ƙa’ida da ƙulla zumunci yayin da ƙungiyar ke shirin gudanar da bikin cika shekaru 25 da kafuwa a watan Nuwamba 2025.   Yayin jawabin sa a taron Kwamitin Amintattu da aka gudanar a ofishin ƙungiyar dake Kaduna, Alhaji Dalhatu ya jaddada muhimmancin zama masu daidaito da kulawa a cikin bayanan da jami’an ƙungiyar ke yi wa kafafen yaɗa labarai.   Ya bayyana cewa taron da ya samu halartar shugabanni da sakatarorin jihohi da mambobin ƙungiyar Arewa 100% Focus Group, zai tattauna kan batutuwa biyu — yadda jami’an ƙungiyar Tuntuba ta Arewa za su...
    Hukumar kula da yan gudun hijirar a majalisar dinkin duniya ta jinjinawa kasar Iran game da kokarin da tayi wajen kulawa da miliyoyin yan gudun hijira kasar Afghanistan , da suka zauna a kasar na tsawon shekaru, Babban darakta na hukumar ta IOM shi ne yayi wannan bayani ga Mohammad Batgae mtaimakin ministan harkokin cikin gidan kasar iran a birnin janeva a jiya litinin, a wani taro da suka gudanar a bayan babban taron Majalisar dinkin duniya karo na 76 da hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya take gudanarwa. Ana sa bangaren bathaei babban jami’I na kasar Iran ya bayyan yadda jamhuriyar musulunci suka bada kula ta musamman  ga dubban yan gudun hijiran kasar ta Afghanistan...
    Irabor ya ƙara da cewa dole ne gwamnati ta bi hanyoyi daban-daban wajen magance matsalar tsaro, ba ta hanyar amfani da sojoji kaɗai ba.Ya ce ya kamata a samar da manufofi masu inganci da za su rage talauci, rashin aiki da yawan yara marasa zuwa makaranta.“Idan muka rage yara marasa zuwa makaranta da kuma marasa aikin yi, za mu rage yawan mutanen da ‘yan ta’adda ke iya ɗauka aiki,” in ji shi.Ya kuma gargaɗi ‘yan siyasa da su daina sa siyasa a batun harkar tsaro.A ranar bikin cikar Nijeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa dakarun Nijeriya suna samun nasara a yaƙi da ta’addanci da garkuwa da mutane, amma jam’iyyun adawa sun ce matsalar...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sake rage kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026 nan take, kuma ta fitar da sabon farashin cikin kwana biyu. Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan hukumar ta sanar da rafin kimanin N200,000 a kan farashin da maniyyata suka biya a bara. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya isar da umarnin shugaban kasa yayin wani taro da ya yi da shugabanni da mambobin hukumar NAHCON a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a ranar Litinin. Shettima ya buƙaci a samu hadin kai tsakanin jami’an jihohi da na tarayya, ciki har da gwamnoni, wajen fitar sabon farashin da ya dace da yanayin tattalin arzikin ƙasar. An fara...
      Manufofin da aka tsara sun karfafa kashe kudi. Kafin wannan hutu, gwamnatin tsakiya ta ware yuan biliyan 69 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 9.7 a matsayin lamuni na musamman don tallafa wa hada-hadar kayayyakin masarufi, wanda hakan ya kai ga jimillar abin da ake warewa a shekara ta kai yuan biliyan 300. Daga watan Janairu zuwa na Agusta, shirye-shiryen ba da tallafi na hada-hadar kasuwanci sun jawo hankulan masu nema miliyan 330, wanda hakan ya haifar da cinikin sama da yuan tiriliyan 2. (Abdulrazaq Yahuza Jere)     ShareTweetSendShare Sulaiman Related Daga Birnin Sin Karamin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas Ya Yi Bikin Bunkasa Al’adu Na Bikin Tsakiyar Kaka 1 hour ago Daga Birnin...
    Kwamandan Kare Juyin Juya Halin Musulunci ya jaddada cewa: Duk wani motsi na abokan gaba daga teku ko tsibirai zai gamu da martani mai tsanani A yayin da yake duba shirye-shiryen yaki a tsibiran Tekun Pasha, babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), Manjo Janar Mohammad Pakpour, ya jaddada cewa: Duk wani mataki da makiya za su dauka a teku ko a tsibiran, za su fuskanci kwakkwaran martani daga rundunar sojojin Ruwan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta IRGC. Babban kwamandan rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta IRGC, Manjo Janar Mohammad Pakpour, ya duba shirye-shiryen da ake yi na yaki da rundunonin yaki a tsibirin Tekun Fasha. Manjo Janar Pakpour ya jaddada cewa: “Sun shirya tsaf...
    Firaministan ƙasar Faransa, Sebastien Lecornu, ya yi murabus daga muƙaminsa kwana guda bayan ya kafa gwamnatinsa. Fira Minista Sebastien Lecournu ya sanar da ajiye mukaminsa ne a safiyar Litinin ɗin nan bayan ya yi wata da Shugaba Emmanuel Macron. Ya yi murabus ne washegarin da ya kafa majalisar ministocinsa domin tafiyar da gwamnati, kuma ƙasa da wata guda bayan Shugaba Macron ya naɗa shi a kujerar. A jiya  Lahadi ne ya sanar da sunayen mambobin sabuwar majalisar ministocinsa inda ya naɗa sabbin muƙamai, amma ya bar wasu da dama a kan kujerunsu, lamarin da bai yi wa ’yan adawa daɗi ba. Zargin takardun bogi: Jami’ar Nsukka ba ta taɓa ba ni takardar digiri ba — Minista ’Yan bindiga sun kashe...
    Kwamandan dakarun kare juyin juya hali na kasar Iran (IRGC) Manjo Janar Mohammad Pakpour ya yi rangadi a sananonin sojin ruwa na kasa Iran  da ke yankin Gulf, inda ya yi duba  shirye-shiryen da suke yi na tunkarar kowace irin barazana daga waje a kan kasar. Da yake jawabi ga sojojin ruwa na kasar ta Iran a yayin wannan rangadi,  kwamandan na IRGC ya bayyana cewa, kamar yadda sojojin ruwa suka taka rawar gani wajen tunkarar shishigi na makiya a lokacin yakin kwanaki 12, har yanzu ma suna a cikin Shirin ko ta kwana domin mayar da martani da dukkan karfinsu a kan duk wani aikin wuc gona iri a kan kasar. Janar Pakpour ya kuma duba hotuna na jiragen...
    Iran ta sanar cewa tana goyon bayan “duk wani shiri” da zai ba da damar samar da ‘yancin kai ga al’ummar Falasdinu, gabanin tattaunawa da ake shirin farawa a Masar tsakanin Isra’ila da Hamas da nufin kawo karshen yakin zirin Gaza. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, iran ta ce “a ko da yaushe tana goyon bayan duk wani yunkuri na kawo karshen laifukan yaki, da cin zarafin bil’adama a Gaza da duk wani yunkuri na share fagen tabbatar da ‘yancin kai na al’ummar Palasdinu.” Sanarwar ta ce, tilas ne yanke duk wata shawara kan tsagaita bude wuta ko sasantawa ta siyasa ta rataya a wuyan Falasdinawa da kansu. Tehran ta ce tana maraba da...
    Gidauniyar Nelson Mandela ta yi Allah wadai da Isra’ila kan dalike duk wani yunkuri na ‘yan fafatuka dake kokorain shigar da kayan agajin jin kai zuwa Gaza.   Gidauniyar ta ce ba zai yuwu a yi shiru ba dangane da dakile ayyukan jin kai a Gaza da kuma tsare wadanda ta kira “masu kare mutuncin bil’adama.” A cikin wata sanarwa da Gidauniyar ta fitar, ta yi kakkausar suka kan katsalandan da Isra’ila ta yi wa jirgin ruwa na Sumud Global Flotilla dake shirin shiga Gaza domin aikin jin kai. Daga bisani gidauniyar wacce kungiya ce mai zaman kanta ta Afirka ta Kudu da aka kafa domin ci gaba da dawwamar da tafarkin shugaban kasar bakar fata na farko a Afirka...
    Bisa labarin da ma’aikatar kula da harkokin sufuri ta kasar Sin ta bayar, a ranar 4 ga wannan wata, yawan mutanen da suka yi zirga-zirga a kasar Sin ya kai miliyan 301 da dubu 291 da dari 1, wanda ya karu da kashi 6.1 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Yawan mutanen da suka yi zirga-zirga a rabin farko na hutun bikin kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin PRC da bikin Zhongqiu ya kai matsayin koli a tarihi, wato ya kai biliyan 1 da miliyan 243, wannan ya shaida cewa, an fi yin zirga-zirga a lokacin hutun.   Game da hanyoyin zirga-zirga a lokacin wannan hutu, an fi zabar hanyoyin mota. Game da yankunan da aka fi sha’awar ziyarta, an...
    A karon farko a tarihin kwallon raga ta mata ta Iran ta zami lashe kofin zakarun Asiya, bayan samun galaba akan kawarta ta kasar Uzbakestan. An fara wasan fidda gwani a tsakanin kungiyoyin kwallon raga na mata na Asiya a ranar 2 ga watan nan na Oktoba, a birnin Tashqand wanda ya zo karshe a yau Lahadi da samun galabar Iran. Tun da fari kungiyar kwallon ragar ta Iran ta sami nasarori har sau uku a jere, da a karshe ta kai ga samun nasara akan mai masaukin baki kasar Uzbakestan. Mai bayar da horo ga ‘yan wasan Li Du Hi, ta bayyana jin dadinsa da nasarar da su ka samu, musamman saboda wannan ne karon farko aka sami wannan...
    Wasu da ake zargin ’yan fashin daji ne sun kashe ɗaya daga cikin kwamandojin maharba a yankin Gangara da ke Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna. Lamarin ya faru ne a yau Asabar, 4 ga watan Oktoba, 2025, inda aka tabbatar da mutuwar Malam Kabiru, wanda yake ɗaya daga cikin kwamandojin ƙungiyar maharba ta ƙasa, reshen Giwa. Hukuma ta fara binciken Ganduje kan zargin karkatar da N4bn a Kano An yi wata gagarumar zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Turai Rahoto ya bayyana cewa Malam Kabiru ya rasu ne yayin aikin ceto wasu mutane da ’yan fashi suka sace daga yankin Danja na Jihar Katsina. Shugaban ƙungiyar maharba ta ƙasa, Kwamanda Usman Taju, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, jim kaɗan...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki. Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta da aminci a Najeriya. Wike ya gana da Fubara da dattawan Ribas kafin kafa sabuwar majalisar zartarwa Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki Uwargidan gwamnan, wacce Asi Akiba, matar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kalaba, Kalaba ta Kudu da Odukpani ta wakilta, ta ce hayaƙin itacen girki da sauran hanyoyin da ba su da inganci sun zama hanyar mutuwa ta...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki. Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta da aminci a Najeriya. Wike ya gana da Fubara da dattawan Ribas kafin kafa sabuwar majalisar zartarwa Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki Uwargidan gwamnan, wacce Asi Akiba, matar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kalaba, Kalaba ta Kudu da Odukpani ta wakilta, ta ce hayaƙin itacen girki da sauran hanyoyin da ba su da inganci sun zama hanyar mutuwa ta...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki. Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta da aminci a Najeriya. Wike ya gana da Fubara da dattawan Ribas kafin kafa sabuwar majalisar zartarwa Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki Uwargidan gwamnan, wacce Asi Akiba, matar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kalaba, Kalaba ta Kudu da Odukpani ta wakilta, ta ce hayaƙin itacen girki da sauran hanyoyin da ba su da inganci sun zama hanyar mutuwa ta...
    Sanata Mohammed Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, ya yaba wa Gwamna Babagana Zulum da Sojojin Operation Hadin Kai bisa gaggawar da suka nuna wajen ziyartar garin Kirawa bayan hare-haren da Boko Haram ta kai, wanda ya yi sanadin mutuwa da ƙone gidaje da fadar dagaci. Sanatan ya bayyana cewa harin ya tilasta wa mazauna da dama guduwa zuwa ƙasar Kamaru. A wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri ranar Lahadi, Ndume ya gode wa gwamnan bisa alƙawarin tura Sojoji domin kare garin da kuma amincewa da gina asibiti, da rijiyoyi, da wasu muhimman ayyukan raya ƙasa a yankin. Ya ce irin waɗannan matakai za su taimaka wajen dawo da ƙwarin gwuiwar jama’a. Zulum Ya Rabawa Talakawan Dikwa  Tallafin...
    Dubun dubatar mutane ne suka fito zanga-zanga jiya Asabar a sassan wasu ƙasashen Turai domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa, tare da kiran a kawo ƙarshen yaƙin Gaza. Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun kuma buƙaci a saki masu fafutuka da ke cikin ayarin jiragen ruwan nan da ke hanyar kai kayan agaji ga Falasɗinawa a Gaza. Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki Fitaccen ɗan jarida a Kano, Aliyu Abubakar Getso ya rasu ’Yan sanda a birnin Rome na Italiya sun ce kimanin mutane dubu 250 ne suka fito zanga-zanga a rana ta huɗu a jere, bayan da Isra’ila ta kama ayarin jiragen ruwa 45 da ke ƙoƙarin isa Gaza domin kai wa al’umma agaji...
    Iran ta yi kira ga kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da ta dauki matakin haramtawa Isra’ila shiga harkokin wasanni na kasa da kasa. A cikin wata wasika da ya aike zuwa ga ministocin harkokin wasanni na kasashe 57 na kungiyar ta OIC, ministan wasanni da matasa na kasar Iran Ahmad Donyamali ya bukaci takwarorinsa da su hada karfi da karfe wajen ganin an kawar da Isra’ila daga wasannin kasa da kasa. Mista Donyamali ya yi kira da a kafa kungiyar wasanni ta kasashen musulmi domin neman kwamitin Olympics na kasa da kasa (IOC) ya dakatar da gwamnatin Isra’ila a gasar wasannin duniya. A cikin wasikar tasa, ya jaddada cewa gwamnatin Isra’ila ta keta yarjejeniya wassanin Olympics da duk...
    Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Fu Cong ya wakilci kasashe masu ra’ayoyi kusan iri daya wajen yin jawabi kan takunkumin da aka saka daga bangare daya, a gun kwamiti na uku na babban taron MDD cewa, a yayin da aka cika shekaru 80 da kafuwar MDD, tilas ne kasa da kasa su maida hankali da kara yin hadin gwiwa don kin amincewa da wannan takunkumi da ake kakabawa ba bisa doka ba. Fu Cong ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana samun ra’ayin bangare daya da ka’idar mai karfi ya samu fifiko a duniya, sannan ana samun takunkumin da aka saka daga bangare daya. Kasashe masu tasowa da jama’arsu suna fama da takunkumin, wanda ya saba wa daidaiton...
    Hukumar sararin samaniya ta kasar Iran ta bada sanarwan shirin cilla tauraron dan’adam a cibiyar cilla taurarin dan’adam na Chabahar tare da amfani da sandarerren makamashi. Kamfanin ndillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban hukumar Hassan Salarieh yana fadar haka a yau Asabar ya kuma kara da cewa, an kammala bangare na farko na cibiyar cilla taurarin yan’adam na Chabahar kuma hukumar ta fara shirin amfani da sandarerren makamashi don cillan taurarin yan’adam da suke gabanta, wadanda a shirye suke a cillasu. Salarieh y ace a halin yanzu akwai tauraron dan Adam mai suna Pars-2 da ke jiran  cillawa, sannan hukumar zata ci gaba da aiki a bangare na 2 na cibiyar don kammala aikin cibiyar cilla tararin...
    Shugaban cibiyar fasaha da kere-kere ta Pardis a nan Tehran ya bada sanarwan cewa, wakilai daga kasashe 65 ne suka bayyana anniyarsu ta halattan gasar fasahar kere-kere ta shekara ta 2025 a cibiyarsa. Kamfanin dilancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Mehdi Saffaari –Nio yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa gasar ta dai-dai kun mutane, wadanda zasu gwada korewarsu da kuma fasahar da suke da ita a gasar wacce za’a gudanar daga ranar 27-30 ga watan Octoba damukeciki a nan Tehran. A taron yan jaridun da ya kira don bada wannan sanarwan Mehdi Safaari-nio ya ce mafi yawan mahallata gasar matasa ne musamman daliban makarantu wadanda suke son gwada korewarsu da kumailminsu.  Kuma a...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ƙaddamar da shirin tallafa wa mata 1,400 da kayan sana’ar ɗinkin hula domin bunƙasa harkokin kasuwancinsu. A wajen bikin raba kayan, Gwamna Namadi ya ce ɗinkin hula tsohuwar sana’a ce da mata suka gad tun daga iyaye da kakanni, wadda ke taimaka musu wajen dogaro da kai da kuma kula da iyalansu. ’Yan sanda sun bindige Lakurawa 3 har lahira a Kebbi Dalilin da ya sa na tsere Kamaru bayan Boko Haram ta ƙone fadata a Borno — Basarake Waɗanda suka ci gajiyar wannan shiri na farko, sun fito daga ƙananan hukumomi bakwai na masarautar Dutse, waɗanda suka haɗa da Dutse, Kyawa, Birnin Kudu, Buji, Gwaram, Jahun da Miga. Gwamnan ya ce da...
    Ana ta rade-radin an baki sarauta, shin mene ne gaskiyar maganar? Alhamdulillah, maganar an bawa Zahra’u sarauta ba karya ba ne, hakkun haka ne an ba ni sarauta.   Mutane za su so su ji, shin daman Haj. Zahra’u ‘yar Ghana ce, tana da sarauta a Ghana? A’a! Ni ba ‘yar Ghana ba ce, ba abin da na hada da Ghana, sai dai so da yarda, saboda ma’abota kallon finafinan hausa ne. Ni kuma ina cikin wannan masana’anta ta finafinan hausa, musamman Dadin Kowa na Arewa24. Alhamdulillah Arewa24 ta sa sunanmu ya tafi a duniya. Ta yi mana riga ta yi mana wando babu abin da ba ta yi mana ba, domin dalilin fuskanmu da ta tafi ake kaunar mu...
    Shugaban Amurka ya ce: Dole ne gwamnatin mamayar Isra’ila ta daina kai hare-hare kan Gaza nan take domin samun damar sakin fursunoninta Shugaban Amurka Donald Donald Trump, bayan da kungiyar Hamas ta fitar da martanin kan yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza, ya yi kira ga gwamnatin mamayar Isra’ila da ta gaggauta dakatar da kai hare-hare a zirin Gaza. Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a daren Juma’a da ta dakatar da harin bam da take kaiwa Gaza, yana mai cewa; “Dole ne gwamnatin mamayar Isra’ila ta gaggauta dakatar da kai hare-hare a zirin Gaza domin a samu damar zakulo mutanen da aka yi garkuwa da su cikin aminci da gaggawa.” Da yake mayar da...
    Babban jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Mika fursunoni da gawarwaki cikin sa’o’i 72 ba gaskiya ba ne a halin da ake ciki yanzu. Babban jami’in kungiyar Hamas Musa Abu Marzouk ya tabbatar a ranar Juma’a cewa, batun mika fursunoni da gawarwakin yahudawan sahayoniyya cikin sa’o’i 72 lamari ne na nazari, ba tabbas ba, a halin da ake ciki yanzu.” Abu Marzouk ya bayyana cewa: Kungiyar Hamas ta amince da shirin Amurka da aka gabatar “a bisa ka’ida,” yana mai cewa “aiwatar da shi yana bukatar tattaunawa.” Ya kuma lura da cewa dukkan bayanai da suka shafi rundunar wanzar da zaman lafiya “yana bukatar fahimtar juna da fayyace shi dalla-dalla.” Dangane da batun makamai kuwa, Abu Marzouk ya bayyana a...
    ’Yan bindigar da ke addabar yankunan karkara sun kaƙaba sun ƙaƙaba musu haraji da ke kaiwa Naira miliyan 10 a Ƙaramar Hukumar Mashegu Jihar Neja. Rahotanni sun nuna cewa an umarci al’ummomin yankunan Babban Rami da Kaboji su su biya Naira miliyan biyu-biyu. Yankin Sabon Rijiya da Sabon Rami an umarce su da su Naira dubu 500, yayin da aka umarci ƙauyukan da ke kusa da Dajin Keji su tara Naira miliyan 10 gaba ɗaya. Haka nan, ana ƙaƙaba wa al’ummar Khizi an kaƙaba musu harajin Naira miliyan shida, da wa’adin ranar Juma’a, 3 ga Oktoba, 2025. Wata mata ta banka wa kanta wuta a Bauchi Sharri Jonathan ke wa Buhari don lashe zaɓen 2027 —Garba Shehu Wani mazaunin yankin...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Kasuwar Dutse Ultra-Modern Market, inda ya cika alkawarin gwamnatinsa na samar da tsaftataccen makamashi ga ‘yan kasuwa a jihar Jigawa.   Aikin wanda Hukumar Samar da Tattalin Arzikin Kasa da Samar da ayyukan yi ta Jihar Jigawa ta gudanar, ya hada shaguna 300 da wutar lantarki daga na’urorin hasken rana da aka sanya a cikin kasuwar, inda kowane shago kuma an saka masa fanka amfani da hasken rana kyauta.   Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da kasuwar a hukumance, Malam Umar Namadi ya ce shirin zai saukaka harkokin kasuwanci, da rage kashe kudi, da kuma bunkasa ribar ‘yan kasuwa.    ...
    Bincike ya kuma kai ga cafke wani bangare na kungiyar karkashin jagorancin Babangida, wadanda aka gano sun hada da Isah Musa da Usman Abdullahi, wadanda suka amsa laifin karya shaguna da kuma yin fashi a yankin Rigasa. Lokacin bincike, wadanda ake zargin sun ambaci masu karbar kayan sata da suka taimaka musu wajen sayar da su. Wannan ya kai ga cafke Kabiru Sabitu, wanda aka fi sani da Baban Godiya, Abdullahi Shehu da Yusuf Saleh. Haka kuma, a ranar 10 ga Satumba, an kama wani mai suna Bello bisa zargin satar waya. Kamen nasa ya kai ga kwato wayoyi hannu 45 da kwamfutar tafi-da-gidanka, tare da kama masu karbar kayan sata nasa. A wani nasara daban, a ranar 15 ga...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadin cewa amincewa da takunkuman da kasashen yamma suka kakaba wa Iran ba bisa ka’ida ba ya sabawa dokokin kasa da kasa, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su bijirewa haramtattun takunkuman. Jakadan Iran a Colombo Alireza Delkhosh ya bayyana cewa, gargadin na ministan harkokin wajen kasar na kunshe ne a cikin wasikun da ya aike wa takwarorinsa na Sri Lanka da Maldives. Araghchi ya yi kira ga takwarorinsa na kasashen da su dau mataki mai tsanani kan takunkumin da Amurka da kasashen yammacin Turai suka kakaba iran, bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar a ranar 28 ga watan Satumba sake dawo da takunkuman da aka kakaba wa Iran,...
    Kasashen duniya na ci gaba da yin Allah wadai da farmakin da Isra’ila ke ci gaba da kai wa kan jiragen ruwan ‘yan fafatuka dake dauke da kayan agaji ga al’ummar Gaza. Hamas ma ta yi Allah wadai da farmakin kan Global Sumud Flotilla a iyaka da Gaza wanda ta danganta a matsayin “laifi na fashin teku da ta’addanci kan fararen hula”, tana mai kira ga “dukkan masu kare ‘yanci a duniya” da su yi Allah wadai da harin. Kungiyar Jihad Islamic ta Falasdinu ta fitar da irin wannan sanarwa, inda ta bayyana harin a matsayin ” fashin teku da kuma keta yarjejeniyar kasa da kasa da kuma na jin kai”, Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya nemi...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Jihar Legas zuwa Jos, babban birnin Jihar Filato, a ranar Asabar, 4 ga watan Oktoba, domin halartar jana’izar Nana Lydia Yilwatda Goshwe, mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nantewe Yilwatda Goshwe. Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Shugaban Ƙasa zai kuma gana da shugabannin coci daga Arewacin Najeriya a hedikwatar COCIN da ke Jos. Ya ƙara da cewa Tinubu zai koma Legas a ranar bayan kammala ziyarar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai tashi daga Legas zuwa Jos, Babban Birnin Jihar Filato, a ranar Asabar domin halartar jana’izar mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nantewe Yilwatda Goshwe. Zai halarci jana’izar Nana Lydia Yilwatda Goshwe, mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa. Ana fargabar mutuwar mutane a gobarar tankar mai Boko Haram ta wuce yadda mutane ke tsammani — Jonathan Bayo Onanuga, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, ya ce Shugaban Ƙasa zai kuma gana da shugabannin coci daga Arewacin Najeriya a Jos. Ana sa ran Tinubu zai koma Legas a ranar bayan kammala ziyarar. A gefe guda kuma, Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Jihar Filato ta sanar da taƙaita zirga-zirgar ababen hawa a...
    A kan zaben 2027, Abdullahi ya ce ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar sun yarda za su goyi bayan duk wanda ya lashe zaben fid da gwani. “Dukkan ‘yan takarar shugaban kasarmu sun yarda za su goyi bayan wanda ya ci zaben fid da gwani da jam’iyyar za ta gudanar,” in ji shi. Ya kara bayyana cewa nan gaba kadan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar zai sanar da ranakun zaben fid da gwani a Osun da Ekiti kafin zaben gwamna a kowace jiha. Wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban jam’iyyar na kasa, Dabid Mark da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da sakataren jam’iyyar na kasa, Ogbeni Rauf da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai da tsohon gwamnan...
    Bisa labarin da ma’aikatar harkokin albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayar a kwanakin baya, ana sa ran cewa, fadin sabbin gonakin da za a shawo kan matsalar zaizayewar kasa a Sin a karshen shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14 ya kai muraba’in kilomita dubu 340, fadin gonakin da aka tabbatar da yanayin ruwa da kasar da ke cikinsu ya kai kashi 73 cikin dari. Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana cewa, a yayin gudanar da shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14, an kiyaye kyautata yanayin zaizayewar kasa a kasar Sin, kuma an cimma burin rage fadin gonakin da suka gamu da matsalar, da kuma rage illar da ruwa da iska suka haddasa wa gonaki....
    Bayanan sun bayyana cewa; “Jimillar makarantu 228 suka ci gajiyar shirin, inda kimanin dalibai 829,423 suka nema. Ya zuwa yanzu kuma, dalibai 510,378 ne suka samu wannan tallafi na bayar da rance. “Zuwa 10 ga watan Satumba, an biya kimanin Naira 53,801,717,293.00 a matsayin kudaden makaranta na daliban, yayin kuma da aka biya Naira 45,751,360,000.00 a matsayin alawus-alawus na daliban. Idan aka tattara kudaden baki-daya, jimillarsu ta kama Naira 99,553,077,293.00,” a cewar rahoton. Duk da nasarar da aka samu a fadin kasar, shirin ya fuskanci kalubale wajen ganin an yi adalci a rabon a dukkanin shiyoyin fadin kasar guda shida da ake da su. Alkaluman da LEADERSHIP ta tattara a watan Mayun 2025, sun nuna dimbin gibin da ke tsakanin...
    Sojin Isra’ila sun kame dukkan jerin jiragen ruwa masu dauke da kayan agaji da ke ƙoƙarin shiga Zirin Gaza, inda suka kama daruruwan masu kai agajin tare da ɗaruruwan jiragen. Bidiyon da ken una tafiyar jiragen kai tsaye ya nuna yadda sojojin Isra’ila suka kutsa cikin jirgin ƙarshe da safiyar Juma’a. Fashewar tukunyar gas ya haddasa gobara a jami’ar Gombe An naɗa Remi Tinubu Sarauniyar Yaƙin Akko Jirgin Marinette mai tutar ƙasar Poland, wanda ke da ma’aikata shida, shi ne jirgin ƙarshe daga jerin Global Sumud Flotilla, wanda a baya ya ƙunshi jirage 44, da Isra’ila ta kama. Kwamitin Ƙasa da Ƙasa na Ƙoƙarin Karya Takunkumin Gaza ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa wasu daga cikin waɗanda aka kama...
    Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya ziyarci Oke Ode da ke karamar hukumar Ifelodun domin jajanta wa al’umma da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu sakamakon hare-haren da masu garkuwa da mutane suka kai kwanan nan.   A cikin sanarwar gwamna AbdulRazaq ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu.   Ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi, sannan kuma ya baiwa al’umma tabbacin dawo da zaman lafiya cikin kankanin lokaci.   Sanarwar ta kuma aike da sakon ta’aziyya da jaje ga daukacin al’ummomin da aka samu cikin wannan rikici — daga Ifelodun zuwa Irepodun, Isin, Ekiti, Edu, da Patigi.   A cewarsa ana tanadin komai don rage illar hare-haren da kuma tabbatar da kawo...
    Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce ta ware naira biliyan biyu domin biyan kudaden tallafin karatu da alawus alawus na guraben karatu a jihar.   Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da biyan alawus-alawus na shekarar 2023/2024 da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta karamar hukumar Akwanga ta jihar.   Gwamnan a lokacin da yake kaddamar da shirin raba kudaden ya jaddada cewa baya ga biyan kudaden NECO, gwamnatin jihar tana biyan dalibai sama da 155 tallafin karatu na kasashen waje da sama da dalibai 30,000 a fadin kasar nan.     Shima da yake nasa jawabin, kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Dokta Danladi Jatau wanda shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ilimi Mista Abel Yakubu Bala...
    Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ofishin Kano, ta gudanar da wani taron kara wa masu yi wa kasa hidima na NYSC aiki a karkashin Hukumar Ba da Agajin Gaggawa (EMVs).   An zabo mahalarta taron ne daga kungiyoyin ci gaban al’umma (CDS) a kananan hukumomin Tarauni da Dawakin Kudu Kano.   An tsara horon don ƙarfafa ilimin membobin ƙungiyar a matsayin wakilai na gaba na rage haɗarin bala’i da amincin al’umma.   Da yake jawabi a lokacin bada horon, shugaban ayyuka na hukumar NEMA Kano reshen jihar Jigawa, Dakta Nura Abdullahi, ya bukaci jami’an tsaro da su ci gaba da jajircewa wajen ci gaba da koyo.   Mahalarta taron sun nuna haɗin kai mai ƙarfi a duk...
    “Muna tabbatar da inganta tsarin na PCS domin a kara tabbatar da karfafa gasa a fadin diniya a fannin na sufurin Jiragen Ruwa na NPA wanda hakan zai kuma kara samar da damar janyo masu zuba hannun jari daga waje na kai tsaye da kuma kara karfafa tattalin arzikin kasar, a nan gaba,”. A cewarsa, za mu ci gaba da kulla hadaka domin mu cimma burin da aka sanya a gaba, na kara inganta ayyukan Hukumar ta NPA. Ya ci gaba da cewa, a rabin zangon farko na shekarar 2025, ingancin da aka samar a bangarorin Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar sun bayar da gudunmawar da ta karu, zuwa kaso 19.6 a fannin fitar da kaya waje, da ba su shafi...
    Sule ya bayyana cewa, “ilimi shi ne abu mafi mahimmanci da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali akai, hakan ne ya sa aka ware kashi 36 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar na shekarar 2025 ga sashen ilimi”.   Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta dawo da tallafin karatu na ƙasashen waje, inda a halin yanzu take ɗaukar nauyin ɗalibai 155 da ke karatu a fannoni daban-daban a ƙasashe daban-daban na duniya.   Ya ƙara bayyana cewa, gwamnatin jihar na ɗaukar nauyin ɗaliban jinya da kuma wasu a jami’o’i daban-daban a faɗin ƙasar.   “Mun kuma biya kuɗin rajistar jarabawar kammala sakandire ta kasa (NECO) ta shekarar 2025 ga ɗalibai sama da 24,000 na makarantun sakandare na gwamnati, domin...
    Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane a Nijeriya (NAPTIP) ta ce ta kama wani mahaifi yana yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi. Mai magana da yawun hukumar NAPTIP na ƙasa, Vincent Adekoye, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Babu wanda na cewa zan janyewa takara a 2027 — Atiku An kama masu kai wa ’yan bindiga makamai da ƙwayoyi Sanarwar ta ce mahaifin na daga cikin aƙalla mutum biyar da ake zargi da safarar mutane waɗanda aka cafke a filin jiragen saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja. TRT ya ruwaito Adekoye na cewa an kuɓutar da mutum 24 a yayin aikin bisa jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello wanda...
    A nasa jawabin, gwamnan ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tsige CP Bakori, yana mai nuni da rashin halartar rundunar ‘yansanda daga faretin bikin a matsayin rashin mutuntawa da tsoma baki cikin siyasa.   Sai dai ga dukkan alamu, kalaman gwamnan sun janyo rashin amincewar jama’a musamman a tsakanin matasan Kano. Zanga-zangar ta ranar Alhamis ta kasance cikin kwanciyar hankali da bin doka da oda, inda masu zanga-zangar ke jaddada muradin su na CP Bakori ya ci gaba da rike mukaminsa da kuma ci gaba da aikinsa ba tare da cikas na siyasa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....