2025-09-18@04:19:44 GMT
إجمالي نتائج البحث: 349
«wannan shekarar»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Tashar talabijin din Aljazira ta bayar da rahoton da yake cewa; Rashin abinci mai gina jiki da karewar madarar jarirai a yankin Gaza, ya sa jarirai biyu sun yi shahada. Majiyar asibitin Nasar ta a birnin Khan –Yunus dake kudancin Gaza, ta ambaci cewa jariran biyu sun rasa ransu ne saboda rashin abinci mai gina jiki da kuma madarar jarirai.
Kwanan baya, jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Cing-te, ya fitar da wani bayani a fili, inda a ciki ya canja asalin tarihin kasar Sin, kana ya musanta cewa yankin Taiwan wani yanki ne na kasar Sin tun da da can, kuma, ya kauce wa yin tsokaci kan jerin takardun dokoki na kasashen duniya, wadanda suka bayyana yankin Taiwan a matsayin wani yanki na kasar Sin bayan yakin duniya na biyu. Kazalika, ya kalubalanci kuduri mai lamba 2758 na babban taron MDD da dokokin kasashen duniya. Babu shakka, abin da Lai Cing-te ya yi ya sa ya zama abokin gaban dukkan al’ummomin kasar Sin, da yawansu ya zarce biliyan 1 da miliyan 400, kana ya mai da shi kansa...
Ofishin kula da aikin harba kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ba da labari cewa, jiya Alhamis da karfe 9 da mintuna 29 na dare agogon Beijing, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20, wato Chen Dong da Chen Zhongrui da Wang Jie sun cimma nasarar fitowa daga akwatin gwaji na Wentian, yin tattaki a waje na tsawon sa’o’i 6.5, da kuma komawa akwatin, bisa taimakon na’urori masu hannun injin dake tashar sararin samaniya da jagorancin masu nazarin kimiyya da fasaha dake doron kasa. Yayin da suke aiki a waje, Chen Dong da Chen Zhongrui sun cimma nasarar hada na’urorin kiyaye tashar sararin samaniya daga sassan wasu na’urorin da aka daddasa a sararin samaniya, da binciken na’urorin dake waje...
Gwamnatin Kano ta ayyana gobe Alhamis, 26 ga watan Yunin 2025, a matsayin hutun rana daya na sabuwar shekarar musulunci ta 1447. Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da ofishin shugaban ma’aikatan Kano ya fitar a yammacin wannan Larabar. Gwamnatin Gombe za ta biya ’yan fansho Naira biliyan 6.6 kuɗin ritaya Arsenal za ta ɗauki ɗan ƙwallon Brentford Christian Norgaard Sanarwar wadda babban sakatare a ofishin shugaban ma’aikatan, Ashiru Abdullahi ya fitar, ta bukaci ma’aikatan jihar da su yi amfani da wannan dama domin yi wa jihar da kuma kasa baki ɗaya addu’ar zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa. Aminiya ta ruwaito Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, a jiya Talata yana ba da umarnin fara duban watan Muharram na...
Gwamnatin Jihar Gombe ta amince da fitar da Naira biliyan 6.563 kuɗin giratuti domin biyan haƙƙoƙin ’yan fansho da suka yi ritaya daga shekarar 2021 zuwa 2023. Wannan sanarwar ta fito ne bayan taron Majalisar Zartarwa karo na 48 wanda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta. Arsenal za ta ɗauki ɗan ƙwallon Brentford Christian Norgaard Za mu ci gaba da tattaunawa da Iran kan yarjejeniyar nukiliya — Trump Kwamishinan Kuɗi da Tattalin Arziki, Muhammad Gambo Magaji, ya bayyana cewa Naira biliyan 1.954 za a biya a watan Oktoba ga waɗanda suka yi ritaya a shekarar 2021, sai Naira biliyan 2.267 a watan Nuwamba ga waɗanda suka yi ritaya a 2022. Sannan kuma za a biya Naira biliyan 2.342 a watan...
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya da umarnin fara duban watan Muharram na sabuwar shekarar musulunci ta 1447 daga gobe Laraba, 29 ga watan Zulhijjan 1446, wanda ya yi daidai da 25 ga watan Yulin 2025. Hakan na ƙunshe cikin wata takarda da Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin bai wa majalisar Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addinin musulunci, Farfesa Sambo Wali Junaid ya raba wa manema labarai. Harin asibiti ya kashe mutum 40 a Sudan — WHO EFCC ya kama manyan jami’an NNPC kan badaƙalar Dala 7.2bn Sarkin Musulmi ya ce duk wanda ya samu ganin jinjirin watan ya sanar wa hakimi ko uban ƙasa mafi kusa da shi don sanar da majalisar sarkin musulmi. A ƙarshe sanarwar ta ce...

CMG Ya Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Da Kwamitin Shirya Gasar Wasannin Olympics Ta Milano Cortina Ta Shekarar 2026
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, ya sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da gidauniyar Milano Cortina 2026, wanda aka dorawa alhakin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina ta shekarar 2026 dake tafe. Yayin sanya hannu kan yarjejeniyar, sassan biyu sun amince su zurfafa hadin gwiwa a sassan yayatawa, da tsara ayyukan watsa gasar ta Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina, tare da aiwatar da musayar jami’ai. Sakamakon wannan hadin-gwiwa, CMG ya samu ikon watsa gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina dake tafe a shekara mai zuwa a hukumance. An kafa gidauniyar Milano Cortina 2026 a watan Disamban shekarar 2019, domin ya tsara, da...
Rundunar Sojin ƙasar Columbia ta tabbatar da cewa fararen hula sun yi garkuwa da dakarunta guda 57. Janar Federico Alberto Mejía na Rundunar ya sanar a ranar Lahadi cewa mutane kimanin 200 sun yi garkuwa da sojojin ne bisa umarnin ’yan tawayen FARC da suka addabi ƙasar. Ta bayyana cewa al’ummar ƙasar suna fuskantar matsin lamba daga ’yan tawayen masu ɗauke da makamai. Sanarwar ta ƙara da cewa an sace sojoji 31 a ranar Asabar, ragowar kuma ranar Lahadi. Erik Rodríguez ya bayyana cewa sace sojojin na da alaƙa da kama wani jagoran ’yan tawayen kungiyar EMC da sojojin suka yi. Ya ce a yayin da suke ƙoƙarin daukar sa a jirgi ne mutanen suka yi musu ƙawanya suka yi...
Wasu mutum biyu sun rasu a cikin masai a yayin da suke ƙoƙarin ciro wata ƙaramar waya da ta faɗa a ciki shaddar a yankin Ƙaramar Hukumar Albashi ta Jihar Kano. Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce mutanen biyu sun gamu da ajalinsu ne a ranar Asabar a unguwar Bazabe da ke ƙaramar hukumar. Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya sanar cewa a safiyar ranar Asabar ne aka sanar da ofishin kwana-kwana ta samu kiran gaggawa game da lamarin. Ya bayyana cewa wani ɗan shekara 40 ya shiga masai domin ciro wayarsa da ta faɗa a ciki, amma sai ya maƙale a ciki. A sakamakon wani mai suna Ibrahim ya shiga domin ciro shi, amma bayan ya yi nasarar...
Wasu mutum biyu sun rasu a cikin masai a yayin da suke ƙoƙarin ciro wata ƙaramar waya da ta faɗa a ciki shaddar a yankin Ƙaramar Hukumar Albashi ta Jihar Kano. Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce mutanen biyu sun gamu da ajalinsu ne a ranar Asabar a unguwar Bazabe da ke ƙaramar hukumar. Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya sanar cewa a safiyar ranar Asabar ne aka sanar da ofishin kwana-kwana ta samu kiran gaggawa game da lamarin. Ya bayyana cewa wani ɗan shekara 40 ya shiga masai domin ciro wayarsa da ta faɗa a ciki, amma sai ya maƙale a ciki. A sakamakon wani mai suna Ibrahim ya shiga domin ciro shi, amma bayan ya yi nasarar...
Bayan karar, lauyan masu shigar da kara, Abdulhamid L. Tukur, ya kira Nnadikwu Izuchukwu Collins, wani jami’in binciken EFCC, domin ya gabatar da gaskiyar lamarin. Collins ya shaida wa kotun cewa wasu gungun masu zuba jari sun mika koke ga hukumar EFCC a ranar 21 ga Oktoba, 2022, kan FARM360 da MCBHADMOS Trans-Atlantic Trade Limited, bisa zargin cewa kamfanonin sun yaudare su wajen saka hannun jari a harkar noma da kasuwanci tare da “alkwarin mayar da hannun jari.” Ya bayyana cewa kungiyar ta hada baki ta zuba jarin Naira miliyan 93 tare da kamfanonin. “A yayin gudanar da bincike, an aika da wasikun ayyukan bincike zuwa Hukumar Kula da Canje-canje (SEC), Bankuna, Babban Bankin Nijeriya (CBN), da Hukumar Kula da...
Aminu Boyi ya kara da cewa ido ba mudu ya san kima, idan dai batun nagarta da kwarewa da jajircewa, lallai Shettima ya yi zarra, wannan tasa ba za su laminci wani ya sauya sunansa ba a takatar 2027. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kasar Sin ta cimma nasarar aikin gwajin tserewa lokacin da ake gamu da matsala a matakin farko na harbar kumbo mai dauke da mutane na “Mengzhou” a yau Talata, a cibiyar harbar taurori dan Adam dake birnin Jiuqiu, abin da ya alamanta cewa, Sin ta cimma sabuwar nasara a aikin binciken duniyar wata tare da kumbo mai daukar mutane. Wannan ita ce nasara irinta ta biyu da Sin ta samu a wannan bangare, bayan shekaru 27 da suka gabata, da samun nasara ta farko a aikin gwajin da ta gudanar a shekarar 1998. Aikin gwajin tserewar da aka gudanar ya kasance muhimmin mataki na ba da tabbaci ga rayukan ’yan saman jannati, wato idan an gamu da hadari ko matsala...
Ƙungiyar Palermo ta ɗauki Filippo Inzaghi a matsayin mai horas da ’yan wasanta bayan raba da gari da ƙungiyar Pisa wadda ya kafa tarihin jagorantar haurowarta gasar Serie A. Cikin wata sanarwa da Palermo ta fitar ta ce Inzaghi ya rattaba hannu kan kwantaragin shekaru da dama wanda zai soma aiki daga watan gobe. Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mutum 20 a Chadi Jirgin alhazai ya yi saukar gaggawa kan barazanar harin bom A cewar kafofin watsa labarai na Italiya, Palermo ta biya Pisa kusan dala miliyan 1.1 wajen ɗaukar Inzaghi. Pisa dai ta ƙare gasar Serie B a mataki na biyu a ƙarƙashin jagorancin kociyan mai shekaru 51, lamarin da ya ba ta nasarar haurowa gasar Serie A karon...
Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta ce ta gano wata sabuwar dabarar satar kudi da wasu ’yan siyasa ke amfani da ita a yanzu ta hanyar amfani da ’yan damfara wadanda aka fi sani da ’yan yahoo a fadin kasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede na wannan furuci ne yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Litinin. Tinubu zai je jaje bayan kisan fiye da mutum 100 a Benuwe Gwamnati ta kasa ɗaukar matakin da ya dace a kan kashe-kashen Benuwe — Atiku Olukoyede wanda ya ce wadannan matasa ’yan yahoo da suke zubar da kimar Nijeriya a idon duniya sun kuma faɗa dumu-dumu ta’adar nan ta garkuwar...
Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta ce ta gano wata sabuwar dabarar satar kudi da wasu ’yan siyasa ke amfani da ita a yanzu ta hanyar amfani da ’yan damfara wadanda aka fi sani da ’yan yahoo a fadin kasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede na wannan furuci ne yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Litinin. Tinubu zai je jaje bayan kisan fiye da mutum 100 a Benuwe Gwamnati ta kasa ɗaukar matakin da ya dace a kan kashe-kashen Benuwe — Atiku Olukoyede wanda ya ce wadannan matasa ’yan yahoo da suke zubar da kimar Nijeriya a idon duniya sun kuma faɗa dumu-dumu ta’adar nan ta garkuwar...
Garkuwan sararin samnaiyar kasar Iran a lardin Zanjan ya bada labarin kakkabo jiragen yakin na HKI guda biyi wadanda ake sarrafasu daga nesa a sararin samaniyar. Kamfanin dillancin lbaran Tasnim na sojojin kasar Iran ya nakalto majiyar dakarunn juyin juya halin musulunci na kasar Iran tana fadar haka. Labarin ya kara da cewa rubuce rubucen da aka rubuta a jikin jiragen da aka tarwatsa sun bayyan cewa kirar kasar Amurka ce. Wannan yake tabbatar da irin hannun da Amurka take da shi a cikin yakin da Iran take fafatawa da HKI. A wani labarin kuma yansandar yanar gizo sun kama mutane biyu wadanda suke yada labaran karya dangane da yaki da kuma shuwagabannin kasar. Har’ila yau an kama wasu wadanda...
Wasu Hare-haren da gwamnatin Isra’ila ta kai ya haddasa gobara a wasu matatun mai a lardin Bushehr da ke kudancin kasar Iran. Gobarar ta tashi ne a wurin a ranar Asabar bayan da wasu kananan jiragen yakin Isra’ila guda biyu suka kai hare-hare a kan kayayyakin sarrafa iskar gas da ke yankin kudancin Pars. Hare-haren sun yi haddassa fashe fashe a matatar iskar gas ta Fajr-e Jam, daya daga cikin mafi girma a Iran, da kuma wata karamar matatar mai a mataki na 14 na tashar iskar gas ta Kudu Pars. Har yanzu ba a fitar da kiyasin barnar a hukumance ba. Bayan gobarar, ma’aikatar mai ta Iran ta fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar da harin. Sanarwar ta...
Dakarun Operation Haɗin Kai sun kama mut biyar da ake zargin suna taimaka wa ’yan ta’adda da kayan aiki. Daga cikinsu har da wani ɗan ƙasar China da ya ce shi mai harkar ma’adinai ne. Damina: NiMet ta gargaɗi jihohi 13 kan barazanar ambaliyar ruwa Ya kamata Isra’ila da Iran su kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu — Gwamnatin Tarayya An kama su ne a lokacin kai wani samame da aka gudanar daga 5 zuwa 7 ga watan Yuni a ƙananan hukumomin Kukawa da Ngala na Jihar Borno, da kuma Geidam a Jihar Yobe. A lokacin wannan aiki, dakarun sun ƙwato wasu kayayyaki da suka haɗa da mota, babur, wayoyin salula, fasfo na ƙasar China, da kuma kuɗi Naira 10,000....
Kwamandan sararin samaniya na dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Janar Amir Ali Haji Zadeh yana cikin wadanda su ka yi shahada sanadiyyar harin da sojojin HKI su ka kawo wa da asubahin yau Juma’a. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto majiyar juyin juya halin musulunci ta Iran tana tabbatar da shahadar Janar Amir Ali Haji Zadeh.
Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya ce shekara biyu da Bola Ahmed Tinubu ya yi a matsayin shugaban ƙasa sun fi kowane lokaci muni tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar. Yayin da yake magana da BBC a ranar Dimokuraɗiyya da Najeriya ke cika shekaru 26 tana mulkin farar hula, Dalung ya ce ba wani abin arziƙi da talaka ya amfana da shi daga wannan gwamnati. An kama ’yar Najeriya da laifin safarar ɗalibai 15 a Australia Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi Ya ce: “Kawai abin da talaka ya samu daga gwamnatin Tinubu shi ne tsadar rayuwa, yunwa, wahala da matsalar tsaro.” Ya zargi gwamnatin da cewa cire tallafin...
Rundunar ’yan sandan ƙasar Australia ta kama wata ’yar asalin Najeriya da ke ƙasar Australia, Binta Abubakar bisa zarginta da safarar ɗalibai daga ƙasar Papua New Guinea tare da tilasta musu yin aikin da ba a biya a gonaki a faɗin jihar Ƙueensland da sunan bayar da tallafin karatu. Binta mai shekara 56, an kama ta ne a ranar Laraba a filin jirgin saman Brisbane a lokacin da ta isa ƙasar Papua New Guinea, inda take zaune. Ambaliyar Mokwa: An sake gano gawar mutum bayan kwanaki 8 Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi Kamen nata ya biyo bayan wani bincike na tsawon shekaru biyu da ƙungiyar masu fataucin bil-Adama ta AFP ta...
Rundunar Ƴanandan Jihar Bauchi ta kama wani matashi mai suna Umar Yau, wanda aka fi sani da “Snake,” bisa zargin damfara ta yanar gizo da satar bayanan wasu mutane. An kama Yau, mai shekaru 25 daga unguwar Yelwan Makaranta a Bauchi, bayan binciken da aka fara sakamakon ƙorafi daga wata mata da ya damfara. Fatimah Faiz Ali Bawahab, wata ’yar kasuwa ta yanar gizo, ta kai ƙorafin cewa wani ya ƙirƙiri asusun bogi a Facebook da sunanta da hotunanta don damfarar mutane. CSP Ahmed Wakil, kakakin rundunar, ya ce wanda ake zargin ya ƙirƙiri asusun “Amizeebaby Muhd” inda ya ke tallata kasuwancin ƙarya, yana karɓar kuɗi daga mutane ta asusun banki. Gwamnatin Bauchi Ta Fara Shirin Kirkirar Sabbin Masarautu Da...
A cewar Bawa, gwamnatocin da a karkashinsu aka wawashe dukiyar kasa, su ne na Mulkin Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo (daga 1999 zuwa 2006), sai Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua (daga 2007 zuwa 2009), kazalika a mulkin Shugaba Goodluck Jonathan daga (2010 zuwa 2014), sai kuma mulkin Muhammadu Buhari (daga 2015 zuwa 2023). Wadannan bayanai na kunshe cikin littafin, ‘The Shadow Of Loot and Loss – Uncobering Nigeria’s Petrol Subsidy Fraud,’ wanda tsohon sarkin yaki da cin hanci da rashawa ya rubuta. Alkaluman da Bawa ya bayyana daga cikin gwamnatocin hudu, shugaba Buhari ne ke kan gaba wajen biyan tallafin da ake ta cece-kuce akai na Naira tiriliyan 11, sai kuma na Jonathan wanda ya kashe Naira tiriliyan 3.9. Gwamnatin...
Abdulazeez pleaded not guilty to the two-count charge. Abdulazeez ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da su biyu. Bayan rokon da ta yi, lauyan ICPC, Hamza Sani, ya bukaci kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Yuni, 2025, domin masu gabatar da kara su gabatar da shaidu. Sai dai daga baya kotun ta ba da ranar sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Yunin 2025 domin sauraron karar. Lauyan wanda ake tuhuma ya nemi a ba shi belin, wanda ICPC ba ta yi adawa da shi ba. Mai shari’a Iheabunke ya bayar da belinta a kan kudi naira miliyan 10, tare da mutane biyu da za su tsaya mata. Ya ce dole ne...
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cikakken shirin Iran na tunkarar duk wani mataki na wuce gona da iri a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar barazanar daukar matakin soji kan kasar. Manjo Janar Hossein Salami ya bayyana hakan ne yau Alhamis, yayin da rahotanni ke nuni da cewa, Amurka ta sanya ofisoshin jakadancinta da sansanonin sojinta da ke yammacin Asiya cikin shirin ko-ta-kwana saboda fargabar yiwuwar kai wa Iran hari. “A wasu lokuta makiya suna yi mana barazana da daukar matakin soji, mun sha bayyanawa, kuma muna maimaitawa a yau, cewa mun shirya tsaf don fuskantar duk wani yanayi,” in ji shi. “Muna da kwarewa, mun karfafa karfinmu tare da samar...
Bankin Duniya ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka ba tare da taɓarɓarewa nan da shekaru uku masu zuwa. Bankin ya yi hasashen haɓakar ma’aunin tattalin arzikin cikin gida, GDP da kashi 3.6 cikin 100 a shekarar 2025, sai kashi 3.7 a shekarar 2026 da kuma kashi 3.8 a shekarar 2027. Dalilin da babu abin da gwamnatin NNPP ta taɓuka a Kano — APC Amurka da China sun cimma sabuwar yarjejeniyar kasuwanci A cewar sabon rahoton tattalin arzikin duniya da Bankin ya fitar, ana sa ran za a tallafa wa matsakaicin lokaci na Nijeriya ta hanyar samar da ingantattun albarkatun mai, da gyare-gyaren da ake ci gaba da yi, da kuma farfado da ƙwarin gwiwar masu zuba jari....
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi wa ’yan Najeriya jawabi da misalin ƙarfe 7 na safiyar ranar Alhamis, domin bikin ranar dimokuraɗiyya na 2025. A cewar wata sanarwa daga kwamitin shirya bikin, shugaban ƙasa zai kuma je zaman haɗin gwiwa da ’yan majalisar dokoki da rana. Na shirya yin haɗaka don ƙalubalantar Tinubu a 2027 – Amaechi Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar da shugabar ƙaramar hukuma na wata 3 Sanarwar ta kuma bayyana cewa ba za a yi faretin bikin a bana ba. A maimakon haka, za a yi muhawara da jama’a a fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 4 na yamma. Bikin bana na zuwa ne yayin da Najeriya ke cika shekara 26 a gwadaben mulkin dimokuraɗiyya...
Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamitin da zai binciki musabbabin gobarar da ta tashi a kwanan nan a kasuwar wayoyin hannu ta Farm Center da ke jihar. A ranar Juma’ar da ta gabata ce dai gobara ta tashi a kasuwar wacce aka yi kiyasin ta kone shaguna sama da 300 tare da janyo wa ’yan kasuwa asarar miliyoyin Naira. Za a dauke wa jihohin Arewa maso Gabas wutar lantarki na tsawon kwana 4 Kotu ta yi fatali da bukatar Akpabio, ta umarce shi ya biya Natasha N100,000 Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Ibrahim ne ya rantsar da kwamitin a madadin Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf. Kwamitin dai kasance karkashin jagorancin Kwamishinan Ayyuka na Musammanna jihar, Alhaji Umar Ibrahim kuma...
Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta yi fatali da bukatun Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, sannan ta ci shi tarar Naira 100,000. Kotun, wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Hamman Barka dai ta yi watsi da bukatun ne kan karar da aka shigar ranar 21 ga watan Mayun 2025, bayan neman bukatar janye karar da aka daukaka. Bukatun dai na kunshe ne a cikin wasu kararraki masu lamba CV/395/M1/2025 da kuma CV/395/M2/2025, wadanda aka shigar a ranakun uku da kuma 25 ga watan Mayun 2025, wanda a cikinsu aka ambaci sunan Akpabio a matsayin mai daukaka kara. DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Rikicin Filato:...
Gidauniyar Hind Rajab (HRF), mai rajin kare hakkin Falasdinawa, ta shigar da kara kan laifukan yaki bayan farmakin da sojojin ruwan Isra’ila suka kai kan jirgin ruwan agaji na Birtaniya Madleen a ruwan kasa da kasa a yammacin Lahadi. Koken dai ya shafi rundunar sojin ruwa ta Isra’ila Shaytet 13 da kwamandan ta, Vice Admiral David Saar Salama. Gidauniyar ta HRF ta yi kira da a gaggauta sakin masu fafutuka 12 da ake tsare da su, ciki har da mai fafutukar kare muhalli Greta Thunberg, dan wasan kwaikwayo Liam Cunningham, da Rima Hassan ta faransa, wadanda ke hannun Isra’ila. Jirgin ruwan na Madleen, na kungiyar Freedom Flotilla Coalition, na dauke da kayayyakin jinya, da abinci, da madarar jarirai, da sauran...
Gwamnatin Sudan ta zargi ‘yan tawayen kasar na dakarun kai daukin gaggawa da kai hari kan ayarin motocin agaji kai a yankin Darfur Gwamnatin Sudan ta sanar da cewa: “Dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan ayarin motocin agajin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Darfur ta Arewa ta hanyar jiragen sama marasa matuka ciki.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Sudan ta bayyana matukar bacin ranta tare da tofin Allah tsine da Allah wadai kan wannan mummunan lamari, tana mai jaddada cewa: “Yunkuri ne na ganganci na nufin toshe kungiyoyin agaji da dakile ayyukansu na kai kayan agaji ga fararen hula da suka makale a birnin El Fasher da sansanonin gudun hijira.” Sanarwar ta...
Ministan leken asiri na kasar Iran ya ce asiran tsaron HKI da suka shiga hannun ma’aikatansa sun shafi makaman nukliya na HKI kuma sun nuna kwarewar da jami’an leken asirin kasar suke da shi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan bayanan zasu taimakawa sojojin JMI wajen sanin wuraren da zasu kai hare hare a duk lokacinda yake ya barke tsakanin Iran da haramtacciyar kasar, na makamai da kuma na yanar gizo. Labarin ya kara da cewa da jami’an ma’aikatar hukumar leken asiri suka yi kama daga daukar ma’aikatan da suka dace da yin hakan da dabar barun da suke yi amfani da su don kaiwa da bayan da suke bukata ya nuna irin koreawarsu a...
Ministan leken asiri na kasar Iran ya ce asiran tsaron HKI da suka shiga hannun ma’aikatansa sun shafi makaman nukliya na HKI kuma sun nuna kwarewar da jami’an leken asirin kasar suke da shi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan bayanan zasu taimakawa sojojin JMI wajen sanin wuraren da zasu kai hare hare a duk lokacinda yake ya barke tsakanin Iran da haramtacciyar kasar, na makamai da kuma na yanar gizo. Labarin ya kara da cewa da jami’an ma’aikatar hukumar leken asiri suka yi kama daga daukar ma’aikatan da suka dace da yin hakan da dabar barun da suke yi amfani da su don kaiwa da bayan da suke bukata ya nuna irin koreawarsu a...
Ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin ta ce kasar ta samu ingantuwa a banagren amfani da ruwa a shekarar 2024. Sanarwar da ma’aikatar kan fitar kan albarkatun ruwa a duk shekara, ta ce a bara, ruwan da kasar ta yi amfani da shi da na kwatankwacin yuan 10,000 ko dala 1,391.5 na alkaluman GDP ya ragu da kaso 4.4 bisa dari. Haka kuma idan aka kwatanta da yuan 10,000 na darajar bangaren masana’antu, adadin ya ragu da kaso 5.3 bisa dari. A cewar sanarwar, saukar ruwa da albarkatun ruwa sun wuce matsakaicin matakin na shekaru da dama. Matsakaicin adadin ruwan da ya zuba a kasar a shekarar 2024 shi ne milimita 717.7, wanda ya haura na shekarun baya...
Sojojin mamayar Isra’ilan sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi a birnin Rafah, inda suka kashe mutane da dama a kusa da cibiyar rarraba kayan agaji Fararen hula 23 ne suka yi shahada yayin da wasu kusan 200 suka jikkata a yau Talata lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka bude wuta kan mai uwa da wabi wa fararen hula a kusa da wata cibiyar rarraba kayan agaji a birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza. Majiyoyin kiwon lafiya sun bayyana cewa: Shahidan sun fadi ne a lokacin da suke jiran agajin jin kai a titunan Rafah, lokacin da jirage masu saukar ungulu suka bude musu wuta. An tantance biyar daga cikin shahidan, yayin da wasu fiye da 20 kuma...
Ya bayyana kamen na su biyo bayan kama wasu alhazai biyu – Ibrahim Umar Mustapha da Muhammad Siraj Shifado a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, da ke Kano a ranar Litinin 26 ga watan Mayu. An kama mutanen biyu ne a lokacin da ake tantance fasinjojin jirgin na Ethiopian Airline ET 940 da zai tafi zuwa Jedda, ta kasar Saudiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Haka kuma an yi zaratan ‘‘yan kwallo irin su Johan Cruyff da Eusébio da Gerd Müller mahaifin Muller na yanzu da Zinedine Zidane da Ronaldo na Brazil da sauransu amma tabbas ba a samu zazzafar muhawara ba saboda bbau kafafen sadarwa na zamani wadanda yanzu kusan su ne suka hura wutar zazzafar muhawarar a sassa daban-daban na duniya da ake Kallon kwallon kafa. A yanzu dai Messi ne ya fi lashe Ballon d’Or, inda yake da guda takwas: 2009, 2010, 2011, 2012, 2015, 2019, 2021 da 2023, sai Cristiano Ronaldo mai guda biyar: 2008, 2013, 2014, 2016 da 2017. Sannan Messi ya zo na biyu sau biyar, shi kuma Cristiano Ronaldo ya zo na biyu sau shida, sannan dukkansu sun...
Kyaftin din tawagar Super Eagles ta Nijeriya Ahmed Musa, ya auri matarsa ta 4, Asmau Moriki, a wani biki na sirri da aka gudanar a jihar Kano, Musa da amaryarshi Asmau sun zama mata da miji watanni kadan bayan haduwarsu, Musa ya bar sansanin tawagar Super Eagles dake birnin Landan domin ya halarci bikin wanda aka gudanar a birnin Kano. Dan wasan dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ya shiga wasan da Nijeriya ta doke Ghana da ci 2-1 a minti 60 na wasan, Musa na daya daga cikin yan wasan da sukafi taka leda a tarihin tawagar kwallon kafa ta Nijeriya inda kuma ya zamo wanda yafi jefawa Nijeriya kwallaye a gasar kofin Duniya a...
Kasar Brazil ta jaddada goyon bayanta ga ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya A yayin ganawarsa da sakataren kwamitin kolin tsaron kasar Iran, mataimaki na musamman ga shugaban kasar Brazil ya sanar da cewa kasarsa tana goyon bayan ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na yin amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya da kuma aiwatar da shirin inganta sinadarin Uranium don bunkasa harkokin ilimi cikin gida ta hanyar fasahar makamashin nukiliya. A yayin ganawar tasu, Ali Akbar Ahmadian, sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran, da mataimaki na musamman ga shugaban kasar Brazil Celso Amorim, sun jaddada muhimmancin ci gaba da gudanar da hadin gwiwa da tuntubar juna tsakanin kasashen biyu masu cin gashin...
Fararen hula 10 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da jiragen yaki mara matuki suka kai kan birnin Kordofan na kasar Sudan Kafofin yada labarai na cikin gidan kasar Sudan sun rawaito cewa: Akalla fararen hula 10 ne suka rasa rayukansu, wasu kuma suka jikkata sakamakon hare-haren da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kai kan jihohin Yamma da Kudancin Kordofan. Shafin yanar gizo na Sudan Tribune ya watsa rahoto cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun zafafa kai hare-hare ta sama a garuruwa da biranen yankin Kordofan tun farkon wannan wata. Yankin dai ya sha fama da tashe tashen hankula tsakanin bangarorin da ke gaba da juna, inda kungiyar Rapid Support Forces ke...

Sin Da Kasashen Yankin Pasifik Sun Yi Nasarar Gudanar Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Karo Na Uku
Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, da shugaban kasar Kiribati, kuma ministan harkokin wajen kasar Taneti Maamau, sun jagoranci taron ministocin harkokin wajen kasar Sin da kasashen yankin Pasifik karo na uku a birnin Xiamen dake kudu maso gabashin kasar Sin. A yayin taron, Wang Yi ya gabatar da shawarwari guda shida kan kafa kyakkyawar makomar bai daya ta Sin da kasashen yankin Pasifik. Na farko shi ne dagewa kan mutunta juna. Ya ce kasar Sin tana goyon bayan kasashen yankin wajen kiyaye cikakken ’yancinsu, tsaro da muradunsu na ci gaban. Kuma Sin ta yi imanin cewa, kasashen yankin za su ci gaba da bin manufar kasancewar kasar...
An kammala gasar fada tsakanin mutum-mutumin inji cikin jerin gasannin mutum-mutumin inji ta kasa da kasa a ran 25 ga watan nan da muke ciki a birnin Hangzhou dake gabashin kasar Sin. Gasar ta fada tsakanin mutum-mutumin inji da aka yi a wannan karo, ita ce irinta ta farko a duniya, inda kuma ta zama wani dandali dake yi wa masu kallo a daukacin duniya karin haske game da kimiya da fasaha a wannan bangare. An watsa gasar ga masu kallo na cikin gidan kasar Sin da ketare kai tsaye, matakin da ya ba su damar sanin gajiyar da ake ci daga kimiya da fasaha. CMG ta gabatarwa al’ummun duniya wata dama mai kyau ta fahimtar kimiyyar mutum-mutumin inji...

Afirka Ta Kudu Ta Zargi Shugaban Kasar Amurka Da Rashin Dalili Akan Zargin Yi Wa Fararen Fatar Kasar Kisan Kiyashi
Ministan ‘yan sandan kasar Afirka ta kudu, ya ce, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na cewa an yi wa fararen fatar kasar kisan kiyashi a yayin ziyarar da shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya kai. A yayin ganawar da ya yi da shugaban kasar Afirka ta kudu, shugaban kasar Amurka ya kunna wani faifen bidiyo da a ciki aka nuna gicciye a gefen hanya domin tunawa da fararen fata manoma da aka yi wa ksian gilla. Ministan ‘yan sandan kasar ta Afirka ta kuku Senzo Mchunu ta cewa; Wadannan gicciyen ba su nuni da cewa suna akan kabarurruka ne, ko wani wuri na tunawa da matatu, an Sanya su ne a 2020 domin tunawa da dukkanin...
Afrika ta kudu ta karyata ikirarin da shugaba Donald Trump na Amurka ya yi kan cewa kasar ta aikata kisan kiyashi kan manoma fafaren fata a Afrika ta Kudun. Ministan ‘yan sandan Afirka ta Kudu, Senzo Mchunu, ya yi fatali da ikirarin naTrump, yana mai cewa bai da tushe balle makama, in ji jaridar Daily Maverick ta Afirka ta Kudu. Ministan ‘yan sandan Afirka ta Kudu ya fada jiya Juma’a cewa babu wani abu da ya yi kama da hakan a game da ikirarin da Trump na kisan kiyahsin fararen fata a yayin ganawarsa da shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa. Trump dai ya nuna wani faifan bidiyo yayin ganawarsa da takwaransa na Afrika ta Kudu, inda har ma ya...
Ministan ya kuma zayyano jerin shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ta kirkiro da nufin zaburar da matasa rungumar kiwon dabbobi, musamman don samun riba ciki har da sama musu hektar noma 51,000, a karkashin hadaka da shirin fitar da kaya na ‘Gulf’ na jihohi da kuma shirye-shiryen farfado da guraren kiwon dabbobi 417 a daukacin fadin kasar nan. “Muna da abubuwan da za mu yi amfani da su a kasar nan, domin yakar yunwa a fadin kasar baki-daya,” in ji Ministan. “Akalla a kasar nan, muna da Shanu kimanin miliyan sha biyar da Tumakai miliyan 60 da Kaji da miliyan 600 da Akuyoyi da miliyan 1.4 da Rakuma miliyan 700,000 tare kuma da kasar noma, amma sai dai har yanzu, kasar...
Don haka, ya zama dole kasashen Global South su hada kansu su dauki matakan dakushe duk wani radadi da matakin harajin da Amurka ta dauka zai haifar, ciki har da bunkasawa da inganta cinikayya tsakanin wadannan kasashe,ta hanyar hada kansu domin rage dogaro da tattalin arzikin Amurka ko na kasashen yammaci, wannan yunkuri zai bunkasa tattalin arzikin kasashen yankin Global South. Kasashen na Global South suna sake zayyana tsarin tattalin arzikinsu ta hanyar bayar da fifiko ga bunkasuwar tattalin arzikinsu da bayar da dama ta bai daya ga kowace kasa wajen taka rawa a harkar kasuwanci. Domin kuwa kasashen sun hade kansu wajen nuna turjiya ga wannan tsarin haraji na Amurka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Daga Bello Wakili Dukkan ‘yan majalisun tarayya daga Jihar Katsina sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Umar Dikko Radda domin ya sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shekarar 2027 mai zuwa. An bayyana wannan matsaya ne a lokacin wani taron hadin gwiwa da ‘yan majalisar suka gudanar, inda Honourable Sada Soli, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jibia da Kaita, ya yi magana a madadin takwarorinsa. Ya bayyana cewa wannan shawara ta samo asali ne daga nazarin hadin gwiwa da suka yi kan nasarorin da gwamnan ya samu da kuma goyon bayan da al’ummar jihar suka nuna daga kowane bangare. ‘Yan majalisar sun yaba da irin salon shugabanci na Gwamna...
’Yan Najeriya daga kowane ɓangare daban-daban sun caccaki jam’iyyar APC bisa yanke shawarar goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027, duk da cewa shekararsa biyu kacal da hawa mulki. Wasu na ganin matakin ya nuna rashin tausayi da rashin damuwa da halin ƙuncin da al’umma ke ciki. Cutar lamoniya ta kama alhazai 99 ’yan ƙasar Indonesiya a Saudiyya NAJERIYA A YAU: Dalilin ’Yan Adawa Na Ƙulla Ƙawance A Ƙarƙashin Inuwar ADC Jagororin jam’iyyar APC, gwamnoninta da ’yan majalisa ne suka fito suka nuna goyon bayansu ga Tinubu. Amma jama’a na ganin hakan na nuna burin ci gaba da riƙe madafun iko ne kawai, ba wai taimakon talakawa ba. Ra’ayoyi daga sassa...

Jam’iyyar APC A Najeriya Ta Tabbatar Da Tinubu A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar A Shekara Ta 2027
Jam’iyyar ‘All Progressives Congress” (APC) mai Mulki a tarayyar Najeriya ta tabbatar da shugaban Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar Jam’iyyar a zaben shugaban kas ana shekara ta 2027 mai zuwa. Shafin yada labarai na Afrika ya bayyana cewa a jiya Alhamis ce a taron Jam’iyyar wanda aka gudanar a Abuja, kuma wanda ya zo dai-dai da cika shekaru biyu da zagayensa na farko na shugabancin kasar Jam’iyyar ta nada shi Shugaba Bola Ahmed Tinubu dan shekara 73 a duniya a matsayin dan takararta a zaben na shekara ta 2027, don ya sami damar kamala shirinsa nag yare-gywaren tattalin arzikin kasar da y afara. Shugaban Tinubu dai ya kara farashin man fetur a ranar da ya hau kan kujerar...

Masanan Najeriya Sun Bayyana Muhimmancin Hadin Gwiwar Afirka Da Sin A Fannin Tinkarar Kalubalen Harajin Kwastam Na Amurka
Wasu masana a tarayyar Najeriya sun jinjinawa yadda Najeriya da Sin suka daga dangantakarsu zuwa huldar abota bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni a bara, matakin da ya tabbatar da goyon bayansu ga kokarin tinkarar kalubalen karin harajin kwastam da Amurka ke dora musu bisa radin kai. Kwanan baya, an gudanar da taron tattaunawa kan yadda za a tinkari harajin kwastam da Amurka ke kakabawa sauran kasashe a birnin Abuja hedkwatar Najeriya, inda babban darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin ta Najeriya Charles Onunaiju ya bayyana cewa, hadin gwiwar Sin da Najeriya bisa dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka, da shawarar “ziri daya da hanya daya” da dai sauransu, ba ingiza bunkasuwar manyan ababen more rayuwa a Afirka kadai...
Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ya amince da wannan batun na takwaransa cikin gaggawa. “Na tsaya a madadin Sanatoci 109 da ‘yan Majalisar Wakilai 360 don amincewa da wannan matakin na Akpabio,” in ji Abbas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani dattijo mai aikin kwashe shara da ya shekara 40 yana tara kuɗin domin zuwa aikin Hajji ya samu cika burinsa a bana. A karshe dattijoin dan qasar Indosauke ya samu damar zuwa sauke farali inda ya isa Kasa Mai Tsarki tare da matarsa. Wanni dattijon wanda ya nuna tsananin juriya da jajircewa ya bayyana yadda kwashe shekara 40 yana tara 1,000 na kuɗin ƙasarsu a kullum, domin tara kuɗin da zai sauke farali shi da mai ɗakinsa. A yayin da ake yake hira da Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Saudiyya bayan isarsu ƙasar domin sauke farali, dattijoin ya bayyana cewa tun ashekarar 1986 ya fara tara wannan kuɗi bayan samun goyon bayan matarsa. Dangote ya sake...
Shuwagabannin Amurka da Afirka ta Kudu sun yi arangama kan zargin kisan kare dangi a Afirka ta Kudu Fadar White House ta shaida wata zazzafar musayar wuta tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda ya musanta zargin da ake masa na cewa Pretoria na cin zarafin ‘yan kasar fararen fata. An yi ganawar ne mako guda bayan da Trump ya yi zargin cewa gwamnatin Afirka ta Kudu na yin kisan kiyashi ga ‘yan kasarta ‘yan asalin Turai. A yayin tattaunawar da ta samu halartar jami’ai daga bangarorin biyu, shugaban na Amurka ya bukaci ma’aikatansa da su nuna masa faifan bidiyo da ke da alaka da zargin kisan kiyashin, sannan Ramaphosa ya kuma mika...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta ce, a ranar 19 ga wannan wata, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya yi bayani game da yanayin tafiyar tattalin arzikin kasar Sin a watan Afrilu, inda kafofin watsa labaru na kasa da kasa suka yi amfani da kalmomi kamar “wuce zaton da aka yi” da kuma “ da karfi” wajen yabawa tattalin arzikin kasar Sin. Mao Ning ta bayyana hakan ne a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Laraba, inda ta ce, bisa yanayin tinkarar harajin kwastam mai yawa, kasar Sin ta tabbatar da bunkasar cinikayyar kasa da kasa. A farkon watanni 4 na bana, yawan kudin kayayyakin shige da fice na kasar Sin...
Ta kuma yi kira da a cafke masu safarar mutane tare da fallasa sunayensu bayan an gurfanar da su a gaban kotu, domin daƙile laifi. NiDCOM ta miƙa waɗanda aka ceto ga hukumar NAPTIP domin tantance su da kuma ci gaba da ba su kulawa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kamfanin kirar jiragen sama na kasar Sin wato AVIC ya ce ya cimma nasarar samar da jirgin sama dake iya tashi a kasa da ruwa irinsa na farko samfuri AG600 da aka yiwa lakabi da “Kun Long”. An kuma cimma nasarar gwajinsa a jiya Lahadi a birnin Zhuhai na lardin Guangdong. Hakan ya nuna cewa, ingancin jirgin ya dace da ma’aunin da aka tanada, kuma ya alamta cewa jirgin samfuri AG600 ya samu iznin kira wato PC. Rahotanni na cewa a ranar 20 ga watan Afrilun bana, jirgin samfurin AG600 ya samu takardar shaidar inganci ta samfurinsa, matakin da ya nuna cewa, nazarin da aka yi a wannan bangare ya cimma cikakkiyar nasara, kuma jirgin ya samu izinin shiga kasuwa....
Hawa wannan babbar katangar na koyar darussa masu masu ma’ana,- daya daga cikinsu shi ne tsayin daka da ya kai ga Sinawa zuwa ga samun daukaka. Wannan gogewa ta nuna kyakkyawar dabi’ar aikin Sinawa, wanda ya ba da gudummawa ga ci gaban da suka samu a cikin shekaru 40 da suka gabata. Kafin wannan lokacin, jami’ar Yang Boazhin ya lura cewa, kasar Sin ta fi sauran sassan Afirka talauci. Ta ba da labarin ziyarar da ta kai Afirka a shekarar 1985 a matsayin jami’ar diflomasiyya, inda ta tabbatar da cewa Afirka na da gagarumin ci gaba a wannan lokacin. Jamhuriyar kasar Sin, mai yawan al’umma biliyan 1.4, ta kunshi gundumomi hudu da larduna 23, tare da yankuna biyar masu cin...
Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda, ta biya wa maniyyatan jihar 2,047 kuɗin hadaya domin sauƙaƙa musu wajen hidimomin aikin Hajji na shekarar 2025. Amirul Hajji kuma Mataimakin gwamnan jihar, Malam Faruk Lawal Jobe, ne ya bayyana haka a ranar Lahadi yayin da yake yi wa mahajjatan jirgin farko bankwana kafin tashin zuwa ƙasa mai tsarki. An tafka asara bayan gobara ta ƙone Kwalejin Sheikh Dahiru Bauchi Jami’in Sibil Difens ya mayar da N800,000 da wata Hajiya ta zubar a Adamawa Ya ce an biya wa kowane maniyyaci Riyal 600. Mahajjatan da za su fara tafiya sun fito ne daga ƙananan hukumomin kudancin jihar, kuma za su tashi a jirgin kamfanin Max Air. Gwamna Radda ya...
Gobara ta tashi a Kwalejin Karatun Alƙur’ani da ilimin addinin Musulunci mallakin fitaccen malamin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, da ke Rafin Albasa, a Jihar Bauchi, inda ta ƙone ginin makarantar da kayan cikinta. Binciken wakilinmu ya gano cewa gobarar ta lalata bene mai ɗakuna da dama ciki har da ofisoshi, ajujuwa, ɗakunan gwaje-gwaje, ɗakunan kwamfuta, da ɗakunan karatu. Jami’in Sibil Difens ya mayar da N800,000 da wata Hajiya ta zubar a Adamawa Yadda ’ya’yan shugabanni ke musu yaƙi da ’yan adawa An kuma rasa kayan sawa na malamai da ɗalibai, katifu, barguna da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum. Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba. Sai dai daraktan makarantar, Sayyadi Aliyu Sise Dahiru, ya ce sun...
Rahotanni daga kasar DRC sun ce a ranar Litinin din da ta gabata kungiyar ‘yan tawaye ta M23 ta kori fararen hula 181 daga garin Goma zuwa kasar Rwanda. Kungiyar ta zargi fararen hular da ta kora da cewa, ba ‘yan kasa ba ne, asalinsu daga kasar Rwanda ne. Bugu da kari an gabatar da wasu dubban mutane tare da iyalansu da ake daukar cewa masu laifi ne, da aka zuba su a cikin manyan motoci a yankin Karenga dake yankin Kivu ta arewa. Mafi yawancin iyalan da aka dauka suna a yankin da yake karkashin ikon kungiyar ‘yan tawaye da Democratic Forces For Liberation of Rwanda ( FDLR). Gwamnatin Rwanda da kuma kungiyar M23 suna zargin kungiyar FDLR da...
A wani rahoton da MDD ta fitar a cikin kwanakin nan, ya bayyana cewa, tun daga 2024 ne yunwar da ake fuskanta a duniya ta kara tsanani domin ta shafi mutanen da sun kai miliyan 295. Rahoton ya kara da cewa; wannan adadin na mutanen dake fama da yunwa mai tsanani suna warwatse a cikin kasashe 53 na duniya. A Juma’ar da ta gabata aka fitar da wannan rahoton. Haka nan kuma an bayyana cewa idan aka kwatanta da yunwar da aka yi fama da ita a shekarar 2023, to da aka shiga 2024 an sami karuwar masu fama da matsananciyar yunwar da adadinsu ya karu da miliyan 13.7. Shekaru shida kenan a jere da ake samun karuwar yawan mutanen...
Hukumar kula da al’adun gargajiya ta kasar Sin ta bayyana cewa, gidajen tarihi na sassan kasar sun gudanar da bukukuwan nune-nunen kayayyaki 43,000, da tarurrukan ilimi 511,000. An bayyana wadannan alkaluman ne a yau Lahadi a wani bikin tunawa da ranar gidajen tarihi ta duniya a gidan adana kayayyakin tarihi na babban mashigin ruwa wato Grand Canal a Beijing. A cikin shekarar 2024, an yi rajistar sabbin gidajen tarihi 213 a kasar Sin, inda hakan ya kara yawan adadin gidajen tarihi na kasar zuwa 7,046, kamar yadda hukumar kula da su ta bayyana. Kazalika, ta kara da cewa, kasar Sin tana kara fadada manufofinta na shiga gidajen tarihi ba tare da biyan kudi ba, inda sama da kashi 91 cikin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Habakar matsayi na kasafin kudi ya inganta a cikin 2024, ta hanyar habaka kudaden shiga. Gibin kasafin kudi ya ragu daga kashi 5.4 na kudin shiga a shekarar 2023 zuwa kashi 3.0 na kudin shiga a shekarar 2024, babban ci gaban da aka samu sakamakon karuwar kudaden shiga na daukacin tarayyar kasar, wanda ya karu daga naira tiriliyan 16.8 a shekarar 2023 (7.2 na kudaden shiga) zuwa kimanin naira tiriliyan 31.200. Rahoton ya kara da cewa hauhawar farashin kayayyaki ya tsaya tsayin daka amma ana sa ran zai fadi zuwa matsakaicin shekara da kashi 22.1 cikin 100 a shekarar 2025, yayin da tsayin daka mai tsayi ya tabbatar da amincin manufofin kudi tare da rage tsammanin hauhawar farashin kayayyaki. Ko...
Aƙalla mutum biyar ne sun jikkata bayan da gobara ta tashi a gidan man Nobpet da ke kusa da mahaɗar Sojojin Sama a garin Fatakwal, Jihar Ribas. Gobarar ta kuma ƙone sama da motoci takwas da aka ajiye kusa da ofishin Hukumar Sufuri ta Jihar Ebonyi. Sojoji sun kashe ’yan bindiga da ƙwato shanun sata 1000 a Taraba Tinubu ya ƙaddamar da jirage 2, ya buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro Ma’aikatan kashe gobara na Jihar Ribas tare da haɗin gwiwar na Sojojin Sama ne suka yi aiki tare har suka iya kashe gobarar. Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Emmanuel Ninyaegwu, wanda direba motar haya ne, ya ce motarsa mai ɗaukar fasinja 18 ta ƙone gaba ɗaya. Ya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Jam’iyyar NNPP wadda Dakta Boniface Aniebonam ya kafa a shekarar 2001, ta samu ƙarfi sosai a Jihar Kano bayan tsohon Gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga cikinta a shekarar 2022 tare da mabiyansa na Kwankwasiyya. Shigowarsa ta farfaɗo da jam’iyyar, inda ta samu gagarumar nasara a zaɓen 2023 ta hanyar lashe kujerar gwamna da wasu kujerun majalisa. Sai dai rikicin cikin gida da na shugabanci sun dabaibaye jam’iyyar, wanda hakan ya haddasa ficewar wasu manyan ’ya’yanta zuwa APC, lamarin da ke haifar da tambaya kan makomar NNPP a Kano. Shin NNPP za ta kai labari a Kano, musamman bayan ficewar wasu jiga-jiganta? NAJERIYA A YAU: Kuskuren JAMB Da Ya Haddasa Faduwar Ɗalibai...
Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wata mata mai shekara 21 mai suna Fatima Salisu da ake zargi da safarar makamai, biyo bayan samun bayanan sirri. Kakakin rundunar ’yan sanda, Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis. Ganduje ya halarci Majalisar Wakilai don sheda ’Yan Majalisa 2 zuwa APC Sabon Hari: An kashe makiyayi da shanu sama da 100 a Filato Kakakin ya ce an kama Fatima ne da laifin safarar alburusai ta yankin Keana da Doma a cikin Jihar Nasarawa don taimakon masu aikata laifuka a Katsina, inda take zaune. “Cikin gaggawa kan bayanan sirri da aka samu, Kwamishinan ’yan sanda CP Shetima J. Mohammed, ya ba da umarnin tura sashin yaƙi da masu garkuwa da...
Amma sai yanzu gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwa a hukumance. Masana tattalin arziƙin sun bayyana cewa kammala biyan wannan bashi wata alama ce ta daidaituwar tsarin kuɗi na ƙasar da kuma yunƙurin rage dogaro da lamuni daga ƙasashen waje. Wasu sun ce hakan na iya ƙara jawo amincewar ƙasashen duniya da hukumomin ba da lamuni ga Nijeriya, musamman idan aka yi la’akari da ƙoƙarin da gwamnatin Bola Tinubu ke yi na farfaɗo da tattalin arziƙi. Wani ƙarin bayani daga ma’aikatar kuɗi ya ce an biya bashin ne a matakai daban-daban tun daga shekarar 2021, kuma an kammala biya a farkon shekarar 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Wani hari kan gidan yarin Al-Obeid yayi sanadiyyar mutuwa da jikkatan mutane da dama a kasar Sudan Ministan al’adu da yada labarai, kuma kakakin gwamnatin Sudan, Khaled Al-Aiser, ya tabbatar da cewa: Mutane 20 ne suka mutu, yayin da wasu 50 na daban suka jikkata a wani harin da ‘yan ta’addar Daglo na kungiyar Rapid Support Forces masu aikata laifuka suka kai hari kan gidan yarin Al-Obeid. Al-Aiser ya bayyana cewa: Harin da aka kai ya hada da asibitin birnin, inda ya yi sanadin mutuwar mutane musamman majinyata masu yawa tare da raunata wasu kimanin 50, wadanda dukkansu fararen hula ne, yana mai cewa wannan yana daga cikin manyan laifukan yaki. Ministan ya kara da cewa: “Abin da ya faru...
Ɗan majalisar jihar Kano mai wakiltar mazabar Sumaila, Hon. Zubairu Hamza Masu, ya bar jam’iyyar NNPP ya koma APC. A cikin wasiƙar murabus da ya aika wa shugaban majalisar, Hon. Ismail Falgore, Masu ya bayyana cewa rikice-rikice da shari’o’in cikin NNPP a matsayin dalilin ficewarsa. Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar 2027: PDP Ta Mutu, APC Na Shirin Sake Yin Nasara – Martanin Ganduje Ga Lamido Shugaban majalisar ya karanta wasiƙar a zaman majalisa na ranar Litinin, inda ya bayyana cewa Masu ya fice daga NNPP tun daga ranar 12 ga Mayu, 2025, kuma ya samu amincewa ga shugabannin APC a dukkan matakan da suka dace su karɓe shi. Ɗan majalisar ya...
Sai dai a cikin takardar murabus din, Edema ya bayyana rashin tsarin jam’iyyar a matsayin dalilin da ya sa ya fice daga jam’iyyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Bayan Cin Kamfanin META Tarar Dala Miliyan 220: Sun Yi Bazaranar Katse Kafofin Facebook, WhatsApp, Da Instagram A Nijeriya
BBC ta rawaito cewa, babban abin da ke damun kamfanin na Meta shi ne, yadda al’amarin ya shafi Hukumar Kare Bayanan Sirri ta Nijeriya (NDPC), wanda kamfanin ke zargin karya dokokin kare bayanan sirrin kasar. Baya ga tarar Hukumar FCCPC, hukumar ta NDPC ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 37.8, bisa zargin satar bayanan sirri, yayin da hukumar kula da tallace-tallace (ARCON) ta fitar da wani hukuncin daban na dala miliyan 37.5, kan abin da ta kira da cewa, tallan da ba a ba da damar aiwatar da shi ba. Daga cikin ka’idojin da ake da su, akwai bukatar kamfanin na Meta ya samu izini kafin tura bayanan ‘yan Nijeriya zuwa kasashen waje, yanayin da kamfanin ke ganin “ba...
Farfesa Bamaiyi ya bayyana ainihin aikin IAR a matsayin habaka nau’ikan dimbin amfanin gona da kuma jure fari wadanda suka dace da bukatun noma a Nijeriya. Ya bayyana masarar TELA a matsayin wata sabon salo da kirkira ta zamani a kimiyyance domin magance matsalolin da ake ci gaba da addabar amfanin gona, kamar kwari da canjin yanayi. Aikin “Masarar TELA bai takaita kan inganci da wadatar abinci ba, har ma tana ba da kariya ga rayuwar manoma, da inganta noman da kuma magance ainihin illar da tsutsotsi ke haifarwa, gami da juriya a yayin fari,” in ji shi. Shi ma da yake jawabi a yayin ziyarar, Farfesa Muyideen Oyekunle, wani masani a fannin tsirrai kuma daya daga cikin jagorori masu...
Ƙungiyar Allied Group of Nasarawa Professionals (AGNP), wadda ta ƙunshi ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu, ta goyi bayan tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu, wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a 2027. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ofishinta da ke Keffi, AGNP ta ce matakin da Adamu ya ɗauka na tsayawa takara ya sanya al’ummar jihar cikin farin ciki. ’Yan sanda sun kama harsasai 500 a Filato Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum “Wannan lokaci ne na kyawawan fata ga jiharmu,” in ji ƙungiyar. Ƙungiyar ta yi alƙawarin tattara ƙuri’u aƙalla miliyan daya domin mara wa Adamu baya a zaɓen. AGNP ta yaba...
Hukumar kare hakokin masu sayayya ta ta kasa tare da haka da Hukumar Kare Data ta kasa NDPC ne, suka gudanar da binciken na watanni 38. A cikin binciken na su, sun bayyana yadda ake take saba ka’ida tare da take dokar kasa da kuma take hakkin ‘yan Adama na kasa da kasa. Wannan Jaridar na da ra’ayin cewa, ‘yayan Kotun uku da Mai Shari’a Alkalan Kotun Thomas Okosun da ya yanke wannan hukunci, sun canci yabo kan tsaywar da suka yi kai da Fata na yanke wannan hukuncin, duk da matsin lambar da suka fuskanta, inda suka tabbatar da ikon da Hukumomin FCCPC da NDPC suke da shi. Kazalika, abinda ya kara nuna mahimmancin hukuncin Kotun,...
Burin Arsenal na lashe gasar UEFA a karon farko a tarihinta ba zai cika a wannan shekarar ba, sakamakon rashin nasarar da ta yi a hannun PSG a wasan zagayen na kusa da na karshe, Arsenal ta buga wasan karshe a UEFA sau daya a shekarar 2006 tsakaninta da Barcelona. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani rahoto na musamman da HKI ta gudanar akan asarar da ta fuskanta sanadiyyar yaki da Hizbullah, ya bayyana cewa, a fagen aikin gona kawai sun yi asarar dalar Amurka miliyan 108 wacce ta fara daga 8 ga watan Oktoba 2023. Kungiyar ReGrow Israel” ta ce, yakin da aka yi da Hizbullah ya yi barna gagaruma a fagen aikin gona da asarar da ta kai ta dala miliyan 108 a kan iyaka da Lebanon. Nazarin wannan kungiyar ya kuma kara da cewa; Tun daga ranar 8 ga watan Oktoba 2023 har zuwa lokacin tsagaita wutar yaki a karshen 2024, hare-haren Hizbullah sun lalata muhimmacin cibiyoyi a “Isra’ila” da kuma haddasa gobara mai girma, da hakan ya tilastawa mazaunan yankin, musamman...
Mamba a majalisar gudanarwa ta kungiyar Ansarulla ta kasar yemen Muhammad Bukhaiti ya bayyana cewa hare-haren da HKI da Amurka suka kai fararen hula a kasar yemen wuce jan layi, ko ketare haddi ne na kungiyar don haka su jira maida martani mai tsanani. Kamfanin dillancin labaran Iran ya nakalti yana fadawa tsahar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lenamon a yau Talata. Ya kuma kara da cewa hare-haren da Amurka suke kaiwa ma’aikatu da wuraren fararen hula a kasar Yemen na baya-bayan nan duk sun nuna cewa an sami nasara a kansu. Albukhaiti ya kara da cewa sadaukarwa da mutanen kasar Yemen suke yi saboda Gaza, ba zai tsaya ba, sannan muna son fadawa kasashen Amurka da ingila da kuma...
Shugaban Ghana a wannan Litinin ɗin ya bayyana ɗaukar mataki kan ministoci da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa fiye da 40 da suka gaza bayyana kadarorin da suka mallaka. Wannan na zuwa ne a yayin da Shugaba John Mahama ke ci gaba da zage dantse wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar da ke yammacin Afirka. ’Yan bindiga sun kashe matar aure bayan karɓar N10m kuɗin fansa ’Yan fashi sun kashe matashi a Kano A yayin karɓar rantsuwar kama aiki a watan Janairun bana ne Shugaban Ghana ya sha alwashin yaƙi da rashawa domin fitar da ƙasar daga ƙangin matsalar tattalin arziki A watan Afrilun da ya gabata ne mahukunta suka gurfanar da wani babban jami’in tsaro...
Kotun duniya ta yi watsi da karar da Sudan ta kai Hadaddiyar Daular Larabawa tana mai zarginta da hannu a kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar wannan kasa. A yau Litinin ne kotun duniyar ta yi watsi da karar ta Sudan, tana mai wanke Hadaddiyar Daular Larabawa. Ita dai Sudan ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawar da cewa ta hada baki da dakarun kai daukin gaggaawa wajen yi wa mutanen yankin Darfur kisan kiyashi. A nata gefen Hadaddiyar Daular Larabawan ta ki amincewa da tuhumar da Sudan ta yi mata tana mai siffata ta da cewa; Farfaganda ce, kuma Sudan din ta yi hakan ne domin kawar da hankulan duniya daga kan laifukan da sojoji suke aikatawa.
Sojojin kasar Pakistan sun sanar da yin nasarar gwajin makamai mai linzami da ake harbawa daga kasa, wanda yake cin Zangon kilo mita 450. Sanarwar sojojin kasar ta Pakistan ya kunshi cewa; Sun yi gwajin ne dai domin tabbatar da zama cikin shiri na sojoji, da kuma tabbatar da ingancin aikin makamin. Gwajin makamin na sojojin Pakistan ya zo ne a daidai lokacin da ake zaman dar-dar a tsakaninta da kasar Indiya, bayan wani harin ta’addanci da aka kai a yankin Kashmir. A ranar 22 ga watan Afrilu ne dai aka kai wani hari akan masu yawon bude ido a yankin na Kashmir wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane 26. Da akwai fargabar cewar kasashen biyu za su tsunduma cikin...
Ya ci gaba da cewa, tuni aka fara gudanar da wasu manyan ayyukan a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, musamman a ta Lekki da ta Tin Can Island. Shugaban ya bayyana cewa, an kuma samar da kafar sadarwa ta zamani ga masu ruwa da tsaki a daukacin Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, domin a rinka yin musayar Data, har da lokacin da ya dace, a fara gudanar da aiki. Ya sanar da cewa, idan an kammala wannan aikin, za su kara taimaka wa wajen kara inganta ayyukan Hukumar, na tsawon sa’oi 24. Dantosho wanda Manajan Sashen Tashar da ke a jihar Legas Lawal Ibrahim ya wakilce shi a wajen taron ya bayyana cewa, Hukumar ta kuma yi hadaka da Rundunar Sojin Ruwa,...
Masana harkokin tsaro sun ja hankalin hukumomi su ɗauki matakan da suka dace bayan gobarar ma’ajiyar makamai a babban Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Sun bayyana damuwa game da mummunan abin da ke iya biyo baya ta fuskoki daban-daban, tare da bayar da shawarar matakan da ya kamata a ɗauka domin daƙile ayyukan miyagu da ke iya ƙoƙarin cin gajiyar yanayin a matsayin wata dama ta aikata mugun laifi ko ta’addanci. Damuwar ƙwararru kan ƙarsashi da karfin sojoji Wani ƙwararre kan harkokin tsaro, Kabiru Adamu, ya ce illar wannan lamari ta wuce ɓarnar zahiri da kuma yiwuwar asarar rayuka. Ya ce, “Lalacewar makamai, harsasai, da sauran muhimman kayan aikin soja a barikin babban asarar...
Masana harkokin tsaro sun ja hankalin hukumomi su ɗauki matakan da suka dace, lura da abin da ke iya biyo bayan gobarar ma’ajiyar makamai a babban Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Sun bayyana damuwa game da mummunan abin da ke iya biyo baya ta fuskoki daban-daban, tare da bayar da shawarar matakan da ya kamata a ɗauka domin daƙile ayyukan miyagu da ke iya ƙoƙarin cin gajiyar yanayin a matsayin wata dama ta aikata mugun laifi ko ta’addanci. Damuwar ƙwararru kan ƙarsashi da karfin sojoji Wani ƙwararre kan harkokin tsaro, Kabiru Adamu, ya ce illar wannan lamari ta wuce ɓarnar zahiri da kuma yiwuwar asarar rayuka. Ya ce, “Lalacewar makamai, harsasai, da sauran muhimman...

Sabon Tsarin Ci Gaba Na Sin Ya Kawo Sauyi Daga Samar Da Takalma Miliyan 100 Zuwa Kera Mattarar Bayanai Ta Microchip
Kamar yadda firaministan kasar Malaysia Anwar bin Ibrahim ya fada a kwanan baya cewa, yayin da kasa da kasa ke fuskantar mawuyacin hali, suna bukatar samun tabbaci da wani nagartaccen shiri na samun ci gaba. Don haka, ana ganin yadda kasar Sin ta samu nasarori, an nuna yabo ga kasar ta Sin, kasar Sin ta kawo tabbaci da kuma kyakkyawar makoma ga duniya. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kimanin Naira biliyan ɗaya ce aka ƙiyasta ta salwanta sakamakon gobarar da ta ƙone wani sashe na babbar kasuwar da ke tsakiyar garin Jos, babbar birnin Jihar Filato. An rawaito cewar gobarar ta laƙume shaguna fiye da ɗari biyar, galibinsu na masu sayar da kayan gwanjo. Mutane da dama dai sun rasa hanyar cin abincinsu, kasancewar galibinsu sun dogara ne da samun da suke yi a kullum a wannan kasuwa don ciyar da iyalansu. Ko a wane hali waɗanda suka tafka wannan asara suke ciki bayan wannan ibtila’i? NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya Wannan na...

Masifar Gobara Tana Kara Bunkasa A Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tare Da Fara Raba Yahudawa Da Muhallinsu
Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi. Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar. Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa,...
A ranar Laraba ne jami’an sojojin ruwa na Najeriya da ke Fatakwal suka ceto fasinjoji 99 daga wani hatsarin kwale-kwale da ya rutsa da su a kogin Bukuma da ke ƙaramar hukumar Degema a Jihar Ribas. Jirgin ruwan, wanda yake na jigilar fasinja yana kan hanyarsa ta daga Fatakwal zuwa Ƙaramar hukumar Akuku-Toru, inda ya yi karo da wani jirgin ruwa a tsakiyar kogin. Gobara ta lalata shagunan kasuwar waya a Kwara Dalilin da ya sa aka samu fashewar abubuwa a barikin Maiduguri – Sojoji Jami’ar yaɗa labarai na sansanin, Laftanar Kwamanda Bridget Bebia, a wata sanarwa da ta fitar a Fatakwal, ta ruwaito Kwamandan sojojin masu aikin bincike, Commodore Cajethan Aniaku, ya tabbatar da faruwar lamarin. A cewar Aniaku,...
Haka kuma ya nemi kotu da ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kuɗi na Naira 200, 500 da kuma 1000. Baya ga haka, ya buƙaci a umarci su da su nemi gafara ta hanyar wallafa bayani a manyan jaridu biyu na ƙasa. Amma a zaman kotu na ranar Litinin, wanda ya shigar da ƙarar da lauyansa ba su halarci zaman kotu ba. Lauyan da ke kare Emefiele da CBN, Mista Chikelue Amasiani, ya sanar da kotu cewa tun da aka shigar da ƙarar, mai ƙarar da lauyansa ba su nuna wata alama ta son ci gaba da shari’ar ba. Ya roƙi kotun da ta kori ƙarar. Mai shari’a Ekwo ya amince da buƙatar kuma ya...
Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa kuskure ne abin da jami’anta ke yi na cin zarafi da cin zalin fararen hula saboda sun sanya kayan sojoji. Shugaban Sashen Hulɗar Sojoji da Fararen Hula na rundunar, Manjo-Janar Gold Chibuisi, bayyana cewa rundunar tana hukunta duk jami’inta da aka kama da laifin cin zalin farar hula saboda sanya kayan sojoji. Ya ce duk da haka doka ta haramta wa fararen hula sanya kayan sojoji ba bisa ka’ida ba, kuma laifi ne da zai iya kai su gidan yarin. Manjo-Janar Gold Chibuisi, ya ci gaba da cewa doka ba ta ba ta ba sojoji ikon hukuntawa balantana cin zalin masu aikata hakan ba. Sai kuma ta ba su ikon kama masu sojan gona...
Ministan harkokin cikin gidan Iran Askandar Mumini wanda ya kai Ziyara zuwa wurin da gobarar ta tashi ya sanar da cewa adadin wadanda su ka jikkata sun kai 750 da kuma wadanda su ka rasa rayukansu zuwa 14. Sai dai kuma daga baya ma’aikatar shari’a ta kasar Iran din ta ta sanar da karuwar wadanda su ka kwanta dama zuwa 21 Mai shigar da kara na gundumar Hurzumgan, Mujtaba Kahraman ya sanar da cewa; Daya daga cikin aikin da suke yi shi ne tantance wadanda su ka su ka rasa rayukansu. Haka nan kuma ya kara da cewa; Ya zuwa yanzu sun tabbatar da mutuwar mutane 21. Har ila yau ya bayyana cewa bayan tantance gawawwakin wadanda su ka rasa...
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya EFCC, ta ayyana neman wasu jami’an CBEX waɗanda take zargi da hannu a damfarar ’yan kasar miliyoyin kuɗaɗe a wani tsarin zuba kuɗi. Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafinta ranar Juma’a. An gano tsohuwar da ake nema a cikin maciji A soma laluben watan Zhul Qi’da — Sarkin Musulmi Sanarwar ta ambato EFCCn tana zargin mutanen takwas da yaudarar jama’a su zuba kuɗi don samun riba – daga bisani suka tsere da kuɗaɗensu. Hukumar ta bayyana sunayen mutanen da Seyi Oloyede da Emmanuel Uko da Adefowora Oluwanisola da Adefowora Abiodun Olaonipekun. Sauran sun waɗanda ta ce ’yan ƙasashen waje ne sun haɗa da Johnson Otieno...
Koton tsarin Mulki ta kasar Gabon din ta tabbatar da nasarar da Brice Clotaire aOligui Nguema a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi. Sakamakon zaben dai ya nuna cewa Nguema ya sami kaso 94.85.% da hakan ya mayar da shi akan gaba a tsakanin dukkanin ‘yan takara. Nguema dai tsohon janar ne wanda ya yi juyin Mulki a cikin watan Ogusta na 2023 da ya kifar da gwamnatin Ali Bongo Odnimba. Magoya bayan Nguema sun yi bikin hukuncin da kotun ta yanke na samun nasarsa. Zaben ya kawo karshen matakin rikon kwarya bayan kifar da gwamnatin iyalan Bongo da su ka yi kusan rabin karni akan karagar Mulki. Zababben shugaban kasar ta Gabon ya yi alkawalin...
Ya koka kan halin da kasar ke ciki, kuma ya bukaci ‘yan arewa da su yi taka-tsantsan da ‘yan siyasa masu rarraba kawunan mutane da yaudara, gabanin babban zabe mai zuwa. “Muna son gwamnati da za ta fahimci matsalolinmu kuma ta magance su. Bayan shekaru takwas na mulkin Muhammadu Buhari, mun dauki darasi. ”Yanzu haka muna cikin wata gwamnati, kuma har yanzu muna kuka. Kuka kadai ne muka san yadda za mu yi?” Baba-Ahmed ya tambaya. Baba-Ahmed ya ce arewa ta sha wahala sosai a lokacin Boko Haram, wanda ya shafi dukkan kungiyoyi, ciki har da Musulmi da Kiristoci da Fulani da Baju, da sauransu, yana mai jaddada bukatar hadin kai. “Kafin Buhari ya zama shugaban...
Sabbin ‘yan sama-jannatin da aka tura, za su gudanar da gwaje-gwaje da bincike game da yanayin rayuwa a sararin samaniya, da kimiyyar karamar fizgar kasa ko jazibiyya (micro-gravity physics) da sabbin fasahohin sararin samaniya. Kazalika, za su kuma yi tafiye-tafiye mabambanta a sararin samaniya don kakkafa shingayen kariya daga baraguzai da tarkacen sararin samaniya, da kuma girkewa da dawo da na’urorin da aka makala a wajen tashar. Ya zuwa yanzu dai, ‘yan sama jannatin kasar Sin 26 ne suka yi nasarar zuwa sararin samaniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
Mutane 47 ne suka rasa rayukansu tare da jikkatan wasu da dama a harin da aka kai da jirgin sama kan birnin El-Fasher na kasar Sudan Runduna ta 6 da ke yankin El- Fasher ta sanar da mutuwar fararen hula 47 tare da jikkata wasu da dama sakamakon kazamin lugudan wuta da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka yi kan birnin El- Fasher, fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa. A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce: Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces na ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula, inda suka yi amfani da harsasai masu yawa a yayin da suka yi ruwan wuta a kan unguwannin birnin El-Fasher a...

Rohoton Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam Ya Tabbatar Da Tafka Manyan Laifukan Cin Zarafin Bil-Adama A Siriya
Wani rahoton kare hakkin bil adama ya tabbatar da aikata manyan laifuka a gabar tekun Siriya tare da yin kira da a kare fararen hula Kwamitin da ke bin diddigin kare hakkin bil adama a kasar Siriya karkashin jagorancin dan gwagwarmaya Haitham Al-Manna, ya fitar da wani cikakken rahoton take hakkin dan Adam mai shafuka 72 da ke kunshe da jerin munanan laifukan da aka yi wa fararen hula a gabar tekun Siriya, yana mai bayyana shi a matsayin “neman shafe wata al’ummar daga kan doron kasa a kan tubalin sabanin Mazhaba”. Rahoton wanda masu fafutuka 12 suka shirya, ya zo ne bayan kisan kiyashin da aka fara a ranar 6 ga Maris. Rahoton ya yi nuni da wani tsari...